Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
tambayi kan ta cike da ɗaurewar kai. Baki ta taɓe ta mayar da wayar ta ajiye ta cigaba da aikinta....!
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS
Writers Association
WOW
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(17)
Kamar yadda aka saba yau ɗin ma hakan ce ta kasance, da kan shi yake kasafin kuɗin. Bayan ya gama ya ware nasa ya miƙa musu sauran. Shi kam sam hankalinsa baya ga kuɗin yana kan wayarsa. Gabansa kuma shisha ce da ya haɗa da kan shi yake zuƙa a hankali. Sai bayan tafiyarsu sannan ya warewa yaran nasa nasu ya ajiye nashi a gefe, can kuma ya miƙe ya ɗauki jakar ya fice domin yin abin da ya dace da su. Duk suka bi shi da kallo har ya fice "Wai ni ka san me yake ɗaure mini kai game da lamarin Babba?" Cewar maiyagi. "Sai ka faɗa" Goje ya ba shi amsa. "Inda yake kai kuɗinsa mana, ina lura da shi fa duk lokacin da aka yi kason nan fita yake yi da nashi kuma baya dawo da su, kamar ma ba da su yake amfani ba."
"To ka sani ko ajiya yake kai wa ko kuma a banki yake zuba su?"
"I, to da wannan, amma duk girman gidan nan ya rasa wurin ɓoye kuɗi naga mu har filo muke yi da su, kuma gaskiya ba na tunanin a banki yake zubawa akwai dai wani abu"
"To mu ina ruwanmu ma da me yake da su idan ma zubarwa yake yi, mu ma ba ga namu nan ba, sai mu yi yadda muka ga dama ai. Mu yi abin da ke gabanmu don Allah kar mu fara abin da babu ruwanmu saka ido a rayuwar wani."
Ya ƙarasa yana zama a inda Babba ɗin ya tashi ya cigaba da zuƙar shishar da ita yake kan sha ya fita. Yatsina fuska ya yi "Na ji ta salam, a ba zan iya shan wannan abar a haka kamar lemo ba."
"Hhhhhh ai kai ma ka san babba ba ya zuba kayan maye a ciki, bari na haɗa mana wadda za ta mana caji sosai mu yi codumo." Suka sheƙe da dariya.
A gajiye ta isa gida ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Aikam ta yi faringani domin da shi suka haɗa ido tana shiga. Ta ƙarasa da gudu ta faɗa kan shi "Daddyna oyoyoo" Yana dariya ya riƙe ta yana faɗin "Yawwa mai babban suna fatan na same ku lafiya"
"Lafiya ƙalau daddy mun yi kewarka sosai gidan ba daɗi"
"Ni ma haka, amma ba ga shi na dawo ba yanzu ba?"
Ta yi dariya, sai kuma ta juya wurin Mamyn "Barka da gida Mamy"
"Hmmm sai yanzu za ki kula ni kenan, yawwa ya aikin?" Ta ɗan sosa kai "Afuwan Mamy, aiki Alhamdulillah, ga shi nan na dawo liƙis, akwai fa labari mai daɗi yau mamy kun san an kama ƴar damfarar nan kuma ashe namiji ne ke shigar mata?" Ido suka zaro dukkansu "Kamar ya ya?" cewar mamyn "Wallahi, ke dai bari na yi wanka na huta zan ba ki labari duk da ba cikakke ba ne ban samu magana da shi ba, har da ɗayan ma."
Ta ce tana miƙewa ta shige ɗakinta, duk suka bi ta da kallo cike da so da ƙauna.
"Tana da ƙoƙari sosai, ba ta wasa da aikinta." Cewar daddy yana murmushi. "Hmmm amma wani lokacin tana saka kanta a haɗari abin da ba na so kenan ni kuma" Mamy ta faɗa fuskarta na ɗan canjawa. "Yo ai aikin jarida ya gaji haka dama, shi yasa ba kowa zai iya shi ba face jajirtacce kuma jarumi."
"Ni fa wallahi ban so aikin jaridar nan ba tun farko, aikin asibiti shi ya dace da ita." Ta kuma faɗa.
"Kar ki manta duk abin da Ubangiji ya tsarawa bawansa shi yake yi a rayuwarsa. Wannan aikin shi ne burinta tun fara karatun ta, ni ma kuma sai na mara mata baya, domin kin san idan yaro abin da ya so yake karanta ya fi mayar da hankalinsa akan karatun, yanzu ba ga shi ta kammala cikin nasara ba kuma tana cin moriyarsa?"
"Haka ne, Allah ya dafa mata ya kuma cigaba da tsare mana ita a duk inda za ta shiga ta fita.
"Yawwa kin ga adduar da take buƙata daga wurinki kenan ba. Amin summa amin."
Daga nan suka cigaba da tattauna maganar har ta fito, suka ɗora firar da ita tana ba su labarin da tace ɗin, sai dai dole sai a washegari za ta samu tattaunawa da shi ta ji cikakken bayanin duk yadda ake ciki sai ta samar musu.
Sai da aka yi sallahr isha'i sannan suka yi niyyar cin abincin, da ma tuni an gama shirya musu wurin cin abinci kai tsaye can ɗin suka nufa suka zauna. "Amma daddyn Yara Nura bai shigo gidan nan ba fa ma ci abincin mu kaɗai?."
"Ke rabu da wannan shashashan, namiji ne ai lokacin da ya ga dama ya shigo ba za mu jira shi ba. Kuma da ma haka yake yin dare a waje ina dokar da na saka masa?" Ya ce cikin ɓacin trai.
"Ba ya kai wa i yanzu, ba koina ma nake barinsa fita ba don ya yi kwana biyu ko bakin get ban bar shi ya je ba, yau ɗin ma bikin abokinsu ake yi ya tafi, to kuma ka ji har yanzu shiru." Ta ce cikin damuwa, shiru ya yi da farko, sai kuma ya ɗauki waya ya danna masa kira amma tana ruri ba a ɗaga ba. Cigaba ya yi da kiran shiru.
Ran shi ne ya fara ɓaci "Kin ga irinta ai kiransa nake yi amma saboda ya raina ni ya ƙi ɗaga wayar." Tana shirin magana kawai suka ji an banko ƙofar falon da ƙarfi an shigo. Da kallo duk suka bi shi, atamfa ce a jikinsa zani da ɗankwali sai doguwar jallabiyya da ya saka daga ciki.
Takaici hana Mamy magana ya yi. Sai daddyn ne ya ce "Daga gidan uban wa kake? Kuma wannan shegiyar shigar ta jikinka ban hana ka yin ta ba?" Bai yi magana ba sai juyar da kai da ya yi gefe yana harare-harare haɗi da tauna cingam. "Ba da kai nake magana ba ka mini banza, me ya hana ka ɗaga kiran da na dinga yi maka?"
"Haba daddy ni fa gaskiya ba na jin daɗin abin da ake yi mini a cikin gidan nan bayan ni ma ɗa ne ba agola ba. Yaushe rabon da na gan ka ai ka bari na rungume ka na ji ƙamshin mahaifina mana amma kana ta faɗa." Ya matsa zai rungume shi. Fincike jikinsa ya yi jin kamar yana warin kayan maye "Wallahi ka kiyaye ni Nura idan ba haka ba zan saɓa maka, kuma in dai baza ka daina wannan shigar ba sai ka bar mini gidana."
"To! Inji mai tallan totuwa, na bar gidan nan na koma ina? Ai duk lalacewarka gidan ubanka gidanku ne tunda da uba ake ado riga ko a kasuwa ka sayo ta. Wallahi zama daram mai naƙuda ta samu katifa." Yana mele baki
"Tasss" Mamy ta ɗauke shi da mari tana huci. "Ashe ba ka da mutumci uban naka kake faɗa wa haka? Kar fa baƙincikin ka ya sa zuciyar shi ta buga"
"To sai ya ce zai kore ni, duk tsiya dai ai gidan iyaye shi ne gidanka na musamman, darajar ungulu ta hau saman kuka ehe, kuma zuciyar shi ta jima ba ta buga ba ta zama ganga." Wani marin ta kuma ɗauke shi da shi har uku a jere tana fashe wa da kuka.
"Wallahi haihuwarka ba ta mana amfani ba, Allah ya...." Cikin sauri Nuratu da ta iso wurin ta toshe mata baki tana girgiza kai hawaye fal idonta. "A'a Mamy kar ki masa baki don Allah, gabaɗaya ba a hayyacinsa yake ba da alamu wani abu suka ba shi ya sha a wurin bikin. Bari na kai shi ɗaki." Sai ta miƙe ta iso kusa da shi ta kama hannunsa tana jan shi, kamar raƙumi da akala haka ya bi ta ɗakin. Suna shiga kuwa ya zube a katifa bayan ya yi wurgi da ɗankwalin kansa sai bacci. Takalmin ƙafarsa ta zame ta ajiye masa a gefe sannan ta fito ta ja masa ƙofar.
Daddy na zaune inda yake ya dafe kan shi da hannu biyu. Ya yin da Mamy ta zuba tagumi tana share hawaye akai-akai. Ta ƙarasa ta zauna a tsakiyarsu tana ƙoƙarin mayar da tata ƙwallar ta ƙirƙiro murmushin dole ta wanzar a fuskarta kafin ta ce "Don Allah ku yi haƙuri da abin da ya faru, a yanzu yaya ba fushi yake buƙata ba face cigaba da masa fatan shiriya. Fushi babu abin da zai ƙara face lalata shi balle bakin ku da yake da dafi a gare shi. Na tabbata wani abu ya sha yanzu haka ya yi bacci, ina fatan za ku yafe masa." Sai lokacin mamy ta ɗago da jajayen idanunta ta ce "Ni na san haihuwar Nura yana cikin ƙaddarata, adduar nake yi amma kamar ba na yi, zan cigaba da yi masa Allah ya shirya shi."
"Yawwa amin amin Mamynmu daddy saura kai, ka yafe masa?" Ta mayar da tambayar kan shi. "Ban yafe masa ba kuma dole sai ya bar mini gidana a daren nan."......!
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS
Writers Association
WOW
WOMEN OF WORDS
Writers Association
(WOW)
18
"Don girman Allah daddy ka yi haƙuri, idan yaya ya bar nan ina zai je? Tafiyarsa ba alkairi ba ce sai dai ma ya kuma kangarewa zuciyarsa ta bushe ya ji babu abin da ba zai iya aikatawa ba. Haƙurin dai shi za ku yi mu cigaba da bin sa da addua in sha Allahu zai zama labari."
Shiru ya yi yana huci ba tare da ya kuma magana ba.
Sam abincin sai ya kasa shiga domin duk kasa ci suka yi. Ita dai ta haɗa ruwan tea ta sha ta kwanta.
Baccin ma bai zo ba sakamakon abubuwa da suka cunkushe mata kai, tunaminta ta inda ya kamata ta fara, waɗancen azzaluman ƴan taaddan ko binciken da ta saka a gaba? Ga kuma matsalarsu ta cikin gida da take son zamowa silar kawar da ita. Tana kallo kiran Barister Sahabi na ta shigowa amma ta kasa ɗagawa don ba ta cikin yanayin da za ta iya wata waya da shi.
Washegari haka ta tashi ido luhu-luhu domin sai wurin asubahi bacci ya ɗauke ta, kuma alfijir na ketowa alarm ɗin wayarta ya buga mata dole ta tashi. Sai da ta watsa ruwa mai ɗumi a jikinta sannan ta yi alwala ta tayar da sallah, tana kan daddumar bacci ya sure ta. Ba ita ta farka ba sai wurin tara na safe shi ma alarm ɗin ne dai don a haka ta saita shi saboda a lokacin take fara shirin fita aiki.
Ta yi mamakin ganin saƙon da yake saman wayar tata da aka turo shi tun bakwai na safe. Take ta shiga don ganin cikakken saƙon. "Barka da safiya alƙabbar mata sarauniyar zuciyata, ina fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya. Wani bawan Allah."
Shiru ta yi da farko tana tunani, sai kuma ta taɓe baki ta miƙe tsaye "Hmmm ka yi ka gama, na ga irin ka da yawa ai wa za ka wahalar?" Ajiye wayar ta yi ta fice daga ɗakin. A falo ta tarar da Mamyn a zaune. "Sannu da hutawa mamy ina kwana?" tace bayan ta ƙarasa ta zauna a kusa da ƙafafunta "Lafiya ƙalau ƴar albarka fatan kin tashi lafiya."
"Lafiya ƙalau, yaya Nura fa ya fito?" Taɓe baki ta yi kafin ta ce "Ina fa?" Miƙewa tsaye ta yi "Bari na duba shi" Daga nan ta nufi corridor ɗin da zai sada ta da ɗakin nashi ba tare da ta jira amsawar mamyn ba. Tsayawa ta yi a ƙofar ɗakin nasai tana ƙwanƙwasawa "Waye?" yace daga ciki. "Ni ce yaya ka tashi ashe?"
"Da ban tashi ba za ki ji muryata ne haka sumul raɗau?"
Ta girgiza kai tana ayyana shi dai ba a masa gwaninta "Zan iya shigowa?"
"A'a baza ki iya ba koma inda kika fito dama ban kira ki ba ai." Murmushi ta yi sannan ta tura ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Yana tsaye a bakin madubi yana ta ƙalƙale ƙalƙalan nasa. "Ina kwana" ta faɗa "Ƙalau me ya shigo da ke ko sa idon ne ya motsa." Yana mata kallon sama da ƙasa "Ba komai kawai shigowa na yi mu gaisa matsayinka na yayana." Ya taɓe baki "Kya ji da shi ciwon rai a ɗan yatsa." Ba ta kuma magana ba sai ma samun wuri da ta yi ta zauna har lokacin tana murmushi "To zaman me kika yi kuma? Ni fa ba na son gulma."
"Jiranka nake yi ka gama mu fita tare, saboda ina so mu je ka ba wa su daddy haƙuri."
"Me na yi to kuma, tunda ni ne sarkin laifi?"
"Au har ka manta abin da ya faru jiya da dare? yadda ka rufe ido ka gaggasawa daddy magana? Haba yaya bai dace ba abin da ka yi su iyaye ba abin wasa ba ne, duk wannan abin suna yi ne don ganin rayuwarka ta inganta amma kai sam ba ka gani....?"
Hannun da ya ɗaga mata ne ya dakatar da ita daga maganar da take yi. "Sannu uwale mai dattin ɗankwali yi mini faɗa. Ai dama tun da na ga kin shigo simi-simi kina wani sinne kai na san da walakin goro a miya tunda koyaushe tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Idan kina mini faɗa kamar kece yayar ni ƙanin." Yace cikin hayagagar tashi "Ba haka ba ne yaya gyara kayanka ba ya taɓa zama sauke mu raba, ina so ka daidaida da su ne saboda ka tsira a gobe ƙiyama tunda ita mutuwar nan ai ba ta sallama kuma aljannar namiji tana ƙarƙashin ƙafar iyayensa."
"To na ji je ki Allah ya bada ladan shaida. Ke wallahi kyanta turmi za ki fara hawa kina waazi shi ya fi dacewa da ke ba wannan aikin wahalar ba na gajiya da rayuwa." Ta yi murmushi jin abin da yace, kamar ta kuma magana sai kuma ta miƙe lokacin da ta kalli agogo ta fice da sauri don ta je ta shirta. A gurguje ta kuma yin wankan ta shirya cikin shigar tata ta gado wato doguwar riga.
Ta ji daɗin ganin shi zaune Mamyn na masa magana da alamu faɗa take masa, duk da fuskar nan tasa tamau take kamar magribar ɗinya. "Mamy ni bari na wuce" Ta ce tana gyara zaman jakar kafaɗarta. "A'a tafiya kuma ba za ki jira ki karya ba?"
"Sauri nake yi mamy idan na je can na karya. Ga shi har zan tafi daddyn bai fito ba ko duk gajiyar ce?"
"Aikuwa dai kamar ya tashi na jiyo motsinsa a ɗakin ciki."
"Bari kawai na leƙa mu gaisa ko a gurguje ne." Ta fara ƙoƙarin hayewa saman, da sauri mamyn ta dakatar da ita "Amma dai kin san ya hana mu bin shi can ɗin ko? Kin manta yace ko menene a jira shi ya fito tukunna?"
"Ina zan iya jiransa Mamy? Kuma gaskiya dai ina son ganinsa kafin na fita, zan masa magana daga bakin ƙofa ba sai na shiga cikin ba."
Daga haka ta haura saman ba tare da ta jira mamyn ta kuma dakatar da ita ba. Ba ya ɗakinsa kamar yadda mamyn tace kuwa yana ɗakin ciki domin ta jiyo maganarsa sama-sama. Ƙarasawa ta yi fuskarta ɗauke da murmushi ta taɓa ƙofar da niyyar turawa ta shiga, sai kuma ta dakata cak sakamakon maganar da ta ji yana yi a wayar. Tsugunnawa ta yi ta kara kunnenta a jikin ƙofar sosai ta yadda za ta fi ji.
Wani irin yankewa gabanta ya yi ya faɗi, take ta fiddo idanunta gabaɗaya cike da tsoro. Maganar da ta ji ya yi ta ƙarshe ta saka ta dafe ƙirjinta da yake ta dakan lugude da dukkannin hannayenta biyu tana matsawa daga jikin ƙofar. Cikin sauri ta bar wurin ta nufo ƙasan, bibbiyu ta dinga haɗawa wurin sauka a benen, da mugun gudu ta fice a falon ba tare da ta kuma bi ta kan mutanen falon ba.
Mota ta faɗa ta dafe kan ta da dukkanin hannayen tana maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihirrajiun. "Allah ka sa kunnuwana ba daidai suka jiyo mini ba. Ta ya ya daddy zai yi hakan? Ta tambayi kan ta ƙirjinta na cigaba da bugawar da yake yi.
Har suka isa ba ta san sun iso ba sai da ta ji magana a kan ta ta ɗago firgigit. A hankali ta ziro ƙafarta ta fito daga motar ta doshi ciki. Duk wanda ya mata magana hannu kawai take ɗaga masa har ta isa ta buɗe ta shiga.
Tagumi ta zabga da hannu bibbiyu ta lula dubiyar tunani.
Har ba ta san lokacin da Zaitun ɗin ta shigo ba tana mata magana amma ba ta ji ba. "Nuratu" Tana girgiza kafaɗarta. A firgice ta ɗago ta kalle ta, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. " Lafiya me ya faru?"
"Ba komai me kika gani?" Tana ƙaƙalo murmushin dole ta wanzar a fuskarta
"Ya za ki ce me na gani bayan ga hawaye nan a idonki shaɓe-shaɓe abin da ban taɓa gani ba?"
"Hawaye kuma?"