Chapter 14 Reading Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat Arewa Novels

Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat

Author :  Hilfat Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 19

39K to 42K   out of 54.7K words

shiga uku!"

Gabaɗaya mutanen cikin ɗakin suka ɗauki salallami, yayin da mahaifiyarta da mijinta suka daskare tsaye sake da baki da hanci suna bi na da kallo tamkar baƙauyen da ya ga majigi.

Shi kam maigidana wani murmushi ya saki mai ciwo yana girgiza kai.

Ban damu da yawan mutanen da ke wurin ba na ci gaba da jaddada musu tabbas ni ce silar faruwar komai, domin ji nake yi kamar an matse bakina tare da tilasta mini tona wa kaina asiri, ina jin kamar idan ban fallasa ba zuciyata fashewa za ta yi.

"To kukan me za ki yi Bintu? Ai da ma haka kike so, domin na jima ina zargin ki a kan wannan baiwar Allahn, ƙarara kike nuna baƙincikin ki a kanta, duk da irin sha tara ta arziƙin da suka mana. To ai haka kike so sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha don daɗi." Maigidana ya faɗa a ƙufule kamar zai kai mini bugu, idanunsa sun yi jajir kamar gauta. Kafin ya bangaje ni ya fice a ɗakin yana faɗin wallahi sai na girbi abin da na shuka. Faɗuwa ce ta zo daidai da zama, domin yana ture ni na yi zaman daɓaro a ƙasa gabaɗaya jikina babu ƙarfi da ma, sai kawai na zauna dirshan na ci gaba da share hawaye da shuɗin hijabin da yake jikina.

Kamar fitar shi mutane suke jira suka fara la'anta gami da yi mini tofin alatsine, zagi kam na sha shi ya fi shurin masaki, ya yin da kunya ta rufe ni, kamar ƙasa ta tsage na shige ciki.

Take ƙwaƙwalwata ta soma tariyo mini abubuwan da suka faru tiryan-tiryan tamkar a faifan majigi.

Komai yana da sila, sanadin dai yawon haya ne da muke ta yi kamar wasu tsuntsaye. Ganin hakan ya sanya yaya Abubakar raɓa mu a muhallinsa.

Shi da mijina uwarsu ɗaya, ubansu ɗaya, kuma akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsu. Bayan tarewar mu a gidan matarsa Aishatu ta mana tarba mai kyau tare da burin kyautata mana. Yayin da ni kuma ba ƙaramin haushi take ba ni ba. Domin dai tun can ba na haɗa inuwa da ita idan mun haɗu, domin koyaushe zan ganta fes tana shiga tana fita kuma dangi kowa na nan-nan da ita saboda kyautar da take yawan yi musu. Wannan ya dasa mini tsanarta nake jin ta kamar kishiyata.

Ina son ganin na mata zarra a komai sai dai abu ya ci tura domin dai sama ta yi wa yaro nisa, saboda mijinta ya fi nawa rufin asiri nesa ba kusa ba. Haka nake ɗaga masa hankali tare da tilasta shi yi mini abubuwa kamar yadda ake yi mata, duk da yana iya ƙoƙarinsa don dai a zauna lafiya amma idona ya rufe. Domin ko na matsa ya mini ɗinki na shiga sabga sai na ga nata kayan ya dame nawa ya shanye.

Haɗuwarmu a inuwa ɗaya shi ya ƙara rura wutar ƙiyayya, domin dai cima ma ta bambanta, duk da idan ta dafa za ta ba ni amma ba zan ci ba, haka ba zan bar ɗana ya ci ba. Babban abin da ke ƙular da ni idan na ce ya je ya nemi taimako wurin shi ko da na abinci ne ba zai je ba, ko da zai fita ya dawo hannu Rabbana. A wannan tsakankanin da muka shiga matsin rayuwa a shi ne kuma buɗi ke ta kuma zuwa wa yaya Abubakar, domin an masa ƙarin girma wurin aikinsa, A lokacin zuciyata ta fara yi mini saƙa da mugun zare.

Haka na tattare duka 'yan kuɗaɗena na je wa da wani malami buƙatata, ba tare da ɓata lokaci ba ya aiwatar mini da aikin da na nema, domin rana ɗaya tana tsaye ta yanke jiki ta faɗi.

Bayan tsawon lokaci tana jinya ta fara ɗan magana har tana miƙewa ta yi tafiya, sai dai a shagiɗe take yinta da taimakon iyayenta tare da jajircewar mijinta. Ganin ana shirin komawa gidan jiya za ta miƙe ga liyafa ta cigaba, kulawa ta ninku tsakaninta da mijinta bayan kayan ɗaki da ya sauya mata ga gyaran gidan ya tsira, sai na mata mai gabaɗaya.

Domin asirin na kuma sakawa aka yi mata da za ta dawwama a kwance ba uhm bare uhm-uhm. Sai lokacin hankalina ya kwanta ganin na dankwafar da ita ba ta da damar watayawa cikin gidan yadda ta saba, har ta kai mahaifiyarta ta dawo gidan tana jinyarta inda bai fi da sati guda ba ta rasu.

"Ga ta nan ku kama ta" Wannan furuci shi ya tsamo ni daga karanto wasiƙar jakin da na tafi, ashe fitar da ya yi 'yan sanda ya je kira. Ba tare da ɓata lokaci ba wata jami'a ta zo ta damƙi hannuna ta miƙar da ni tsaye ta ja ni waje, suka danna a mota.

Na yi shiru cikin motar ina tuna kalmar sakin da mijina ya fesa wa ramukan kunnuwana lokacin da na zo gifta shi, idona ya kuma hasko mini Walid da ya dinga bi na yana kuka. Na ɗaga kaina na kalli 'yan sandan da ke kusa da ni, bayan an ja motar mun fara tafiya.

Haka suka kai ni akurkin adana masu lefi suka killace, a cewarsu za su tattara bayanai tunda na amsa laifina daga nan su miƙa ni kotu domin alƙali ya yanke mini hukunci daidai da laifin da na aikata. Tabbas rayuwata ba ta yi amfani ba, domin ba ni ga tsuntsu ba ni ga tarko.

"Hmmmm" Na sauke ajiyar zuciya bayan kammala karanta labarin, kafin na ɗora da. Ai da ma shi son zuciya ɓacinta, kuma ita hassada mugun ciwo ce, domin duk mai ita to akwai tsatsa a cikin zuciyarsa. Annabi S A.W ne ya faɗa, ita hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta ke cinye ƙirare. Ga shi dai yadda wannan baiwar Allah mai suna Bintu ta tsinci talatarta a laraba. Ƙalubale gare ku mata masu ɗaukar facalolinku tamkar kishiyoyinku, wata ma yadda take kishi da facalarta baza ta yi da kishiyarta ba. Allah ya kyauta.

Anan muka kawo ƙarshen shirin, muna jiran raayoyinku kamar kullum akan wannan labari na wutar ƙiyayya, taku a kodayaushe Nuratu Attahir Mai nasara nake cewa mu huta lafiya."

Daga nan ta cire abin kan ta ta miƙe ta fice. Kai tsaye office ɗinta ta wuce. Ta cigaba da duba abin da za ta yi Next kuma. Ta shiga aikinta ka'in da na'in. Sai da aka kusa tashi sannan suka haɗu ita da Zaitun domin itama ayyuka ne suka sha kan ta.

Bayan an tashi a hanyarta ta komawa gida tana kallon waje kawai ta hango wani yaro ya yanke jiki ya faɗi. "Dakata!" Ta cewa direban da sauri, yana tsayawa ta ɓalle murfin motar ta fice ba tare da ta tsaya amsa tambayar da yake yi mata ba na lafiya? Kai tsaye wurin yaran ta nufa da suka duƙa akan wanda ya faɗi suna jijjiga shi "Me ya same shi haka?" Ta ce tana duƙawa itama. "Faɗuwa ya yi" Ƙaramin ya ba ta amsa "Subhanallahi garin ya ya?" Sai kuma ta fiddo ido ganin yadda kumfa ke fita a bakinsa, idon shi na neman kakkafewa. Ɗago shi ta yi jikinta "Me ya ci?"

"Wannan ya sha" Ya nuna mata wani farin abu a ƙuƙƙule a leda, ta karɓa tana dubawa sai kuma jikinta ya fara rawa "Wannan ai hodar iblis ce a ina kuka samu? Ku taimaka mu kai shi asibiti." Ta mayar da maganar kan masu tsaron nata da suka iso wurin a lokacin, ba musu suka cicciɓe shi suka shigar mota. Ita ma shiga ta yi bayan ta saka ƴan uwan nashi su biyu sun shiga motar su ma......!

[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*

_Writers Association_

*(WOW)*

*TURMIN DANYA*

*NA*

*FATIMA UMAR KAS*

_HILFAT_

25

Duk bugun da suke yi ta ƙi buɗe ƙofar, tana jin su ta yi shiru amma ta daina buge-bugen tana ta sauke numfashi. Dole haƙura suka yi suka bar wurin, duk falo suka koma suka yi jigum-jigum. Areef ɗin ne ya tashi ya kuma komawa saman domin ya bi su a baya da suka tafi a ɗazun ba ta buɗe ƙofar ba. Yana zuwa ya hau buga ƙofar "Aunty Nawwara ki zo ki buɗe mini." Shiru ta masa da farko sai da ya yi kamar zai yi kuku "Aunty Awwala ni ki buɗe in ba haka ba na yi kuka." Ya ce da sunan da yake kiranta kafin ya iya Awwala. Sai kuwa ya ji alamun buɗe ƙofar.

Tana buɗewa ya shige ciki, ta yi saurin cafko hannunsa ganin ya nufi ciki "Tsaya a nan kar ka taka kwalba." Ya tsaya yana bin ɗakin da kallo, kama hannunsa ta yi suka fice. Suna zaune sun yi shiru sai gani suka yi tana sakkowa ita da Areef, ɗan murmushi Mum ta yi sannan ta ce "Da yake ɗan gaban goshin ki ne ai kin buɗe kin fito, amma mu kina jin mu kika share mu."

"Kyale ta ba ki ga yanayin da take ciki ba? Doughter wa ya ɓata miki rai ne ki faɗa mini kowanene sai ransa ya ɓaci shi ma ko da ya kai dubu." Ta ɗago ta kalle shi lokacin da ya zauna a ɗaya ɓarin nata, kamar ta faɗa musu sai kuma wani tunani ya faɗo mata kawai sai ta girgiza kai ta ce "Ba komai Dad ya wuce. A kira Barira ta je ta gyara mini ɗakin ina so zan yi wanka." Ta kuma basar da maganar. Ba wanda ya takura ta sai ya ji suka rabu da ita.

Barira ce ta gyara mata ɗakin tas sannan ta sakko da bolar, kama haɓa mum ɗin ta yi "Haka kika yi wa ɗakin da ma? Wai me yasa baza ki rage wannan zafin ran ba?"

Shiru ta kuma yi, yayin da shi kuma yake ta aikin rarrashinta, ta miƙe ta haye saman.

Sai da ta yi wanka ta shirya sannan ta sakko, yunwa take ji sosai don haka ta wuce can kai tsaye. Su ma duk suka hallara ganin wadda ta hana su cin ta je za ta ci ita.

A baki Mum ta dinga ba ta abincin duk don ta samu ta saki ranta.

Suna isa asibitin aka karɓi yaron zuwa emagency. Sintiri ta shiga yi a harabar cike da fatan yaron kar ya mutu, sai kuma ta kalli babban ta ce "A ina makarantar taku take ne yakama malaminku ta san halin da ake ciki."

"Ba a makaranta muke ba mu, muna da gida ƙanina ne, wannan ne yake wurin kakarsa da suka zo tare."

"Cikin rashin fahimta ta ce "Kana nufin ba almajirai ba ne ku kuna da iyaye, da saninsu kuke yin bara?" Kai kawai ya gyaɗa mata alamun eh, mamaki ne ya ƙume ta a tsaye, sosai abin ya ɗaure mata kai, ace yara ƙanana kamar waɗannan suna gararamba a titi da robobi kuma iyayen su na nan ras da su. "Ina ne gidan naku?" Ta tsinci bakinta da furtawa. Faɗa mata ya yi ta ce bari ya farfaɗo sai su je ya raka ta.

Suna nan tsaye shiru ba labari, juyawa ta yi ta fice, kai tsaye inda suke a jikin motocin ta nufa "Ina ganin ku je kawai, ba zan iya tafiya ba sai na ga yadda jikin nasa yake, har yanzu likitocin ma ba su fito daga kan shi ba."

"Ba matsala za mu jira ki sai mu tafi tare" Ɗaya ya ba ta amsa, ta juya ciki. Ya yi daidai da fitowar wani likita, da sauri ta nufe shi tana faɗin "Dr ya ake ciki ne ya farfaɗo?"

"Ina iyayen yaron?" Ya tambaya maimakon ya ba ta amsa "Ba sa kusa ko menene za ku iya faɗa mini ni na kawo shi." Muna buƙatar ganin iyayensa gaskiya mu ji wanne irin sakaci ne zai saka a bar yaro ɗan shekara goma ya sha cocain."

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" Ita ta shiga maimitawa dafe da kanta. "Zan iya ganin shi yanzu?"

"Eh ki shiga kar a yi hayaniya a kan sa, amma ina son ganin iyayensa da gaggawa."

Ya yi gaba, ita kuma ta tura ɗakin ta shige, yana kwance kamar gawa ba inda ke motsi a jikinsa. Hawaye ta ji ya cicciko mata idanu, sheshsheƙar kuka ta ji a kusa da ita. Yaran ne ke kuka, "Ku yi shiru zai sami lafiya in sha Allahu" ta riƙe hannunsu suka fice.

"Mu je ku kai ni gidan naku." Tare suka fice, suna gani ta fito suka miƙe "Ba gida zan tafi ba, akwai inda zan je na dawo."

"Bari na kai ki to" Cewar direban, "A'a ba buƙata na ce maka yanzu zan dawo ku jira ni."

"Amma Hajiya magriba ta kus..." Hannu ta ɗaga masa tun kafin ya ƙarasa maganar.

Ba ta kuma jiran cewarsu ba ta fice wajen, adaidaita ta tarar musu ta faɗi inda zai kai su suka tafi.

Kwatancen yaron suka dinga bi har suka iso ƙofar gidan, ta bi gidan da kallo, da gani masu gidan ƙaramin ƙarfi gare su. Daga gefe wata majalisa ce da suke ta musun ball sai duk suka zubo mata ido. Saurin ɗauke kai ta yi ta shige gidan da yaran suka shiga bayan ta miƙa wa mai napep ɗin kuɗinsa. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga. Matashiyar matar ta gani ta riƙe ƙaramin yaron tana tambayarsa ina ɗan uwansa.

Sai kuma ta ɗago tana amsa sallamar da Nuratun ta yi, ta ɗan bi ta da kallon rashin sani kafin ta ce "Sannu da zuwa"

"Yawwa, ke ce mahaifiyar yaran nan?"

"I ni ce amma ban da ɗayan nan shi abokinsu ne."

"Ina mahaifinsu ina son magana da ku"

"Me ya samu Adamun ne jikina na ba ni ba lafiya ba."

"Ina son dai ganin nasa sai na muku bayani tare"

"Kai Mukhtar kira babanku a waje." Tana kallon yaron.

Ya juya ya fita "Ki zauna don Allah ga wuri" Ta nuna mata tabarma, ba musu ta zauna tana ta ƙoƙarin danne fushinta.

Sallamar shi ta saka suka kalli ƙofar, mamaki ya ƙume Nuratu ganin har da shi a cikin majalisar nan, kuma ya fi uban kowa zaƙalƙalewa akan musun nan, duk an fi jin muryarsa. "Ga ni me kuma zan miki? Idan ma wani abin za ki ce za a siyo ni ba ni da ko asi." Ya ce cikin hargagi yana fito mata da aljihunsa. Takaici ya kuma kamata don haka ta ji ba za ta iya gaida shi ba ma. "Ga wadda ke nemanka nan" Ta nuna Nuratu, ya ɗan kalle ta kafin ya ce "To lafiya?"

"Lafiya ba lau ba, domin ɗanku na can rai a hannun Allah ba ya ma cikin hayyacinsa. A ce yara kamar waɗannan ku sake su sakaka ku kuna gida ba abin da ya dame ku da ko ma mene zai same su, to wallahi ƴaƴa amana ne kuma sai Ubangiji ya tambaye ku game da amanar da ya ba ku."

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Adamun ne a asibiti me ya same shi to? Lafiya fa suka fita a gidan nan ɗazu." Mahaifiyar tasu tace tana fashewa da kuka.

"Yana wanne asibitin yanzu?"

"Duk ba lokacin wannan, likitan ya ce lallai ku yake son gani, za mu iya tafiya" Ta miƙe ta yi waje cikin takaici.

Bayanta ya biyo, itama ta sako hijabin sallahrta ta rufe gidan.

Tsaye suke a titin, shi na ƙoƙarin tarar musu abin hawa ita kuma sai aikin kuka take yi, ya yin da Nuratun ta ƙule don haka ta harɗe hannu a ƙirji tana juyar da kan ta gefe, a ganinta kukan me za ta yi bayan sakacin su ne? Suna tsayen wata adaidaita da har ta yi gaba ta dawo da baya ta ja ta tsaya, sai kawai suka shige a ruɗe suna faɗa masa inda zai kai su, juyawa ta yi itama ta shiga, sai da aka fara tafiya sannan ta ɗago kan ta. Gabanta ne ta ji ya faɗi lokacin da ta ga bayan mai adaidatan, ɗauke kai ta yi tana cigaba da kallon waje.

Wayarta ce ta hau ruri, tana dubawa ta ga Mamy ce, ta san a rina dama, ta ɗaga bakinta ɗauke da sallama "Lafiya dai shiru ba ku dawo ba har yanzu?" Ta tambaya daga can ɓangaren. "Lafiya ƙalau Mamy kawai dai akwai abim da ya tsayar da ni ne, kuma na cewa su Bala su taho ni na taho daga baya sun ƙi wai tare za mu tafi"

"Kin tabbata dai kina lafiya ko?"

"Lafiyata sumul Mamyna, anjima kaɗan za ki gan ni." Ta ce tana murmushi. "To shike nan Allah ya kawo mini ke cikin ƙoshin lafiya."

"Amin amin, sai na ƙaraso" Daga haka ta ajiye wayar tana cigaba da murmushin."

Suna isa asibitin har ciki ya shigar da su, ta zaro kuɗi ta miƙa wa mai napep ɗin amma sai ta ga bai karɓa ba, ɗagowa ta yi aikuwa karaf suka haɗa ido domin idanunsa na kanta. Rasss gabanta ya kuma yankewa ya faɗi "Ka karɓa mana" Ta ce cikin jin haushi, amma sai ya cigaba da kallonta, watsa matsa kuɗin ta yi cinyarsa tana maka masa wani kallo sannan ta juya ta shige ciki, sai kuma ta tsaya tana son tuno inda ta san waɗannan idanun nasa, waigawa ta yi da sauri amma har ya bar wurin, ta ɗage kafaɗa irin shi ya jiyo ɗin nan, tana juyawa ta shige cikin asibitin ƙirjinta na luguɗe....

[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*

_Writers Association_

*(WOW)*

*TURMIN DANYA*

14 / 19