Chapter 18 Reading Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat Arewa Novels

Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat

Author :  Hilfat Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   18 / 19

51K to 54K   out of 54.7K words

gudun kilomita biyar." Tana murmushi "Na ƙi wayon ba inda za ki je sai nan da kwana biyu." Ta marairaice "Don Allah mamy kar ki hana ni, wallahi fita ta na da muhimmanci."

"To ai ni sababbin masu tsaron nata ma da na ɗauka jibin na ce musu za su fara aikin nasu." Daddyn ya faɗa, take ta haɗe rai "Wai daddy wasu ka ɗauka mini? Wallahi ni ba na so kawai a bar ni nake fitata ni kaɗai ko direban nan ba na so wallahi"

"A kan me za ki ce ba kya so, wai meyasa ba kya tattalin lafiyarki ne ke?" Mamyn ta ce cikin faɗa. "Ni wallahi takura mini suke yi kwata-kwata ba na samun sakewa idan suna tare da ni kamar an ɗaɗɗaure ni haka nake ji, ni wallahi wannan ba gata ake mini ba takura ce" Mamyn ta buɗe baki za ta kuma magana daddyn ya ɗaga mata hannu. "Rabu da ita tunda ni za ta baɗawa ƙasa a ido, na mata abin kirki ta ce ba gata aka mata, ki je duk inda za ki je ɗin ke ɗaya sai ki kula da kan naki ni ma kuɗina ya huta."

"Yawwa daddyna godiya nake" Ta fice da sauri, mamyn ta girgiza kai "Ɗan yau ma a bar shi, ita sam ba ta gane gatse ka mata ba, naga kamar ranka ya ɓaci kar ka ɓata ranka akan ɗan wannan, tunda ba ta so ɗin a ƙyale ta a bi ta da addu'a da ma Ubangiji ne ke kare bawansa ai. Kuma kwana nawa ya rage mata ma a gaban namu." Ta cigaba da rarrashin shi har ya fahimta, daga nan ta shiga kicin domin ganin ayyukan da ta saka yadda suke gudana, kasancewar a ranar za a kawo lefen Nuratu ɗin shi ne ake ta shirya abubuwan tarar baƙin.

Tana fita ta doshi get, direban ya taso da sauri, ta ɗaga masa hannu kawai ta nufi motar da Barister sahabin ya zo a ciki, ta shige, get aka buɗe musu suka fice. Sai da suka fara tafiya sannan ta kalle shi ta ce "Kasan me yasa na ce ka zo?" Ya girgiza kai "Sai kin faɗa gimbiya"

Garin tone-tone na fa na tono wani babban al'amari da zai girgiza mutane da dama."

"Hmmm agogo sarkin aiki kenan, wai ke kam ba kya gajiya ne daga wannan sai wannan?"

"Ka manta abin da na karanta? Ai aikin mu da aikin police ba na ragwaye ba ne sai jajirtattu."

"Mu namu aikin shi ne na ragwayen ko?"

Ta yi dariya "Ni ban ce ba kar ka canja mini magana, kuma aikin ku yana taimakawa al'umma sosai ai, duk tafiyarmu ɗaya da ku ɗin."

"To na ji, amma ni ban yarda ki yi wannan aikin da kike faɗa ba gaskiya, saboda kina wahalar mini da kan ki kuma jikinki ba na wahala ba ne."

"Ni kuma ka ga ina jin daɗin aikin nan nawa musamman idan na zaƙulo wani abu da aka samu gyara a cikinsa silata, ko na karanta labarai aka samu mutum ɗaya ma da ya zama izina ga rayuwar shi to ni fa an biya ni"

"Gaskiya to wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe, kuma ko kin gama ko ba ki gama ba ana ɗaura aure da ma a waje za ki bar aikin nan ki shiga gidana salin'alin, da ma na faɗa musu ma kar ya wuce sati biyu ko kwana goma, da sati ɗaya ma zan ce."

Ta ɗan fiddo ido "Haba dai sati biyu, kamar an gaji da ni a gidan, mamy ma wata ɗaya ta ce da don ta ni ce ma wata uku za a tsayar wallahi"

Ya ɗan ɓata rai "A'a kin manta shekara uku, ai da ma ba damuwa kika yi da ni ba na jima da fahimtar haka."

Ganin ransa ya ɓaci ta ɗan saki fara'a "Kar ka ce haka don Allah, kawai dai aikin nawa ne ba zai kammalu a tsukun nan ba saboda guda biyu ne, a bar shi a wata ɗayan zan yi iya yina wurin kammala shi a cikin wannan lokacin."

"Shike nan na ji, yanzu wanne irin aiki ne kuma wanne taimako kike so na ba ki." Ta kalli agogo ganin sun iso ciki "Yanzu ina kan bincike ne saboda ina buƙatar ƙwararan hujjoji, duk hujjar da na samu zan dinga damƙa ta a hannunka, idan komai ya kammalu sai mu je ga hukumar." Ya gyaɗa kai yana mai sara mata, ta yi murmushi ta fita a motar ta shiga ciki, sai da ya ga shigarta sannan ya ja motar ya bar wurin, shi kaɗai ya san yadda yake jinta a ran shi, ji yake kamar ya ce a ɗaura auren ma a ranar kawai a wuce wurin, amma ya san hakan ba zai yiwu ba wata gudan kamar yau ne ai.

Kamar yadda yace ɗin kuwa a ranar aka kawo lefen, kuma sati huɗun aka tsayar, gaskiya ya yi bajinta sosai akwati goma sha biyu shaƙare da kaya masu tsada, aka yi komai cikin mutunci dangi na ta zuzuta Nuratun ta yi goshi, ko da ta dawo suna ta tsokanarta ta gudu ɗaki ta kulle. Tana ganin abin kamar ba gaske ba.

Tsawon sati guda tana tana ta harhaɗa hujjojinta kuma tana damƙa su ga shi. A ɓoye ta shirya ta je hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta faɗa musu abin da ke tafe da ita, kuma suka ƙarfafa mata gwiwa akan lamarin. A yanzu hujja ɗaya ta rage mata kuma ta rasa ta yadda za ta same ta. "Yau ta kama Week end gidan shiru sai ita kaɗai, duk sun fita gidan bikin da ake yi a dangin nasu, yayin da ta lafke cikin bargo tace ba ta da lafiya.

Tafiya suka yi bayan ta ce ta kula da kan ta kafin su dawo. Sai da aka ɗauki aƙalla awa ɗaya sannan ta fito a ɗakin nata. Ta leƙa wajen sun tafi tuni sai mai gadi da ta hango, da ma ta ji fitarsu, rufe ƙofar shigowa falon ta yi ta bar makullin a jiki. Kai tsaye ɗakin nasa ta nufa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi. Ba ta yi mamakin jin shi a garƙame ba, da ma ta san hakan za ta faru. Inda ake ajiye spare keys ɗin gidan ta nufa ta ɗauko sannan ta dawo, tana sakawa kuwa ɗakin ya buɗu.

Ta bi koina da kallo sannan ta shiga ta fara ɗaɗɗagawa amma ba ta samu komai ba. Sai ta buɗe sif tana ɗaga kayan a hankali. Daga can ƙasan kayan ta ji ta taɓa abu, janyowa ta yi, ba shiri ta saki a ƙasa tana dafe bakinta da dukkan hannuwanta cikin zaro ido. Duk da abu ne da ta jima da sani amma ganinsa a zahiri ya yi matuƙar kiɗimata. Ta duƙa ta ɗauka hannunta na rawa, kallon ledar kawai take yi, sai kuma ta yi sauri ta fara ƙoƙarin mayar da komai yadda yake, sai da ta kimtsa su sannan ta fito ta mayar da ɗakin ta rufe.

Kai tsaye ɗakinta ta shiga ta ɗauki wayarta ta lalubo lambar ta danna kira ƙirjinta na lugude har wata zufa ce ke karyo mata "Na samo, wallahi na samo hujja ta ƙarshe bincikena ya kammala komai ya bayyana, ka zo an jima sai mu ji yadda za a yi."

"Kash! Ba ka gari, to mu bar wa goben Allah ya kai mu, zan tura maka inda za mu haɗu da lokaci, yawwa na gode." Ta kashe wayar sannan ta kira ɗaya lambar, ana ɗagawa ta ce "Yallaɓai na samo abar fa a ɗakinsa, na gama nawa aikin saura naku, za mu shigo gobe na kawo muku, shike nan to bari na ɗauka ɗin sai na turo."

Ta ɗauki hoton ta ta tura musu ta whatsapp sannan ta goge duka. "Haba biri ya yi kama da mutum, abubuwan da kake yi ya yi yawa, lokacin fallasuwar komai ya yi ba zan zuba ido yayan jama'a na cutuwa ba kuma ina da ikon daƙilewa." Wani tunani ne ya zo ranta.

Sai kawai ta ɗauka ta saka a jakarta ta ɗauki hijabi da key ɗin motarta ta fice a ɗakin. Sai da ta kulle koina sannan ta bar gidan.

Lokacin da ta dawo tana fargabar abin da za ta ce idan har sun riga ta dawowa, sai kuma ta tarar ba su dawo ba, hamdala ta yi a ranta sannan ta shige ciki. Zama ta yi tana tunanin abin da ta ci karo da shi da ta fita, wanda shi ne dalilin jimawarta ba ta dawo ba.

"Wato idan kana wannan aikin ka dinga gamuwa da matsaloli kenan. Na yi alƙawari daga iya ayyuka biyun nan zan ajiye aiki amma ga wani na yi karo da shi lokacin da na gama ɗaya ya kenan" Ta yi shiru take wani tunani ya faɗo mata. Wayarta ta janyo ta shiga rubuta wani dogon saƙo da ya ɗauke ta lokaci tana rubuta shi sannan ta tura ga lambar da ta samo ɗin ta ajiye wayar. Wanka ta yi sannan ta dawo falon ta zauna, tana zama suna sallama suka shigo.

"Sai yanzu mamy bayan kun san kun bar ni ni kaɗai a gidan?" Ta ce a shagwaɓe "Yenyenyenyenn mai kama da kwallar shayi tsabar gajerta" Nuran ya gwasale ta yana riƙe ƙugu, ƙin kula shi ta yi sakamakon wani iri da ta fara ji yanzu game da shi mai kama da jin haushi ko tsana ya mamaye ta "Afuwan ɗiyar kirki, wallahi riƙe ni suka yi ƴan uwan suka hana ni tahowa kin san an jima ba a haɗu ba, to ya jikin" "Da sauƙi Mamy"

"Amma ya naga idon ki ya yi wani iri kuma ya yi ja kuka kika yi ma,kai gabaɗaya ma ba a nutse kike ba." Ta tsatstsare ta da ido tana son gano wani abu....

[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: *WOMEN OF WORDS*

_Writers Association_

*(WOW)*

*TURMIN DANYA*

*NA*

*FATIMA UMAR KAS*

_HILFAT_

32

Ta yi ƙoƙarin daidaita nutsuwarta, sannan ta ƙaƙalo murmushi ta wanzar a saman fuskarta ta ce.

"A'a Mamy baccin da na yi ne, kin san tunda kuka tafi nake bacci sai yanzu na tashi. Ina daddyn?"

"Kiran gaggawa ne aka masa ya tafi shiru bai dawo ba kuma, sai kawai da na kira shi ya ce mu taho." Ta gyaɗa kai alamun gamsuwa. Ko da daddyn ya dawo bai kula kowa ba ya haye sama. Kasancewar duk a gajiye suke da wuri suka nufi makwanci. Ga Nuratun kuwa ta matsu gari ya waye ta fita su ƙarasa aikin nasu, ta yarda aski idan ya zo gaban goshi ya fi zafi.

Nawwara ta janyo wayar tata ganin saƙo ya shigo da baƙuwar number, take ta buɗe ta fara karantawa. "Assalamu alaikum, na miki sallama ne saboda sanin muhimmancinta a cikin addininmu. Bari na tafi kai tsaye ga abin da ya kawo ni, amma idan kin ji ruwanki ki yi abin da ya dace ruwanki ki banzatar kamar yadda kika saba. Kar ki yi mamaki idan na ce na san komai game da ke, tun daga makarantar da kika yi karatu Police academy wudil, zuwa yadda kika dinga faɗuwa jarabawa mahaifinki na siya miki, kawo yadda lokacin da aka zo yi muku training kika dinga faɗuwa, ko atisaye ba kya iya wucewa da an fara kike cewa kin gaji. A tsalle ma ba ki dace ba faɗuwa kike yi, haka a wurin iya harbi ma kin kasa iya saiti. Amma a hakan ya tsaya miki kai da fata sai da kika samu aiki. Kuma abin da yake so wato sufeta ta yankinsa. Ba wannan ne a gabana ba tukunna sai kin cigaba da shiga mini hanci da ƙudundune ne zan fato ki. Abin da ke tafe da ni ɗazu na haɗu da wata mahaukaci ta faɗo titi ƙiris na bige ta Allah ta taƙaita, abin mamakin matashiya da ba ta wuce shekaru ashirin ba a duniya, na siya mata abinci na ba ta kuɗi, a lokacin ƴan uwanta suka zo suka fara janta tana turjewa domin komawa da ita gida, anan na ji ashe ba a san ta fito ba. Na taya su riƙe ta muka je har gidan nasu, sai dai maganganun da take yi ya nuna wani babban al'amari ya faru da ita. Tana ta cewa "Allura uku ya caka mini, ya ba ni wahala, ina so na yi kuka ban iya ba." Abin da take ta maimatawa kenan da ƙarfi tana muzurai kamar zata kai duka, suka samu suka tura ta ɗaki, na tambayi mahaifiyarta dalilin haukanta kawai sai ta ce mini sanadin fyaɗe ne da aka mata daga nan ta haukace. Hankalina ya tashi sosai na nemi su mini cikakken bayani amma sun ƙi sun ce abin da suka sani kenan su ma tsintar ta suka yi a haka, na lura suna ɓoye wasu abubuwa ne sai kawai na rabu da su. Na yi iya tunanina kuma abin da na fahimta shi ne wannan yarinyar fyaɗen da aka mata sai da aka gusar mata da hankali sannan ba sau ɗaya aka mata ba, da alamu wanda ya mata ɗin ajiye ta ya yi a gidansa yake ta banka mata allurar miyagun ƙwayoyi har sai da ta rasa hankalinta duba da maganganun da take ta faɗa. Ya rage naki ki binciki al'amarin don gano me ya faru kuma wanene azzalumin? Yarinya kyakykyawa an ɓata rayuwarta tur da dabbanci irin na wasu mutanen. Yanzu zaɓin naki ne, ko ki tsaya ki yi aiki tsakani da Allah ki tsira a ranar gobe ƙiyama ko ki cigaba da aiki saboda mahaifinki, abu ɗaya nake so ki dinga tunawa rantsuwar da kika yi kafin ki fara aikin. Idan kina son cikakken bayani na gidansu yarinyar za ki iya tuntuɓata. Na barki lafiya, Nuratu Attahir Mai nasara (Abokiyar tsamarki)

Shiru ta yi bayan gama karanta saƙon, gabaɗaya jikinta ya mutu murus zuciyarta kuma ta yi rauni da wannan alamarin, me ya kamata ta yi yanzu? ta shiga dogon nazari tunani haɗi da nazarin maganganun.

Washe gari Nuratun ta fito cikin shirinta na fita, ta iso wurin Mamyn dake zaune ita kaɗai a falon "To mamy a mini addu'a yau aikina guda ɗaya zai kammala." Cikin sanyin jiki ta ce "Anya ba haƙura za ki yi da fitar nan ba?"

"Me yasa mamy"

"Haka kawai nake jin zuciyata na yawan tsinkewa tunda na tashi, ni dai da za ki haƙura da abin nan da kike yi da yafi" Ta ƙarasa a sanyaye, murmushi ta ƙaƙalo saboda itama gabanta faɗuwa yake ta ɗan yi "Ba abin da zai same ni sai alkairi Mamyna, koyaushe fa cikin adduarku nake yanzu ma ita za ki mini."

" Shike nan Allah ya tsare ya bada sa'a, ki kula mini da kanki"

"Amin in sha Allahu, sai na dawo." Tana shirin juyawa ta bangaje shi har wayar da ke hannunta ta make shi a gefen ido. "Ke kula mana kina neman yi mini ido ɗaya ki mini toshi." Ya ce yana riƙe wurin

"Wayyo sorry ban kula ba" Ta faɗa da sauri "Da ma ai ba za ki kula ba kina sauri ki tafi inda za a ke wasa da rayuwarki kina neman ki rage mini farashi." Dariya ta yi tana girgiza kai jin abin da ya ce "Yaya, yaya, Allah ya barka" Ta juya ta fita tana musu sallama.

A daidai inda suka yi za ta jira shi ta tsaya tana waige-waige, amma ba ta hango shi ba. Wayarta ta zuge jaka ta ciro da niyyar kiran shi, kwatsam ta ga wata baƙar mota ta tsaya a gabanta, kafin ta yi wani yunƙuri wasu majiya ƙarfi suka fito su uku suka damƙe ta, ɗaya ya shaƙa mata farin ƙyalle, take ta fita hayyacinta tana neman silalewa a wurin. Suka cusa ta a motar suka bar wurin da mugun gudu.

Sun yi tafiya mai nisa kafin suka isa gidan, ciki suka yi da ita. A saman wata kujera suka ɗaura ta sannan suka ɗaɗɗaure ta a jikin kujerar. Ta ɗau aƙalla minti talatin a haka kafin wani ya shigo da ruwa ya kwara mata.

Ruwan da ta shaƙa ne a ya sanya ta farkawa a gigice tana sauke wata wawuyar ajiyar zuciya. Take jikinta ya hau kakkarwa kamar mazari sakamakon ruwan na da azabar sanyi ga kuma muƙu-muƙun da ake yi, sai ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye sai dai ta ji ko gezau bata yi ba domin ko ɗan yatsanta ba za ta iya motsawa ba sakamakon ɗaurin huhun goron da ta sha jikin kujerar da take kai, ta hau kici-kici amma a banza man kare. Sai lokacin ne ta shiga ƙarewa inda take kallo, kafin idanunta suka sauka a kan basamudan mutanen da suke tsaye ƙiƙam a kanta sun zubo mata maganansu, dukkan su sun murtuƙe fuska tamkar magribar ɗinya babu alamun ɗigon imani a tattare da su.

Sai lokacin ƙwaƙwalwarta ta shiga dawo mata da dalilin wanzuwarta a wurin daki-daki. Ta runtse idanunta da ƙarfi. 'Tabbas na san dama a rina an saci zanin mahaukaciya, amma alƙawari ne na ɗauka wa kaina kuma duk wuya duk rintsi na yi zaman turmin danya a bisa bigiren da aka dasa shi kan cimma abin da na saka a gaba koda za a daddatsa naman jikina' Ta raya a ran ta.

Fincike baƙin gam ɗin da yake liƙe a bakinta da aka yi shi ya dawo da ita daga taƙaitaccen tunanin da ta tafi. Ta yi 'yar ƙarar azaba

18 / 19