Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
wurin daƙile matsalar nan tun kafin ta yi ƙamari." Ya kuma faɗa.
"Yallaɓai a matsayinka na Ministern tsaro fa dole kai za ka saka ido sosai akan aikin da ya zamo nasu ne, ka dinga bibiya, idan ka ga alamun wankin hula na shirin kai mu tsakar dare sai ka nemi wasu jami'an ka ƙara akan lamarin, amma sai mun motsa fa zaman nan a cigaba da tafiya a haka ba zai yiwu ba fa ba."
Wani mutum mai jiki da ke zaune ya faɗa cikin ɓacin rai. Take kowa ya fara amayar da abin da yake ransa game da sha'anin matsalar tsaron. Sun jima suna tattauna batun sannan taro ya tashi. Kasancewar har da ƴan jarida a cikin taron sun ɗauki abubuwan da za su wallafa a shafukansu.
Kan kace me zancen kama ɗan damfarar nan ya baza gari kowa da abin da yake cewa. Don ya amsa laifinsa suna gama tattara bayanai suka tura shi kotu. Mutane suka dinga turereniya kuwa wurin zuwa ganin yadda shari'a za ta kaya. Da yawa so suke yi su gan shi a zahiri, kasancewar duk an gan shi a hoto, domin haɗawa aka yi da waɗanda ya yi kwalliyar da aka ciro a shafukansa na sada zumunta da yake ta yaudara da sunan mace har ya tara mabiya sosai, aka haɗa da wanda aka ɗauke shi a hannun ƴan sanda. Kotun ta cika maƙil ba masaka tsinke. Yana cikin mutane a zaune tsakiyarsu, kamar koyaushe yanzun ma fuskarsa a rufe take ruf idanunsa kawai ake gani.
Isowarsu kenan wurin ita da waɗansu maza biyu abokan aikinta da aka haɗo su tare domin du ɗauki yadda shariar za ta kasance kuma live. Tun zuwansu idon shi ya sauka a kan ta har ya kasa ɗaukewa. Waigowar da za ta yi idanunta ya faɗa cikin nashi da ya kafe ta da su, gabanta ne ya yanke ya faɗi, ta ɗan ƙure shi da ido kamar yadda ya ƙure ta....
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
21
Saurin ɗauke idanunta ta yi jin ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta mayar da hankalinta kan abin da take yi. Babu ɓata lokaci aka fara gabatar da shari'a kamar yadda doka ta tanada. Kasancewar ya amsa laifinsa tun a hannyn ƴan sanda anan ɗin ma bai ɓata wa kotu lokaci ba ya faɗi komai. Inda a take kotu ta zartar masa da hulunci daidai da lefinsa na zaman gidan kaso bayan ta fahimci baza a samu kuɗaɗen a hannunsa ba kamar yadda ya faɗa waɗanda suka yi garkuwa sa shi sun kwashe komai. Iya gidansa ne da sauran kayan cikin gidan za a saka a kasuwa a rage wa mutanen da ya damfara asara.
Bayan fito da shi ƴan jarida suka dinga kutsawa domin ji ta bakinsa amma ya yi gum. Ita kam Nuratu daga gefe ta cigaba da aikinta domin ta riga ta gama samun duk bayanai a hannun nasa, abin da take yi a wurin kawai ɗaukar wa mutane bidiyo live na komai da ya wakana a kotun domin hankalin dayawa ya kwanta tunda ba kowa ya samu halartar zaman ba, haka ba kowa ya fito ya bayyana yana cikin wanda ya damfara ba.
Cikin sassarfa mai cike da izza take ta kutsowa tana ture mutane "Ku matsa don Allah, duk ku ba mu hanya ba mu da lokacin duk wannan. Kuma tsaiwar me kuke yi anan ɗin ne." Ta ce cikin daka musu tsawa. Sauke abin ɗaukar Nuratu ta yi tana bin ta da ido cike da mamaki, sai kuma ta shafa fuskarta ta kuma bin jikinta da kallo, ta yi matuƙar kaɗuwa kuwa.
Ita kam tsawar da take ta yi wa mutane da ture su ya ya sa aka ba ta hanya, a gaba ta saka mai lefin da hannunsa ke cikin ankwa sai ƴan sanda guda biyu da suka tiso shi da wasu a bayansu. Har motar suka kai shi bayan ya zauna suka shige su ma. Waigowa ta yi ta watsawa ƴan jaridar wani mugun kallo haɗi da furta "Mayu iyayen naci, da bin ƙwaƙwƙwafin tsiya, na tsani ƴan jarida wallahi" Daga haka ta shige motar aka ja suka tafi.
Karaf maganar da ta faɗa ta shige cikin kunnuwan Nuratu, take ranta ya ɓaci "Mu wannan ballagazar ke zagi? Mu ne mayu iyayen nacin?" Maganar ta dinga yi mata amaa kuwwa a kunne. Take baƙinciki ya kuma lulluɓe zuciyar Nuratu "Mu ma mun tsane ki, shashasha kawai da ba ki san darajar ɗan adam ba." Ta ce a fili tana tuna a yanayin da ta gan ta. Sanye take cikin kayan ƴan sanda ta ci ɗamara, kayan sun kama ta, kuma bayan kayan ba komai a jikinta don gashinta ma ya leƙo ta ƙasan hular kan ta.
"Gaskiya wannan jami'ar ba ta da kirki, ji yadda take hantararmu, ni ban ma santa ba " Ta ji wani ɗanjarida ya faɗa daga bayansu. "Sabuwar zuwa ce ba a jima da dawo da ita nan ba, ƙaramar sifeta ce, sunanta Nawwara Inuwa Wakili a ofishin MBP take aiki, ni ma na ji wani ɗan sanda ya faɗa ranar da na je samo bayanai game da shi wannan da aka yi shari'a ɗin."
Nazari ta tafi yi game da maganganunsu. Dafa ta da aka yi ya sanya ta saurin waigawa, Zaitun ce cikin ruɗu tace "Kin ga abin da na gani kuwa game da jamiar can?"
"Na gani" Ta ce a takaice "Ba ki ji wani abu ba game da kamanninta?"
"Eh ban gani ba" Ta kuma cewa, daga nan ta juya ta bar wurin. Ita ma dole ta bi bayanta suka tafi don komawa can office.
Yinin ranar fa da tunanin abin Nuratu ta yini, ita kamar ta san sunan nan INUWA WAKILI amma ta manta a ina, sai can da ta yi zurfi da tunanin sannan ta gano, a fili ta ce Yesss! Shi ne wallahi Senator Inuwa Wakili. To amma me zai sa ƴar shi ta shiga aikin ƴan sanda? Tabbas akwai wata a ƙasa kuma sai na nemo koma menene. Take ta shiga tunanin dalilin da ya sa ta san sunan nashi.
Akwai wani lokaci da aka kama wani Lanƙwasa dilan wiwi da yake rabawa ƴan shaye-shaye a can ƙasan layinsu. Cikin sa'a suka shiga hannu, kuma da aka yi musu tambayoyi na wanda yake saka su duk sun ƙi magana, sai guda ɗaya da yake a ɗan buge ne ya ce "Waye idan ba shi ba, sai mun sha ai za mu yi masa aikin da ya saka mu, kuma a koyaushe karatun da yake kwanyarmu mu dama mu kashe ne ko a kashe mu." Jin ya yi shiru cikin sauri suka kuma daka masa tsawa da tambayar ya sunansa. " Su sunansa Inuwa Wakili, domin ko lokacin zaɓe ma shi ya raba mana kayan maye muka tada rukici a wurin muka hargitsa komai."
Ogan nasu ne ya dalla masa mari a lokacin da faɗin ba shi da hankali ne ya musu shiru, shi kuwa ana marinsa ya baje a wurin sai bacci. Daga inda take tsaye ta jiyo komai akunnenta kamar ita ya faɗawa, sai da ta jira ta ga ɗan sanda ɗaya suka tattauna game da su sannan ta tafi.
To tun a ranar ta yi rubutu ta wallafa a shafin nasu na gidan jaridar cike da takaici. Aikuwa a daren ranar ba a fi minti talatin ba kira ya dinga shigo mata amma ta ƙi duba wanene balle ta ɗaga, ƙarshe ma kawai ta kashe wayar duka, ta kuma kwanta zuciyarta wasai, musamman ganin sharhin da ake ta yi a ƙasan post ɗin da ke nuna an yi walƙiya mutane sun fara gano shi. Ba tare da wani ɗar-ɗar ba washegari ta wuce wurin aiki.
Tana zama kuwa shugaban gidan ya tura aka kira ta. Tun daga yadda ya amsa sallamart da kuma yadda ta ga fuskar shi ta san ran shi a ɓace yake. Gefe ta koma ta tsaya ta sunkuyar da kai tana jiran ta ji me zai ce mata, ta yi minti goma sh biyar a tsaye sannan ya ɗago ya kalle ta rai a ɓace ya ce "Yaushe kika fara yin gaban kan ki a ofishin nan ban sani ba?" Shiru ta yi har lokacin kan ta a ƙasa. "Me kenan kika yi kin je kin yi rubutu a kan Sanata Inuwa Wakili ba tare da sanin kowa ba kika wallafa a shafinmu, har ga shi kin sa yana ikirarin rufe mana gida, me ya shiga kan ki da ba ki yi tunanin me zai je ya dawo ba?"
Sai lokacin ta yi magana ganin yadda ransa ke ɓace "Ka yi haƙuri don Allah ban san ranka zai ɓaci ba"
"Ba wani nan kin sani, ai kin jima da sanin abin da suke so shi muke wallafawa, kina sane tunda har wayar ki na dinga kira kija ƙi ɗagawa saboda kin san me kika yi."
"A mini aikin gafara tunda wannan karon ne na yi gaban kaina shi ma ƴan ƙwayar da aka kama ne suka kama sunansa da cewa shi ke raba musu kayan maye kuma a gaban ƴan sandan, idan aka cigaba da yin shiru a kan su abin da za su yi anan gaba sai ya shafi kowa ciki har da mu."
"Ki yi mini shiru anan, ai baza ki karɓi laifinki ba da ma, tunda kina ganin kin fi kowa gaskiya da amana. Ki tabbata kin goge wannan posting ɗin kuma ki bada haƙuri da cewar an samu mistake ba sunan shi aka faɗa ba ashe, ki ƙirƙiri wani sunan ki maye gurbi da shi. " Ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi "Amma..."
"Ya isa ki je ki yi abin da na saka ki" Ya katse ta. Juyawa ta yi ta fice a sukwane. Sai da ta zauna a ofishin nata sannan ta kunna wayarta. Kai tsaye cikin post ɗin ta shiga bayan ta kunna data, aikuwa ta yi mamakin sharhin da aka yi. Ta ɗan bibiyi wanda za ta iya ta bar sauran, wani saƙo ta gani da ya ja hankalinta "Ki taka a sannu tun kafin ki jangwalo abin da zai hana ki bacci, domin ba kowa ake taɓawa a wanye lafiya ba, ni na san biyan ku aka yi kika masa wannan sharrin, don babu wanda bai san mutumin kirki ba ne" Kamar ta yi reply amma ba suna sai adireshin email, sai kuma kawai ta bi abin da ya ce mata ta goge posting ɗin gabaɗaya zuciyarta ba daɗi. Ba tare da ta yi amai ta lashe ɗin da ya so ta yi ba na canja magana.
Hmmm ta sauke ajiyar zuciya bayan gama tunano abin da ya faru. "Tabbas akwai lauje cikin naɗi, ƴar sanata mai ci a yanzu a matsayin jamiar tsaro? Dole na gano koma menene a ƙasa. Sai kuma tunaninta ya koma kan mutumin da ta gani a office ɗazu da rufaffiyar fuska har suka haɗa ido, tabbas ta so ta gane shi amma ta manta a ina, ta so kuma ganin shi da suka fito hakan ne zai sanya ta tuna inda ta san shi sai kuma ta ga ba ya wurin zaman nasa. Ta fara waige-waige aka fito da ɗan damfarar nan kawai sai hankalinta ya koma kan shi "Kai ma ina buƙatar dogon nazari domin gano ka." Ta ce a fili, sai kuma ɗiil ta ji shigowar saƙo wayarta, janyota ta yi ta hau dubawa........
09036257038
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
22
"Yau baccina har da munshari, saboda na ga sanyin ruhina har ma mun haɗa ido da kyawawan idanuwanta."
Ta yi shiru tana bin saƙon da ido cikin nazari. "Kenan shi ne wanda na gani a kotu da yake ta kallona?" Ta tambayi kan ta.
Ganin za ta ɓata wa kan ta lokaci sai kawai ta bagarar da tunanin da faɗin "Ina da abubuwa masu muhimmanci da suka fi wannan." Daga nan ta shiga wata sabgar.
"A gajiye ta isa gida ta ƙarasa falon kamar ba ta son taka ƙasa, cikin tafiyar ta ta ƙasaita tana ɗaga hanci da shan ƙamshi, ko ta kan ma'aikatan gidan da suke ta kai kawo suka mata sannu da dawowa ba ta bi ba ta shige haɗaɗɗen falon nasu. "Hajiya Iklima na hakimce akan kujera tana waya ta bi ta da kallo. A ɗaya daga cikin kujerun ta zube tana sauke numfashi, sai da ta ƙare wayar sannan ta kai dubanta kan ta "Sannu ƴar lele" Ta ce cikin sakin fuska tana wani murmushi mai wuyar fassaruwa. "Yawwa Mum ya gidan"
"Lafiya ƙalau, kin kwaso gajiya ko? Haka kawai kika ɗorawa kan ki aiki mai wahalar da ƙwaƙwalwa kina mace" Ta ce tana canja fuska zuwa ta damuwa. "Ba haka ba ne Mum, aikin ƴan sanda abu ne mai kyau. Kuma mace ma tana da rawar takawa a fannin." Ganin ba ta kuma bi ta kan ta ba sai ma waya da taje dannawa ya saka ta ɗan yin murmushi kawai ta miƙe ta haura saman, don sam mum ɗin nata ba son aikin nan take ba kuma ko me za ta ce ba yarda take ba.
Da wani irin kallo ta bi bayanta tana taɓe baki. Sai kuma ta saki wani mamalacin murmushi mai ma'anoni da dama "Uhm yaro man kaza, mu cigaba da tafiya a haka dai" Ta ce a fili tana cigaba da abin da take yi. Ita kam tana haurawa saman kai tsaye ɗakinta ta buɗe ta shige. Kayan uniform ɗin ta tuɓe ta shige wanka, bayan ta fito ta saka marasa nauyi, wata doguwar riga ce mara hannu da ƙyar ta wuce gwiwarta, ko ɗan kwali ba ta ɗaura ba ta fito daga ɗakin zuwa ƙasan. Tana sakkowa shi kuma na shigowa falon.
Yaro ne da bai fi shekara bakwai ba, da gudu ya nufo wurinta jikinsa sanye da uniform "Aunty Nawwarata" Ya ce cikin zumuɗi "Oyoyo My Areef" Tana ƙarasa sakkowa suka rungume juna suna dariya, sai kuma ta ja shi suka zauna a kujera.
A lokacin direban da ya ɗauko shi ya yi sallama ya shigo, jakar shi ya ajiye da lunch box ɗin shi sannan ya duƙa ya gaida hajiya iklima ya juya ya fita. "Aunty yau kin dawo da wuri."
"Eh mana na riga ka dawowa ba, yanayin aikin ne haka" Ta ba shi amsa "Ai Auny Nawwara ina jin daɗi da kika zama ƴar sanda, na taka duk wanda na so ko ya taɓo ni tunda yayata ƴar sanda ce"
"Eh mana Auta duk wanda ya maka ban ce ka raga masa ba, ai kana da ni ba ka da case" Ta ba shi hannu suka tafa.
Mum ta girgiza kai kawai tana miƙewa tsaye tace "Idan kin gama ɗora shi a keken ɓerar ku taso mu ci abinci don tun ɗazu Safara'u ta gama shirya wurin.
"Bari a cire wa boy kayan tukunna,Talatu" Cewar Nawwara ta ƙarasa da ƙwalla wa mai aikin kira, ba jimawa wata mata ta shigo, rissinawa ta yi sannan ta ce "Ga ni ranki ya daɗe"
"Yawwa a je da Auta a masa abin da ya dace sai a dawo da shi." Ta amsa tana kama hannun shi suka bar wurin.
Kai tsaye ɗakinsa ta kai shi ta masa wankan yana ta wahalar da ita wai ba za a wanke masa fuska ba. Ƙarshe dole a haka ta bar shi ta sako masa shimi da ƙaramin wando sannan ta kamo hannunsa suka dawo falon.
Suna fitowa ta miƙe da sauri ta karɓe shi suka nufi wurin cin abincin, anan ma taɓara ya dinga zubawa yana zaɓe-zaɓe ita kuma tana ta biye masa.
Tana miƙewa shi ma ya miƙe, kai tsaye falon suka dawo suka zauna. Plasma ɗin da ke jikin bango tana ta aikinta, remote ya ɗauka ya canja tasha, sai ga shi a inda ake haska zaman kotun nan.
"Lah Aunty kalli" Ya ce da ƙarfi, yana waro ido kamar ya ga abin tsoro, da sauri ta ɗago don kan ta na ƙasa tana danna waya. Karaf idanunta ya sauka akan ta itama. Ɗan zabura ta yi da ta gan ta "Mum zo ki gani Aunty Nawwara ta zama biyu" Ya ce da ƙarfi, ƙarasa shigowa falon ta yi ta kai kallonta kan tibin da ya nuna mata, turus ta yi itama tana bin budurwar da ke tsaye da recorder a hannunta da alama ƴar jarida ce, ga kuma ita Nawwara da aka hasko sanye cikin kayanta na ƴan sanda tana ta masifa da su.
"Wacece wannan ɗin kuma da take kama da ke?" Ta mayar da kallonta kan ta "Yo ni Mum ta ina zan sani? Yadda kika gan ta haka ni ma na gan ta yanzu, sam ɗazun ma ban kula da ita ba da alama ma ƴar jarida ce masu nacin tsiyan nan." Ta ƙarasa tana hararar plasma ɗin.
"Amma abin da mamaki, kodayake ba a mamaki da ikon Allah, zan so ganinta a zahiri kuwa, don kamar ku har ta ɓaci" Kafin ta yi magana suka ji Nawwaran na faɗin "To masu bibiyarmu a wannan wuri anan muka kawo ƙarshe, na san kun ga komai da ya wakana ba sai na ƙara yi muku bayani ba. Daga taku Nuratu Attahir Mai nasara na gode."