Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
sauri take yi ƙafafunta na harɗewa kamar za ta kifa. Tun daga nesa ta fara ɗaga masa hannu, kamar ya wuce sai kuma ya tsaya, yana shirin tambayarta inda ta nufa kawai ya ga ta faɗa ciki. "Ina za ki je ne?" Da hannu take masa alamar su tafi kawai, ya yi ɗan jim sai kuma ya ja suka tafi yana ayyana ko wasu ne suka biyo ta, amma yanayin ta ya fi kama da mara gaskiya.
Takadda ya ga ta miƙo masa, ya karɓa ya duba, sai ya ga wurin da zai kai ta ne ta rubuta ta miƙo masa. Ya ɗan waigo da niyyar tambayarta ba ta magana ne? Kawai sai ya ga ta buɗe wayarta ta ciro wani layi ta cillar, sannan ta mayar da wayar ta rufe tana cigaba da ɗan kalle-kalle duk zufa ta tsatstsafo a goshinta.
Daidai inda ta rubuta masa za ta sauka ya tsaya, fita ta yi sannan ta zuge jaka, ta zaro masa dubu ɗaya kawai sai bandir ɗin ƴan dubu-dubu ya faɗo a jakar, cikin rawar jiki ta duƙa ta ɗauko ta cusa a ciki wanda hakan ya ba shi damar hango wasu bandir ɗin kuɗaɗen da suke cikin jakar ya yin da ta duƙa. Zugewa ta yi ta miƙa masa dubun, yana shirin ɗauko mata canji kawai ya ga ta ɗaga masa hannu, sannan ta juya ta bar wurin da sauri.
Ya bi ta da kallon rashin yarda har ta shige wani gida sannan ya ja mashin ɗin ya tafi. Sai misalin shaɗaya ya tashi a aikin ya nufo gida. Bayan ya ajiye mashin ɗin a cikin wani wuri mai kama da kango ya miƙa wa wani dattjijo makullin. Zagayawa ya yi ya ɗauki wata leda, karaf idanunsa ya sauka kan layin waya a bakin ƙofar fita. Duƙawa ya yi ya ɗauka yana juya shi a hannunsa. Tabbas layin nan ne da ya ga budurwar nan ta jefar ashe bai faɗa waje ba sai ya maƙale a abin da ke shimfiɗe a ƙasan adaidaita ɗin, kasancewar a can ciki take sai ta jefo shi.
Gyaɗa kai ya yi sannan ya juya ya fice a kangon yana amsa sai da safen da dattijon ke yi masa. Yana isa gidan nashi ya saka makulli ya buɗe idanunsa akan wani ɗaki da ke rufe shi ma, sai kuma ya tura na jikinsa take ya gan su cikin wani yanayi sun yi ɗaiɗai suna bacci alamun a buge suke sun yi mankas, mayar da ƙofar yadda take ya yi ya juya ya tura wanda ke kallon nasun ya shige.
A bakin katifa ya zauna sannan ya buɗe ledar dake hannunsa. Takeaway ne na abinci sai ruwa da lemo. Ci ya yi ya ƙoshi sannan ya kwanta bayan ya yi wa layin ajiya ta musamman.
"To Alhaji ko ƴan sandan za a faɗa wa halin da ake ciki?" Cewar Mamy bayan ta sauke tagumin da ta yi. "Kar ki fara wannan kuskuren idan ba so kike mu rasa ta ba, ki bari mu lallaɓa mu karɓo ta kawai, ba kuɗi kawai suke so ba? za mu ba su ai. Sanarwa ƴan sanda daidai yake da siya mata tikitin tozarta a hannunsu."
"Amma Alhaji kuɗin fa da yawa, ina ka ga wannan kuɗin? Miliyan ɗari fa ba dubu ɗari ba ce?" Ya yi murmushi "Kar ki damu za a lalubo, idan sun kuma kira za mu nemi ragi ai."
"Oh ni Iyami wai ake cinikin mutum kamar ana cinikin dabba, Allah ka mana maganin wannan rashin tsaro da ya addabe mu a ƙasar nan albarkacin Annabi Muhammad S.A.W."
"Amin dai" Ya amsa yana miƙewa ya fice zuwa masallaci ya yin da itama ta nufi ɗakin tana jan ƙafa domin yin sallahr.
Tun da taga duhu ya fara tsoro ya fara shigarta. Jin an buɗe ƙofar ya saka ta saki ajiyar zuciya, amma sai ta ga an ziro mata abu an mayar da ƙofar an rufe da ƙwaɗon.
Ta san ba zai wuce abinci ba shiyasa ko motsawa ba ta yi ba. So take yi ta yi sallahr magriba amma babu ruwa. Tunawa ta yi a ɗazun ta hangi wata ƙofa a zaton ta uwar ɗaki ce, sai kawai ta miƙe tana bin hanyar cikin duhun Allah ya taimake ta ta ji ta taɓa ƙofar. Tura ta ta yi ta shige tana cigaba da lalube kawai sai ta ci karo da abu, taɓa wa ta yi sai ta ji ashe masai ce ta tangaran. Sai lokacin ta fahimci banɗaki ne ashe. Jikin bango ta dinga laluba cikin sa'a ta ji ta taɓa famfo.
Kawai ta murɗa cike da fatan ya kasance da ruwa, aikam shaaaa ruwa ya hau zuba. A haka ta yi tsarki ta ɗauro alwala ta fito.
Anan ta kuma yin sallahr kamar ɗazun, cikinta ƙugin yunwa yake yi amma ta kasa cin abincin da suka kawo mata har sau biyu. Jingina ta yi a bango tana tunanin ko za ta kuɓuta daga hannunsu? Domin ita dai ta san ba ta yadda za a yi daddynsu ya iya biyan rabin kuɗin nan ma da suka ce balle duka, kasancewar a gabanta ogan nasu ya yi waya da su.
Kukan da sauraye ke mata a kunne ya dawo da ita tunaninta. Yuuuu haka suka dinga binta, tun tana bige su har ta haƙura ta haɗe kai da gwiwa, tana ji suna ta cizonta. Ta san har da baƙar rigar da ke jikinta yasa suka takura mata.
Can dai ta gaji ta saka kukan takaici lokacin da ta tuno lafiyayyen gadonta na can ita na nan sauraye na watandar ta.
A hankali yake jin kamar sheshsheƙar kuka. Har ya share sai kuma ya miƙe ya fito, kai tsaye ɗakin nata ya nufa. Ilai ilailan lemo kuwa daga ɗakin ne kukan ke fitowa "Ke lafiya za ki hana mutane bacci, kukan uban me kike yi?" Ya ce a kausashe bayan ya matsa jikin ƙofar "Sauro" Ta faɗa cikin dasashshiyar murya da ta ci kuka ta ƙoshi, tsaki ya ja ya juya ya koma ɗakinsa. wata ƙaramar Fitila ya ɗauko da makullin ɗakin ya dawo ya buɗe, jefa mata fitilar ya yi ya mayar da ƙofar ya rufe. Tana jin abu ya bugi ƙafarta ta juyo. Ɗaukar fitilar ta yi tana haska ɗakin cike da tsoro. Da ɗan sauƙi-sauƙi kibiya a ido domin hasken ya ɗan rage saurayen.
Haka ta kwana ƙirga daƙiƙu domin yadda ta ga rana haka ta ga dare. Duk iya sata irin ta bacci kyale ta ya yi ya ƙara gaba. Gabaɗaya tunanin halin da iyayenta ke ciki take yi har da ma ɗan uwanta da ƙawarta ga kuma mutumin nata da ya mace a kan ta.
Barister Sahabi sam ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa da rashin samun masoyiyar tasa a waya. Hakan bai taɓa faruwa ba, dalili kenan da ya sa ya fara shirin zuwa gidan ya gano ko lafiya? Isar shi kuma ya tarar da mummunan labari na ɓatan ta, sai dai shi ma sun ɓoye masa batun ƴan garkuwa ɗin da suka kira waya. Shi ma ta ɓangaren sa ƴan sandan ya sanarwa.
Kuma shi abin da ya fi tunani magauta suka ɗauke ta ta yiwu akwai wanda taɓa haɗa wani rahoto akan sa musamman ƴan siyasa shi ne ya saka aka ɗauke ta. A ƙarshe dai ya samu kan shi da fatan Ubangiji ya tsare musu ita daga dukkan sharrin abin ƙi. Shi ma dai a ranar baccinsa rabi da rabi ne kamar yadda su Mamyn suka gagara baccin su ma, don kuwa ba ƙaramin so yake yi mata ba.....
NEXT
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOW
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(9)
"Masu sauraronmu a halin yanzu muna yi muku sallama irin ta addinin musulinci. Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Sannunku da jimirin bibiyarmu a cikin wannan shiri namu na TSUMAGIYA da masu iya magana kan ce fyaɗe yaro ta fyaɗe babba. Domin a cikin shirin mukan zaƙulo manya musamman masu ruwa da tsaki akan wasu harkoki da suka shafi al'umma da ma ƙasa bakiɗaya mu tattauna da su. Kuma a yau cikin ikon Allah mun kamo mari babban kifi wato Alhaji Badamasi Ajingi. Wanda na san dayawanku kun san shi tunda ba ɓoyayye ba ne ba.
A yanzu kuma za mu shiga cikin tattaunawar tamu gadan-gadan, tare da ni Zaitun Abdussalam Bawa. Yallaɓai za mu so mu ji wacce matsaya kuke kai game da rashin tsaro da ake fama da shi har yanzu?"
Ya gyara zamansa akan kujerar falon nasa kasancewar tattaunawar har gida aka same shi bayan ya bada mintina ashirin kacal. Ya ce "To game da matsalar tsaro dai muna nan muna yi iya yin mu, kuma a hakan alhamdulillah za a ce don yanzu a cikin kaso ɗari saura kaso arba'in za a ce mun ci ƙarfin aikin."
"Ma sha Allahu. Yallaɓai za a iya cewa abin ya canja salo yanzu kamar ana yin kwangaba kwan baya. Sai ana ganin kamar komai ya kusa zuwa ƙarshe sai kuma katsam a ji an ce yau an kwashe ɗaliban makaranta an yi garkuwa da su, gobe an kwashi wasu a hanyar su ta tafiye tafiye zuwa ga neman abin da za su sauke nauyin iyalansu. Abin har ya kai yanzu a cikin unguwa ake ɗebe mutane a nemi kuɗin fansa, me za ka iya cewa game da wannan."
Ya ɗan ƙura mata ido yana nazarinta kafin ya ce "Zan iya cewa muna tufka ne ana warware mana ita. Domin duk ƙoƙarin mu idan ya kasance akwai masu son ganin bayanmu a gefe da za su dinga rushe mana aiki ai muna aikin baban gwiwa ne. Kuma ai da ɗan gari akan ci gari, informers sun yi yawa yanzu cikin unguwanni da ake haɗa kai da su a ɗauki mutum.
Jamian mu na ƙoƙari, haka sojojin da ake turawa cikin dajika domin su ba wa gari tsaro su ma ana bin su ana yi musu kisan gilla. Inda kuma muke ganin cigaban shi ne ana samun sauƙi sosai fiye da baya. Don haka muna fatan al'umma za su cigaba da taya mu da addu'a game da wannan al'amari da yake ci mana tuwo a ƙwarya, da sannu komai zai zama tarihi."
Cikin rawar murya ya ƙarasa maganar kamar mai shirin fashewa da kuka. Hakan ne ya karya mata zuciya itama. "To masu saurarenmu da haka wannan shiri namu na yau ya zo ƙarshe, da fatan kun samu ƙwarin gwiya ta cikin kalaman ƴallabai. A ƙarshe kuma ina roƙon da ku taya mu da addu'a domin abokiyar aikin tawa da muke gabatar da shirin tare wato Nuratu Tahir mainasara yau kwana biyu kenan ba a san inda take ba. Muna fatan duk inda take ta kasance cikin ƙoshin lafiya, da kariyar ubangiji a nan nake cewa assalamu alaikum, mu huta lafiya"
Iya nan firar ta ƙarƙare, wannan kam ya jawo cecekuce domin da yawa sun kaɗu da jin labarin ɓatan, kasancewarta ƴar jarida mai farinjini, wasu kan ce ɗauke ta aka yi don wata manufa yayin da wasu ke cewa ɓarayi suka sace ta.
Koyaushe cikin shirin jiran wani kiran nasu suke yi amma shiru. Yanzun ma suna zaune sun yi jigum-jigum, fitar wasu jami'ai guda biyu kenan ba jimawa, da suka zo saboda jin ko an samu wata madafa daga nan ɗin amma daddyn yace musu shiru ne. Sun rabu kan za su je su cigaba da nasu binciken.
"Oh ni ƴar nan wannan rayuwa, a ɗauke mutum sukutum da guda shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu, mu dai kam Allah ya isa tsakaninmu da waɗannan azzalumai macuta mahainta waɗanda iyayrnsu suka ce je ku kwa gani." Nura (ƴar dubai) ya faɗa cikin takaici yana watsa hannu. Babu wanda ya tanka masa daga Mamyn har Daddyn saboda su kaɗai suka san halin zullumin da suke ciki. Koyaushe cikin fargaba suke da kuma tarin damuwa ko ishashshen bacci ba sa samu tsawon kwana biyun nan, abinci ma ba ya taɓuwa.
Suna murna sun ji inda take amma ga murnar na niyyar komawa ciki tunda ba su kuma kira ba balle su ji ta yadda za su karɓi ɗiyarsu.
Miƙewa Nuran ya yi ya doshi ƙofa "To ni bari na fita wannan lamari ai ba na zama ba ne, gara na ɗan cigita na kuma faɗawa ƴan uwana ko addu'a a taya mu.
Kamar jiran fitarsa ake yi wayar daddyn ta hau ruri, cikin rawar jiki ya ɗaga, tun kafin ya yi sallama aka ce. "Dama mun jira ne mu ga ko za ku yi taurin kai wurin sanarwa ƴan sanda to amma mun ga ba ku yi hakan ba, don haka ku shirya gobe ku kawo mana kuɗin ku karɓe ta, idan ya wuce gobe sai dai a yi wani zancen ba wannan ba, domin mu kashe mutum mu jefa wa kura gawarsa ta yagalgala ba babban aiki ba ne a wurinmu."
Aka ce cikin wata kausasshiyar murya. Cikin rawar baki Daddy ya ce "Don Allah ku taimala ku rage mana kuɗin ba mu da kuɗi masu yawa haka?"
"Kai ka rufe mana baki anan, mu za ka faɗa wa ba ka da wannan kuɗin? To ka sani a tafin hannunmu kake babu abin da ba mu sani ba game da uwar dukiyar da ka tara, don kuwa wannan kuɗin da muka karɓa tamkar an tsoma allura a cikin mai an cire ta ne ba ta inda arziƙinka zai taɓu.Amma shikenan mun fahimci wani abu ɗaya ka fi son kuɗinka da yarinyarka da ma duk cika baki ne ashe, to goben ka zo daidai inda za mu tura maka ka ɗau wulaƙantacciyar gawart...."
"A'a kar mu yi haka da kai, zan bayar, wallahi zan bayar ko nawa ne, don Allah kar ku mata komai. Ina za mu kawo kuɗin yanzu?" Daddyn ya tare shi da sauri jin zai kashe wayar. Wata shegiyar dariya ya sheƙe da ita kafin ya ce "Zan turo maka adireshin inda za ka je gobe, ka tabbata ƙarfe shidan safe ta maka a wurin. Za ka ajiye jakar ka koma gefe za mu ɗauka mu duba, idan sun cika cifff sai mu sako maka ƴarka."
Daga haka ya ji kitttt an kashe wayar. Daddy ya bi wayar da kallo yana sharce gumi "Ya kuka yi da su Alhaji?" Ta ce da sauri "Sun ce gobe na kai kuɗin inda za su faɗa mini sai na taho da da ita."
"Har sai gobe ba ma yau ba? Ni fa hankalina ya kasa kwanciya da yarinyar nan hannun ƙatti, ga shi har yanzu ba mu ji muryarta ba."
"Babu abin da ya same ta in sha Allahu, kawai mu bar wa goben kamar yadda suka ce, zan yi ƙoƙarin haɗa musu kuɗin yau ko da rance ne."
"To Alhaji Allah ya ɗora mu a kan su."
"Amin dai."
Yana fita bai zame koina ba sai gidan Momyn tasu wato Ramatu dillaliya da suke kira momy saboda ɗaure musu gaban da take yi. Wuri ya samu ya zauna ya yi jigum haɗi da zabga tagumi, tana kallonsa ba ta tanka masa ba har sai da ta gama cinikayyarta tsakaninta da wata budurwa da wasu samari su biyu da suka kawo mata abubuwa kala-kala wai ta siya. "Duka dubu goma zan bada waɗannan suturun" Ta ce idon ta kan budurwar
"Haba dai dubu goma? Hajjaju kayan nan fa masu tsada ne ko less ɗin nan ai da gani ya haura hamsin, ga dogayen riguna ban da atamfofi" Cewarta.
Sai kuwa ta turo ɗankwali gaban goshi "To hakan ma ai na yi da arziƙi, kayan da ba karen ki ne ya kama ba? harkar nan fa kar ta san kar ne babu ficikar ki a ciki, kawai kin yayibo a igiya ne kika kawo don ki samu na kashewa."
"To na ji ba sai an yi tone-tone ba yanzu dai ki ƙara ko goman ce"
"Gaskiya biyar ba zan ƙara miki ba saboda ni ma siyarwa zan yi kuma kin ga sai na yi takatsantsan sai dai a siyar da su a can wani garin nesa da nan saboda gudun ɓacin rana. Ki karɓi hakan ma haɗu a wani ai ana tare" ta ƙarasa da taunar cingam.
"Shikenan kawo hakam" tana zumɓura baki
Karkacewa ta yi ta ciro kuɗi masu yawa a ƙugu ta ƙirga goman ta miƙa mata sannan ta mayar da sauran. Juyawa ta yi ta fice tana gunguni. Ta waiga ga ax m samarin ta duba nasu kayan sannan ta sallame su su ma. Suka zari dubu ɗaya suka miƙa mata. Ta san kwanan zancen, don haka ta miƙa musu kwalin sigari da wani ƙullin abu guda biyu, duka karɓe suka samfe a aljihu sannan suka fice.
Suna fita ta dawo da kallonta kan shi "Kai kuma lafiya ka wani yi zumui kamar an jiƙa biri?" Ya sauke tagumi "Hmmm kedai bari momy muna cikin damuwa ne ƙanwata aka sace yau kwana biyu babu ita babu alamunta."
"Subhanallahi, ko da na ji kai dai a ji bakin ka shiru ai an san da walakin goro a miya, amma ba ita ce kake cewa ta saka maka ido da yawa haushinta kake ji ba?"
"Ita ce fa momy amma ai kin san dole zan damu, ƴar uwata ce fa ta jini, kuma kin san jini ai ya fi ruwa kauri, duk ƴar tsamar da