Chapter 1 Reading Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat Arewa Novels

Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat

Author :  Hilfat Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 19

1 to 3K   out of 54.7K words

[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS

Writers Association

( WOW)

TURMIN DINYA

NA

FATIMA UMAR KAS

HILFAT

1/4/2026

(1)

Ruwan da suka sheƙa mata ne a jikinta ya sanya ta farkawa a gigice tana sauke wata wawuyar ajiyar zuciya. Take jikinta ya hau kakkarwa kamar mazari sakamakon ruwan na da azabar sanyi ga kuma muƙu-muƙun da ake yi, sai ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye sai dai ta ji ko gezau bata yi ba domin ko ɗan yatsanta ba za ta iya motsawa ba sakamakon ɗaurin huhun goron da ta sha jikin kujerar da take kai, ta hau kici-kici amma a banza man kare. Sai lokacin ne ta shiga ƙarewa inda take kallo, kafin idanunta suka sauka a kan basamudan mutanen da suke tsaye ƙiƙam a kanta sun zubo mata maganansu, dukkan su sun murtuƙe fuska tamkar magribar ɗinya babu alamun ɗigon imani a tattare da su.

Sai lokacin ƙwaƙwalwarta ta shiga dawo mata da dalilin wanzuwarta a wurin daki-daki. Ta runtse idanunta da ƙarfi. 'Tabbas na san dama a rina an saci zanin mahaukaciya, amma alƙawari ne na ɗauka wa kaina kuma duk wuya duk rintsi na yi zaman turmin dinya a bisa bigiren da aka dasa shi kan cimma abin da na saka a gaba koda za a daddatsa naman jikina' Ta raya a ran ta.

Fincike baƙin gam ɗin da yake liƙe a bakinta da aka yi shi ya dawo da ita daga taƙaitaccen tunanin da ta tafi. Ta yi 'yar ƙarar azaba domin ba a yi mata a hankali ba. "Ki gaggauta ba mu duk wasu bayanai da shaidu da kika tattara idan ba haka ba sai na lahira ya fi ki jin daɗi." Cewar babbansu, babu alamun wasa a fuskarsa, ta masa wani irin kallo kafin ta buɗi baki ta ce "Ban gane a kan me kake magana ba."

Bai tanka mata ba ya kalli na kusa da shi. Bata yi aune ba sai ji ta yi ya damƙi gashin kainta kafin ya sa ƙarfi ya fara dukan bakinta. Azaba ta sanya ta rintse ido ta fara ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa, ji take yi kamar ba a duniyar take ba. Shi kam bakin nata kamar ba a jikinta yake ba haka take ji. Take jiri ya fara kwasarta, jini kuwa tuni ya gama wanke mata gaban doguwar riga ruwan madara da take jikinta.

"Har yanzu ba ki fahimci me nake magana a kai ba ko? Wannan ba iya tunaninki ba ne, ke da su waye ke shirin tono sirrin da muka ɗauki lokaci muna binnewa a doron ƙasa? Ina mai tabbatar miki za ki yi dana sani mai girma, domin allura ce za ta tono garma, wuƙa ce kike shirin daɓa wa kanki da kan ki, da ma kaza garin tone-tone take tono wuƙar yanka ta."

Numfashinta na fita da ƙyar ta fara ƙoƙarin magana "Ko za ku kashe ni ba zan taɓa ba ku bayanan da na ɗau lokaci mai tsayi ina ƙoƙarin haɗawa ba, domin ni ba raguwa ba ce ballantana barazanarku ta tsorata ni, kuma ni kaɗai nake gudanar da aikina ba tare da taimakon kowa ba, aikina na saida rai ne na yarda na mutu ko na rayu domin kawo ƙarshen matsalar da ta addabi al'ummar ƙasata."

"Hahhhhh ba ki daku ba ne, idan kin ji wahala ai za ki magantu." Ya kuma faɗa, ba ta san ya iso gabanta ba sai ji ta yi an ɗaga fuskarta kafin aka buɗe bakinta ta ƙarfi, wani irin ƙarfe ne a hannunsa ya zura cikin bakinta sai ji ta yi yana ƙoƙarin cizgo mata haƙori, tun daga jijiyar idonta zuwa kanta ne ya amsa take jikinta ya ɗau karkarwa, jin fincike mata haƙori daga bakinta ya yi silar ɗaukewar jinta da ganinta, daga nan ba ta kuma sanin a duniyar da take ciki ba.

*** *** ***

Zaune take ta barbaza takaddu a gabanta tana bin su ɗaya bayan ɗaya tana dubawa. Littafin da take rubutu ta janyo ta haɗa da wata takadda sannan ta fara tattare takaddun. Kwashe su ta yi zuwa inda ta ciro su sannan ta mayar da hankali tana kwafar rubutu daga jikin takaddar zuwa cikin littafin.

Jin motsin shigowa ya sanya ta kai kallonta bakin ƙofar. Sai ta miƙe da sauri bayan ta ajiye abubuwan hannunta ta nufe shi, tana zuwa ta rungume shi cike da jin daɗin ganin shi. "Barka da dawowa daddyna"

Shi ma murmushin ya saki yana dafa kanta kafin ya ce "Yawwa maman daddy ana nan ana ta fama ko?"

Ya ƙarasa yana murmushi, itama murmushin ta yi ba ta ce komai ba.

"To Allah ya taimaka"

"Amin daddyna"

Ina Mamyn naki ban ji ɗuriyarta ba" Ya ce yana leƙen fuskarta, sakin shi ta yi ta juya ta kalli bayanta, kafin ta nuna masa ita da hannu, shi ma wurin ya kalla sai kuwa karaf suka haɗa ido da ita tsaye a ƙafar bene ta biyun ƙarshe ta harɗe hannunwanta a ƙirji tana murmushi itama.

"Au yo ai ni ko motsin sakkowarki ban ji ba, balle na gan ki" Ya faɗa yana ƙarasa wa cikin falon ya tallaɓo ta a jikin shi. Itama ta ƙarasa sakkowa ta zauna tana faɗin "Yo ai kai Alhaji indai kana tare da Nuratu baka ji ba ka gani."

Murmushi ya yi kafin ya ce "To kin ga laifina Iyami? Uwar masu gida take fa, ko ba haka ba mamana?" Sunkuyar da kai kawai ta yi tana cigaba da murmushin.

"Alhaji abincin ne ko wankan?" Hajiya Iyami ta tambaya fuskarta a kan shi. "A'a wankan dai, idan na yi sai mu ci abincin. Ina yaron nan ne Nura ko bai shigo ba?" Cewar Alhajin. "Bai shigo ba tukunna duk inda yake dai yana hanya yanzu tunda magriba ta yi." Ta ba shi amsa, bai kuma magana ba ya miƙe ya haura saman, ita ma ta rufa masa baya. Nuratun kuma ta koma kan aikin da take yi kamar daga sama ta jiyo maganarsa yana nufo falon yana waƙa "Ke kika san kisisinar da za ki yi wa saurayi ko angon ki in ya biɗo komai ya ba ki warrrr. (Baitin waƙar ado gwanja ta warrr)"

"To fa Allah ya masa dawowa yanzu zai zo ya takura mini" Ta faɗa a fili, daidai lokacin ya ƙarasa shigowa falon yana tafiya yana kwarkwasa "Me kike cewa ne?" Ya faɗa yana riƙe ƙugu. Matashi ne da a ƙalla zai kai shekaru ashirin da bakwai. Dogo ne mara jiki, fuskar nan tashi ya ci mai har da ƙananun ƙuraje, kamarsu ɗaya da Nuratun. Jikinsa Jallabiyya ce fara, ya ɗaura kallabi a kan sa.

"Ni babu abin da na ce" Ta faɗa tana tura baki "Ƙarya kike yi kin yi magana kuma daga ji gulmata kika yi ai kin saba, kuma wallahi ki kiyaye ni kafin na yi ƙuli-ƙulin kubra da ke." Ya ƙarasa da tura ɗankwalin kansa gaban goshi, sai kuma ya yi gaba bayan ya sa ƙafa ya wargaza takaddun ya kuma bi ta kai ya shige ciki abinsa.

Cike da jim haushi ta bi shi da kallo ganin ya zauna a kujera "Ko za a saka mini duka ne?" Ya ƙarasa yana girgiza ƙafa, ba ta kuma bi ta kan sa ba ta fara tattara takaddun, tsaki ya ja kafin ya ƙara da "Aikin kenan ke kullum abu ɗaya ko gajiya ba kya yi daga wannan ki koma wannan, maza ki je ƙwaƙwalwarki ta tarwatse a aikin banza, kuma wallahi tsufa za ki yi da wuri kina tarawa kan ki aiki ato ni dai babu abin da ya shalle ni."

Duk cikin maganarsa ta ƴan daudu yake yi da ya dage ta ƙarfi sai ta koma maganar mata, yana yi yana tauna cingam gami da yin ƙwai da shi. Tana gama tattare takaddun ta nufi ɗakinta sai da ta shiga sannan ta ziro kai ta ce "Ai wallahi gara ni sau dubu a kan ka, Allah ya yo mutum a halittar maza sannan ya ce sai ya mayar da kan shi mace ta ƙarfi da yaji kaico, kuma ai ba a taɓa canjawa tuwo suna" Zabura ya yi ya nufo ta, ba shiri ta datse ƙofar.

"Ai da kin bari na iso wurin, wallahi ban ƙi na tuɓe mu dambatu ni da ke ba kuma ko a kwalar rigata."

"To Allah ya maka dawowa ko? Tun ɗazu nake jiyo maganarka sama-sama ai." In ji Hajiya Nuratu tana saukowa ƙasan, Alhajin na biye da ita a baya. Sosa kai ya hau yi, sai kuma ya yi farrr da ido "Ni da Nuratu ne rashon kunya take yi mini kuma wallahi ta ji gaba ni da ita ɗan halak ka fasa." Ya ƙarasa yana hararar ƙofar ɗakin nata bayan ya zungura baki gaba

"Ai kai ne ba ka jan girmanka wani lokaci, kai ke takalo ta." Cewar Daddyn yana nufar danning table ɗin. "Kirawo ta ta fito mu ci abinci" Ya kuma faɗa. "A'a daddy ni sai na yi wanka tukunna, ka gan ni yanzun nan na shigo gidan duk warin rana nake yi" yana maganar da yatsunsa guda biyu a haɗe yana girgiza su. Sai ya juya ya doshi ɗakinsa yana rangwaɗa. "Allah ka shirya mana." Cewar Mamyn. "Amin dai, kira ta a waya ta fito mu fara ci, don ba za mu jira shi ba" Daddy ya faɗa. "Aikam dai, don kuwa kafinya gama ƙalƙale-ƙalƙalen ya fito ma aiki ne, a kai awa guda." Mamyn ta faɗa tana ciro waya domin kiran Nuratun....!

Comment and share pls

[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*

_Writers Association_

*(WOW)*

*TURMIN DANYA*

*NA*

*FATIMA UMAR KAS*

_HILFAT_

(2)

Yana zaune kan wata kujera ya ɗaura kan shi saman kujerar, hannuwansa ma na kan saman kujerar, a lumshe idanunsa suke da za ka zaci bacci yake yi, sai ka lura da girgiza ƙafar da yake yi sannan za ka tabbatar idanunsa biyu. Ingarman namiji mai ƙirar sadaukanta, a ƙalla zai yi shekaru talatin da takwas. Yana da ɗan haske ba sosai ba, leɓensa baƙiƙirin a buɗe, sumar kan sa duk ta cukurkuɗe kamar sheƙar angulu.

Yaran da ke gabansa ne suka kuma gyara tsayuwa kawunansu a ƙasa, domin sun gaji da tsayawar ga shi ba su da damar tafiya sai lokacin da ya ga dama don kan shi, domin a kodayaushe umarninsa kawai suke bi.

A hankali ya buɗe idanun nasa da suka yi fici-fici kuma sun yi ja ya sauke akan su. Sai kuma ya buɗe kwalin sigari ya zari ɗaya ya kunnata ya fara zuƙa yana fesar da hayaƙin. Sai da ya yi mata zuƙa biyar sannan ya yar a ƙasa ya bi da ƙafarsa da wani ƙaton takalmi ke ɗaure jikinta ya murje sigarin. Kamar wanda baya son magana ya fara faɗin "Kuna nufin har yanzu ba su kawo kuɗin fansar yaran nan ba? Me suke jira ne? Ko an faɗa musu muna da lokacin ɓatawa ne?"

"Ai kawai sun raina mana hankali ne Gadanga, kawai a aika yaran barzahu a aika musu da gawarsu tunda hakan suka zaɓa." Cewar Goje yana wani ciccijewa irin ta riƙaƙƙun ƴan dama. "Ai ni da an bi ta tawa tun suna kwana uku za mu gama da su, tunda iyayen nada kuɗin fansar tasu amma kuɗin suka fi so akan rayukansu." Cewar mai yagi yana huci.

Shiru ya kuma yi kan shi a ƙasa, ya ɗau aƙalla minti goma kafin ya ɗago idanunsa a kan su ya ce "Ku ƙara basu lokaci daga nan zuwa gobe, a yau za mu matsa musu lamba har muryoyin yaran ku tura musu da su ku kuma jaddada musu za mu kashe su nan da gobe idan ba su biya kuɗin da muka yanka ba."

"An gama ƙusar yaƙi." Goje ya faɗa "Za ku iya tafiya," Ya ce kamar baya so ya koma yadda yake da farko ido lumshe yana girgiza ƙafa. Suna juyawa da niyyar fita wani matashi ya shigo ɗakin da sallama. Da ganin shi shi ma irin ƴan iskan unguwar nan ne, duba da shigarsa da kuma askin kansa, ga leɓensa da ya yi baƙiƙirin."

"Babba ina gaisuwa" Hannu kawai ya ɗaga masa alamun amsawa "Abokan harƙalla sannunku" Ya ce da su "Yawwa ɗan uwa, akwai wani labari ne?" Maiyagi ya ce da shi. "Zazzafan labari ma kuwa, domin wannan karon za a samu gwagwgwaɓar riba idan komai ya kammala cikin sa'a." "Yi gaggawar sanar da mu, kana iya zama" Goje ya faɗa. Sai da ya zauna sosai kafin ya fara faɗin. "Akwai wata yarinya da na samo muku, budurwa ce don baza ta haura shekara ashirin da biyar ba. Mahaifinta nada kuɗi sosai don an ce shi kan sa bai san nawa ya mallaka ba, sunansa Alhaji Tahir Mai nasara. A nan bayan layinmu suke, mahaifin yarinyar yana ƙaunarta sosai domin gata iya gata yana mata ba ta nemi komai ta rasa ba. Duk da tana da ɗanuwa su biyu ne ƴaƴan nasa amma idan aka yi amfani da ita za a fi tatsar shi yadda ya kamata. Yanzu haka yana gari komai sai ya fi tafiya daidai."

"Ina ne unguwar, ka ba mu cikakken adireshin." Cewar goje. "To kamar yadda na ce a bayan gidanmu ne, zan muku cikakken kwatance na tura muku kamar yaddaaka saba. Yarinyar ai tana zuwa aiki saboda ƴar jarida ce."

"Ƴar jarida?" Sai lokacin ya yi magana yana buɗe idonsa. "Eh tana aiki a wani gidan jarida kuma na san ranakun da take fita da lokacin da take dawowa. Sannan a shawarce idan kun tashi ku nemi manyan kuɗaɗe domin ina da tabbacin ko nawa kuka ce mahaifinta zai ba ku."

"Shike nan, aikinka na kyau ɗan uwa, ka je za mu yi magana, abu na gaba ka kuma lura sosai fa haɗi da takatsantsan matsayinka na informer ɗin mu kar ka bar wata ƙofa da za a gano ka."

"Ai ba zan taɓa bari a gano ni ba, ko ka manta inkiyar tawa? Dila fa ake ce mini, dila kuwa da wayo aka san shi, na bar ku lafiya, ina fata kasona ya zama na musamman ni ma." "Ba ka da matsala" "To godiya nake. Daga nan ya musu sallama ya fice.

Alhaji Ubale Lamiɗo na zaune a tanƙamemen ofishinsa yana cike wasu takaddu, mutum ne mai jiki da tsayi zai iya ba wa shekaru hamsin baya. Wayarsa ce ta fara ruri, kai kallonsa kan wayar ya yi, sai ya tsaida idanunsa akan wayar, ganin sunan da ke yawo jikin screen ɗin ne ya saka ya ajiye aikin da yake yi ya ɗauki wayar ya kanga ta a kunnensa. "Aliyu ya ake ciki?" Bayan ya ɗaga wayar. Ba a jin me ake cewa daga can ɓangaren sai ya kuma cewa "Ok to indai kayan aiki ne ba ku da matsala da su, za a kawo muku nan da kwana biyu, ku cigaba da lura. yawwa to" Daga nan ya kashe wayar.

Sai kuma ya lalubo wata lambar ya danna kira, ana ɗagawa ya ce "Kayan hannun yaran nan fa sun yi ƙasa, ya ake ciki da waɗanda aka shigo da su ɗin nan an samu wucewa kuwa?" Ya yi shiru yana jin me ake cewa, sai ya kuma faɗin "Yawwa ka ƙoƙarta don Allah ba na so a samu matsala, kuma kar sunana ya fito. To shike nan sai na jika." Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar ya cigaba da aikin da yake yi bayan ya gyara zaman glass ɗinsa.

Misalin ƙarfe huɗu na yamma ya fito daga ɗakin nasa bayan ya datse shi, cikin falon ya shiga, nan ya tarar da Hajiya Iyami a zaune tana waya, sai da ya jira ta gama kafin ya karkace kai "To Mamy Allah ya mana fitowa."

"To Nura Allah ya tsare, don Allah kar ka jima fa ka dawo da wuri."

"Ke ma dai Mamy da wani zance, ni fa na ce miki Allah ya sanya alkairi kawai zan yi na dawo, shi ma don kar ya ce ban je ba ne kuma na masa alƙawari shi kuwa kin san kaya ne."

"To na ji sarkin zuba, ka fara magana kamar kanyar da ba ta nuna ba." Yana shirin magana Nuratu ta yi sallama ta shigo falon, a kujera ta zube tana cire ɗankwalinta ta ajiye kan kujera "Sannu da gida Mamy" Tace a gajiye. "Yawwa Nuratu an dawo ya aikin."

"Alhamdulillah kin gan ni nan na dawo liƙis." Ta ƙarasa da lumshe ido

"Jiki duk gajiya" Suka tsinci muryarshi ya faɗa, sai kuma ya zuge jakar hannunsa ya cire hodar madubi, soson hodar ya ɗauka yana ƙara goge fuskarsa. "Yaya sai ina kuma?" Ta tambaya "Ina ruwanki, ni fa ba na son shishshigi da ƙwala kai a faranti."

"Allah ya ba ka haƙuri daga tambaya?"

"Riƙe haƙurin ki zai yi miki amfani watarana."

"Wai walima aka gayyace shi shi ne zai je?" Mamyn nasu ta bata amsa "Mamy da yamman nan?"

"Ina ruwan ki munafiuka?" Ya ce yana kai mata ranƙwashi mai kyau a ka da zoben hannunsa.

"Wayyo Allah kaina" Ta faɗa da ƙarfi tana dafe kan, tuni idanunta ya tara ƙwalla don sosai ranƙwashin ya

1 / 19