Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
da yake yi. "Ina da kuɗi nawa kuke buƙata ku rabu da ni na tafi?" Ya tambaya.
"Duka kuɗin hannunka da na accaunt ɗinka za ka tattaro ka ba mu, sannan ka haɗa mu da wani mai kuɗi a danginka idan iyayenka ba su da shi ya fanshe ka." In ji Maiyagi
"Wabillahillazi kaf danginmu talakawa ne, babu wanda za a kira a nemi ya bada kuɗi ya fanshe ni, kuma ni yanzu ba ni da numbersu ba su da tawa, na yi shekaru rabona da garinmu, ko nawa kuke buƙata ni zan biya."
"Mu ga wayar shi" Gadanga ya faɗa cikin miskilanci, ciro ta suka yi suka miƙa masa, sai dai ga mamakin shi babu layi a wayar. "Ina layukan wayar" ya kuma tambaya
"Sun faɗi" Ya ce kan shi a ƙasa. "Ni za ka faɗa wa sun faɗi ina suke nace" Ya buga masa tsawar da ta ƙara razana shi. "Wallahi sun faɗi ba ni da layi ko ɗaya yanzu."
"Hmmm sun faɗi ko ka zubar" Ya saki wani malalacin murmushi yana tuno wani abu. "Ni ina da layin naka ai, akwai abin da na gano game da kai da ya haɗa da ƙyarya zamba cikin aminci da kuma cutarwa, ban damu da rayuwar mutum ba ko wani laifi da yake aikatawa da sai na ji komai daga bakin ka a yau kuma na haɗa ka da hukuma. Ku kai shi ɗaki na musamman ku ajiye kayan da safe zan duba." Daga haka ya fice a ɗakin.
Cukuikuye shi suka yi zuwa wani ɗaki suka watsa shi ciki sannan suka garƙame da kwaɗo. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya kwanta domin ya huta gajiyar da ya sha don ya yi aiki sosai a daren ranar, sai da ya rage kayan jikinsa, ya cire abubuwan fuskarsa sannan ya kwanta, sai dai baccin ya ƙi samuwa tunaninta ya cika masa zuciya.
Ko ya ya runtse idanun shi ita yake gani lokacin da ta ƙura masa ido da jajayen idanunta ga shatin yatsu a farar fuskarta da ya fito raɗau. Kallon da take yi masa ya fi kama da na tsana, abin da ke faɗar masa da gaba kenan. Inda ya gode ba ta ga fuskarsa ba, don ko yaransa ba wanda zai ce ga kamanninsa ko yaushe rabin fuskarsa a rufe take da wani jan ƙyalle idanunsa a zagaye da wannan abin na gwaska baƙi.
Wani tunani da ya faɗo ransa ne ya saka shi miƙewa zaune zumbur, tsai ya tsayar da tunaninsa wuri guda. Wannan shirin da ya saurara anya ba shi da alaƙa da wannan matashi da suka kamo? Ji ya yi yana so karo na farko ya aikata wani abin kirki a rayuwarsa.
A ranar ma yadda ya ga rana haka ya ga dare, aikam idanunsa duk a kumbure ya tashi. Tun a safiyar ranar ya saka suka fito masa da buhun ya zazzage su, ya dinga ɗaga kayan yana dubawa, sai kuma ya ware takaddun gidajen da filayen a gefe da kuma kuɗaɗen sannan ya mayar masa da kayan cikin buhun.
Da kan shi ya shiga ɗakin, yana ji an taɓa ƙofar ya zabura yana rarraba ido. "Mun samu takaddun kadarori da kuma wasu tsirarun kuɗaɗe. Yanzu muna buƙatar ka ba mu duka kuɗin cikin asusunka, sai mu sallame ka."
"Sai dai na ba ku ATM ɗin ku cire layin da na buɗe da shi na jima da yar da shi." Ya faɗa cikin nutsuwar da ya samu don ya gama tabbatar da kuɗi kawai suke so su ƙyale shi, kuma ya tabbata zai samu ninkin su nan ba da jimawa ba, don ya gama yanke Abuja zai tsallaka tunda manyan alhazawa sun fi yawa a can ɗin. Cikin sa'a kuwa a cikin kayan da suka tarkato an samu ATM ɗin har uku, nan suka ritsa shi ya faɗi pin ɗin.
Da ido Gadanga ya yi wa Mai yagi magana, sai ya ɗauki ATM ɗin ya fice, ya kuma yin magana da Maiyagi da idon shima, kai ya gyaɗa alamun gamsuwa, daga nan ya juya ya fice a ɗakin bayan ya damƙa masa waya a tafin hannunsa.
Can bayan kamar minti talatin ya dawo da kuɗaɗen da ya ciro a wata baƙar leda. Sai da Maiyagi ya leƙa ya gani sannan ya ce masa ya tashi su tafi. Har ya yi gaba yace ya dawo ya ɗauki buhun kayansa. Ya duƙa ya ɗauka daga nan ya ɗaure masa fuska katamau ya fice da shi a gidan.
Bayan ya hau mashin ɗin ya ɗora masa buhun a cinya sannan ya ɗaure masa hannuwa shi ma ya hau ya fige shi da gudu. Sun ci tafiya mai nisa sannan ya tsaya ya sauka. Buhun ya buɗe ya saka masa wayar a ciki bayan ya kunna ta, sai ya kunce masa hannuwan sannan ya koma ya haye mashin ɗin ya bar wurin da gudu.
Yana ji an kunce hannunsa ya yi saurin since ƙullin idonsa. Waige-waige ya shiga yi amma bai ga kowa a wurin ba face bishiyu, sai kawai ya ɗau buhun ya saɓi sauri har ya fito titi.
Sam babu ababen hawa a titin, kamar daga sama ya hango Napep na tahowa, ya dinga ɗaga masa hannu da sauri har ya tsaya. Hayewa ya yi da sauri, shi ma mai Napep ɗin bai tsaya tambayar inda za shi ba ganin yanayinsa ya ja suka tafi. Sai da ya ji shi a ciki sosai sannan ya fara samun nutsuwa. A lokacin ya samu damar faɗa masa inda zai kai shi.
A ɗaya ɓangaren kuwa wata alama ce ta fara bayyana a jikin na'urarsu tare da wata ƴar ƙara, cikin sauri ɗaya ya miƙe ya isa jikin naurar, tabbas kuwa lambar ce da suka ɗau lokaci wurin kasawa da tsarewa ta fara aiki. Cikin sauri na tsayen ya ɗaga waya ya kira wata number. Sai da ta kusa tsinkewa aka ɗaga. Ko gaisawa bai bari sun yi ba ya fara faɗin. "Alhaji Tajuddeen lambar nan fa da ka bada ta fara aiki yau, yanzu haka ga shi nan wayar a kunne take."
"Maza-maza ku yi wani abu akai kar ku bari damar nan ta wuce" Ya faɗa cikin sauri bayan ya miƙe tsaye a zabure.
Katse kiran ya yi ya fara kiran wani abokinsa, yana ɗagawa ya sanar masa abin da ake ciki. Da kuma inda za su haɗu, daga nan can ɗin ya nufa shi ma.
Kusan lokaci guda suka isa a lokacin tuni sun yi nisa a aikin har sun gano inda wayar take. Jamiai biyu aka ɗauka sai shi Alhajin da maaikacin ɗaya suka tafi.
Bibiyar inda wayar take suka cigaba da yi.
A wannan lokaci ne shi kuma suka iso, a bakin lungun ya sauke shi, sauka ya yi da buhun nasa ya nufi cikin lungun cikin sassarfa. Makullin da suka ba shi ya saka ya buɗe gidan ya shige.
Mai Napep ɗin na tsaye yana jira ya fito ya kawo masa kuɗin shi ya ga mota ta tsaya a bakin lungun, mutanen da suka fito daga motar ya bi da kallo, aikuwa suna shiga ciki ya ja adaidaitan shi ya bar wurin da gudu bayan ya saki wani malalacin murmushi. A daidai ƙofar gidan nasa suka tsaya, ana tunanin wanda zai fara shiga. Ƴan sandan su biyu ne suka shige da sauri. dama ƙofar a buɗe take bai rufe ba.
Shi kuwa tun shigarsa cikin sauri ya hau haɗa kaya yana tura wa a buhun, duk wasu abubuwansa masu muhimmanci ya fito da su, tunaninsa kayan gadon da suke ɗakin ta yadda zai sayar da su cikin ƙanƙanin lokaci ya haɗe kuɗinsa, har ya fara tunanin ya bar su kawai, to amma babu kuɗi isassu a hannunsa da za su kai shi abuja, .
Yana cikin wannan tunanin kawai ya ji an shigo gidan. Bai yi aune ba aka shigo ɗakin, cikin sauri ya saki kayan hannunsa ya ɗaga hannuwa sama "You are under arresting" ɗaya daga cikin jamian ya faɗa yana saita shi da bakin bindiga. "Ku bincike mini gidan ku fito da kowa da komai" Ya kuma faɗa, baki ya buɗe zai yi magana ya dakatar da shi "Kana magana zan fasa kan ka, da ganinka ba ka da gaskiya. Kai ku zazzage mini buhun nan na gabansa." Daga shi suka yi suka juye a ƙasa komai ya yi filla-filla. Wani irin yankewa gaban Alhaji Tajuddeen ya yi ya faɗi, yayin da duk suka zazzaro ido kamar sun ga abin tsoro.....
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS
Writers Association
(WOW)
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(16)
Budurwar na zaune a bayan adaidaita sahun ta bada hankalinta kacokam a kan shirin da mai napep ɗin yake saurara. Ba ta ji ya farkon yake ba tararwa kawai ta yi ana yi amna jikinta ya yo sanyi sosai.
Ana zuwa ƙarshen labarin ta yi saurin dunƙule hannayenta tana ɓoye su a bayanta cike da tsoro, tana zazzare ido, ji take kamar hannuwanta aka yanke, sai kuma ta kai kallonta kan kayan da suke cinyarta. Take ta shiga tunanin ta yadda ta same su.
Amaryar da ta tare a unguwarsu ce almajiri ya mata wanki ya shanya a rilarta. Ita kuwa tun da ta gani take ta fakar idon mutane tana son ko kala ɗaya ne ta samu ta samfe, ba ta samu wannan damar ba sai bayan sallahr magriba. Ta saɗaɗa ta shiga gidan ga zatonta kuwa ba kowa a rilar sai kawai ta ja wata doguwar rigar abaya da ta sha stone, da ganin rigar mai tsada ce. Ta naɗe ta a hijabi ta fice wuff ta faɗa gida.
Mahaifiyarta na sallah hakan ya ba ta damar shigewa ɗakinta da rigar ta cukuikuiyeta ta ɗora filonta akai. Allah-Allah ta dinga yi gari ya waye ta fita da rigar domin kwana biyun ba ta samu kuɗin kashewa ba saboda kaffa-kaffa da ta lura matan unguwar tasu sun fara yi da kayansu.
Da safe kuwa ta samu leda baƙa ta saka a ciki ta ɓoye sannan ta fito ta ɗora musu abin kari. Bayan ta gama ta hau gyaran gidan, sai da ta kammala tsaf a lokacin goma ta wuce sannan ta hau shirin fita. Ɗakin mahaifiyar tata ta leƙe da zumbulelen hijabinta "Mama zan leƙa gidansu Aisha yanzu zan dawo"
"To" Kawai tace mata ta cigaba da abin da take yi. Ɗaki ta koma ta ɗauki ledar ta fice. Idonta akan gidan amaryar da alamu ko tashi a bacci ba su yi ba ta bar layin. Tana fita titi ta tari Napep ta sanar masa inda zai kai ta wato unguwarsu Ramatu dillaliya.
Firgigit ta dawo daga tunanin da ta tafi "Don Allah bawan Allah a wacce tasha ce ake karanta labarin nan?"
Ya ɗan waigo ya kalle ta sannan ya yi dariya "Rigasa Radio kenan ake faɗa miki. Ai ni shirye-shiryen su ba sa wuce ni musamman na yarinyar nan Nuratu Mai Nasara, wannan shirin DANDALIN MARUBUTA ne, maimaici ne ma suka yi, na saurara jiyan amma yau ma na kuma ji saboda daɗin shirin nake ji."
Ta gyaɗa kai don ta lura yana da surutu mai Napep ɗin "Don Allah ko za ka taimaka ka kai ni gidan rediyo ɗin yanzu?"
Cikin mamaki yace "Inda za ki je kuma fa?"
"Na fasa can ɗin, gidan rediyon zan je ina son ganin wannan ƴar jaridar akwai maganar da zan faɗa mata mai muhimmanci."
"Ba damuwa in dai za ki biya ai sai a kai ki"
"Mu je ɗin ba zai gagara ba"
Daga nan ya juya akalar adaidaitan ya nufi can ɗin.
Tana tsaka da aiki a ofishin nata aka sanar mata tana da baƙuwa, tace a ba ta minti biyar ta ƙarasa abu. Sai kuma ta miƙe ganin ba zai kammalu a minti biyar ɗin ba ta fice.
Ta ɗan bi baƙuwar tata da ido, budurwa ce a ƙalla za ta yi shekaru ashirin tana sanye da hijabi da niƙabi. Tana ganin nuratun ta ɗage niƙab ɗin tana gaida ita, cikin sakin fuska ta amsa bayan ta nemi wuri ta zauna kusa da ita.
"Aunty da ma na saurari shirin da kika gabatar ne ɗazu na littafi, kuma shi ne ya sauya mini wata ɗabia da nake da ita a rayuwata. Amma kafin na cigaba na tsayar da mai adaidaita a waje ba kuɗi a hannuna, don Allah ko za ki ɗan ba ni na ba shi?"
"Ba damuwa" Ta ce tana zuge ƙaramar jakar hannunta ta zaro dubu ɗaya ta miƙa mata. miƙewa ta yi ta fita. Nuratun ta bi ta da kallo tana ɗan nazartar yanayinta. Ba jimawa ta dawo ta miƙa mata ɗari uku. "Ki riƙe" Ta ce da ita.
"Na gode Aunty." Sai kuma ta fito da ledar hannunta ta ce "Wannan labarin da kika karanta ya yi kamanceceniya da rayuwata, domin ni ma dai ina da ɗabiar nan ta son abin wani har tana kai wa na ɗauka na kuma karyar ko nawa ne na kashe buƙatar gabana."
"Kina nufin halin ɓera?" Ta tambaya tana ƙanƙance ido a kan ta. Kai ta gyaɗa tana ɗorawa "Tabbas hakan ne, sai dai ni a gida nake yi zuwa gidajen ƴan unguwa ban taɓa tsallake nan ba. Kuma a yau na tsorata sosai na kuma yi nadama in sha Allahu na daina ɗaukar abin da ba nawa ba. Yanzu haka wannan rigar ta amaryar layinmu ce na ɗauko jiya da dare da niyyar na kai ta kasuwa ko gidan dillaliya yau na siyar, to a hanyata na ji wannan labarin shi ne na fasa na nufo nan."
Ajiyar zuciya Nuratun ta sauke sannan ta ce "Gaskiya na ji daɗin faruwar hakan sosai, da alamu kwalliya na biyan kuɗin sabulu. Ina fatan za ki yi tsarkakkakken tuba da niyyar baza ji kuma aikatawa ba. Ki tuna duk wanda ya ɗauki abin wani ba tare da mai abin ya yafe masa zai biya shi a ranar gobe ƙiyama....!" Nan ta cigana da yi mata nasiha mai ratsa zuciya inda a ƙarshe ta ɗora da faɗin "Kuma ki cigaba da bibiyar shirin har ma da waɗansu shirye-shiryen musamman na tasoshin da ake ɗora labarai yanzu na zamani. Kin ga kamar tashoshin Umar Mai Sanyi, irin su Tsakar gida, limamin tsakar gida, tashar tsakargida duk idan kina bibiya za ki samu labarai masu ma'ana da faɗakarwa gami da wa'azantarwa. Kuma can cikakkun dogayen labarai ne ba kamar ni da nake karanta gajeru ba. Sannan Kuma ki nutsu ki ɗauki darasin labari ki kuma yi amfani da shi shi ne kin ci riba."
"In sha Allahu Aunty na gode sosai, idan babu damuwa ki ba ni numberki don Allah mu dinga gaisawa, sannan ki faɗa mini a inda zan samu tashoshin nan da kika lissafa."
"Da kin shiga cikin youthube kika yi serching na sunan tashar za ki samu, to a nan za ki ga littafai birjik sai kin zaɓa. Bari na ba ki katina har gidanmu idan kin so za ki iya zuwa, ni dai fatana yadda kika ce mini kin daina ɗaukar abun wani ya zama har abada hakan."
"In sha Allahu, na gode." Ta miƙe ta koma office ɗin nata, katin ta bata suka yi sallama ta tafi.
Cike da farin ciki ta zayyanewa Zaitun yadda suka yi da budurwar, itama ta ji daɗi sosai, daga nan ta je ta sanar wa Jagaba komai, shi kusan ma ya fi su jin farin ciki da abin, domin suna yawan samun saƙonnin jama'a na yadda ake ƙaruwa da shirin yadda yake sauya rayuwar mutane amma ba su tama samun wadda ta zo har nan ta faɗa kuma da gaske ta daina ɗin ba.
Suna cikin wannan farincikin wani ya kuma riskarsu na kama wannan ƴar damdarar da suke nema ruwa a jallo. Abin da ya ɗaure musu kai kuma da aka ce wai Namiji ne ashe ba mace ba. Take kuwa suka fice ɗauko rahoto don sun san labari ne mai zafi da zai yamutsa hazo. Sun tarar da unguwar a cike sai dai an ce tuni ƴan sanda sun tafi da shi, dole suka juya akalar su zuwa zuwa ofishin ƴan sandan, nan ma dai ba su samu ganinsa ba yana can ana tuhumar shi ga mutane da suka taru a gaban division ɗin.
A dole suka juyo duk yadda suka so ɗauko rahoto a ranar abu ya faskara dole sai sun bar wa goben.
Tana zama a ofishin ta saƙo na shigowa wayarta. Lambar ba suna kamar kar ta buɗe saƙon don har gajiya take da saƙonnin mutane, ko ta sauya lamba a banza ba ta san ta yadda suke kuma samu ba, sai kuma ta buɗe.
"Na san a halin yanxu kina cike da farinciki na tagwayen lamuran da suka kasance a safiyar yau, hakan ya sanya ni ma nake jina cikin farinciki fiye ma da ke.
Na shirya miki wannan farinciki ne domin fatana ki dawwama a cikinsa. Na hutar da ke na binciken da kike gudanarwa akan tauraruwa mai wutsiya, hakan ya sa na shirya masa gadar zaren da ya taka ya rufta har ga shi ya shiga hannu, namiji na shigar mata ya kuma ƙi magana a nufin baya yi shi kurma ne, yana yaudarar maza ƴan uwansa abin da ɗaure kai. Na bar ki lafiya. Ina miki fatan alkairi Alƙyabbar mata.
Wani bawan Allah."
Iya nan saƙon ya ƙare, ta maimaita ya fi sau uku. "Wani bawan Allah, wnene wannan? Me kuma yake nufi da saƙon nan na shi wai shi ya shirya komai?" Ta