Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
wuƙar da aka sare ni da ita, akwai tsatsa a jikinta kuma ba a kai ni asibiti da wuri ba har ciwon ya fara zagwanyewa. Tamkar ruguzowar aradu da ka haka na ji maganar, wani guntun fitsari ya kufce mini. Take na shiga magiyar a bar mini hannuna zai warke, amma dayake bakin alƙalami ya bushe sai da aka yanke su.
Rayuwa ta jefa ni a jarabawar da na shirya da kaina. Kuma na girbe abin da na shuka, na ɗanɗani ɗacin ɗanyen abin da na dafa shi da hannuwana. Take ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo mini, yadda rayuwata ta kasance tamkar a faifan majigi.
Sunana Karimatu, shekaruna ashirin da biyu. Mahaifimu ya yi faɗi-tashi a kanmu don ganin rayuwarmu ta inganta, amma abu ya faskara sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita. A dole muka haƙura da karatun boko, domin babu halin biya mana. Mu uku ne a wurinsu, daga yayana sai ni sai autanmu. Na kasance mafi soyuwa a zuciyar iyayena, musamman mahaifiyata sam ba ta ƙaunar ganin laifina. Ina da farin jinin mutane, da dama na cewa kyawuna yake janyo mini soyayyar jama'a, amma daga baya sai kyawun ya zama na ɗan maciji.
Tun tasowa ta nake da ƙaunar kashe kuɗi, duk abin da na gani ina so sai na tada ɓalli an siya mini. Kasancewar mama tana 'yan ƙananan sana'o'i, ya sa take kwance mini bakin aljihu har ta kai na san ma'ajiyar kuɗinta, don ta sha cewa na je na ɗauka. Mahaifina ya so nusar da ita illar hakan, amma ta ce ai ƙuruciya ce zan daina.
A wannan tsakankanin mahaifinmu ya kwanta dama, a lokacin ne muka kuma shiga matsin rayuwa. Sai na daina samun kuɗin kashewa daga wurinta, ta so dakatar da ni amma da yake na yi nisa ba na jin kira. Domin na yi wa kuɗi mugun sabo, wannan tasa na fara ɗaukar nata idan ban samu ba har na maƙota. A haka na taso har na zama budurwa, wannan ɗabi'a ba ta fita a jikina ba. Daga baya ma sai likafa ta ci gaba, domin kasuwanni nake shiga ina ɗauke hankalin maza mayun kyawawan mata da labari na yashe su. Ban taɓa soyayya ba, domin ba ita ce a gabana ba. Ko a gidan biki da na suna duk wacce ta yi wasarere da jakarta, ko wayarta za ta rasa ta. Kai hatta gidan kitso da ƙunshi, ba na ƙasa a gwiwa wurin yada zango na yagi rabona. Har sai da ta kai an gane ni, ko dangi na shiga kowa yana kaffa-kaffa da kayansa. Wannan ya janyo wa mamanmu hawan jini, saboda baƙincikin da nake cusa mata. Yayana kuwa tun yana jibga ta kamar Allah ya aiko shi, har ya zuba wa sarautar Allah ido. Domin kuwa idan ƙaho ya fara girma da wuya a iya lanƙwasa shi.
Wajen Ramatu dillaliya na haɗu da wasu mata da samari sun kawo mata kayan sata ta saya, a nan muka ɗinke da muka fahimci duk kanwar ja ce. Muka ci gaba da cin karenmu babu babbaka. Tuni na yi ƙaura daga gida na tare a gidan ɗaya daga cikinmu, saboda zaman uwa babu kwaɓa uba babu tsanani muke yi.
A wurinsu na san bin malaman neman sa'a da kuma rufa ido, na san mallakar makullai na kowanne kwaɗo da kuma almakashi. Watarana dubunmu ta cika aka kama mu, sakamakon satar gwala-gwalai da muka yi wa wata hajiya a wurin gyaran kai. Bayan mun fito sai abin ya yi gaba, domin zuciyoyinmu ƙara ƙeƙashewa suka yi, sakamakon haɗuwa da waɗanda suka dame mu suka shanye a laifi.
Sai muka ƙara fantsama sabbabin unguwa, wannan karon wacce muka shigar wa amaryar ce.
Cike da tsantsar rashin tsoro, muka ci gaba da haɗe kayan matar wuri ɗaya muna ɗure wasu a buhu. Sai da muka yashe ta tsaf, sannan muka nufi ƙofar fita. Turus! Muka yi jin ana ƙwanƙwasawa, muka shiga kallon-kallo tsakaninmu bayan mun sandare a tsaye kamar gumaka.
'Shi ke nan kwaɓarmu ta yi ruwa tsululu.' Na raya a raina haɗe da nufar ƙofa kai tsaye, bayan na ajiye kayan na zare sakatar. Take na yi arba da wani kakkauran mutumi, ya zubo mini idanuwa. Wani gigitaccen mari ya ɗauke ni da shi, wanda ya yi silar ɗaukewar jina na wasu sakanni, kafin na dawo hayyacina ya ƙara mini wani. Sama-sama kafar jina ta tsinkayo mini fusatacciyar muryarsa yana faɗin.
"Azzalumai macuta, ɓarayin banza ɓarayin wofi! Uban me kuke yi mata a gida ba ta nan? Ai na ga shigar ku ɗazu. Jama'a ku fito, yau dubun ɓerayen da suka addabe mu a unguwar nan ta cika!"
Ya faɗa cikin ƙaraji, kafin na tantance abin yi na hango wasu gungun matasa masu jiran ƙiris da makamai sun nufo gidan da gudu. Babu shiri na mayar da ƙofar na rufe, suka shiga bugawa kamar za su ɓalla ta suna faɗin sai na lahira ya fi mu jin daɗi, da ma cikinmu ne da su sai sun haife shi a take. Muka yi tsuru-tsuru a tsakar gidan, sai ka ce bayin da suka yi wa sarki ƙarya. Babu zato muka ga wani ya diro ta saman katanga, ya rufe mu da duka da gorar hannunsa muka hau karewa, sai ga wani ma ya diro a sukwane muka afka ɗakin matar. Ina shirin rufewa wani ya kawo mini sara sai a dantsen hannuna, na saki ƙarar azaba sai na kuma jin wani saran a hannun da na dafe ɗayan. Cikin ƙarfin hali, na datse ƙofar da bayana domin na san idan suka shigo kashinmu ya bushe. Tabbas wanda ya haƙa rami don wani, to shi zai faɗa a cikinsa.
Nan suka shiga jera mini sannu ina gyaɗa kai da cije leɓe, ɗankwalina Tijjani ya yaga ya ɗaure mini hannun domin tsayar da jinin. Kafin wani lokaci gidan ya cika maƙil, don sun buɗe ƙofar kowa yana ta faɗar albarkacin bakinsa.
Ƙura ba ta lafa ba sai da jami'ai suka iso bisa jagorancin mutumin nan, suka kora kowa waje suka ce mu fito.
Daga nan aka zuba mu a motar shiga ba biya, ni kaɗai ce mace a cikinsu sauran huɗun duk maza ne.
Ɗakin adana masu laifi aka jefa ni, na samu wuri na zauna cike da takaicin kamun kazar kukun da aka yi mana. Wai ya aka yi aka haihu a ragaya mu da muke da sa'a a jikinmu? An gurfanar da mu gaban alƙali, an kuma kamo sauran har dillalan da muke kai wa kayan satar idan mun yi.
Na sauke ajiyar zuciya, bayan dawowa daga tunanin da na tafi. Tabbas duk ganyen da ya riga ya bushe ba zai sake zama kore ba.
Gaskiya ne da aka ce komai nisan dare gari zai waye. Kuma kowane rai yana ɗauke da sakamakon abin da hannayensa suka aikata.(Suratul Jathiya: 22)
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: TURMIN DINYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(12)
Sai da ta samu sati biyu a gida sannan ta koma aikin shi ma sai da ta yi da gaske domin sam iyayen sun ce sai ta samu a ƙalla wata guda. Gefe guda kuma jamian na cigaba da binciken gano waɗanda suka ɗauke ta ɗin duk da daddyn ya ce tunda an sameta shike nan, kasancewar har lokacin daga shi sai Mamy suka san yadda aka yi sai kuma ita ,domin ko suda akun gidan ba wanda ya sanar masa. Domin idan ya ji kamar kowa ya ji ne.
Bayan ta fito ta shiga mota tana ta ɓata rai suka tafi, masu tsaron nata na biye da ita, ita kam ba ta so aka haɗa ta da su ba, a ganinta za su takura mata ne.
Tun daga harabar suke gaisawa da mutane ana ƙara jajanta mata. Ofishin shugaban nasu ta shiga. Ta samu gefe ta zauna "Barka da warhaka Jagaba ya aikin"
"Barkan mu Nuratu ya ƙarfin jikin."
"Alhamdulillah"
"Ma sha Allahu Allah ya tsare"
Ta amsa da amin, sai kuma ta ƙara gyara zama tana son yi masa maganar da ta kawo ta.
"Jagaba da ma akwai wata magana da muke son yi maka akan wani rahoto da za mu fitar, sai kuma wannan tsautsayi ya afku." Ya ba ta hankalinsa duka.
"Zaitun ta zo mini da wata magana akan wata budurwa ƴar damfara da ta ɓullo, tana nan tana yawon damfarar waɗanda suka shiga komarta. idan ka mana izini na haɗa rahoton kuma ina son a saka shi a shirin yau"
"Ma sha Allahu hakan ya yi. Ki kammala duka sai ki kawo mini na gani idan komai ya yi sai a saka ɗin, saboda gara a fargar da mutane su ankare da ita."
"To godiya nake jagaba. Bari na ƙarasa sai nakawo maka ɗin, na barka lafiya." Ta miƙe ta fice, daga nan ofishinta ta shige. Daga gefe ta hango Zaitun, ɗagowa ta yi suka haɗa ido. Harara ta maka wa Nuratun tana cigaba da abin da take yi. Murmushi ta yi ta matsa ta dafa mata kafaɗa "To me kuma na yi ake ake mini kallon tara saura kwata?"
"Ban sani ba, dalla sake ni" Ta cire mata hannu daga kafaɗa. Wuri ta samu ta zauna "A huce dai haka a sanar da ni laifina"
"Hmmm wallahi kin yi mugun ɓata mini rai, rumi-rumi muka yi magana da ke kika ce yau za ki dawo aiki, kin san kuma dole zan biyo miki shine kika wani yi tafiyar ki,sai da na je wai kin taho, kuma na zo yanzu ba kya office ɗin, banza kawai." Ta ƙara maka mata wani kallo.
"Ayya ƙawalli ki yi mini afuwa. Wallahi daddy ne ya haɗa ni da wasu ƙatti wai su za su ke tsaro na duk inda zan tafi da su za mu tafi. Ina ta magiyar a ƙyale ni ni dai ya dage Mamy ma ta goyo baya, takaici kawai ya sa na fito ko sallama ban musu ba na faɗa motar muka taho.
Da na shigo kuma na shiga office ɗin jagaba ne akan haɗa rahoton yarinyar nan da kika mini maganarta.
Sai lokacin ta ɗan saki fuska "Amma ai ya kamata ki sanar da ni ko ta waya ne."
"Na amshi laifina to ki yi haƙuri, na faɗa maki raina ne a ɓace."
"Ya wuce, yanzu ya kuka yi da shi." Ta tambaye ta, take ta kwashe komai ta sanar mata. Kai ta gyaɗa cike da gamsuwa kafin tace "Amma kin san yau akwai shirin ki na DANDALIN MARUBUTA da kike gabatarwa duk rana irin ta yau, za ki yi ɗin ne ko sai wani satin."
"Zan yi shi gaskiya saboda na san dayawa za su yi ta dako duba da yadda shirin ke da farinjini, kuma kusan sati uku ba a gabatar ba."
"Gaskiya kam za su jira ɗin amma dayake na sanar da batun ɓatan ki a cikin shirin Tsumagiya da na gabatar wancen satin. Yanzu ki samu ki gama haɗa rahoton sai mu ga ta inda za mu fara ƙoƙarin zaƙulo yarinyar."
"Ai na kammala haɗawa, karantawa kaɗai ya rage, yanzu zan shiga studio na karanta sai na tura wa jagabaa ya ji idan komai ya yi za a saka a shirin Hantsi da ake sakawa ƙarfe bakwai na dare."
"Hakan ya yi, Allah dai ya dafa mana" Ta amsa da amin tana tattara takaddun gabanta da take yin rubuce-rubuce a jiki ta fice zuwa ɗakin karatun.
Bayan ta shiga ta rufe koina sannan ta zauna a gaban mic ɗin ta maƙala abin da suke zirowa ta kan su su rufe har kunnensu da shi, zama ta gyara sannan ta fara magana.
"A cikin shirin mu na Hantsi a wannan rana ta talata, za ku ji wata matashiya ko mu ce tauraruwa mai wutsiya da ba a gano ko ita wacece ba, da ta kasance mai fuska biyu. Domin kuwa ta yi shura wurin fakar numfashin duk wanda ya faɗa komar ta ta yashe shi ta gudu. Budurwar da a ƙalla za ta yi shekara ashirin da biyar tana da kyawun da take ɗauke hankalin maza kuma take amfani da wannan dama ta talauta mutum ta gudu. Da fatan al'umma za su hankalta wurin saka ido da kuma takatsantsan domin gujewa faɗawa tarkon wannan matashiya musamman maza.
Taku a kodayaushe Nuratu Tahir mainasara nake cewa assalamu alaikum, na bar ku lafiya."
Daga haka ta kashe recording ɗin ta cire abin kan nata ta ajiye. Miƙewa ta yi ta fice, sai da ta je ta kunnawa Zaitun ɗin kafin ta nufi babban ofishin ta kai domin a duba mata daga nan a miƙawa shugaban shirin. Sai ƙarfe biyar ta fito Zaitun na biye da ita. Nan ta tarar da excort ɗinta na jiranta, mota ta faɗa suka nufo gida.
A daidai kan titin da zai sada ta da unguwarsu ta hangi dandazon mutane a tsaitsaye, can ta gano ɗan uwan nata tsaye bakin shagon Abdul fata mai ɗinki yana ta bala'i, ta fahimci hakan ne ta hanyar hango sa da ta yi yana ta watsa hannuwa da nuna cikin shagon kan shi ya ƙi tsayawa wuri ɗaya. Direban ta yi wa magana ta sauka Zaitun na biye da ita. Kai tsaye wurin ta nufa ta kutsa har ta isa gabansa, dafa shi ta yi aikuwa ya doke mata hannu yana cigaba da jaraba "Yaya mene hakan ka tara wa kan ka jama'a, me ya faru?" Jin muryarta ya saka shi juyowa. "Ba dole na yi bala'i ba ji nake kamar na aro baki wallahi, wai ni zan kawo ɗin ki a mini ɗinkin maza, duk yadda na dinga jaddada a zuba mini ɗinki mai kyau na cake kuɗinsa cass na ba shi amma ya mini wannan abin aljihu a gaban riga? To wallahi sai ya biya ni kuma ba zan gusa daga nan ba a take anan za a biya ni kayana eheee" Ya ƙarasa da tura ɗankwali gaban goshi. "Wannan-wannan an yi fitinanne, yo in ban da fitina ta ya kana gansamemen ƙato ka kawo ɗinki an yi maka ka ce wai na mata za a maka? To kai mace ne? Ai Allah ne ma ya rage wa aya zaƙinta da a macen ka zo ai wallahi babu mai kwasarka a haka, kai ba ka kallon ƙirar jikinka ne, ƙirji kamar allon sha baya kamar an miƙar da ɗan akuya?" Wani dake gefe ya faɗa cikin takaici.
"Ba ruwanka malam, raba ni da kai ni cikinku ba ni da abin ba ku, kuma idan ban shiga a gidan aure ba ai zan shiga a tasha eheee! Ni ko lokacin da na yi suyar doya da ƙwai a bakin titi kostomomi na yi kala-kala sai na zaɓa na darje, to kawai ba abin da ke gabana ba kenan" Ya ba shi amsa yana fari da ido.
"Auzubillahi, waiyazibillahi"
"A kan ka, a kan ka, kamar ka ga wani shaiɗani za ka dinga ja mini auziyya?"
"Don Allah yaya ka zo mu tafi gida wannan fa zubar mana da ƙima kawai kake yi a wurin nan, mu je gida zan ba ka atamfofi ka zaɓi wadda ta maka sai a ɗinka maka." Nuratun ta shiga jan shi tana magana. "Ni wallahi tallahi tawa nake so, gobe ne fa bikin, haka zan je wurin bikin babu anko ake yi mini gani-gani? Ni wallahi Abdulfatah ka cuce ni ka gama da ni ka karya mini bajat."
"Na ji a yau zan nemo maka irin atamfar za a kawo maka har gida, ko zani da ɗankwali sai ka ɗaura ka je bikin."
Ta cigaba da lallaɓa shi da ƙyar ta samu ta janye shi suka tura shi mota masu ɗaukar bidiyo na ta yi. Shagon ta koma ta ba su haƙurin tara musu jamaar da ya yi "Bakomai mu ma da laifinmu da ba mu tambayi wanne kalla za a masa ba. Ni dai da ya kawo yace mini nashi ne sai na yi zaton atamfar ya yi sha'awa kawai shi ne na masa ƙaramar riga da dogon wando. Don na ga atamfar turmi ce ma da na zaci rabin turmi ce za a masa iya riga ya saka da jeans, Allah ya kyauta."
Ta amsa da amin ta juya ta koma motar suka tafi gida.
Ko bayan isar su gidan faɗan yake ta yi wanda Mamy takaici ya hana ta magana jin abin da ya faru. Bakinsa bai mutu ba sai da aka kawo masa wata atamfar irin tashin sak tukunna, don atamfofi uku ta ɗebi masa duk yace ba su masa ba irin tashi yake so, haka ta bi shi a hakan sanin halin tijararsa sai shi.....!
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS
Writers Association
(WOW)
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(15)
Suna isa gidan suka fito da shi sannan suka angiza shi ciki idanunsa rufe da baƙin ƙyalle. A gaban babba ɗin suka durƙusar da shi sai buhun kayan a gefe. "Buɗe masa idon" Ya ce kamar baya son magana. Ana buɗewa kam ya fara waige-waige da bin wurin da kallo idanu a zare. "Don girman Allah kar ku kashe ni wallahi tunda nake wannan harƙallar ban taɓa kashe kowa ko raunata kowa ba."
Wuri ya samu ya zauna idanunsa a kan shi ya ce "Babu ruwanmu da koma mene kake yi, wannan tamu ce ta haɗa mu da kai domin mu yagi namu kason mu ma, babu abin da za mu yi maka idan ka ba mu haɗin kai.
Mun yi garkuwa da kai muna buƙatar ka biya kuɗi ka fanshi kan ka."
Sai lokacin jikinsa ya fara rage rawar