Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
yi shawara ai duk inda ta faɗa ruwa sha ne." Cewar Goje
"Shike nan za mu yi waya"
Daga haka suka ɗauki jakunkunansu suka fice a gidan, shi kuma ya fara tunanin ta yadda zai yi abin da ya tsarawa kan shi, Abu biyu yake son yi a ranar dole kuma ɗaya zai fara sannan ɗayan.
Nuratu na zaune a falo tana kurɓar shayi a hankali, domin kwana biyu kenan da aka sallama mo ta daga asibiti, jikinta da sauƙi sosai. Duk yadda Mamy da daddyn suka matsa ta ta faɗi ta yadda ciwon ya same ta ta ƙi kawai cewa take yi tsautsayi ne. Haka Barister Sahabi duk zuwan da ya yi ta ƙi faɗar komai, ya san tabbas akwai abin da ya faru kawai ta ɓoye ne. Yanzun ma tana zaunen maigadi ya yi sallama ya shigo yake sanar mata ta yi baƙo. Ta ɗan yatsina fuska domin ta san shi ne, shi ko gajiya da zuwa ba ya yi? Ta miƙe ta shiga ɗaki, ta ɗan gyara fuskarta ta sako hijabi sannan ta fesa turare ta fito. Mamyn ta ɗan bi ta da kallo tana nazarin fuskarta, ta jima da fahimtar yaron ba wai ya shiga zuciyarta ba ne, amma kuma ita ba ta ga makusar shi ba ne.
Iso ta masa zuwa ɗakin baƙi, yana ta murmushi domin shi kaɗai ya san son da yake yi mata. "Barka da zuwa"
"Yawwa gimbiya ya ƙarfin jiki"
"Alhamdulillah na warware."
"Ma sha Allahu amaryata, a daina zura jiki sosai don Allah ko don lafiyar ki da muka fi kowa buƙatarta a tare da ke."
"Tom in sha Allahu" Suka ɗan yi shiru don ita har lokacin ba wani sakewa take iya yi da shi ba. "Cikin satin nan za a kawo lefe fa, da ma saboda rashin lafiyarki aka ɗan dakata, amma tunda kin warware idan sun tsayar da ranar zan faɗa miki" Rasss ta ji ƙirjinta ya buga da ya yi maganar lefen auren fa kenan ya taho, shiru ta yi tana tunani, ita fa wallahi ba wani son auren nan take ba."
"Kin yi shiru" Ta ƙaƙalo murmushi " Kaina ke ɗan ciwo ne, ma sha Allah zan faɗa wa Mamyn to, sannu da ƙoƙari" Ta yi ƙoƙarin faɗa. "Yawwa sannunmu dai, yanzu ki je ki kwanta da wuri idan kin sha maganin, Allah ya sawwaƙe, ni bari na tafi." Ta gyaɗa kai kawai.
Daga nan suka yi sallama ya fita ita kuma ta shige cikin gidan, kai tsaye ɗakinta ta nufa ba tare da ta zauna a falon ba. Shiru ta yi cikin tunani kamar daga sama ta ji wayarta na ruri, ta janyo ta duba. Gyara zama ta yi tana bin lambar da kallo, sai kawai ta kara a kunne. Shiru ta yi tana saurara, anan ta fahimci lambar da ta haɗa da lambarta ce. Abin da ta ji ana faɗa a wayar ya sanya fitsari ya kusa kufce mata, ta cire wayar da sauri ta danna recorder tana naɗar abin da ake cewa cikin tsananin tashin hankali, jikinta ba inda baya rawa har wayar ta suɓuce ta faɗi akan gadon. Hannuwanta duka ta saka ta dafe kan ta da su ƙirjinta na wani irin bugawa fat fat fat........
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
30
Wani irin sarawa kan ta yake yi, take ciwon kan da ta yi ƙarya da shi ya tabbata, kuma ta kasa katse kiran tunda tana jin abin da duk ake cewa daga zaunen. Sun kusa minti talatin suna wayar sannan suka gama. Kiran na katsewa ta ɗauki wayar ta ƙura mata ido, take hawaye ya silalo mata. "Yanzu ni? Kamar ni a ce a samu mai wannan taasar a cikin ahlina? Kai Hasbunallahu waniimalwakil."
Jin bugun ƙofa ya saka ta saurin fara goge hawayenta, ta gyara yanayin fuskarta sannan ta nufi ƙofar ta buɗe tana murmushin yaƙe. Ƙura mata ido ta yi tana nazartar ta ya yin da ita kuma ta sunkuyar da kai. "Ki same mu wurin cin abinci." Ta juya ta tafi. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bi bayanta. Duk sun hallara ban da daddyn ta kalli mamyn don neman ƙarin bayani "Yanzu zai sakko ya ce mu fara kafin ya zo." Kai ta gyaɗa ta fara cakalar abincin da alamu ba jin daɗinsa take ba.
Mamyn ta kuma kallonta aka yi sa'a ta ɗago suka haɗa ido, ta ɗauke kai tana sakin numfashi, sai kawai ta miƙe ta koma falon ta zauna ta yi shiru fuskarta a haɗe. Jikin Nuratun ya yi sanyi ta miƙe ta isa kusa da ita ta zauna. "Mamy lafiya?"
"Ke zan tambaya lafiya ai, tunda yanzu kin daina tattauna matsala da ni sai dai ki ƙunshe ta a ran ki."
"Ba haka ba ne Mamy, wallahi kaina ciwo yake yi sosai"
"Bayan wannan akwai wani ai"
"Eh akwai mamy, akan yaran nan da ya mutu ne abin ya tsaye mini arai. Kin san na ce miki hofar iblis ya sha har ya rasa ran shi, to da na koma gidan su yaran na ritsa su, ashe wani ke ba su suna yi masa cinikayya, yana ta ɓata rayuwarsu tun suna ƙanana, idan sun siyar ya ba su abinci da kuɗin kashewa duk saboda sakacin iyayensu na ɗaukar ɗawainiyarsu.
To ranar da na fita nace miki na tafi aiki can na fara biyawa, daga nan na je na ɗau police muka je wurin ashe ya gudu, to daga nan ne muka tafi inda yaran ke kai wa ana siya, aka kama su kusan su shida, shi ne har ɗaya ya shammace ni ya yanke ni."
"Hmmm! Nuratu, na san duk abin da kike yi akan gaskiyar ki ne, amma ni wallahi aikin nan ba son shi nake ba saboda akwai haɗari a cikinsa ke macece. Wani abin ma fa aikin jami'an tsaro ne ba na ku ba. Ki haƙura don Allah ki zauna a gida ki yi auren ki ya fi kwanciyar hankali."
"Har kin tuna mini ma Mamy. Barister ya ce cikin satin nan za su kawo lefe, na san duka bai fi wata guda ya rage mini na yi aure ba. Abubuwa biyu nake son cimmawa a cikin watan nan, daga su ko da wasu sun ɓullo ba zan bi ta kan su ba, don Allah ki cigaba da mini addua kamar yadda kika saba."
"Yanzu ke ashe lefen za su kawo shi ne ba ki faɗa ba kuma? Ko don ba auren ne a gabanki ba? Zan roƙe shi ai idan kuka yi auren kar ya sake ya bar ki ki cigaba da aikin nan ki zauna a gida ki yi zaman aure"
"Kai Mamy kin daina sona fa"
Ta ce a shagwaɓe "Idan ta daina son ki ni kina nan maƙale a raina ai." Suka ji muryar daddyn a kan su. Murmushi suka yi dukkansu.
Tasowa ya yi ya zauna a kujerar shi ma ya harɗe hannu a ƙirji yana huhhura hanci. Murmushi Nuratun ta yi don ta san kwanan zancen. "Kai kuma da kake ta cika kana batsewa fa sai ka ce balam-balam?" Cewar daddyn "Uhm ba komai daddy?" Ya amsa yana mele baki "Kai ma dai har ka tambaya, ka san yadda ka san kishiyar shi haka ya ɗauke ta, da ya ga ana nuna mata kulawa yanzu ya ƙule." Mamy ta ba shi amsa, ya yi dariya daddyn yana faɗin "Ban da abin ka Nura ai kai ma yayanta ne, kai ya kamata ka fi mu nuna mata kulawa ma."
"Ni ai ba a sona a gidan nan na jima da gane hakan, sai a yi ta nuna mini wariyar launin fata."
"My son kai ma ina ƙaunarka, kawai halinka ne bana so, da za ka gyara da ka ga gata, amma duk muna son ku, kuma albishir mai daɗi na kusa zuwa dubai za ka mini rakiya kamar yadda ka saba." Cewar daddyn har lokacin yana dariya. Sai kuwa ya miƙe ya fara rawa yana waƙar Ado gwanja, sai kuma ya rungume daddyn har da masa kiss a kumatu "I love you wujiga-wujiga daddynmu mai capacity ai ni kam ka biya ni, ina son zuwa dubai ɗin nan ai ba ka ji shiyasa ƙawayen nawa ke ce mini ƴar dubai ba?" Suka yi dariya Mamyn ta ce "Faɗa masa dai, kuma itama ai ina mata faɗa idan ta yi ba daidai ba, yanzu fa wai yaron nan ne ya ce za a kawo lefe cikin satin nan kuma wai sai yanzu take faɗa mini, ta kyauta kenan"
Fara'ar fuskarsa ce ta ƙaru. "Abu ya zo ashe, to Allah ya tabbatar da alkairi muna jira. Yanzu ku zo mu je mu ƙarasa cin abincin." Ya yi gaba, miƙewa suka yi dukkansu suka nufi can, ita kuma sai ta nufi ɗaki. "Ina za ki kuma?" Ya tambaya "Na ci abincin ai ni, zan sha magani ne na kwanta kaina na ciwo" Ta ba shi amsa "To Allah ya sawwaƙe, ki kwanta ɗin kuma kar ki tsaya ko wanne aiki don na san ki." Kai ta gyaɗa ta shige ciki, su kuma suka cigaba da tattaunawa akan yadda za a tsara bikin nata.
A ranar yadda ta ga rana haka ta ga dare, gabaɗaya tunanin abin da ta ji ya hana ta runtsawa, ta inda za ta ɓullowa lamarin ma kawai take tunani, abu na farko da ya fara zuwa ranta shi ne zuwa ƙungiyar...sai kuma tattaunawa da barister domin ta san zai ba ta gudummawa shi ma. Daga nan kuma ta shiga bincike akan son gano wacece Nawwara, menene gaskiyar lamari game da kasancewarta jami'ar tsaro. Sai can wurin asuba sannan ta samu bacci don ma ba laifi ta samu abubuwa dayawa a daren.
Suna zaune a falon suna game ita da Areef ya yin da Mum ke can gefe tana lissafa kayan da ta yi oder suka iso. Yaron gidan ne mai ba wa filawowi ruwa ya yi sallama ya shigo, ta ɗago tana amsawa "Hajiya Madam ce ta yi baƙo" Yana ɗan rissinawa, kai kallonta kan Nawwara ta yi, ganin ba ta ɗago ba kuma tana ji ya sanya ta faɗin "Ba ki ji me yace ba ne?"
"Me ya ce?" Tace bayan ta ɗago tana ɗan yatsina fuska "To kai ka ji ba ta ji ba, sai ka kuma faɗa mata, ni ma halin za a nuna mini yau" Ta cigaba da lissafinta "Baƙo kika yi ranki ya daɗe"
"Baƙo? Ai ni ban yi da kowa zai zo ba, amma ya yake?"
Ta tambaya tana cigaba da yatsina fuska "I, to ba laifi dai ɗan gayu ne gaskiya, yana da jiki amma ba sosai ba kuma dogo ne amma baƙi mai kyau kuma, kun dace fa sosai" Ta yi shiru tana nazari, Mum ɗin ta girgiza kai kawai ba ta saka musu baki ba.
"Je ka gani nan zuwa." Ya juya ya fice ita kuma ta cigaba da abin da take yi, ta kwashe kusan minti goma a zaune ba ta miƙe ba. "Shanyar da kika yi ai ta bushe haka madam, ko duk cikin jan ajin ne?" Cewar mum ɗin ba tare da ta kalle ta ba. Miƙewa ta yi tsaye ta ba shi wayar sannan ta nufi ciki.
Doguwar riga ta sako ta naɗe kanta da mayafin rigar sannan ta sakko ta fice, mum ta bi ta da kallo.
Harabar gidan ta isa tana rarraba ido, sai kuwa ta hango shi tsaye ya kwanta jikin motar hannun shi akai yana latsa wayarsa, gabanta ya ɗan faɗi don ta so ta gane shi, ta matsa ta masa sallama. Juyowa ya yi ya zuba mata manyan idanunsa. Ta sunkuyar da kai don kwarjini yake mata sosai.
"Hajiya Nawwara, da fatan na faɗi sunan daidai." Ta gyaɗa kai kawai ba ta ɗago ba. Sai kuma ta ce "Mu ƙarasa daga ciki" Ba musu ya bi ta suka jera "Bissimillah ina zuwa." Ya gyaɗa kai ya shige ciki ita kuma ta juya cikin. Kicin ta leƙa ta tarar ƴan aikin na ta hidima "Salame ina da baƙo ki kawo masa abin motsa baki ɗakin baƙi." Daga haka ta juya ta koma can ɗin.
Ƙamshin turarensa ya dake ta, sosai ƙamshin ke mata daɗi, ta zauna kan kujerar ita ma tana satar kallonsa sannan ta ce "Barkan mu da warhaka" Yawwa shalele"
Ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido, ta sunkuyar da kai "Ya Salam!" Ta furta a ƙasan ranta, domin ita kaɗai ta san halin fa take shiga idan suka haɗa ido. Sallama mai aikin ta yi ta kawo masa abubuwan sannan ta juya ta fita. Ya dawo da kallonsa kan ta ya ce " To da farko dai ni sunana Aliyu, Ali zaki kenan. Kuma tun ranar da na gan ki Allah ya dasa mini ƙaunarki a raina, a kodayaushe da shi nake kwana nake tashi har kuma na ji ba zan iya cigaba da jurewa ba tunda na gano gidanku har sai na zo na isar da saƙon zuciyata, ban zo da wasa ba idan har kin amince da ni ina son ki da aure." Ta yi shiru ta kasa magana, domin idan ta ce wannan haɗaɗɗen gayen na gabanta bai mata ba ta yi ƙarya kuma ta yaudari kan ta. "Kin yi shiru, ina son jin gaskiyar abin da yake ranki game da ni" Idon shi a kan ta. Har lokacin ba ta yi magana ba "Shirun ki na nuna kin aminta da ni kenan" Sai kawai ta saki murmushi ta tsinci kanta da gyaɗa kai."
Shi ma murmushin ya yi yana furta Alhamdulillah.
Bai taɓa zaton abin zai zo masa da sauƙi haka ba, ko maganar da yake ta yi ɗin ma ya daure ne sosai a hakan gudun damar shi ta kufce "Shike nan ni bari na tafi da ma ina da uzuri, kuma na ga kin kasa sakewa da ni yau ɗin, kar ki yi bacci da wuri zan kira ki anjima"
"Da ma kana da numberna?"
"Ina da ita mana, idan na kira ki na san za ki gano abin da na ce na na jima ina tare da ke."
"Ok" kawai ta ce, daga nan ya mata sallama ya tafi bayan ya dire siye-siyen da ya zo mata da shi ya sa aka shigar mata da su ciki.
Misalin sha ɗaya na dare Nuratu na zaune a tsakiyar makeken gadon nata da ya cinye rabin ɗakin, tana gudanar da binciken da ta saka gaba a kwanakin, domin ranar ma ba ta je aiki ba sun ba ta hutun sati ɗaya ta gama warwarewa gabaɗaya, sai dai kullum Zaitun ɗin sai ta zo ta duba ta take wucewa. Kamar daga sama ta ji wayarta ta hau ruri, gabanta ne ma ya ɗan faɗi domin ba a taɓa kiranta a irin wannan lokacin ba, sun yi waya da Barister tun tara na daren. Ta bi lambar da kallo ba suna sai kawai ta katse, aka kuma kira ta kuma katsewa, daga ƙarshe ma sai ta yi banza da wayar sai dai ta ƙaraci rurinta ta katse. Gabaɗaya takaici ya gama cika ta don ba ƙaramin takura mata kiran ya yi ba.
Kiran ƙarshe na katsewa ba a fi minti biyu ba ta ji saƙo ya shigo, da farko ta share sai kuma ta ji tana son sanin wanene. Abin mamaki lambar da ake turo mata saƙonnin nan ce "To! Sabon salo kiran sallah da usur, ka shirya bayyana kan ka kenan shi ne kake kirana, buɗe saƙon ta yi "Na so kuma jin zazzaƙar muryar ki kafin na kwanta ashe hakan ba zai samu ba, bayan na roƙi alfarma ɗazu akan a jira ni zan kira, bakomai na haƙura ma yi magana gobe. Amma dai yau ni kaɗai na san yanayin da nake ciki na farinciki tunda har na kawo miki ziyara mun ga juna, da fatan bawan Allahn ya shiga zuciyar ki kamar yadda kika shige tashi ya rufe ruf, sai da safe ki yi bacci mai daɗi haɗi da mafarkina, wani bawan Allah"
Ta kuma maimaita karanta saƙon, kanta ya mata wani dum. "Anya wannan kan shi ɗaya kuwa? A ina muka haɗu ɗin yaushe na gan shi? Da alamu kana shan ƙwaya." Ta kuma duba lambar da ya kira ta ita ɗin ce dai da yake turo mata saƙo don ba ta adanata ba. Danna lambar ta yi a black list, don ita ba ta son takura da ma duk wanda ta ji zai takurata yanzu za ta rufe shi rufff ta ci gaba da abin da take yi, sai ɗaya na dare ta kwanta.....
[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
31
Yau ta tashi da niyyar komawa aiki, tun dare suka yi da Barister kan ya zo tana son ganin sa, ya ce da yaushe ta ce idan ta fito aiki sai ya ɗauke ta su tafi.
Tana fitowa a ɗakin suka yi kiciɓis da daddy "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, a'a ina kuma za ki je?" Ya tambaya ganinta cikin shiri "Aiki zan koma yau."
"Aiki kuma? Ba hutun sati suka ba ki ba? har yanzu fa ba ki gama warwarewa ba." Mamyn ta caɓe zancen "Na warke fa sumul ƙalau Mamy, yanda nake jina zan iya