Chapter 2 Reading Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat Arewa Novels

Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat

Author :  Hilfat Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 19

3K to 6K   out of 54.7K words

shige ta.

"Ka fa kiyaye ni Nura, sai ka fasa mata kai da waɗannan ƙwandala-ƙwandalan zobunan da suke hannunka, ka fita idona na rufe wallahi idan ba haka ba yanzun nan na hana fitar "

"Haba Mamyna ƴar baiwa mai farar aniya, kar mu yi haka da ke mana, yarinyar ce take shiga mini hanci da ƙudundune shiyasa nake fato ta. Uhmmm kin ga tafiyata na bar ku lafiya" Ya duƙa a gabanta kamar mai ruku'u cike da gwalangwaso, sai kuma ya juya zai fice.

"Wai ba na hana ka fita da ɗankwalin nan ba? Dawo ka cire shi."

"Kai Aunty, haba Auntyna, kin hana ni ɗaura zani firrr duk yadda nake ƙulafici na haƙura, kuma shi ma kallabin sai a hana ni ɗaurawa haka zan ke yawo tsirara-tsirara. Duk ƙawayen nawa fa da cikakkiyar suturarsu suke yawo kin san ita mace duk inda take da rufe jiki aka san t....!

"Jeka jeka don Allah, na ji tafi, yau kuma Aunty na koma, Allah ya shirya ka." Ta ce cike da takaici

"Amin Mamy godiya nake." Ya juya ya fice yana juya mazaunai, ajiyar zuciya Mamyn ta sauke ta raka bayansa da kallo tana girgiza kai.

Yana fita ya nufi parking space, amma bai ga direban nashi ba. "Kai ina Yawale yake ne?" Ya tambayi maigadi "Ya zagaya banɗaki ranka ya daɗe." Cewar maigadin. Wani kallo ya watsa masa yana ƙanƙance idanu, "Ban hana ka mayar da ni jinsin ku ba? Kai wanne irin mai kunnen ƙashi ne? Idan baza ka girmama ni ba ka kira ni da ranki ya daɗe ka bar shi kawai, amma kar ka kuma haɗa ni da jinsin maza ka cire ni a jinsin ƴan uwana mata eheee."

Yana gama maganar yana fari da ido gami da buga cinya, sai kuma ya nufi ƙofar fita. "Ba zan iya jiran sa ba yanzu haka kashi yake yi ga kashinsa kamar na danƙo sai ya kai magriba bai fito ba ni kam sauri nake yi, na hau Adaidaita."

Bai jira cewar maigadin ya fice daga gidan cikin tafiyar da ta zame masa jiki ta rangwada. Dariya maigadin ya yi sannan ya koma ya zauna yana girgiza kai.

Yana fita titi ya tsaya jiran Napep, sai ga wata ta taho ya tsayar da ita. "Wata budurwa ce da wani matashi a ciki. Kasancewar matashin ne a can ciki sai ta fito domin su su haɗe "Ai da kin yi zaman ki ma ƴar uwa."

"A'a kai ne za ka shiga dai ku haɗu sai ni na zauna."

Baki ya kama zai yi magana sai kuma ya kama ƙarfen ya shiga ya zauna, itama ta shiga Mai napep ya ja suka fara tafiya, duk da haka sai da ya yi abin da ya yi niyya "Amma ƴar uwata ban ji daɗi ba, wannan abu bai mini ba sam, lokaci ɗaya kika tsame ni daga cikin ku kika mayar da ni cikin su, to ki canja hali gidan wani za ki je."

Mamaki ya kamata sai kawai ta saki baki tana bin sa da kallo. Shi ma na kusa da shi ɗin juyowa ya yi ya zuba masa ido "Ka ga don Allah ka kalli gabanka kar ka haɗiɗiye ni don an siyar, kuma ka ɗan gyara zamanka na ga kana matse ni ka sake ka taɓa ni alƙur'an sai ka biya........!

NEXT

[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS

Writers Association

(WOW)

TURMIN DANYA

NA

FATIMA UMAR KAS

HILFAT

(3)

"Kuma wallahi ka taɓa ni sai ka biya." Ya ƙarasa da farfara ido hannun shi dafe da haɓa bayan ya rungume hannu ɗayan a ƙirji. "Kai malam kar ka mana sheɗanci a nan, zindiƙin ƙato da kai za ka ke wannan maganar, idan za ka koma yadda kake ma tun wuri ka koma don ba riba" Cewar na kusa da shi ɗin cike da jin haushi "Heeee yau na ga abin da ya ishe ni ɗuwawu ya mutu ya bar zani. Don Allah malam ka yi harkar ka na yi tawa ba na son shiga shara ba shanu, yo ni idan ban da ƙaddara ma me zai saka ni hawa Napep, kuma har da balagaggen namiji a ciki? Ai wallahi tallahi don ina sauri ne da ba zan taɓa hawa ba har ma zauna kusa da kai kana gogar mini cinya ba, don Allah ka ɗan haɗe ƙafarka wuiri guda."

Sai kuma ya koma kan mai adaidaitan "Mai adaidaita kalli gabanka don Allah ni kar ka haɗiɗiye ni, ko ka je ka ɓarar da mu" Ya ce ganin ya juyo shi ma yana kallon shi, sai kuma ya zaro wayarsa daga aljihu da take ruri ya kan ga a kunne." Mai Napep ya girgiza kai ya juya yana murmushi.

"Ƙawata ya garin ya gagarin gari ya kwana a cikin gari?" Ya yi shiru yana jin magana kafin ya ɗaura. "Wallahi ke dai bari ƙawata kin gan ni a adaidaita wai wata walima aka gayyace ni shi ne zan je, da ƙyar fa na samu aka bar ni a gida, wallahi shi yasa na matsu azumi ya zagayo saboda shi ba get, yawona nake ci iya son raina musamman da dare, amma yanzu kin ga fa duk inda magriba ta yi babu ni ba kuma fitowa waje sai washe gari." Ya kuma yin shiru yana sauraren abin da ake ce masa "Hmmmm kema dai kya faɗa ai ina zuwa ina kwana ina gajiya ya taro, to congratulation Allah ya sanya alkairi ya sa ta tsoron Allah aka yi. Da ya nuna mini wurin zama na zauna, yana tafiya zan miƙe na fito. Burina kawai ya gan ni dai na zo kasan tun ina dubai yake ta faɗa mini wannan walima, yana ta roƙon na zo shiyasa......Yawwa to kin gani, na masa alƙawarin zuwa kuma kasan shi kaya ne, na ce maka fa da kyar ta bar ni kuma ta ce kar magriba ta mini a waje ni ma kuma ina son taya ta kare mutumcina da take ƙoƙarin yi,.....Ato buƙatar dai ya gan ni na je shikenan na juyo..... Au haba wai faɗan kuka kuma yi? Kedai ƴar ɗagwas kamar kaji haka kuke, to ya za a yi ita Aunty Cleaner haka take sai dai a bi ta matsayinta na babba, wancen ma ni na kira ta gefe na mata nasiha na ce a dinga kai zuciya nesa ita duniyar ma duka nawa take yau mune gobe ba mu ba ne kuma....

"Ba a nan za ka sauka ba ne?" Ya tsinkayi muryar budurwar kusa da shi. "Ya isa haka mai Napep ai ban kula ba, nawa kuɗinka" Ya sauke wayar

"Ina za ka kula kana ta zuba sai kace kanyar da ba ta nuna ba?" Na kusa da shi ya faɗa "Ka ga ban kasa da kai ba ka rufe mini bakinka a nan, ka ja tsumman rayuwarka ba abin da ya shalle ni da kai." Ya ba shi amsa yana watsa hannu "Mun ji a je umma ta gaida ashsha." ya kuma faɗa

"Sai dai ta gai da uwani, na zauna ma kusa da kai duk ka ishe ni da warin rana, don Allah a dinga saka turare idan za a fito. Ƙawata na gode fa sosai, da na san gidan ku da tsulum za ki ga na kawo miki ziraya."

"Bakomai" Ta ce tana cigaba da danne dariyarta. Kuɗin ya biya shi sannan ya ja suka tafi, yana tafiya kuwa suka kwashe da dariya ita da mai napep ɗin. "Wallahi tunda ya fara maganganun nan dariya ke cina kar na yi na jangwalowa kaina shiyasa na dinga danne ta." Ta faɗa "Hmmm a dole wai shi mace ne, ni kaina dariyar nake yi ciki-ciki don ya yi mugun ba ni ita, ba ma da ya ce wa na bayan nan "Na ga kana ta wani mammatse ni to an siyar, kuma alqur'an ka kuma taɓa ni sai ka biya." Mai Napep ya faɗa yana kuma tuntsireww da dariya. Tsaki na bayan ya ja kafin ya ce "Ni kuma gabaɗaya ya gama ƙular da ni, ji nake yi kamar na mauje shi, ai ni na so ma an wuce da shi wallahi ina sane na ƙi faɗa masa."

"Kai dai Allah ya shirya kawai" cewar mai napep ɗin.

Ƙaton wurin cin abinci ne da ƴaƴan manya kaɗai ke zuwa wurin. Kowa harkar gabansa kawai yake yi, daga gefe wata tsaleliyar budurwa ce ta ci ado, suna zaune da wani Alhaji suna cin abinci hannunta ya sha jan lalle da baƙi. Ɗagowa ta yi suka haɗa ido sai ya sakar mata da ƙayataccen murmushi, take ta mayar masa itama amma nata mai maanoni ne da dama, da sai mai hankali zai lura. Hannun shi ya wara yana mata magana, sai ta ba shi amsa itama da hannun. Yadda suke maganar kurame ya tabbatar ɗaya ne kurman a cikin su. Sai da suka gama cin abincin sai kawai alhajin ya yafito wani daga gefe, yana zuwa ya ce "Nawa kuɗin ku?" Faɗa masa ya yi, sai ya miƙa masa ATM ɗin sa "Ga shi ku cire sai ka kawo mini. 2530 shi ne pin ɗin. Amsa ya yi ya juya ya tafi. Yana dawowa ya karɓa ya miƙe ya mata alamun ta miƙe itama. Ta shi ta yi suka jera suka fice a wurin.

Motarsa suka faɗa ya tayar suka tafi, a wani ƙato kuma haɗaɗɗen hotel ya faka motar suka fito. Sai da ya je ya kama ɗaki ya biya kuɗin komai sannan ya karɓi makullin suka nufi can. A gaban ɗaki mai lamba goma sha biyu suka tsaya, ya buɗe suka shige. Cire mayafin ta yi ta yasar a gefe, shi ma ya cire babbar rigarsa ya ajiye yana zama a bakin gadon "Da hannu ya mata alamun za ta watsa ruwa ne? sai ta gyaɗa masa kai amma ta ce shi ya fara yi. Tana kashe shi da wani murmushi. Ido ya kashe mata yana ƙarasa rage kayan jikinsa bayan ya cire komai dake aljihun nasa ya ajiye kan dirowa. Sai ya tura ƙofar bathroom ɗin ya shige. Ta bi ƙofar da kallo, jin alamun zai fara wankan ya saka ta miƙe zumbur ta fara harhaɗa abubuwan da ya ajiye, tun daga kan wayoyinsa zuwa ATM card ɗinsa, har ta ɗau makullin motar ta mayar ta ajiye. Zuge zif ɗin jakar hannunta ta yi ta zuba su a ciki tana yi tana kallon ƙofar banɗakin. Saɗaf-saɗaf ta doshi ƙofar ta buɗe a hankali ta fice. Daidaita nutsuwarta ta yi gudun a zargi wani abu ta nufi get kan ta tsaye ta fice a hotel ɗin. Cikin azama ta tare adaidaita ta faɗa ko faɗa masa inda zai kai ta ba ta yi ba ya ja suka tafi...

Tassss! Tatassss! Ya ɗauke su da mari lokaci guda, dafe kunci suka yi kan su a ƙasa. Wani irin ɓacin raine a fuskarsa, zuciyarsa har tafarfasa take yi ya kuma duban su a fusace "Wa ya saka ku wannan ɗanyen aiki? Yaushe kuka fara aiwatar da abu ba tare da na ba ku umarni ba?" Ya ƙarasa yana huci "Sorry Babba, mun ga iyayensu suna ta mana yawo da hankali ne shiyasa kawai muka aikata musu hakan saboda....!

"Shut'up, you are very stupid." Ban faɗa muku a cikin harƙallar nan babu kisa babu cin zarafin mace ba? Yanzu ba don Allah ya kai ni ɗakin ba haka za ku keta musu haddi ku ci zarafin su? Ina ni ne da kaina na ce mu bar su zuwa yau ɗin, ku jira ku gani abin da zan yanke mana sai ku je ku yi gaban kan ku?"

"Sorry gadanga hakan baza ta kuma kasancewa ba mun maka alƙawari." Cagwab ya koma ya zauna kan kujera yana furzar da wata iska mai zafi bayan ya sosa goshinsa. "Saarku ɗaya ban taɓa kama ku da laifi makamancin wannan ba, amma da ace kun cika mummunan ƙudirin ku a kan su da kun gane shayi ma ruwa ne kun kuma yaba wa aya zaƙinta. Bana son hakan ta kuma faruwa ko duka ban yarda da shi ba. A je a ba su abinci kuma a fitar da su can bakin hanya su tafi sun yi firi."

Ido suka zaro dukkanninsu, suna shirin magana ya ɗaga musu hannu "Bana son jin komai daga gare ku, kawai ku yi abin da nace kar ku kuma ɓata mini rai" Rissinawa suka yi suka masa godiya sannan suka fice.

Kamar yadda ya musu umarni kuwa abincin suka ba su, bayan sun ci suka ƙulle musu fuskoki da ɗankwali sannan kowanne ya goya ɗaya a bayan mashin, hannuwansu ma sun ƙulle musu ta baya sannan suka tafi da su, bayan sun rataya wasu manyan bindigu saboda shirin ko ta kwana. zuciyoyinsu babu daɗi, domin su dai ba hakan sukaso ba sun so su karɓi kuɗin fansar su don dai kawai ba su da ikon tsallake umarnin babba ɗin.

Sun yi tafiya mai nisa sannan suka ajiye su, hannun ɗaya suka sassauta ƙullin yadda za ta iya kuncewa, sai kawai suka haye mashinan suka bi ta wata surƙuƙin hanya suka bar a wurin a miliyan.

Wadda suka sassautawa ƙullin ce ta fara kiciniyar kuncewa, har Allah ya ba ta sa'a ta kunce, ƙyallen idonta ta zame, sai kuma ta nufi ƴar uwar tata ta kunce mata idon da hannun. "Mu yi maza mu bar wurin nan" ta ce tana damƙar hannunta. Aikuwa itama ta kama nata hannu suka saka gudu, gudu suke yi sosai har Allah ya ba su sa'a suka fito titi. Nan suka tsaya suna sauke numfashin gajiya. Allah ya taimake su suka hango wata akori kura ta taho, tun daga nesa suke ɗaga mata hannu har ta tsaya, kawai suka afka ciki suna magiyar ya taimaka musu masu garkuwa da mutane ne suka sako su. Jin haka ya sa suna hawa ya bar wurin da sauri.....

NEXT

09036257038 chat

[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CnzG3XBNvVVADJgRReevQQ?mode=gi_t

*WOMEN OF WORDS*

_Writers Association_

*(WOW)*

*TURMIN DANYA*

*NA*

*FATIMA UMAR KAS*

_HILFAT_

(4)

Tsaye ta yi a ɗakin nasa tana ƙare masa kallo, komai tsaf sai dai ɗakin ya fi kama da ɗakin mace duba da yadda aka cika gaban madubi da kayan shafa. A hankali ta dinga bin kayan kwalliyar tana kwashewa, sai da ta ɗebe tass iya turarukansa kawai ta bari sannan ta buɗe ƙofar ta fice saɗaf-saɗaf.

Ta ci sa'a ba kowa falon sai kawai ta mayar da spire keys ɗin inda suke ta shige ɗakinta da kayan, tana shiga ta zube su kan madubi tana bin su da kallo cike da takaici. Allah ya sani ba ta son wannan rayuwar da ɗan uwan nata ke yi, amma ta lura ya yi nisa ba zai ji kira ba Kwashe su ta yi ta zuba a leda ta wurga su can ƙarƙashin gado cike da dakiya domin dai ta san ta jangwalo tijararsa. Jakar da take ajiye takaddu masu muhimmanci ta janyo ta fito da su ta fara aikin da ke gabanta.

Alhaji Sammani cike da nishaɗi ya fito a bathroom ɗin, sai kuma ya yi turus ganin ba ta ɗakin. Waige-waige ya fara yi amma bai hango ta. Yana kallon inda ya zube abubuwansa ya ga wayam. Gabansa ne ya ɗan faɗi don haka da sauri ya nufi ƙofa sai kuwa ya ji ta a buɗe, a ruɗe ya fice yana cigaba da dudduba wurin har ya sakko wurin maaikatan hotel ɗin. "Ina yarinyar da muka shigo tare ɗazu kun ga wucewarta ne?"

"Ban kula ba gaskiya Alhaji" Ɗaya ya faɗa "Tabbas na ga wata budurwa ta fice ɗazu ban sani ba ko ita ce." Cewar ɗayan "Wanne irin kaya ne a jikinta?" Ya kuma tambaya "Baƙin less ne da jan mayafi." Ai tun kafin ya gama ji ya doshi ƙofar fita da sauri.

"Alhaji ba kaya a jikin ka fa"

Sai lokacin ya kalli jikinsa, daga shi sai gajeren wando, tsaki ya ja yana komawa ciki, kamar zai kifa, gudu-gudu sauri-sauri ya zira kayansa ya fito, ko rufe ɗakin bai yi ba ya ba su makullin ya ce su je su rufe. Motarsa ya faɗa ya fice a get ɗin yana dudduba ta amma ko mai kama da ita bai gani ba. Duk yadda ya so ƙaryata zuciyarsa da take faɗa masa ƴar damfara ce ta yashe shi ne ta gudu sai da ya fara gasgatawa, ga shi ko lambarta bai karɓa ba.

Rasa abin yi ya yi ma, tunowa da ATM card ɗinsa da ta haɗa da shi ya sanya gabansa yankewa ya faɗi. Sai kawai ya nufi banki duk da ya san lokaci ya ƙure.

Ƙarshe dai abin da yake ta fargabar sai da ya kasance domin ta yashe kuɗin bankin nasa kaf, hannu ya ɗora a ka kamar ya zunduma ihu haka yake ji. Motarsa ya koma ya ɗora kai akan sitiyarin motar yana tuno haɗuwarsu.

Wucewa zai yi cikin motarsa ya hange ta tsaye a bakin titi, tun daga nesa yake kallonta, take ya ji ta masa. Ya matsa gabanta ya taka burki. "Yammata ina zuwa haka?" Shiru ta yi tana kallonsa. Sai ya yi murmushi "Ai kin cancanci ki ja ajin girmanki ne ran ki ya daɗe, idan ba damuwa ki shigo na rage miki hanya mana". Yanzun ma kallonsa take yi sai kuma ta yi gaba. Kashe motat ya yi ya fito ya bi ta. "Bai

2 / 19