Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
Ta ce tana shafo fuskarta, ilai kuwa hawayen ne ashe kuka take ba ta sani ba. Wani murmuahi mai ciwo ta saki tana kallon gefe kafin ta ce.....
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
(19)
Ta yi wani bushashshen murmushi kafin tace "Kin san abin da ba ka taɓa kawo faruwar shi ba ko zai iya kasancewa idan ka gani ko ka ji dole hankalinka zai tashi."
"Me kika gani me ya faru?" Ta kuma tambaya cikin ruɗu.
Girgiza kai ta yi kafin ta ce "Ina fatan abin da na ji ya kasance ba gaskiya ba ne, ko kuma gizo kunnuwana ke yi mini."
"Allah ya sa ba gasken ba ne to ko ma menene ɗin"
"Amin" tace tana rausayar da kai.
"Ya kamata mu je police station ɗin nan yanzu fa mu ɗauko rahoton kafin wansu su riga mu tunda na ga babu gidan jaridar da suka wallafa cikakken labarin har yanzu." Cewar Zaitun ɗin. "Eh kuma haka ne fa, ni ma da ƙudirin da na fito kenan da ma, mu je kawai." Ta miƙe tana tattara abubuwan da za ta buƙata sannan ta bi bayanta don ta fice, ita kulle ƙofar tasu ta yi suka nufi ficewa daga ciki.
Mota suka shiga sai ta ga su ma masu tsaron nata sun buɗe za su shiga tasu, ta leƙo da kanta fuska a ɗaure ta ce "Ba buƙata ba sai kun biyo ni ba, ku yi zamanku yanzu zan dawo. Kai ma ka jira zan yi driving ɗin da kaina." Ta mayar da kallonta kan direban da ke shirin tada motar. Duka suka yi sororo ya bunsuru a mayanka suna bin ta da ido. "Amma me yasa? kin san fa aikinmu kenan a kan tsaron lafiyarki." Wani escort ya faɗa "Ko da ku ko babu ku ni kullum cikin tsaro nake don ubangiji na kare ni. Ni daga yau ba na buƙatar rakiyar kowa don da ma ba ƙaramin takura mini kuke yi ba." Daga haka ta ja motar ta tafi ta bar su kasake da baki.
Ɗaya daga cikinsu ne ya ciro waya ya danna wa daddyn kira. Zaitun ta dube ta tace "Amma me yasa za ki yi haka? Kin san dai daddy ne ya ɗauke su saboda ke ko? Kuma yau rana tsaka ki ce su daina bin ki?"
"Eh na soke daga yau ba na so, kawai a bar ni a haka da can da ba sa nan fa wa yake kare ni idan ba Allah ba? Yanzun ma kariyarsa kawai nake buƙata ba ta wani ƙato ba." Zaitun ɗin ta buɗe baki za ta kuma magana amma ta ɗaga mata hannu, dole ta ja baki ta tsuke ba ta kuma mata magana ba don ta lura ƙawar tata yau gabaɗaya ba a daidai take ba.
Bayan isarsu division ɗin sun ci sa'a an yarda za su gan shi da suka nuna ID card ɗinsu, wuri suka samu suka zauna, kafin ta zuge jaka ta fito da abin ɗaukar magana ta ajiye a kan teburin gabanta. Can kuwa aka fito da shi, da gani ya ci duka ba kaɗan ba domin ko tsayuwa sosai ba ya iyawa. Suka bi shi da kallo dukkanninsu. A ƙasa ɗansandan ya durƙusar da shi. "Sannu bawan Allah" Ta faɗa, bai amsa ba face sauke numfashi da yake ta yi.
"Za mu so sanin sunanka" Tace tana gyara recorder ɗin nata "Sunana Rabilu Baba Abubakar"
"Menene dalilin da yasa aka kawo ka nan?"
"Ɗan damfara ne ni"
"Tsawon wanne lokaci ka ɗauka kana wannan harkar?"
"Na yi shekara uku a ƙalla"
Me yasa kake yi kuma ta wacce hanya kake bi wurin damfara? Sannan kuma mene dalilinka na yi wa iya maza damfarar ba mata ba?" Ya sauke ajiyar zuciya kana ya ce " Ni dai na taso ne a garin Kunkurawa, ni da iyayena duk a can muke da zama, sai dai na samu damar yin karatu da jajircewar mahaifiyata a nan maraya har na samu damar kammalawa da ƙyar, domin burina na yi karatu mai zurfin da zan samu aiki har na taimaka musu. Amma aikin ya ƙi samuwa kasancewar babana ba wani ba ne, duk inda na je neman aiki ba na samu, ƙarshe haka na haƙura na koma gida na sanar musu. Na lura gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi domin duk wani yaƙininsu a kaina yake, kasancewar ƙarfin babana ya ƙare yana zaune a gida ma, itama kuma inna ba ta iya surfen yanzu saboda jikin girma.
Daga baya ma sai ta fara rashin lafiya, aka yi ta banka mata maganungunan gargajiya amma a banxa kamar ma ƙara ciwon ake yi, dole na kuma ɗauko takadduna na dawo nan ƙara gwada sa'ata ko zan dace, domin asibiti nake son kawota kuma na birni, amma jiya iyau maganar dai ɗaya ce na kasa samun aiki, na kuma juyawa jiki a saluɓe na koma, sai na tarar jikin inna ya yi tsanani, a haka muka ɗauko ta zuwa nan. Sai na canja wata dabarar ta yawon neman taimako wurin waɗanda na ga da maiƙo a jikinsu amma haka suka dinga muzantar da buƙatata.
Likitocin sun ce ciwon ƙoda ke damunta mu nemo kuɗin magunguna da sauransu tun kafin ciwon ya yi tsananin da za a cire ta...
"Ka taƙaita labarin saboda lokaci" Ta ce masa, ya gyaɗa kai sannan ya ɗora "Na taɓa zuwa wurin wani Alhaji da na ga ya shigo asibitin a mota ina roƙon ya taimaka mana, amma a ƙarshe sai ya zaro dubu ɗaya ya miƙo mini. Na saka hannu na karɓa sai na ga hankalin shi ma ba ya kaina yana ga wata budurwa da ke tsaye a bakin get ɗin asibitin. Ɓalle murfin motar ya yi ya isa wurinta yana mata magana amma ta ƙi kula shi, ina gani yana marairaicewa sai ma ta juya ta fice a asibitin, ya dawo ya shiga motarsa ya bi bayanta. Na sauke ajiyar zuciya sannan na isa wurin wani Alhaji da na gan shi ya fito daga ciki shi ma da babbar riga, har ya go ta wata budurwa sai kuma ya dawo ganin tana sharar hawaye da gefen hijabinta "Ƴammata lafiya kuwa?" Ya tambaya, ta ɗago ta dube shi sannan ta ce "Babanmu ne ba shi da lafiya muka kawo shi asibiti, kuma aiki za a masa amma har yanzu ba mu haɗa kuɗin ba, ga yayana tunda ya fita da niyyar nemo cikon shiru bai dawo ba kuma jikin nasa ya tsananta."
"Ayya yi haƙuri Allah ya ba shi lafiya, ga wannan ku ƙara akan wancen, ina sauri ne da na shiga na duba shi." Rafar dubu ɗari ce ya ba ta aikam ta duƙa tana godiya sannan ta juya ciki. Ganin haka yasa na isa wurin shi ina faɗa masa tawa mahaifiyar da take buƙatar taimako itama, wani kallo ya mini sannan ya ce "Ka je ka yi sana'a mana" Daga haka ya shige motarsa ya tafi ba tare da ya jira cewata ba. To wannan shi ya canja mini tunani domin na lura mata suna da alfarma a duk inda suka shiga sai na fara ƙoƙarin sajewa da su. A ƙarshe dai gida muka tattaro muka dawo bayan mun siyi magungunan da za mu iya da karo-karon ƴan uwa. Da wata asubahi bayan an tada sallah na dawo gida babana na masallaci inna ma ta tayar, na shiga turken awakin na kunce rago da wata uwar girke tunkiyar inna na fice da su. Kai tsaye kasuwa na kai su na siyar daga nan na hau motar nan.
Ina zuwa na nemi shago ƙarami na kama sannan na shiga kasuwa na siyo duk wani kayan ado na mata na dawo. Tun a ranar na fara shafe-shafen mayuka na saka haske, ina zumbuɗa hijabi ina yawona a gari, cikin sati guda na canja fatata ta yi kyau, na saka haƙorin makka. A ranar cika satin ne na ɗauko wata atamfa da na kai ɗinki na saka ta bayan na sassaka abin ciko gaba da baya, na yi kwalliya da saka yari da ɗankunne. na saka hular gashi sannan na yi ɗauri na yafa mayafi. Ni kaina da na kalle ni a nadubi sai da na firgita ganin yadda na yi, babu wanda zai gan ni ya ce ba mace ba ce. Na saka takalmi da jaka da turare sannan na fita na rufe shagon.
Tun a ranar na yi babban kamu domin ina tsaye a titi wani babban mutum da gani ya ci ya tada kai ya tsaya gabana yana magana, na juyar da kai ina jan aji. Sai da ya fito da magiyarsa na shiga mota muka tafi. Wurin cin abinci muka je har lokacin ban yi magana ba sai na nuna nasa ai ni ina ji amma ba na magana. Bai damu ba muka cigaba a haka har ya kai ni wani gidan gonarsa. Anan na kwashi rabona na fito daga gidan bayan ya shiga banɗaki.
To fa tun daga nan na faɗa harkar gadan-gadan ina ta cin karena babu babbaka, ganin akwai riba, cikin ƙanƙanin lokaci na mallaki abubuwa da dama kadarori kuɗi, na sayi gida da na koma ciki, har na samu wanda nake yi wa iyayena aike ta hannunsa bayan na ce ya sanar musu aiki na samu. Kasancewar na iya takuna ba wanda ya taɓa gano ni sai a wannan karon da ƴar garkuwa da mutane suka zo har gida suka ɗauke ni ashe rabon dubuna ta cika n....!"
"Dakata!" Nuratu ta katse shi da sauri, sai kuma ta fara huci jin ya ambaci ƴar garkuwa da mutane, take ta tuna miƙin da ke ƙasan ranta, ta tsani waɗannan mutane, ba ta ƙaunar ko sunansu ta ji an ambata a inda take, take ranta ke mugun ɓaci, tana ji da za a ba ta bindiga ace ta zaɓi waɗanda za ta kashe to su za ta fara nemowa musamman oganninsu ta kashe su har lahira......
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
20
Duk suka bi ta da kallo "Lafiya dai?" Zaitun ta ce tana karantar yanayinta, ta girgiza kai kawai alamun bakomai "To idan kun gama da shi bari ya koma" Cewar ɗan sandan "A'a ba mu ƙarasa ba, afuwan minti biyar kawai." In ji Zaitun, jin Nuratun shiru ba ta ɗora ba ya sanya ta mayar da hankalinta kan shi ta ce "Daga nan kuma sai me ya faru bayan sun ɗauke ka?"
"Har gida suka zo suka ɗauke ni cikin dare, ni kuma duk zatona jami'ai ne suka gano ni sai na fara musu rantse- rantse. To sai bayan sun kai ni can suka ce na fanshi kaina da dukkan kuɗaɗen da suke cikin asusuna, kuma suka karɓe kadarorina, yanzu haka ba ni da komai sun ƙwace, sannan ba su ƙyale ni haka ba sai da suka tona mini asiri duk da sun ce babu ruwansu da rayuwata. Na yi takatsantsan sosai, domin duk layin da ya gama yi mini amfani yarwa nake yi ko na yar da shi."
"Yallaɓai mun gode sosai, zai iya komawa" Ta faɗa tana kallon ɗan sandan. "Don girman Allah tunda na faɗi gaskiya a sassauta mini hukunci, wallahi na yi nadama." Ya ce cikin roƙo "Sai ka ɗanɗana kuɗarka, don masu ƙararraki a kan ka suna da yawa kowa a shirye yake da a karɓa masa haƙƙinsa." Cewar ɗansandan yana tunkuɗa keyarsa zuwa ciki. "Zancen garkuwa ɗin nan fa shi ma case ne mai zaman kan sa, ya za a yi su ƙwace komai kamar da ma da haɗin bakinsu yake yin abin da ya yi?" In ji Zaitun. "Hmmm indai waɗannan kangararrun ne masu zuciyar fir'auna haɗa bakin ma ai sai su yi don babu abin da baza su iya ba, azzalumai kawai na tsani mutanen nan, wallahi ina nan ina shiri a kan su sai na gano su na kuma tona musu asiri, don abin da suka mini yana nan maƙale a raina, da su nake kwana nake tashi." Nuratun ta faɗa cike da takaici.
Bayan ya mayar da shi cikin cell ne ya dawo wurinsu, a lokacin har sun miƙe domin tafiya "Mun gode sosai yallaɓai da lokacin da ka ba mu ishashshe, Allah ya cigaba da ba ku sa'a kuna kamo waɗannan macutan masu ci da gumin wasu." In ji Zaitun "Ba komai Allah ya dafa mana bakiɗaya." Ya ce su kuma suka juya suka fice.
Turus suka yi dukkanninsu ganin Direban a jikin motar tasu, gefe guda kuma masu tsaron nata ne. "Naci dambun kuturu, ashe biyo mu suka yi" Ta ce tana harararsu, murmushi Zaitun ɗin ta yi ta ce "Mu ƙarasa to, da ma tunda aikinsu ne ai baza su bar ki haka sakaka ɗin ba, sai su yi laifi kuma ai."
Ita dai ba ta kuma magana ba ta ƙarasa motar ta shige ba tare da ta kula direban ba. A baya ta bi ta sannan ta buɗe ɗaya ɓangaren ta shiga ta zauna. A hanya Zaitun ta dube ta duk da cikar da take yi tana batsewa tace "Kin san tun a jiya da na sanarwa Uncle ɗin nawa an kama shi ya zo division ɗin ya ji komai, kuma a daren ya sanar mini. Kin ji ashe wani babba ne da ya damfara ya saka ake bibiyar masa lambar shi da suke chat da ita saboda kuɗin da kadarorin da ya raba shi da su suna da yawa har da na marayu. To duk da sun ce layin ba ya amfani ya ce su cigaba dai da saka ido za a iya dawowa daga baya a mayar da layin tunda ya fahimci cire shi aka yi. Sai ga shi kuwa bayan watanni har an cire rai kwatsam suka ga alamun layin ya fara fara aiki, shi ne fa cikin gaggawa aka bibiyi inda wayar take har aka gano gidan nasa aka je.
Amma abin mamaki sai aka tarar ashe namiji ne ke yin basaja yana shigar mata. Har ma aka samu wasu abubuwan da yake amfani da su a gidan.
Bayan sun kama shi ne da ya ci duka ya faɗi komai tun a jiyan. Kai duniya inda ranka ka sha kallo, gaskiya na yarda ƴan iska a duniya ba za su ƙare ba, sun ce wallahi da wannan shigar matan da yake yi babu wanda ya isa duk ƙwaƙwar shi ya ce ba mace ba ne, kai Allah ya kyauta wasu dai akan kuɗi babu abin da ba za su iya aikatawa ba wallahi. Ya zo nan yana ta ciyar da iyayensa da haram."
"Amin dai" Abin da Nuratun tace kenan tana dafe kai, wanda hakan ya sanya ta kallonta ganin duk bayanan nan da ta mata wai ta bi ta da amin kawai. Amma sai ta rabu da ita ganin gabaɗaya ranar ba ta da wata walwala.
A ranar kuwa suka shirya rahoton suka saka, amma Zaitun ce ta karanta kasancewar kanta da yake ɗan ciwo, daga baya ma sai ta nemi Excuse ta tafi gida.
Kamar mara laka haka ta shiga falon da sallama ciki-ciki. Mamyn ta amsa mata tana nazartar ta. A kujera ta zube tana lumshe ido "Ya dai?" ta tambaye ta "Ba na ɗan jin daɗi ne shiyasa na dawo na kwanta."
"Subhanallahi sannu, ciwon kan ko?" Ta kuma tambaya tana dafa kanta. Kai kawai ta gyaɗa mata alamun eh. "Akwai magani ai, ki samu ki ci abinci sai ki sha maganin ki kwanta."
"To Ammi, gidan sai ke kaɗai daddy ya fita kenan" Tana yunƙurin miƙewa tsaye "Ya ɗan je ya dawo yace ba jimawa zai yi ba, ya sakko ɗazu yana tambayar ki na ce kin je yana bacci kika tafi. Wai me ya faru ɗazun ne na ga kin sakko kamar a ruɗe kin yi waje?"
"Zaitun ce ta kira ni cewar na yi sauri na je za mu tafi ɗauko rahoton ɗan damfarar ne, mun je kuwa kuma ya mana duk wani bayani da muke buƙata, ba don kaina na ciwo ba da na faɗa miki yanzu."
"A'a ki bari ki warware dai tukunna, yanzu ki yi abin da na saka ki ɗin." Kai kawai ta gyaɗa ta doshi ɗakinta tana faɗin "Yaya fa?"
"Yayan kwabo za ki ce, ya ƙunshe a ɗaki yana ta ɗacin rai, saboda an hana shi fita, ko me yake yi a ɗakin oho masa" Ita dai murmushi ta yi ta shige ɗaki ta kwanta
Babban ɗakin taro ne da ya haɗa manya, kowa na zaune a kujerun da aka jera da alamu tattaunawa ce mai muhimmanci. "Wannan fa abin kunya ne a gare mu ace gari kamar wannan matsalar kidnappers ta fara yawa a cikinsa, abin da muke jin shi a garuruwan da suke da maƙotaka da namu. Kuma ku har yanzu kun kasa yin wani abu akai, ko har sai matsalar ta yi tumbatsar da za a kasa yin wani abu akai, itace fa tun yana ɗanye ake tanƙwara shi " Cikin faɗa mai maganar ke yi idanunsa akan wasu jami'ai guda biyu da suke sanye da uniform.
"Afuwan yallaɓai za mu kuma ƙoƙartawa yanzun ma muna iya yin mu, kuma dole sai jama'a sun ba mu haɗin kai sannan komai zai ke tafiya daidai."
"Ba wai za ku ƙoƙarta ba ku yi duk mai yiyuwa ku kuma hana idanunku bacci da tunanin hanyoyin da za ku bi