Chapter 15 Reading Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat Arewa Novels

Turmin Danya Book Compelet BY Hilfat

Author :  Hilfat Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 19

42K to 45K   out of 54.7K words

*NA*

*FATIMA UMAR KAS*

_HILFAT_

26

Tuni mahaifiyar tasu ta shige ciki, tana dube-dube. Nuratun ba ta bi ta kan su ba ta ƙarasa inda ɗakin da aka kwantar da shi yake sai kawai suka mara mata baya su ma.

Karo suka ci da wata maaikaciyar "Don Allah ina Dr." Ta tambaya "Yana office ɗin shi"

"A ina office ɗin yake" Ta kwatanta mata da hannu sannan ta yi gaba, kai tsaye ta nufi can ɗin "Ni dai da an fara kai ni na ga ɗana tukunna." Banza ta mata ta ƙarasa bakin office ɗin ta yi sallama, daga ciki aka ba ta damar shiga.

Ya ɗago ya kalle ta ya gane ta, sai kuma ya bi su da kallo su ma da suka shigo cikin suna rarraba ido.

"Bissimillla ku zauna" Ba musu suka yi abin da ya ce "Ya ake ciki likita ya farfaɗo?" Nuratun ta tambaya "Bai farfaɗo ba kuma da ma ai da wuya ya tashi tunda abin ya fi ƙarfin kwanyarsa, mun yi iya yin mu amma abu ya faskara, Allah ya karɓi abinsa."

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" Suka faɗa kusan a tare "Sakaci da ganganci irin na iyayen shi ya sa ran shi ya salwanta, yaro kamar wannan ace wai ya sha cocain to ta ya ya ma?"

"Kana nufin hodar iblis ya sha? Mun shiga uku" Mahaifin ya ce a ruɗe. "Ba ku shiga uku ba tukunna, sai ubangiji ya tsayar da ku ku da shi a ranar gone alƙiyama yana tambayar ku yadda kuka kula da shi. A hanyq fa ina mota na hango ya yanke jiki ya faɗi, ina zuwa na tarar farar kumfa na fita a bakinsa ga idon shi na kakkafewa, na tambayi ƴan uwansa me ya ci? suka nuna mini wani abu a leda wai shi ya sha, ina karɓa na gane abar ce. Kuma da wata a a hannnsu a baƙar leda a ƙuƙƙule na karɓe na watsa a kwata, yanzu kamar waɗannan yaran bai dace ace suna makaranta ba?"

Nuratun ta faɗa a fusace cikin takaici, mahaifin nasu ya juya ya fita yana haɗa hanya, sai ga shi ya dawo da yaran "Kai wa yake ba ku wannan abin da Adamu ya sha?"

"Wani ne yake ba mu muke siyar masa kullum idan mun fito bara sai ya ba mu abinci da lemo da kuɗi, to shi ne yau shi Adamu ya ce bari ya sha ya ji akwai daɗi? sai kawai ya faɗi yana sha."

Mari ya zabga masa yana huci "A gidan uban wa yake shi laanannen da yake ba ku ɗin?"

"Ya ce idan wani ya tambaye mu inda yake muka nuna sai ya yanka mana wuya, har wuƙar ya nuna mana." a tsorace

"Don ubanku ku faɗa mini inda yake wallahi baza mu yarda ba, ɗana fa ya yi silar kashe mini." Ya kuma kai wa ɗayan mari, cikin sauri uwar ta janye su tana huci itama. "Kar ka kuma dukansu, babu abin duka irinka. Da ka tsaya ka kula da mu hakan za ta faru ne? Kullum kana gida ba ka san cin mu bare shan mu ba sai dai yara su yo bara su zo su ci? Daga wannan inuwa ka koma wannan ba ruwanka da ilminsu shan su cin su suturarsu? Sai Allah ya saka mana wallahi." Ta fice tana kuka. "Likita mu je a ba mu gawar tasa mu tafi" Ya ce cikin sanyim jikin da maganganun nata suka saka masa.

Bayan gama komai aka ba su gawar, ta fito ɗaya yaron na biye da ita za su sauke shi a hanya ta shige motarta suka nufi gida abin duniya duk ya dame ta. "Ka ga ka faɗa mini inda mutumin nan yake, ba tare da kai zan je ba kuma ba zai san kai ka faɗa mini ba" Ya girgiza kai yana hawaye "Zai kashe mu, ya rantse ya kuma rantsewa." Ganin duk a tsorace yake sai ta rabu da shi har ya ce a sauke shi a wata danja, amma ta ƙudurce sai ta yi iya yinta ta samu bayanai a bakinsu, domin Allah kaɗai yasan yawan yaran da ya ɓata wa rayuwa.

Ta tarar da su duk ba a nutse ba suna zaman jiranta, tun anan ta kwashe komai ta sanar musu, su kan su jikinsu ya yi sanyi suka dinga sallalami, daga nan ta shiga ɗaki ta yi wanka ta fito ta ɗan ci abinci. Wannan abin da ya faru shi ya tada mata miƙin da yake ƙasan ranta na wani binciken da take son yi, don haka tun a daren ta fara aiwatar da ƙudurinta. Wasu lambobi ta samo da mutum kan haɗa domin jin wayar wani, ta lalubo lambar da take son bibiya ɗin ta haɗa da tata lambar sannam ta kwanta cike da tunanin abin da ya faru a yau ɗin.

Wata dattijuwar mata ce kwance magashiyan, babu inda yake motsi a jikinta idan ka cire idanunta. Budurwar da ke zaune a gefen kanta ce ta ɗago ta daga kan filo ta saka mata ruwa a baki tana ta jera mata sannu. Ɗayar kuma na ɗayan gefen tana yi mata fifita, sai da ta gama ba ta ruwan sannan ta mayar da ita ta kwantar tana gyara mata kwanciyar sosai. Sallama aka yi daga bakin ƙofa duk suka waiga. Dattijo ne shi ma sosai ya shigo ya ajiye buta sannan ya ƙaraso ya zauna kan kujera ƴar tsugunne da take gefe. "Hamida ki samu ki ba ta abincin mu gani ko za ta ci", Ya faɗa "To baba barina gwada mata mu gani, ɗazu na ba ta ta ƙi karɓa, kwana biyun nan ba ta cin abinci fa." Ta ce cikin rauni "Ni ma na lura da hakan wallahi, amma ƙara gwada mata mu gani, Safiyya ɗago ta sai ta ba ta" Ɗaya budurwar ce ta matsa ta ɗago mata ita. Amma sam ta ƙi buɗe bakin ta karɓa "Yanzu Sahura a ce haka za a yi jinya babu cin abinci? Ko yaya ne ai yakama ki ci shi ma rashin cin abincin ciwo ne mai zaman kan sa."

Tunda ya fara maganar take kallon shi, kawai sai ga hawaye suna silalo mata "Don Allah ki yi haƙuri ki ɗauki ƙaddara, kukan nan ba shi da wani amfani." Yace cikin rauni, jikinsu ne ya yi sanyi, ta mayar da ita ta kwantar tana goge mata hawayen. Duk suka yi jigum-jigum.

Sanye take da wani ɗanɗasheshen leshi mai azabar kyau da tsada ruwan ganye an masa adon fulawowi da ruwan ƙasa, ba ta ɗaura ɗankwali ba sai ƙaramin mayafi da ta yi rolling da shi ruwan ƙasa ta saka ƙaton gilas ɗin da ya cinye rabin fuskar tata. Siyayya take yi a wurin Areef na biye da ita.

Yana shigowa ciki idon shi ya yi faringani, ya tsaya cak yana kallonta, sosai ta masa kyau don haka ya ciro wayarsa yana mata hoto a fakaice, sai da ya mata ya yi kala biyar sannan ya mayar da wayar aljihu yana fakar idon mutane, gyara zaman facemark ɗin fuskar shi ya yi sannan ya ƙarasa wurin da ake biyan kuɗi ya miƙa ATM ɗinsa "Ka ciri duka kuɗinta anan" Ya shuna masa ita sannan ya koma gefe ya cigaba da duba abin da yake buƙata.

Isowa ta yi wurin ta ajiye musu kayan sannan ta zaro nata ATM ɗin ta miƙa musu "An biya hajiya" Cikin rashin fahimta da tsiwa ta ce "Ban gane ba wanne ƙoƙararren ne ya biya ko na ce ba ni da kuɗin biya ne" Ya nuna mata shi da hannu. Ta ɗan bi shi da kallo sai kawai ta nufe shi a fusace "Malam" Ya waigo ya saka idanunsa cikin nata, take ta diririce ta ji tana neman rasa nutsuwarta, kallon da ya mata ne ta ji ya mata kwarjini sosai.

Yana sanye cikin ƙananun kayan da suka amshi jikinsa sosai, tsayayyen namiji kuma dirarre mai ƙirar sadaukai, cikar haiba da zati, ga zallar kyau, idanunsa masu girma ne amma ba su yi fari ba, sun fi kala da idon mage, kuma a ɗan lumshe suke. "Am...In... na je bi.. biyan kuɗi suka ce ka biya, na gode."

"Ba komai, ni ma na gode" Dakakkiyar muryarsa ta dage ta. Daga haka ya cigaba da abin da yake yi, ita ma ta juya ganin bai kuma magana ba.

Yana ganin ta fita ya je ya karɓi ATM ɗin nasa ya fice shi ma, motarsa ya faɗa yana cigaba da kallonta ta cikin motar, sai da ya ga tafiyarta sannan ya ja ya bar wurin shi ma zuciyarsa fall farincikin yau dai ba ta masa wannnan mugun kallon ba mai kama da na tsana......

[6/23, 7:16 PM] ~HILFAT~: WOMEN OF WORDS*

_Writers Association_

*(WOW)*

*TURMIN DANYA*

*NA*

*FATIMA UMAR KAS*

_HILFAT_

27

Cikin dabara yake bin ta a baya ba tare da ya bari ta gane ba, cikin sa'a ba ta lura ɗin ba kuwa har ta isa gida aka wangale mata get ta shige ciki. Sumar kan shi ya shafa yana sakin ƙayataccen murmushi sannan ya juya ya bar wurin cike da nishaɗin yau dai ya gano gidansu. Wayarsa ya zaro ya rubuta mata saƙo "Yau dai ta faru ta ƙare na yi magana da shalelena har ma kuma na gano gidansu, da fatan kin isa gida lafiya sai na kawo miki ziyara, ɓoyayyen masoyi ya bayyana." Yana rubuta saƙon yana murmushi sai kuma ya sauke facemark ɗin shi yana shafa kwantaccen sajensa zuwa gemunsa.

Nuratu da ke zaune ta ga shigowar saƙon, mamaki ne ya cika ta ganin abin da aka rubuta "Ni kuma? Ko yana shan ƙwaya ne tana faɗa masa ƙarya? gara ka zo ɗin ai na san wanene yake addabar rayuwarta, na kuma yi maka last worning akan bibiyata, wai shalelen shi mtsss can ka nemi shalele." Fita ta yi daga cikin saƙon tana ƙarasa bibiyar sharhin jama'a akan labarin da ta karanta na wutar ƙiyayya tana yi musu reply, ta zo kan wani dogon rubutu sai ta bada dukkan nutsuwarta akan shi 'Assalamu alaikum ina miki fatan alkairi, jinjina ga wannan marubuciya da ta yi tunanin yin rubutu akan wanan matsalar. Wallahi sak kamar ni na ba ta shi ta rubuta. Na kasance ni ma dai kamar Bintu na tsani facalata sam ba na haɗa inuwa da ita, amma ni ba gidanmu ɗaya ba kowacce nata gidan daban kuma mazan namu ba laifi suna da rufin asiri. Ba ni da burin da ya wuce ganin wani iftila'i ya faɗa mata ko ace ta bar duniyar ma gabaɗaya, sam ba ma ga maciji ni da ita. Jin wannan labari ya sa jikina yin sanyi kuma na ji nadama ta shige ni, zan je na nemi yafiyarta mu sasanta kar na je na mutu a haka. A yanzu haka ina rubutun nan ina kuka hango kaina nake a matsayin da Bintu take na zaman gidan kaso, ga alhakin rai ga rasa aurenta da mayar da ɗanta maraya, ga kuma tsangwama daga mutane da aibatawa. Jinjina ga marubuciya, jinjina ga makaranciya na gode.'

Hmmmm ta sauke ajiyar zuciya kawai ta ce mata amin summa amin Allah ya sa mu fi ƙarfin zuciyarmu, domin kuwa ƴan comments section sun mata caaaa suna ta mata reply mai daɗi da mai ɗaci. Duk a hanyarta ta zuwa wurin aiki ne amma za ta fara biya wa ta gidan wannan yaron mai rasuwa, ita ta dinga nuna wa direban hanya har suka isa ƙofar gidan. Da mutane sosai ƴan zaman makoki, ta fito kanta a ƙasa ta shige ciki tana harɗewa domin ta tsani kallo, su kuma duk sun zubo mata na mujiya tun tsaiwar motocin.

Kai tsaye cikin gidan ta shiga shi ma da mutane ba laifi, ta ce matar gidan take nema aka nuna mata ita, tana can zaune cikin mutane da hijabi a jikinta. "Ina yininku?" Ta ce da ɗan ƙarfi saboda ta jiyo, sai kuwa ta ɗago tana amsawa, da sauri ta miƙe tana faɗin "Sannu da zuwa baiwar Allah ƙaraso ciki, wannan itace ta tsinci adamu cikin mawuyacin hali har ta kai shi asibiti ta kuma biya kuɗin komai ashe daii kwana ya ƙare." Tana share hawaye sannan ta kama hannuta har tsakiyar matan kusa da ita. Nan aka dinga mata godiya masu saka albarka na yi "Ba komai Allah ya ji ƙansa, ina ɗanuwan nasa yake ina son yin magana da shi don Allah idan ba damuwa."

"Yana ɗakin can tare da yara, bari a kira miki shi" Tace "A'a bari na same shi acan ɗin kawai" Ta miƙe ta nufi ɗakin, da yara da yawa a ciki har da ɗaya abokin nasu "Ku ɗan je waje kun ji ƴan albarka" Ta ce da yaran tana musu murmushi, duk suka fice kuwa, ta dawo da kallonta kan su "Kun ga dai ɗan uwanku ya mutu shike nan ku da shi har abada kenan baza ku sake ganinsa ba kuma na san ba ku so haka ba kun so ku rayu tare da shi ko?"

Kai suka gyaɗa kusan a tare "To wannan mutumin dayake ba ku wannan abin shi ne ya kashe muku shi, kuma ku ma kamar yadda ya mutu haka yake so ku mutun tunda yana sane yake ba ku guba kuna siyarwa mutane, kuna son ku mutu ne yanzu?"

Suka kuma girgiza kai sannan ɗayan ya ce "Ni dai bana so na mutu yanzu saboda iyayena ma mutuwa suka yi, ina so na taimaki kakata idan na girma tunda ita ce ta rage mini."

Ta dafa kafaɗarsa ta ce "To idan haka ne sai kun nuna mini inda wannan mutumin da yake ba ku guba yake, idan ba haka ba zai cigaba da siyarwa mutane suna sha suna mutuwa har ku bazai ƙyale ba."

"Zan faɗa miki" Ƙaramin yace da sauri "To ina saurarenka" take ya shiga yi matai kwatancen wurin. Ta jinjina kai sannan ta zaro dubu ɗaya ta ba su ta juya ta fita, da ido ta yi mata alamar ta biyo ta, suka dawo soro suka tsaya "Na samu sun faɗa mini inda wannan mugun mutumin yake, zan je na samu ƴan sanda mu je wurin tare da su, duk yadda ake ciki zan dawo na muku bayani, domin baza mu bar wannan abin ya tafi a banza ba dole zai fuskanci hukunci kuma za a daƙile cigaba da faruwan hakan." Ta dinga yi matai godiya, ta zaro kuɗi ta miƙa mata itama sannan ta mata sallama ta fita.

Suna ganin ta fito suka miƙe tsaye su ma daga cikin mutane suka tafi "Police station za ka kai ni" ya waigo ya kalle ta kamar ya yi magana sai kuma ya yi shiru ya cigaba da tuƙinsa, ta harari ƙeyarsa a rainta ta raya 'Ai yau yawo za mu sha da ku, ba dai kun na ce na ce ku rabu da ni nake tafiyata amma kun ƙi?' A bakin police station ɗin suka tsaya, ta ɗan bi wurin da kallo tana tuna wancen zuwan nasi, sannan ta shiga ciki. Karaf idonta ya sauka a kan ta tana tsaye tana ta rubuce-rubuce a cikin wata takadda da ke gabanta a cikin wurin, sanye cikin kakinta. Kallo ɗaya ta mata ta ɗauke kanta. Wurin ɗan sandan da yake kusa da ita ta matsa "Yallaɓai barka da aiki" Cak ta dakata da abin da take yi ba tare da ta ɗago ba amma Nuratu na lura ta ƙasan ido take kallonta "Yawwa madam" Ya ce "Sunana Nuratu Attahir Mainasara, ƴar jarida daga Rigasa radiyo, don Allah idan ba damuwa ina son magana da kai wani abu ke tafe da ni." Ya gyaɗa kai yana ba ta dukkan nutsuwarsa.

"Wani yaro ne ya rasa rayuwarsa sakamakon shan cocain da ya yi, kuma yaran da suke tare da shi sun tabbarar wani ne yake ba su suna siyar masa shi ne ya ɗauki ɗauri ɗaya ya sha. A yanzu dai na yi musu dabara sun faɗa mini a inda yake da zama duk da sun so turjewa wai zai kashe su, shi ne na zo a ba ni jamiai biyu mu je a kama shi." Kai ya gyaɗa alamun gamsuwa sannan ya ce "Maaah ga wani case fa, ya za a yi yanzu?" Yana kallon Nawwara "Ai da kai tace za ta yi magana ka ga iya taimakon ka ya wadatar, duk abinda ya kamata kawai ku yi." Tana cigaba da rubutun ta.

"A'a baza a yi haka ba, ai ba za mu yi wani abu ba tare da saka hannunki ba tunda duk gaba kike da mu a nan yanzu haka, ina ganin za mu je ni da ke da kuma Sajen Tukur."

"Ta kuma girgiza kai "Ba zan fa je ba, idan ba a kasa da ni ba ba na ɗauka, da ta zo wurin ka ga ta kula ni ne? to ni ban iya cusa kai ba kwarjini ba" Ta yi tsaki tana hararar Nuratu ƙasa-ƙasa da ita ma ta cika ta yi fum ganin yadda ake lallaɓata tana wani zillewa. "Madam ko za ki mata magana da kan ki, tun farko ma da ita yakamata ku yi magana sai ta tsara yadda za a yi" Ta masa wani kallo "Ga ta uwata ai dole ta faɗa mini yadda zan yi, Kuma ni da ɗan sanda nake magana ba muna ɗan sanda ba, yadda na dama haka za a sha ita ɗin wa? Magana da ita ma ai ɓata lokaci ne, ni na fita idan kun ga za ku ɗau abin da na zo da shi da

15 / 19