Author : Hilfat Category : Romantic Hausa Novels
domin ba a yi mata a hankali ba. "Ki gaggauta ba mu duk wasu bayanai da shaidu da kika tattara idan ba haka ba sai na lahira ya fi ki jin daɗi." Cewar babbansu, babu alamun wasa a fuskarsa, ta masa wani irin kallo kafin ta buɗi baki ta ce "Ban gane a kan me kake magana ba."
Bai tanka mata ba ya kalli na kusa da shi. Bata yi aune ba sai ji ta yi ya damƙi gashin kainta kafin ya sa ƙarfi ya fara dukan bakinta. Azaba ta sanya ta rintse ido ta fara ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa, ji take yi kamar ba a duniyar take ba. Shi kam bakin nata kamar ba a jikinta yake ba haka take ji. Take jiri ya fara kwasarta, jini kuwa tuni ya gama wanke mata gaban doguwar riga ruwan madara da take jikinta.
"Har yanzu ba ki fahimci me nake magana a kai ba ko? Wannan ba iya tunaninki ba ne, ke da su waye ke shirin tono sirrin da muka ɗauki lokaci muna binnewa a doron ƙasa? Ko kin ɗauka ke kaɗai ce mai wayo? To oga ya gano kina bibiyar wayarsa da son tona masa asiri, to yadda ba ki duba kasancewarsa na jikinki ba, ya ce kar mu miki da sauƙi kema ba zai duba wannan ba. Ina mai tabbatar miki za ki yi dana sani mai girma, domin allura ce za ta tono garma, wuƙa ce kike shirin daɓa wa kanki da kan ki, da ma kaza garin tone-tone take tono wuƙar yanka ta."
Numfashinta na fita da ƙyar ta fara ƙoƙarin magana "Ko za ku kashe ni ba zan taɓa ba ku bayanan da na ɗau lokaci mai tsayi ina ƙoƙarin haɗawa ba, domin ni ba raguwa ba ce ballantana barazanarku ta tsorata ni, kuma ni kaɗai nake gudanar da aikina ba tare da taimakon kowa ba, aikina na saida rai ne na yarda na mutu ko na rayu domin kawo ƙarshen matsalar da ta addabi al'ummar ƙasata."
"Hahhhhh ba ki daku ba ne, idan kin ji wahala ai za ki magantu." Ya kuma faɗa, ba ta san ya iso gabanta ba sai ji ta yi an ɗaga fuskarta kafin aka buɗe bakinta ta ƙarfi, wani irin ƙarfe ne a hannunsa ya zura cikin bakinta sai ji ta yi yana ƙoƙarin cizgo mata haƙori, tun daga jijiyar idonta zuwa kanta ne ya amsa take jikinta ya ɗau karkarwa, jin fincike mata haƙoran gaba gaba guda biyun daga bakinta ya yi silar ɗaukewar jinta da ganinta, daga nan ba ta kuma sanin a duniyar da take ciki ba.....!
Turƙashi! Ƙaraƙaraƙaƙa. Anan free pages suka zo ƙarshe, ba a yi komai ba tukunna labari yana gaba. Wasa farin girki yanzu za a shiga cikin littafin gadan-gadan. Na san kuna da tarin tambayoyin da kuke buƙatar amsoshinsu a cikin littafin wanda dole sai a cikin sauran labarin za ku same su.
Shin Nuratu na kuɓuta daga hannun waɗanda suka kamata? Ko tana rasa rayuwarta ne?
Nawwara za ta sauya ƙudirinta daga mai yi wa mahaifinta aiki har ta binciko lamarin mahaukaciyar nan ko za ta ɗora daga inda ta saba ne?
Shin tsakanI Yayan Nuratu da mahaifinta wanene mara gaskiya?
Wanene Aliyu/gadanga/ƙusar yaƙi, menene asalin labarinsa?
Wanne ɗan siyasa ne ke ɗaure ƙugun garkuwa da mutanen da ake yi har yake aiko da makamai ana kashe mu raba da shi?
Nuratu da Nawwara ya ƴar tsamar dake tsakaninsu take kasancewa? shin suna da alaƙa ne ko babu duba da kamar da suke yi?
Tsakanin Nuratu da Nawaara wacece jarumin ke so, kuma ya abin yake kasancewa?
Shin wanene ɗan adaidaita sahun nan a wurin Kidnappers ɗin nan?
Me yasa Gadanga ke kai kuɗin da ya samu gidan mabuƙata ba tare da ya ci ko asi ba?
Menene burin Nuratu na gaba da take son cimma shi, shin yana cika kuwa ko Nawwara ke ƙarasa mata? Wanne hanyoyi take bi?
Wacece mara lafiyar nan mai cutar ɓarin jiki?
Dukkan amsoshimku na cikin cigaban wannan littafin. Ki biya 500 kacal post sau ɗaya a rana, ki more karatun wannan littafi mai cike da hargitsi da kuma turka-turka.
FATIMA UMAR OPAY
9036257038
Shaidar biya ta wannan number 09036257038
KADA KU BARI A BAKU LABARI.
HILFAT