Author : King Boy Isa Category : My Hausa Novels
bullo a office din ganin wayar al ameen da tayi yasata tayi tace da kyau. Wayar ta dauka ta lalubo number zainab ta kira before ta canza murya. dawo da muryarta ta al ameen. Zainab taji wayarta ta hau Ring da sauri ta dauka dan ganin waye. Al ameen ta gani shi yasa tayi Murmushi tace wato baka gaji da jin muryata ba ashe. Ta dauka ta makala a kunne hello Darling.
Daga can marsiyya tayi magana cikin muryar al ameen ba banbanci ko kiris tace hello zeeluv dina. Zainab tace ya naga ka sake kira ko mantuwa kayi ne? Marsiyya tace ko kadan dama kiranki nayi in gaya miki magan mai muhimmanci zainab tace to ina jinka babyna..........................................
Good morning happy juma'a al mubarak
Little of writer's
King boy
🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿
page 69 - 70
|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟5STAR APR 2017 🌟
|_________________________|
***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©5SWA
***** 5 star *****
🌹🌹 dedicated to u zainab yusuf ina godiya da addu'a ki na alkhairi a gare ni ☺
👺👺 sako daga nasmat to readers nasmat tace duk wanda ya karanta wannan page din da rana wuta balbal 😂 ni dai ba ruwana👺👺
Wato a gaskiya dama abunda nake so in gaya miki shini ki fita daga harkata don a gaskiya ba sanki nake ba koda kuwa munci gaba da soyayya to dan in faranta miki kawai zanyi ba wai dan ina sanki ba. Gaban zainab ne ya fadi jin abunda al ameen din ke fada. Koma sai tayi ajiyar zuciya tace.
Naji na gode kuma da ka sanar dani tun yanzu baka bari sanka ya mamaye ko'ina na jikina ba bisa wannan godiya zanyi maka. Amma ina so in shaida maka cewa yaudara ba abu ce mai kyau ba idan kayi wa yayan wasu kaima sai anyi wa naka. Kuma al ameen bana sanka na rabu da kai har abada baza ka sake jina ba. Mtsewwww.ta katse wayen tini ta sankama shi a block wanda ko massage dinsa bazai shigo ba haka ma a whatsapp din tayi block dinsa.
Marsiyya nan take itama tayi block din number zainab wata shu'umar dariya tayi tukun tace shikenan an wuce gun aunty kisha kurumin ki al ameen naki ne ke kadai bari mu koma ga yasmeen itama.
Ba'a dade ba sai naga al ameen ya dawo cikin hanzari ya dauki wayansa da ya manta a lokacin ya kira yasmeen yake shaida mata da cewa tafiya ta kama shi kuma yana tunanin zai fi kwana biyu a can inda zasu din. Gaban yasmeen ne ya fadi ta dafe kirji al ameen me kake fada haka wannan wane irin tafiya ne ni gaskiya ban amince ba.
Kiyi hakuri yasmeen nasan bazamu kai sati ba kuma nasan cewa ban kyauta miki ba amma ba yanda zamuyi domin wannan umarnine daga sama kuma tafiyar nada mahimmanci. Ke dai kawai ki kula.
Al ameen ni gaskiya bazan iya zama a gidan nan ni kadai ba mu biyun ma idan ka tafi aiki karka ga yanda ake tsorata ni balle kuma ace baka nan.
hb yasmeen ba abunda zai kama ki bafa ke kadai bace a gidan ga mai gadi kuma ga driver ni dai dan allah kawai kiyi min fatan alkhairi kinji. Yana fadin haka ya katse wayan domin shi kadai ake jira har ma an fara kwalla mai kira.
Yasmeen jinta tayi jikinta duk ba kwari yanzu gidan nan za'a barta ita kadai gaskiya idan aka cika bata tsoro bazata iya zama ba. Ta gaji da zaman dakin hakan yasata tasowa kamar muna hika take bude kofan sai da ta leko taga magen bata nan tukun ta fito. Fridge ta nufa ta dauko coca cola da dan kofi ta dawo ta zauna gaban katuwar tv din ta kunna kallo.
Arewa 24 ta ke kallo suna wani shiri na addini tsaki tayi ta fito ta fara chanza channel mbc action ta shiga da shigarta da fitowar wani mugun kara duk daya. Nan take ta done kunnuwa. Ta dago kai ta tv da alamu dai film din horror ne domin idanuwanta ne suka yi arba da wata mumunan halita wacce daga ka ganta ma ba sai ance maka zatayi mugunta ba abun wani tsanwa tsanwa ne idanuwansa jajaye hakoransa kuwa wasu zakozako ne dogaye wanda a gabanta ya raba wani mutun gida biyu da hakora.
Tsayawa tayi tana kallan nan ma tana waige waige ita ko me yasa take san kallan horror film ba. Daga cikin dakinta take jin irin karan dabar dake cikin tv abun sai karuwa yake. Zuwa can kuma sai wutar dakin
Dakin yayi duhu baki kirin gabaki daya ko tafin hannunta bata iya gani lalube ta shiga yi ko zata ci sa'a ta iske window ta bude labule domin yanzu rana ce tsaka tunda ynz dudu 12 ne. Kamar makwainiya haka take ta lalube a daki. Garin lalube taji taci karo da wani abu lalubawa tayi taji jikinsa duk gashi ne. Ita kam ta rasa miye wannan domin aduk parllon ta ba abu makamancin haka.
Ci gaba tayi da laluba abun domin ta tabbatr da ko miye nan ta nufi tataba. Saman abun taji kaho a kai. Bata dadare ba tayo kasa da hannu wajen fuska taji ido lafiya lau da baki da hanci duk irin na motane. Ihoo ta kwala taa waaaaahh!! Ta fara ja da baya-baya tana fadin waye mutun ko aljan waye👺 ido abun ya bude taga hasken idanun kamar danja.
Kara tsalla iho tayi a cikin duhun ta fara gudu duk da bata san inda take nufa ba. Wani gun taci karo da kujera wani lokacin taci karo da bango haka tata xagaye parllo tana iho. Ji tayi wata mahaukaciyar dariya ta barke hahahahaha! , hahahahaha!
" ke yasmeen ki natsu cikk ta tsaya tana karkarwa cikin duhu tana dube-dube. yanzu ne lokacin da ya kamata in bayyana miki kaina koma ina umartarki da kisa al ameen ya sake ki domim nice nan kursiyya matar al ameen idan kuma ba haka ba zaki hadu da bala'i da masifu daban daban irin wanda baki taba tsammani ba a cikin gidan nan sannan daga karshe dole ne ki bar gidan wannan zabi ne na baki ki fita da laluma ko ki fita ta tsiya.
Yasmeen wani karfin hali ne da kuma rashin tsoro suka zo mata a lokaci guda. Tace " karya kike ko ke wacece baki isa ki rabani da al ameen ba karyarki tasha karya al ameen nawa ne ni kadai ba wata ya macen da ta isa ta mallaki al ameen a matsayin miji cikin mutun ko aljan bayan ni nan yasmeen kuma in ma kina mafarkin hakan ne to ki daina domin wannan tsafe tsafen naki da kike yi dan ki tsorata ni ki sani daga yau na daina tsorata kuma zan nuna miki ko ni wacece zaki san kin taba yar gado.
Dakin ne gabadaya ya rude da wata irin mahaukaciyar dariya mai fita biyu biyu hahahe hehehehe hhhhh 👹👺 ke yasmeen kinyi kuskure na fada min wannan maganganun yanzu dai kina nufin wato dani zaki ja ko? To mu zuba ni dake. Yasmeen karkarwa tsoro ta fara yi domin tasan cika baki ne take.
Yasmeen dan lumshe idanun da tayi bude warta ke da wuya idanunta sukayi arba da wata irin halita a gabanta daf da ita. Wani irin abu ne kanshi sumul sai gashi da baifi a irga ba. Idanu kwala kwala ba irin na mutane ba. Ga hancin wani dogo da shi. Kunnuwan budewa suke suna rufewa abun ban tsoro. Daga baki abun yayi yasmeen tana ganin hk ta sulale kasa sumamiya domin daga bakin abun ya kara mishi muni da ban tsoro hakoran a rube suke ga wasu bakaken tsutsotsi yan kanana cike da bakin suna ta motsi a ciki.
Kursiyya dake gefe tace sis me yasa kikayi haka ai naso ace kin kyale ta muga abunda zatayi nidai nasan ba . Tunda nasan ba addu'a datayi ba kinga kuwa ko me zatayi bayan wannan ba tsoranta damuji ba.
Wannan halittar ta taho tana dariya ba kyan gani tsutsotsi na zubowa daga bakin ta nan na fahimci cewa ba wata bace marsiyya ce ta zama hannan halittar👹........................................................,.....
😀 GOOD NIGHT muga wacce datayi mafarkin marsiyya yau 😀
Little of writer's ✍🏼
👑king boy 👑
🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿
page 71 - 72
|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟5STAR APR 2017 🌟
|_________________________|
***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©5SWA
***** 5 star *****
Aunty kyale ta ai gwara ayi mata hk kina ji fa abunda take gaya. Kursiyya tace kinsan me yanxu abunda nake bukata shine kafin ta farka mu gyara komai na parllon nan. Marsiyya ta dawo yanda take tace na gane kafin 5minutes tuni har sun gyara komai aka dau yasmeen aka kaita dakinta kan gado.
Yasmeen ta dade a kwance tukun ta farka ji tayi kanta nayi mata ciwo-ciwo nan ta fara tuno abunda ya faru kuma mamaki ya cikata data tashi ta ganta a kan gado ta rasa waya kawo ta. Yasmeen ta taso ta nufi kitchen domin ta girka abinci domin yanzu karfe 1 tayi. Tunani take me zatayi Murmushi tayi domin tinawa da tayi da barjajiyar shinkafarta wace datayi dambun shinkafa ranar al ameen ya hana. Shi yasa tace to bari kawai tayi yanzu.
Bayan ta wanke barzzazar shinkafarta tsaff ta zuba a madam baci ta rufe da leda tukun ta dora wata tukun yar ta zuba ruwa madaidaici ta dora a wuta ta dora madambacin ta rufe ruff. Ta dawo ta tafasa karas dinta da koren wakenta tukun ta yayanka su tare da kabeji da albasa da attaruguzu ta yayanka su gutsin gutsin. Bayan garin yayi laushi ta sauke ta zuba mai ya kama garin shinkafar sosai tukun ta dauki kayan lambun nan ta zuba ta cakude ya gaurayu tukun ta zuba magi da gishiri.
Ta dauko tafasashiyar hanta ta yaya itama ta zuba a ciki ta chakude tukun ta sake kunna wuta ta dora. Dan lokaci kadan ta bashi misalin 5mint taji ya fara kamshi hakan ya tabbatar mata da ya daho takin ta ta nufa domin ta dauko wayarta. Bayan ta dawo kitchen tsaye tayi ganin abunda ya faru an sauke tukunyar an deba abincin duk ga dai wani a plat nan an bari. Karasawa tayi ta duba taga dai tabbas hkn ne ta duduba kitchen din gaba daya bata ga komai ba tace ko dai bera ne ko kuma mage. Murmushi tayi tace haba ai wata dabar bazata iya yin wannan aikin ba kawai matsafiyar matan nan ce wace ke san al ameen. Tace amma ba komai taso zaman lafiya tunda ta bar min nawa abincin. Na cikin plat din ta dauka ta nufi dinner
Abun mamaki a dinner tebur ta iske plats biyu anci abinci a gurin. Kai kai wllh na gaji baxan iya zama ni kadai a gidan nan ba wannan bala'i har ina bari in gama cin abincin nan in kira anty hajara. Gwara tazo asan matakin da za'a dauka.
Tana cikin cin abincin ta wutsiyar ido ta dinga hango wani abu na lekowa daga dakin umma daga ta juya gurin kuma sai taga ba kowa. Har dakatawa tayi da cin abincin ta maida hankalin ta ga kofa. Daga taga abun ciki hanzari take juyawa. Abun mamaki kuma sai taga kofar a rufe ma. Ta ci gaba da cin abincin. Amma ina kofar aka fara budewa ana rufewa da karfi. Abincin bai sama ciyuwa ba ajiyewa tayi ta tashi ta nufi dakin har yanzu dai budewa ake ana rufewa.
Wata dariya taji tana fitowa daga dakin kmr dai dan jariri ne keyin ta Hhihihihiehehe hakan yasa ta juyawa baya da gudu ta nufi dakinta. Tqna shiga ta bank kyauran wayarta ta dauka tayi calling din anty hajara sai a karo na biyu aunty hajara ta dauka. Cikin muryar wanda yake a firgici takr maganar aunty kizo ba lafiya kiyi sauri dan allah gidan ba lafiya pls aunty. Tambaya take lafiya lafiya yasmeen me ke faruwa ne amma ina bata bata amsa ba ta kashe wayan. Da sauri ta dauko gyalan ta ta yafa. Yar yarinya ce karama a zaune tare suke kallan hajara ta kalle ta tace nuratu idan mum ta fito kice mata naje gidan yasmeen kinji. Nuratu tace to mum me zakiyi a can.
Hajara ta juya ta kalleta tace ni ma ban sani ba sai najr na gani. Mum nima zanje. aa nuratu ba ynz ba xamu je dake wqtaran. To ki gaida min mumy na da uncle al ameen da baba mai gadi da driver da..... Kai nuratu surutun ki yayi yawa naji xan gaida kowa da kowa. Hajara ta juya ta fita. Da sauri ta tsaida napep daidai kofan gidan aka ajiye ta ta biya mai adaidaita tukun ta karasa cikin gidan.
Bayan sun gaisa da mai gadi da deriver take tambayar su me ke faruwa. A cikin gidan domin yasmeen ta kirani tace inzo maza maza. M lawal mai gadi da idi suka kalli juna tukun suka ce wani abu kuma aa mu ba abunda ya faru a gidan na. Hjr tace to shikenan bari in shiga cikin in gani har zata wuce kuma sai ta juyo tace na mantq in gaya muku nuratu na gaishe ku ku duka.
Sukayi Murmushi muna amsawa yau ina take ne. A gida na barota domin tahowar gagawa ce nayi. Lawal yace ayya a gaida ta in an koma hajara tace data ji.
hajara da sauri ta nufi cikin gidan kai tsaye ta shiga ko sallama babu. kira ta fara kwallawa yasmeen! yasmeen kina ina. but shiru taji.
kitchen ta leka bata nan hakan yasa ta ta nufi dakin yasmeen din tana tura kofa ta hangi yasmeen din a kan bed ta wani kudundune.
hajara ta fara tambaya lafiya kuwa yasmeen yayin da ta karasa wajenta. anty hajara wllh ba lafiya gidan nan aljanu gare shi ko aljanu ko kuma fatalwa. hajara tayi Murmushi tace haba dai yasmeen ina ganin ki wayya ashe baki waye ba ai wannan maganar duk shirme ne kawai tsorata dai kike yi. ina al ameen din?
ya al ameen sunyi tafiya yau tafiyar gagawa ce tazo mai domin nima sai ta waya mukayi bankwana. hajara tace ohh wato kice dai so kike inzo in tayaki zama a gidan kafin ya dawo ko. to ai dan wannan da ba sai kinyi karya bama da wai aljanu.
yasmeen tace wllh anty da gaske nake domin yau an tsorata ni sosai wllh. hajara tace ke rabani da zancen nan. yanzu dai ina abinci domin ni yunwa ma nake ji me kika dafa. yasmeen tace dambun shinkafa nayi amma har ya kare aljanu sun cinye
Hajara tayi Murmushi tace wai aljanu sun cinye ke me yasa kin cika karya ne wannan maganar ai ba mai yuyuwa bace kinga nidai tashi kije ki girka min domin nasan babu ne. Yasmeen tayi Murmushi to aunty me kike so in dafa miki ne?
Ta dan yi tunani kadan um! Kawai dafa min indomie dan inta ce mai saurin dahuwa kar in wahalar dake. Aa aunty ai ba komai fadi duk abunda kike san ci.
Kinga kedai dafo indomei din domin wllh da yunwa na taho. Yasmeen tace baki ci abinci banr ko ba'ayi ba a gidan. Anyi mana baidai karasa ba. Mum ma bata san tahowa ta ba sai nuratu nace ta gaya mata amma bari in kirata. Nan yasmeen ta tashi ta nufi kitchen cike da jin dadi ns zuwan anty hajara.
Su kursiyya dake jikin bango suna kallan su. Marsiyya tace itama fa wannan naga ta cika shishigi kuma ga alamu itama dai jahilace bata da ilimin addini. Kursiyya tace nima dai naga alamar hkn gashi ma sai wani cika baki take.
Marsiyya tacr kyale ta aunty zan yi maganinta anjima kadan.
Ba'ayi minti 10 ba sai ga yasmeen ta fito da indomei a plat sai kamshi take yi. Dinner Table takai ta ajiye tukun ta nufi daki domin ta kirawo ant hjr.
marsiyya da kursiyya ko wanne da cokalinsa a hannu sun zazauna a dinner chairs din kawai jiran fitowar hajara suke domin su fara ci. Marsiyya tace allah yasa dai kar tayi muna haramiya (wato tayi bismillah) kursiyya tace ameen amma ai daga ganin alamunta baratayi ba domin kinsan mafi yawancin yan adam haka suke cin abinci yanzu ba tare da sun kore mu ba. ( wato sunyi bismillah) marsiyya tace ai gwara hk mu kam irin su muke so ai...................
.................................................
Na kalli nasmat nace to fa nan ake yinta. Su marsiyya yaya da kanwa su ma su yasmeen hk..
GOOD MORNING ALL MY FANS LUV U 2 MUCHHH
Little of writers
King boy
🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿
page 73 - 74
|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟5STAR APR 2017 🌟
|_________________________|
***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©5SWA
***** 5 star *****
😍😍This page In dedicated to you 😍😍
🌻Adams Abubakar Ahmad🌻
🌻Maman Huxaifa🌻
🌻Salamatu Yahaya Mohammed🌻
🌻Rukayya Abubakar Adam🌻
🌻Sajeedah Batulah🌻
🌻Fatima Muhd🌻
🌻Aslamiyyat Islam🌻
Thanks for u dua love and fatan alkhairi a gare ni allah ya bar zumunci ameen tnx
Suna cikin magana sai ga anty hajara ta fito ita da yasmeen suka nufo dinner din. Anty hajara tun kafin a karasa gurin taji wani hadaden kamshi ya bude ta gaba daya gidan ya cika da kamshin indomie din hajara ta juta ta kalle yasmeen. Sis na wai miye ke kamshi ne hk.yasmeen Murmushi tayi tace muje aunty zaki gani ai.
hajara tace to shikenan. taje ta zauna kuwa ta bude plat din hadadar indomie ce wacce ita kanta kalar dahuwar ya burgeta matuka. Yasmeen zuwa tayi zata zauna kan wata kujera bata san a kan kujerar marsiyya take ba. marsiyya na ganin haka tayi sauri ta mayar da yatsarta allura. ai kuwa Yasmeen na kawo duwawunta zata zauna sai kuwa marsiyya ta caka mata🙈 Yasmeen tsalle tayi hade da yar kara tana sosa wajen. tare da juyows tana duba kujerar.
kursiyya ta kyalkyale da dariya ganin abunda kanwartata ta aikata tace gaskiya sis kin kware fanni mugunta. marsiyya tace ai maganinta kenan. yasmeen ta duba gun bata ga