Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
muhimmanci har ku yi wani abu akai to, idan kuma za ku manta aikinku ku bar abin ya tafi a banza shike nan."
"Madam ki yi haƙuri don Allah ina tunanin ba ta san matsayinki a wurin nan ba ne kum..."
"Shut'up you are very stupit, ka san ba na son yawan magana ko, ka wuce ku yi abin da na saka ku, ka ɗauki Sajen tukur da kofur Mudi ku je ku gudanar da aikin naku ku dawo ina jiranku" Ta daka masa tsawa "A yi haƙuri Maaah" Yana duƙawa sannan ya fara ƙwalla wa waɗanda tace ɗin kira, Nuratu na jiyo yadda take yi musu tsawar nan kamar ba su girme ta "Tarbiyya dai ta yi gardama anan, ai ni idan ban damu da kasuwa ba ko sautu ba na bayarwa, haka idan ban damu da bola ba ba na kai shara" Ta faɗa da ɗan ƙarfi yadda za ta jiyo ta tana ƙarasa ficewa daga ciki. Take kuwa Nawwara ta fara huci tamkar baƙin kumurci....
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
28
Tana nan tsaye wayarta ta hau ruri, ganin mai kiran ya saka ta ɗagawa "Ina kika tsaya ne shiru har yanzu?" Aka ce daga can "Wallahi na tsaya abu mai muhummanci ne, amma na kusa ƙarasawa in sha Allahu"
"To sai kin ƙaraso Allah ya taimaka" Suka yi sallama da Zaitun ɗin, a lokacin ƴan sandan suka ƙaraso, ta shiga motar bayan ta dakatar da matsu tsaron nata anan ta ce su jira ta dawo, su ma ƴan sandan suka shiga tasu sannan suka bi ta a baya, kwatancen ta dinga bi har suka isa wurin. Fitowa ta yi daga motar, tana nuna musu kangon da hannu.
Isa suka yi ƴan sanda biyu suka tsaya daga bakin kangon riƙe da bindiga ɗaya ya shiga ciki, sai dai wayam babu kowa a ciki, ya dinga bin koina da ido a ciki babu shi babu alamunsa.
Cikin sauri ya fito "Ba ya ciki fa da alamu ya gudu"
"Kamar ya ya gudu?" Suka haɗa baki, kafin su shiga cikin su ma amma babu kowa a ciki. A lokacin ta ƙaraso wurin itama cike da mamaki "Ta ya ya za a ce ya gudu bayan bai san za a zo kama shi ba? To ko dai ba nan suke nufi ba? Bari ina zuwa ku cigaba da duddubawa ko za ku ga wani abin zargi, bari na je na zo da yaran." Ta shiga mota "Ba ni makullin motar" Ta miƙa masa hannu "Bari na kai ki"
"A'a yanzu zan dawo ai" Miƙa mata ya yi ta tayar da motar ta bar wurin da gudu ya yin da su kuma suka cigaba da bin koina na wurin suna dudduubawa.
Ba a fi minti ashirin ba sai ga ta ta dawo ita da yaran su biyu, ga mamakinsu nan ɗin ne dai "To ai ba ya ciki, ko kun dawo ne kun faɗa masa abin da ya faru?" Ta tambaye su tana tsare su da ido "A'a ba mu dawo ba wallahi, ga cinikin nashi ma a aljihuna" Yaron ya fito da kuɗi ya miƙa mata, ta duba dubu uku ne da ɗari biyar."
"Guduwa ya yi, tabbas guduwa ya yi domin tunda ya ji su shiru zai zargi an kama su ne, da ma tun jiyan muka zo" Tana dafe kai "Gaskiya hasashen ki haka ne, tunda ya ji su shiru zai san an samu matsala dole zai gudu, amma za mu cigaba da saka ido anan ko Allah zai sa ya dawo daga baya, yanzu su nuna mana inda suke kai ta su siyar ko za mu yi nasarar samun wasu." Cewar Sajen tukur." Duk suka yi na'am da shawarar tashi, aka kuma saka yaran a mota aka tafi da su. A bakin kwarin suka tsayar da motocin, ta ce yaran da direban nata su jira su a mota, ita kuma ta fito da recorder ɗinta suka fara kutsawa cikin wurin.
Tun kafin su ƙarasa suka hango wasu matasa na ta shaye-shaye, lallaɓawa suka yi ta bayansu za su zagaye su. "Ga lakwayen nan fa mu yi ta kan mu" Ɗaya da ya hango su ya faɗa yana miƙewa cikin layi da niyyar guduwa kawai ya ji harbi a ƙafarsa, ya fasa ƙara yana riƙe ƙafa, ganin haka sai duk suka dakata suna ɗaga hannaye sama. Ɗaya ne daga cikin jami'an ya zagaya ya kwashe kayan mayen kaf sannan suka tiso ƙeyarsu.
Nuratu ke biye da su tana cigaba da ɗauka, sai da ta gama sannan ta zuge jakarta za ta mayar da ita, ba ta yi aune ba sai jin yanka ta yi a hannunta. "Ahhh! Ta saki ƙara tana riƙe wurin, kawai ya ƙara mata da igiya a goshi. Wanda ke gefenta ne ya shammace su ya zaro wuƙa a gefen cikinsa ya yanke ta. Ɗansandan ya saita shi ya sakar masa harbi a hannunsa cikin sauri.
Tuni jini ya wanke fuskarta ta durƙushe a wurin cikin azaba tana cije leɓe. Bakin bindigar ya kuma buga masa aka cike da takaicin yankan da ya mata, ya saki ihu yana zubewa a wurin sai ga jini.
Sannu kawai suke jera mata har suka samu ta miƙe suka ƙarasa jikin motar, cikin kiɗima direban ya fito lokacin da ya hango ta ta fito tana haɗa hanya ga jini na zuba "Me ya same ki hajiya, innalillahi wa inna ilaihirrajiun." Motar kawai ta shiga, ɗan sanda ɗaya ya shiga shi ma, aikuwa ya ja da gudu, su ma ƴan sandan duk a mota suka zuba su har na sumen suka bar wurin.
Kai tsaye asibiti ya nufa da ita ganin yadda take zubar da jini, ɗansanda ɗayan da ke tare da su yana ta jera mata sannu, yaran ma a motarsu suka zuba su suna ta kuka ganin halin da ta shiga.
Su police station ɗin suka nufa yayin da ita kuma aka yi asibiti da ita. Suna isa suka yi karo da Nawwara tsaye a bakin ƙofar, tana jin tsaiwar motar tasu ta fito "Ya kun same shi?" Suka girgiza kai "Ba mu same shi ba ya gudu."
"Aikin banza, ku kuna wanne shashancin har ya gudu kafin ku je, ta ya ma ya san za ku je ɗin da har zai gudu, kawai ba ku san aikinku ba malamai, ko kuma waccen yarinyar ta yi wasa da hankalinmu ne kawai." Ta balbale su da faɗa, su kuma duk sun sunkuyar da kawunansu ƙasa, a lokacin ɗaya ya koma motar ya fara fito da su "Waɗan nan fa" ya kuma sara mata kafin ya ce "Masu shan miyagun ƙwayoyo ne muka kama, da taimakon yaran nan da kuma goyon bayan ƴar jaridar, yanzu haka ta haɗu da tsautsayi wannan ya yanke ta a hannu da goshinta an tafi da ita asibiti ba."
Sai lokacin ta saki ranta har da sakin murmushi "Daidai kenan, wannan abu ya yi daɗi, an yi mimi maganin iyayinta." Suka kalle ta da sauri "Maah ta ji rauni fa sosai tana ta zubar da jini, yanzu haka Sajen Tukur na tare da su saboda likitocin za su iya cewa sai da ɗan sanda za su karɓe ta" Kafaɗa ta ɗaga irin ko a jikin nan nata ta shige ciki. Ya girgiza kai kawai don ya lura akwai ƴar tsama a tsakaninsu ga shi kuma kamar su ɗaya.
"Sir zaɓe fa ya fara ƙaratowa ya kamata mu yi wani abu akan matsaltsalun da al'umma suke ciki."
"Wannan ai a zaune take, lokaci ya yi da za mu mayar da hankula kan ayyukan da za su dadaɗawa kowa, ciki har da abin da ya yi musu tsayuwar ƙayar kifi a maƙogaro na rashin tsaro."
"Aikin ka na kyau Sir, daɗina da kai ba ka bari kan ka ya yi murfi"
Ya yi dariya "Haba dai kamar ban san me duniya take ciki ba? Ita siyasa ai sai ka iyata take ɓullewa da kai, tuni na gama tsara komai kuma koman zai tafi cikin nasara, kasan su al'umma kamar kaji suke, da ka watsa musu tsaba shike nan, yanzu a shirya mana zama da yaran can mu yi magana, ya kamata a ɗan tsahirta ta ɓangaren nasu su ma. Sannan akwai zama na musamman tsakanina da shugaban ƙaramar hukumar ku da kuma duk wasu masu muƙamai,ka dai haɗo mini duk waɗanda kasan ina buƙata idan irin hakan ta taso, dole ne sai mun yi da gaske tun kafin maƙiya su yi galaba a kan mu"
"An gama ranka ya daɗe" Suka yi dariya.
Bayan isar su asibitin da wuri likitocin suka karɓe ta tunda akwai ɗan sanda tare da su aka yi ciki da ita. Cikin sauri direban ya yi ƙoƙarin kiran Mamy a waya don su san halin da ake ciki. Tana ɗagawa ya faɗa mata Nuratun ce ta ji ciwo suna asibiti, take ta hau sallallami tana tambayar garin ya ya? Ya ce ta zo ɗin dai, take kuwa ta kira daddyn nasu ta sanar masa, a ruɗe ta fito Nura na riƙe da jakarta suka taho tana ta cigaba da sallallami.
Kusan lokaci ɗaya suka isa da daddyn don yana ji shi ma ya taho. Lokacin da suka iso tana bacci, an mata duk abin da ya kamata, goshinta liƙe da bandeji sai hannun. Sai ruwa da aka jona mata, gabaɗaya sun kaɗu da jin wai wani ɗan daba ne ya sare ta, kuma ta zubar da jini sosai dole sai an ƙara mata jinin. "Me ya haɗa Nuratu da ƴan daba kuma ita da ta tafi aiki?" Cewar Mamyn a ruɗe, wayar Nuratun ta hau ruri, mamyn ce ta ɗaga sai jin Zaitun ta yi tana faɗin "Wai har yanzu ba ki kammala abin da kike yi ba jiran ki fa nake yi"
"Ba ita ba ce Mamyn su ce, tana asibiti yanzu haka"
"Asibiti kuma? me ya same ta to?" Ta tambaya a ɗan ruɗe
"To mu ma dai haka muka ji yanzu haka muna can ta haɗu da tsautsayi ne"
Take ta ce gata nan zuwa bayan ta ji asibitin. Tana sauke wayar ta dubi daddyn nasu "Ka ji ba ta je ma wurin aikin ba kwata-kwata."
"To wai ni mene amfanin masu tsaron da na sama mata ne? Ta ya ya suna tare da ita har za su bari wani ya ji mata rauni haka? kenan albashin banza nake biyan su, dole su ajiye mini aikina tunda baza su iya ba?" Ya ce cikin faɗa, mamyn dai ta yi shiru tana tunanin abin da zai haɗa ta da ƴan daba, har su mata wannan yankan. Waya daddyn ya zaro daga aljihunsa ya shiga kiran ɗaya daga cikin masu tsaron nata....
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
29
Yana ɗagawa cikin faɗa daddyn ya ce "Duk inda kuke ku zo nan asibitin ku same ni yanzu." Bai jira cewar shi ba ya kashe wayar, daga can ya kalli ɗayan gabansa na ɗan faɗuwa "Ka ji Yallaɓai ke kiran mu wai mu je mu same shi suna asibiti, Allah ya sa dai ba wani abu ya same ta ba don na ji sai faɗa yake ta yi."
"Kai! Yarinyar nan fa kar ta ja mana matsala, shegen taurin kai gare ta wallahi, yanzu kira shi mu ji asibitin da suke." Ba musu ya kuma kiran daddyn, sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga, sunan asibitin ya nemi ya faɗa musu, yana faɗa ya kashe wayar wayar shi.
Likitan ya buƙaci su je a gwada jinin su a gani na wanda zai yi mata. Na Mamyn ya yi, amma da aka gwada na Nuran sai likitan ya ce a ɗau nashi tunda shi ne namiji. Ba musu ya bada, aka je aka saka mata. Daddyn yana tsaye ya hango shigowarsu asibitin. A tare suka nufo wurin nasa suka duƙa suna gaishe shi. "Ku ba ni makullan motar, ku kama gabanku, daga yau na sallame ku zan nemo waɗanda za su iya kula mini da rayuwar ƴata."
"Alhaji ka yi haƙuri don Allah wani abin ne ya same ta? Wallahi ba laifinmu ba ne, da ma ba ta so muke biye da ita duk inda za ta j...."
"Rufe mini baki, ba laifinku ba ne laifinta ne kenan, da kun san aikin ku za ku bar ta ta matsa ko nan da can ne ita kaɗai? A ce na ɗauke ku saboda tsaron lafiyarta amma har ɗan daba mara hankali ma irin shi ya sare ta? Da ta rasa ranta fa? Ku godewa Allah ma iya sallaɓarku na yi da ban yi sharia da ku ba tunda amana na ba ku kuka ci. Ku wuce ku ba ni wuri mutanen kawai."
Suka ɗuka suna kuma bada haƙuri sannan suka tafi cike da takaicin abin da ya musu bayan ba laifinsu ba ne, sun so bin su ta ce su jira ta a nan bakin police station ɗin kuma shiru ba ta dawo ba, sai kawai suka wuce can departiment ɗin nasu ko wucewa ta yi amma ba su ga motar da suka tafi tare da direban ba, to a can daddyn ya kira su. Suna tafiya ya juya cikin har lokacin ran shi a ɓace yake, suka zauna shi da Mamyn suna jiran farkawarta, a lokacin Zaitun ta iso asibitin itama.
Alwala Hafsat ke ɗaurawa mahaifiyar tasu daga kancen da take, bayan ta gama mata ta karɓi hijabin hannun Asma'u tana ƙoƙarin saka mata. Da ta gama ta ɗan jingina ta kafin ta ce "To Mama an gama, ki yi niyyar sallahr azahar ɗin sai ki yi a hakan" Ta yi shiru tana kallonta "Ko na mayar da ke kwancen ba ki ji daɗin zaman a haka ba?" Ga mamakinta sai ta ga idonta na tara ƙwallah. "A'a mama don Allah kar ki yi kukan nan, bari na kwantar da ke kar ki gaji." Ta mayar da ita kwancen Asma'u ta gyara mata ƙafafunta, samnan suka matsa gefe domin ba ta damar yin sallahr bayan ta yi ƙoƙarin mayar da hawayenta. "Allah ya ba ki lafiya mamanmu, shekara da shekaru mutum na kwance akwai gawjiya walllahi, Allah ya sa ya zame miki kaffarar zunubanki" Cewar Asma'u idon ta na kawo ruwa, girgiza mata kai Hafsan ta yi. Sannan ta amsa da "Amin dai"
Wani matashi ne ya shigo gidan cikin wata irin shiga, wandon ma iyakarsa cinya, ga wani shegen aski a kan shi, leɓen nan baƙiƙirin. "Ke Hafsat karɓi kazar nan ki gyara mini ita."
Yace cikin wata murya ta ƴan ƙwaya. "Hafizu a ina ka samu kaza?" Ta tambaya "Ina ruwanki da inda na samu, kawai ki yi abin da na ce." Yana cigaba da miƙa mata, sai ta noƙe hannu "Wannan kazar fa kamar na san mai ita a unguwar nan, gaskiya ka sakar musu kazar su ni dai ba zan karɓa ba."
"Ke! Ina saka ki abu kina mini gardama?" Ya yo kan ta ta kuma matsawa baya "Wallahi ni ba zan gyara abin sata ba, ya za a yi ka sato kaza ka kawo mini wai na gyara maka Allah ba zan gyara ba" Tace cikin dakiya "Kar Allah ya sa ki yi, Asma'u ke karɓi ki gyara mini ita tare za mu raba naman da ke ko ƙafa baza ta ci ba." Da sauri ta matso jiki na rawa ta karɓa "Yawwa ƙanwata, bari na sayo magi da kayan miya sai na zo na yanka ki mana dafkenta." Ya juya zai fita, sai kawai suka haɗa ido da maman da ke ta bin shi da kallo, ya ɗan sosa kai "Sannu mamanmu" Ya juya ya fice.
Yana fita Hafsat ɗin ta galla mata harara "Ke yanzu dafa masa ɗin za ki yi bayan kinsan ta sata ce?"
"To ya zan yi da shi Aunty Hafsat? Ni fa wallahi mugun tsoron shi nake yi."
"Ban gane kike tsoron shi ba wanene gaba da wani a cikinku? Ca nake ƙaninki ne, kuima sai yake ba ki umarni kina bi cikin rawar jiki ko da ya saɓa wa mahalicci? To tare za a raba muku alhakin ke da shi"
Ta yi shiru, sai kawai ta ji Hafsan ta fizge kazar daga hannunta kawai ta sake ta "Wallahi baza ku ci haram ba ina kallo, daga yau ko me ya kawo an daina karɓa a gidan nan tunda mutanen unguwa sun gano shi sun ce ɓarawon kaji da agwagwi ne." Tana sakin kazar kuwa ta kora ta soro ta buɗe gidan, kazar kuwa ta fice da gudu. Baki Asma'u ta riƙe tana zaro ido domin ta san abin da zai biyo baya idan ya dawo daga cefanen kaza ya tarar an mayar da kaza.
"To wannan dai shine bayanin da ma, umarni aka bada daga sama, yanzu kuma duk za ku kama gabanku ne, sai lokacin dawowa fagen daga ya yi za ku dawo a ɗora daga inda aka tsaya, amma yace wanda zai yi wani aikin a wannan tenuwar tare da shi yana maraba. So ku za ku iya zuwa amma ni ina da abuwa da nake gabatarwa a gefe dole akai zan mayar da hankalina, idan kuma za ku yi wata sanaar ne sai ku yi amfani da wannan kuɗin da na ba ku."
"To babbaaa godiya muke, za mu