Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
/>
"Kai wai ita ce wannan ƴar jaridar mai ƙwaƙwar tsiya?" Tace cike da mamaki "Kin santa ne?" Mum ta tambaya "Na santa, za ki ga tana zaƙulo laifukan mutane tana yaɗawa, a wani gidan jarida take aiki, kuma tana shirye-shirye ma a gidan rediyo, ita ce wallahi na tsani yarinyar nan tun kafin na gan ta." Ta ƙarasa da jan dogon tsaki sannan ta ɗauki remote ɗin ta canja tasha ba tare da ta bi ta kan Mum ɗin mai cewa aikuwa ya kamata su ƙulla ƙawamce tunda kamar su ɗaya. "Allah ya kiyaye na yi ƙawance da wannan kucakar" Ta furta cikin jin haushi tana jin tsanarta na ƙara yawaita a ranta. "Aikuwa dai wannan ta wuce ki kira ta da wannan sunan, kina ganin mace fess ƴar gayu da ita?"
Tana jin Mum ɗin ta yi shiru tana saƙe-saƙe a ranta.
Bincike da son gano wasu abubuwa game da sifeta Nawwara shi ya dakatar da Nuratun daga abubuwan da ta saka a gaba, ta yi bincike cikin ƴan kwanakin har ta gano wasu abubuwan da suka dangance ta, a binciken da ta yi ta fahimci Nawwaran tana da jiji da kai da kuma taƙama, sannan wani bai isa ta bi shi ba sai dai ita a bi ta da duk abin da take so, uwa uba wulaƙanci da tozarci ga na ƙasansu domin ba ta ɗauki ɗan adam da daraja ba. A fili ta ce "Za ki yi wa wanda kika raina dai, amma ƙaryar mace ta juya ni wallahi ba a haife ta" Ta ce tana jin mugun tsanar halayenta a cikin ranta. Ta ƙudurce sai ta je ta same ta har ofishin da take aiki ta tattauna da ita, anan za ta gane alƙiblarta da wasu abubuwan da take son ganowa game da ita.
Yau suna zaune dukkansu a falon sun yi shiru, kana kallon fuskokinsu za ka san basa cikin yanayi mai daɗi, wayar daddyn ce ta hau ɓurari, ya ciro da sauri ya duba, ganin lambar ya saka ya kara a kunne yana shirin magana aka katse shi daga can "Yaronka na hannunmu mun kama su yau da yamma shi da sauran abokan nashi, yanzu haka suna hannunmu."
"Me ya yi aka kama shi? Faɗa mini don Allah" Daddyn ya tambaya a ruɗe "Sai dai idan ka zo ɗin sai ka ji komai."
Tambayar police station ɗin ya yi aka faɗa masa, take kuwa yace ga shi nan zuwa. "Me ya faru daddyn yara
"Kin ji Nura na hannun ƴan sanda wai an kama su ɗazu shi da waɗannan abokan shashancin nasa." cikin takaici
"An kama shi kuma? To me ya yi? Cewar mamy tana dafe ƙirji. "To ni ma dai ban sani ba sun ce idan na je na ji."
"To ai ba mu ga ta zama ba, yanzu ya kamata mu tafi."
"Wannan yaro, wannan yaro, kai!" Ya ja dogon tsaki yana juyawa ya fice fuuu, a baya mamyn ta bi shi bayan ta ja hijabin da ta yi sallah da shi ta saka, ita ma Nuratun bin bayansu ta yi tana kunce ɗankwalin doguwar rigar dake jikinta daga kan ta ta yafa. Duka suka ɗunguma direba ya ja suka tafi. Suna isa police station ɗin direba ya samu wuri ya tsaya. Daddy ne ya fara fita sannan mamyn. Ita ma Nuratun fitowa ta yi ta bi bayansu, tana daf da shigewa ciki ba zato ta ji ta yi karo da mutum, da sauri ta ɗago a lokacin itama ta kai kallonta kan wadda ta bige ta ɗin. Nan fa aka shiga kallon-kallo tsakani Nuratu da Nawwara.......!
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
23
"Ba kya ganin gaban ki ne? Ko ke makauniya ce?" Nawwara ta faɗa cikin izgilanci "Kin manta kurma ce kuma kuturwa, kamar dai yadda mai dattin hula ya zama a cikin al'umma." Cewar Nuratu zuciyarta na tafasa da rainin hankalin Nawwaran.
"Ke kin san da wa kike magana kuwa? Ko kin manta a inda kike?" Ta faɗa a zafafe "Na sani mana da mai ƙafa biyu mai yatsu goma nake magana a kuma caji ofis sai aka yi ya ya. Na ce sai aka yi ya ya?" Cikin ɗaga murya ta yi maganar, hakan ya ƙara tunzira Nawwara ta kai hannu za ta zabga mata mari tana faɗin "Kin san wanene ubana a garin nan kuwa? Ko a haka na fi ƙarfin raini a wurin mace kamar ki?"
Caraf Nuratu ta riƙe mata hannu "Kar ki kuskura ƙazamin hannunki da aka gina shi da haram ya taɓa jikina, wane uban naki idan ba ɓarawo ba."
Wani irin kururuwa ta yi ta cakumi wuyan Nuratu tana jijjigata da zaginta, a daidai lokacin Mamy ta dawo wajen ganin Nuratun shiru ba ta shigo ba, sai kawai ta hango wata sanye da kayan ƴan sanda tana janta zuwa ciki ita kuma ta turje ta ƙi motsawa. "Nuratu meye haka kuma me ya faru, ke da wa kuke faɗa?" Ta ce a kiɗime tana isa wurinsu. "Haka kawai ta ci kwalata tana jana wai sai ta rufe ni, da alamu kan nata akwai motsi." tace cikin halin ko in kula.
"Ni kike dangantawa da mara hankali? Wallahi sai kin yi nadamar sanina a rayuwarki, sai na ga uban da ya tsaya miki a garin nan, kuma dole sai kin yi kwanan cell yaui."
Hayaniyar nan ce ta saka wasu jami'an fitowa, da ƙyar aka ɓanɓare hannunta daga jikin wuyan Nuratun tana ta zage-zagen da za ka rantse taɓin hankalin gare ta.
Ciki aka koma da ita, itama Nuratun Mamyn ta ja ta ciki.
Sai bayan sun shiga ne ta ga fuskar Nawwaran sosai, da take zaune tana ta huci "Wannan ai kamar ku ɗaya Nuratu kalle ta ki gani" Ta ɗago ta ɗan dube ta sannan ta taɓe baki ta ce "Ni kam ban ga kamar ba Mamy sai dai ko idon ki ne ya miki gizo. Yanzu ya ake ciki da yayan?"
"I to daddynku dai na ciki suna magana da Dpo ba su fito ba tukunna." Ta bata amsa tana cigaba da satar kallon Nawaara da har lokacin take ta cika tana batsewa gami da harararsu..
A daidai lokacin kuwa daddyn ya fito DPO na biye da shi sai Nuran da aka sako a gaba jikin shi ba riga yana ta ciccin magani haɗi da rangwaɗa.
Da sauri ta isa wurinsa "Sannu yaya da fatan ba su dake ka ba, wai me ka yi ne?"
"Me na yi kuwa ban da mugunta da cin zali, ni ba kaza ba a kawo ni wannan wurin mai kama da keji akillace, har da cire mini riga kowanne ƙato yana gane mini ƙirji, wallahi an kalli Allah ya isa ban yafe ba." Ya ce cikin watsa hannaye yana harare-harare. "Kai ba ma son shirme da wa kake? Na kuma jin bakin ka sai na saɓa maka. Wuce mu je dallah" Daddyn ya faɗa, rigarsa aka miƙa masa ya karɓa ya saka yana cigaba da gunguni. Sai kuma idon shi ya sauka akan Nawwara da tun fito da shi idonta ke kan shi " "La'hailahaillallahu muhammdu ɗan Abdallah, kun ga abin da na gani kuwa ko idona ne" Ya kama haɓa yana cigaba da ƙare mata kallo, duk suka kai kallonsu inda yake kallo. Daddyn kan shi ya kaɗu da ganinta, sai ya kalle ta sai ya kalli Nuratu ya ma kasa magana, sai sauran ƴan sandan da ke ta tambayar dama su ƴan biyu ne?
Wurinta ya nufa ya kai hannu zai dafa kafaɗarta "Ƴar uwarm...." Tsawar da Mamy ta daka masa ce ta dakatar da shi "Kai duk inda ka je wai sai ka nuna halinka ko? Na kuma jin bakin ka ranka idan ya yi dubu sai ya ɓaci, wuce mu tafi dare na yi" Cikin faɗa, bai kuma magana ba ya juya yana karairaya domin tafiyar ta riga ta bi jikinsa.
Wani murmushi Nawwara ta saki da suka fice tana jijjiga kai gami da cije leɓe. Sai kuma ta miƙe ko bi ta kan masu tambayar abin da ya haɗa su ba ta yi ba ta fice tana huci. Motar ta faɗa ta fige ta da mugun gudu ta bar direban a tsaye. Yadda ta bar wurin ya saka su bin ta da kallo. "Allah mai iko, da ma aka ce duk mutum akwai irinsa a duniya to yau dai na gani" In ji Mamy. "Ni kaina na tsorata da ganinta ba abin da ya bambanta su."
"Abin kam da mamaki da kuma ɗaure kai wai jaka a akurki, kama sak sai kace an tsaga kara? Anya kuwa Mamy ba ƴan biyu kika haifa ba a asibiti suka ɓoye suka ce ɗaya c...."
"Dalla rufe wa mutane baki sakaran banza da wofi ko na saka da kai? Ba ka san yadda nake a ƙule da kai ba ko?" Daddyn ya daka masa tsawa, juyar da kai ya yi jikin ƙofa yana kallon waje. Nuratu na jin su suna ta maganar ba ta tanka ba, don ita yadda take jin haushinta har ba ta so a dinga cewa suna kama ma.
Suna isa gida ya nufi ɗakinsa "Na sallame ka ne? Dawo nan ka zauna ina da magana da kai" Daddyn ya ƙara faɗa cikin tsawa, sumi-sumi ya dawo ya zauna yana sinne kai kamar na kirki. "Wai me ya yi ne suka kama shi?"
"Hmmm suna can gidan wata ɓarauniya aka je kame aka haɗa da su, yo ɓarauniya mana da sunan dilllaliya, take siyan kayan sata a banza tana ɗaure wa ɓarayin ƙugun. Faɗa ne ya kaure tsakaninta da wasu mata wai sun sayi kayan gado a hannunta ta siyarwa wasu kuma ta hana su kuɗinsu shi ne suka je suka ɗauko ƴan sanda. Suka tarar an kawo mata kayan satar suna ciniki shi ne suka haɗa kaf waɗanda ke cikin gidan har da shi suka tafi da shi.
Daga yau kar ya kuma leƙawa ko bakin get ne har tsawon wata guda, kuma na haramta maka zuwa gidan, sannan na raba ka da waɗannan fitsararrun abokan masu hure maka kunne."
"Amma dadd..."
"Ban nemi jin ta bakin ka ba ka yi mini shiru anan wurin." Ya katse shi da sauri jin zai yi magana. Zama ya yi yana turo baki "Hakan shi ne daidai ai, kuma tunda rayuwar da ka zaɓa wa kan ka kenan sai ka je ka yi ta yi ai." Cewar mamyn tana harararsa, tashi ya yi ya tafi ɗakinsa yana gunguni, ita ma Nuratu nata ɗakin ta shige har lokacin zuciyarta ba daɗi. Nan suka cigaba da tattauna maganar daga baya suka sako maganar Nawwara da suka gani.
Sanata Inuwa Wakili ne a zaune a tanƙamemen falonsa, Hajiya Iklima na gefensa suna magana, can ya ce "Ƴar lele ba ta dawo ba ne?" Ta yi murmushi "Tana hanya kasan yanayin aikin nasu wani lokacin yana kai su magriba." Ya gyaɗa kai cike da gamsuwa kafin ya ƙara cewa "Gaskiya fa Iklima kwanyar ki na ja shiyasa nake jin daɗin shawara da ke."
"To ai abin da yakamata ne Sir, zamowarta jami'ar tsaro shi ne kariya a gare ka daga masu son ganin bayanka ta hanyar ƙirƙirar wasu abubuwan suna maƙala maka. Daɗindaɗawa an shiga an fita sun ba ta matsayin sufeta ta yankin nan, wannan tsarin shi ne daidai."
"Sosai ma, aiki da basira ai ya fi aiki da. Mu sauka can ƙasan kafin ta shigo sai mu ci abincin tunda tun ɗazu aka shirya wurin." Ƙasan suka dawo nan falo suna cigaba da tattauna batun yayin da Areef ke can gefe yana game a waya.
Tun kafin ta ƙarasa bakin get ɗin take danna wa mai gadin uban horn, da sauri ya zo ya buɗe get ɗin jin horn ɗin ba na lafiya ba. Yana buɗewa ta shige da gudu kamar za ta bi ta kan shi. Ya bi ta da ido kafin ya mayar da get ɗin ya rufe. Tana tsayawa ta buɗe ta fita a motar ba tare da ta kashe ta ba ta shige ciki. Duk suna zaune a falon amma ta haye saman a fusace ba tare da ta kula kowa daga cikinsu ba. Duk suka bi ta da kallo "Ita kuma lafiya?" Mahaifin nata ya tambaya "Ba ƙalau ba, bari na je na ji" Mum ɗin ta faɗa tana miƙewa tsaye ta haura saman itama. Sai dai tana taɓa ƙofar ta ji ta a rufe "Nawwara, ke Nawwara buɗe ƙofar nan" Ta ce tana bubbugawa, maimakon ta buɗe sai ji ta yi tana ta watsi da kaya a cikin ɗakin tana faɗin "Sai na kashe ta, wallahi sai na kashe ta ni ce ajalinta." Ta cigaba da watsi da komai masu fashewa na tarwatsewa "Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, Nawwara kina cikin hankalin ki kuwa? Ki buɗe ƙofar nan na ce miki." Ta ce cikin tsawa. Jin ba ta da alamun buɗewa kuma ba ta fasa abin da take yi ba ya sanya ta sauka ƙasan a sukwane "Sir ta so mu je ko za ta saurare ka kai, ta ƙi buɗe ƙofar kar ta yi wa kan ta illa." Cikin sauri ya miƙe shima da nufin hawa saman.....
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
24
Sallamar da aka yi a bakin falon ta saka suka kai kallonsu wurin. Direba ne ya shigo ya rissina yana gaida su "Me ya faru ne wai a hanyar taku?" Ya jefa masa tambayar.
"Ba tare muka dawo ba, na je ɗauko ta amma sai ta shiga motar ta taho ta bar ni tsaye a can, da alamu a wurin ne aka ɓata mata rai. Na tari adaidaita sahu na biyo bayanta sai na zo na tarar da motar a tsakiyar gida kuma ba a kashe ba. "
Ya yi shiru alamun ya gama "Za ka iya tafiya." Juyawa ya yi ya fice bayan ya rissina, shi kuma ya bi bayan Mum ɗin don ta jima da hayewa saman...
Abin da ya faru tsakaninsu a police station ɗin nan ya tsaye mata a rai, so take ta gano abubuwa da yawa game da ita tunaninta ta inda yakamata ta fara domin jikinta na ba ta da wata a ƙasa, da wannan tunanin ta ƙarasa shiryawa cikin wani marun ɗin bowl ɗin ta da ya yi matuƙar karɓar fatar jikinta, ta kashe ɗaurin da ƴan matan yanzu ke ya yi. Ƙaramin mayafi ruwan ƙasa mai duhu ta ɗora a kafaɗarta, ta feshe jikinta da turare. Ta tsaya gaban madubi tana ƙare wa kan ta kallo.
Nuratu kyakykyawar mace ce ƴar kimanin shekaru ashirin da uku, mai kyawun fasali da surar jiki. Ƴar jarida mai ƙwazo da jajircewa akan aikinta ba tare da shakka ko tsoron wani ba.
Sallama ta yi musu ta fice da sauri ganin lokacin na shirin ƙure mata. Mota ta faɗa suka fice a gidan. Kai tsaye office ɗinta ta wuce ta fara shirya abubuwan da za ta yi, daga nan ta shige studio ɗin. Sai da ta datse kofar sannan ta gyara zamanta ganin saura munti biyu lokacin ya cika. Ta riga ta zaɓo labarin da za ta karanta, don haka ta buɗe shi kafin ta nutsu sosai a gaban mic ɗin ta fara magana.
"Masu saurarena barkan ku da warhaka, sannunku da jimirin bibiyarmu a cikin wannan tasha a kuma cikin wannan shiri naku mai farin jini na Dandalin marubuta. inda a yau ma muke tafe da labarin da za mu karanta mai suna WUTAR ƘIYAYYA. Ku biyo ni a cikin shirin domin jin shi kuma saƙom da yake son isarwa.
Wutar Ƙiyayya
Hannayena duka biyun na ɗora a kai sannan na taƙarƙare na rusa wani ihu da iya ƙarfina tamkar zan ɓare bakina gida biyu. Maimakon ya rage mini raɗaɗi da zugin da nake ji cikin raina sai ya ƙi ba ni haɗin kai, sai ma wani zafi mai turiri da nake jin shi a ƙirjina tamkar ana hura wuta tsakanin shi da zuciyata.
"Ki yi haƙuri Bintu, addu'armu kawai take buƙata a halin yanzu. Dole haƙuri za mu mayar mayafinmu, domin Ubangijin da ya ɗauke ta ya fi mu son ta. Ya Allah ka sanya wahalar da yarinyar nan ta sha na wannan jinya ta zama kaffarar zunubanta". Mahaifiyar Aishatu ta faɗa tana dafa kafaɗata kafin kuka ya ƙwace mata. A maimakon rarrashin da take yi mini ya sauƙaƙa zuciyata sai ya kuma tunzura ta ta hau azalzala ta. "A'a, ba ku za ku ba ni haƙuri ba, ni ce zan ba ku mama" Na ƙarasa ina sakin wani irin kuka mai gunji da nake yin shi da dukkan zuciyata tamkar wadda ake azabtarwa da ruwan dalma.
Na kalli yadda mata ke ta tururuwar shigowa yalwataccen ɗakin suna cin birki gaban gawar da take lulluɓe a likkafani cikin makara. Mu kuma duk mun yi tsaye cirko-cirko a kanta kamar zakarun da suka yi faɗa suka gaji muna ta koke-koke. Shigowar maza domin ɗaukar ta a miƙa ta gidanta na gaskiya ya kuma dugunzuma hankalina.
Kamar ana ingiza ni na yi caraf cikin tsananin ɗimuwa gami da tashin hankalin da ya rufto mini rana tsaka na ce "Wallahi ban yi da niyyar ta mutu ba, duk zatona a haka za ta dawwama, ga shi yanzu ta mutu, shi ke nan ta rataya a wuyana, na