Chapter 3 Reading MIJIN ALJANAH 1 to end Complete Hausa Novels by King Boy.txt Arewa Novels

MIJIN ALJANAH 1 to end Complete Hausa Novels by King Boy.txt

Author :  King Boy Isa Category :  My Hausa Novels

Chapter   3 / 26

6K to 9K   out of 76.7K words

muryar da yaji bai taba jin zazakar murya mai wani fitar da sauti mai dadi ba irin wannan.




.ameen wa'alaiki salam amaryata. kiyi hakuri fa ynz nake niyar in kiraki sai kuma gashi kinki.




hmm ba wani nan da alamu dai kama manta dani ko. hb dai ni din wa nama isa in manta da amarya ta ke da aka kawoki jiya gida na. ya fada cikin zolaya. .



.

humming tayi tukun tace wow gaskiya angona gidan ka ya hadu ba karamin dadi nake ji a ciki ba. sai dai fa ina tsoran kace zaka min kishiya domin inada masifar kishi.






al ameen da yake daukar zantukan duk a wasa yace hb wa ni din ya za'ayi inyi ganganci hada sarauniyar mata da wata ai bazan taba aikata wannan kuskuren ba




uhm to allah yasa haka. ynz yaushe zaka zo online ne muyi hira domin nifa bana jin dadin chat din ko kadan in baka on. ..





my sweet ki bari ina wani dan aiki ne amma da zarar na gama zaki ganni Yasmeen inaso inga kyakyawar fuskanki wace nasan ta zarce ayi kwatance domin ke din ta daban ce ki a murya kinyi fice.






kursiyya da ita tasan komai amma kawai sai ta basar. "wacece kuma Yasmeen ko dai matarka ce al ameen karfa ka yaudare ni ka jefa ni kogin kaunarka kuma aje kanada mata..





au wai Yasmeen nace srry my one wata yarinya ce tazo wucewa shine na ambaci Yasmeen. kursiyya ranta ne yayi matukar baci jikin ta ya fara wani turiri nan fa ta fara chanza kama duk wasu yan kananun hannuwa ne suka firfito mata a jiki ko wane hannu kuma motsi yake haka idanta ma ya wani koma tsanwa sharrr nan fa tace sai ta dau mataki a kan anbatan sunan Yasmeen da yayi suna waya.







Yasmeen ita kadai a kitchen sai burun -buruntu take tana faman girki domin bata san al ameen ya dawo bata idar ba. bayan yan mintuna ta karasa komai yau kunun gyada tayi mai. mai dadi. bayan ta kamalla komai ne ta shiga jido wa tana kaiwa dinner. kursiyya kuwa zaune take kan armchair tana kallan ta kawai. amma ita Yasmeen bata ganinta.





bayan ta kimtsa komai ta shiga daki ta cire kaya duk abunda take kursiya na biye da ita domin so take ta mata hukunci. bathroom ta nufa dadai kofan kursiyya ta tsaya taji wai ko zatayi addu'a domin indai tayi addu'a na shiga bayi kursiyya bazata iya shiga ba.





Yasmeen kuwa wakar dorobucci ma take lokacin da ta shiga ban dakin hakan yasa kursiyya ta wani harareta tare da yin murmushi mugunta ta bita ciki.







rowa ta hada lafiya lau mai gumi a cikin bath kafin ta je tayi brush ta dawo tuni kursiyya ta bullo a gurin yatsa tasa nan take ruwan yayi mugun zafi ta koma gefe tana murmushi mugunta.




bayan Yasmeen ta taho ne santsi ya dan kwashe ta zata fadi da sauri tace bissmillahi- a'uzubillah. bat naga kursiyya ta tsere daga bandakin domin wani zafi taji lokacin da Yasmeen ta fadin kalmomin nan ruwam ma ya dawo kamar yadda yake.







Yasmeen kuwa zuwa tayi taci gaba da wankanta bata ma san me ya faru ba. ( wannan ya nuna muhimmancin ambatan sunan allah kenan ko wani abun zai same ka idan ka ambaci allah sai ya kubutar da kai ba tare da kama sani ba. be careful.)






kursiyya parllo ta bullo ranta a bace domin tasan muguntar da ta shirya baratayi tasiri ba.





Yasmeen ta gama wankanta ta fito taje gaban mirror bayan ta goge ruwan dake jikinta da gashinta. tsaye take tana kwaliyya tana wakar gwanja asha rawa rawa.








bayan ta shafa hoda ta sa man lips tana cikin sa jagira. ta hangi kamar jariri ta cikin madubi ta hange shi yana mata dariya.





tsayawa tayi chak daga abunda take ta tsura mishi ido ta madubi a hankali take juyowa. ta duba gado bata ga komai ba. tsoro ne ya kamata da ta juyo mirror ba taga komai ba a gagauce ta gama kwaliyyar ta bude wardrobe ta dauko wata doguwan riga ( dress) ja mai kyau mai yan guntayen hannuwa tasa tasa sarka da dankune. tayi kyau sosai kamar yar indian.







parllo ta dawo ta saki sauti wai kafin al ameen ya dawo.( tecon duro) take ji duk fadin gidan gabaki daya karan ya cika shi kasancewar manyan spekune yi take tana bin wakat daga kwance tana jijiga kai.






a hankali barci mai nauyi yayi gaba da ita kursiyya kuwa farinciki ne ya mamaye ta ganin abunda ya faru dama ita tafi san shedan ci. tsullum ta bullo gaban Yasmeen tana kallan ta tana wani murmushi mugunta. dan tsugunawa tayi ta kai bakinta kusa da kunnan Yasmeen.





" hk nake sanki Yasmeen da kin kasance mai riko da addini to da ba abunda na isa in miki amma ynx kin bani dama kuma naji dadin kasan cewar ki shedaniya hkn zaisa in sama damar kwace mijin ki ya dawo hannuna. ta kyalkyale da watq irin dariya mai fita da sauti biyu. ba bata lokaci ta rikide ta dawo yasmeen sak ba banbanci ko kadan.






daukan yasmeen tayi chamak bata zame da ita ko.ina ba sai kan wani dan dogwan dutse dake tsakiyan teku......................................

juyawa nayi na kalli sis zeesa nace dama yasmeen ta farka ynz taka kalanta muga me zai faru......



king boy
















πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 21 - 22


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****

...
.









dutsen da ya kasance a tsakiyan teku hakan yasa wajen wani iska mai dadi yake kadawa nan kursiyya ta ajiye ta bat ta bace ta bullo a gida.





toh dama kursiyya ta kasan ce shedaniya ce akwai ta da san kida da wake wake dayake ba muslma bace ce itama. nan fa tahau rawa kamar Jackson. ita duk karan nan bai ishe taba sai da ta kara volume . man lawal mai gadi shi kansa da yake gate saida kidan ya takura mai yace wannan abu kamar dai club ai dole ma aljannu su dame ki kullum sai kin ishi mutane da kida wllh makwabtan matar nan hakuri gare su yake fadawa driver.







idi driver da yake faman cin garau garau yace hmm kaidai bari ni duk ba wannan ne yake damuna ba wllh ni rashin kawo mn abinci shi yake damuna ka tuna lokacin da umma na gidan nan kullum abinci sai mun koshi amma ynz yarinyar nan wai baxata iya ba ta barmu da abincin saye.






lawal yace to yq zamuyi ai sai hkr badan mai gidan nata nada kirki ba ya kara mana kudin albashi ai da a abinci ma kadai zamu dinga cinye salary din. karan motar al ameen ne ya katse su da sauri lawal ya tashi da sauri ya bude mai gate.







al amern tun da ya shigo layin yake jin tashin kida sai da ya zo saitin gidan ya gane a nan ne. da sauri ya fito a motan yana fada su lawal na gaishe shi amma bai wani tsaya amsawa ba yayi cikin da sauri.





kursiyya idanta ya rufe kawai rawa take tikawa. da niyar marinta ya shigo amma ganin irin kyawan da rigar tayi mata da kuma yanda duk sasan jikinta ke juyawa a rawar da take yi bama kamar breast inta da yake kusan rabi a wajen ya tsaya cikk ya zuba mata ido.



a hankali ya taka har gurin dvd ya kashe sai a lokacin kursiyya ta dakata da rawar duk da ta ganshi. u w welcome my Sweet. murmushi yayi lokacin da ya tako a hankali ya kama hannunta ya jata sofachair ya xaunar da ita a cinyarsa.



" Yasmeen me yasa bakya jin mgn volume din nan ai yayi over ki dinga rage volume pls. kursiyya da takr a matsyin Yasmeen bata rai tayi tukun ta sadda kai kasa alamun tashi fushi. hannu yasa ya dago fuskanta yana kallanta yana murmushi.






" au fushi kikayi dan nace ki dinga rage volume to kiyi hkr my one kinsan cewq bana san bacin ranki ke nake gani inji dadi kallanki yakan fitar dani a damuwan da nake. kursiyya abunda ya bata haushi shine Yasmeen yake cewa. toh amma ba damuwa tunda dai sunan ne kawai ai itace.






wow! tnx my one shi isa sanka kullum ke kara shiga birnin zuciyata yanata gini abunsa. tashi muje in baka abinci sahibina. ta dan shafa cikinsa nasan dai ka debo yunwa a cikin nan naka.




ya kalle ta yayi murmushi kamar kin san kuwa duk abinda nake hankalina a kan abincin yake domin irin kamshin shi da ya cika min hanci. tashi sukayi suka isa dinner din inda suka dinga ciyar da juna abincin a baki suke bawa junansu abincin kursiyya ta zuba mai kunun gyadan ta mika mar tukun itama ta zuba ta suka fara sha tare.







( sis nasmat ta juyo ta kalle ni tace shegiya kursiyya tsuntsu daga sama gasashe kenan ba ita da yin girki ba gatanan tana morewa abunta. zanyi mgn kursiyya ta harare ni tsoro yasa ni yin shiru)








sun dade a gun suna nunawa juna kauna al amern kam sai suburbuda mata kalaman love yake ita kuma kursiyya tana washe baki.






bai fita ba sai karfe 2:30 nan ya bar kursiyya datake da sifar Yasmeen yana fita ta kama wata shu'umar dariya hahahaha wanda yasa gabaki daya fallan amsawa. bacewa tayi taje ta dauko yasmeen da take ta sharar barcin ta har ynx.









kan sofa ta kwantar da ita kamar yanda take da. a hankali fuskan kursiyya ta fara sauyawa ta koma kamanin ta. yasmeen bata tashi ba sai karfe uku harda mint 6 tana tashi ta dubi agogo tayi mamaki sosai saidai ba wannan ya bata mamaki ba dinner da ta hanga alamun ance abinci.







da sauri ta mike zumbur ta nufi dinner din. bata rai tayi tukun tayi tsaki mtseeww wai ni al ameen me yasa yake min hk da safe yaci abincin sa bai tayar dani ba kuma ynz ma haka. ta nufi daki da niyar ta dauko waya ta kira shi taji dalili.









al ameen bayan ya koma office yaga ba aiki hakan yasa shi bude data. nan fa massage suka fara shigowa. al ameen ya shiga dubawa. al ameen ya kasance mutun ne mayaudari amma fa na yan matan whatsapp domin a halin ynz yan matansa sunfi a kirga wasu ma har mantawq yake da su.






massage din wata number mai suna yar wahala naga ya bude massages ne kamar haka"







Β° bayan salama da fatan alkhairi masoyina ina so kasani cewa jiya banyi barci ba kwata kwata dan rashin ganin reply dinka kwana nayi a online amma baka zo ba why.

srry my sweet karki damu kaina ne ke dan yi min ciwo shi isa na dan kwanta.


bai karanta sauran ba yayi tsaki ya fito daga massage din lokacin husaini ya shigo.office din. yayi mai sallama. ah sai ustaz ya akayi ne.






lokacin usaini ya karaso wato kaidai har ynz bazaka canza halin ka ba na kin amsa sallama ko ynz kayi asarar lada goma fa.






al ameen dan sosa keya yayi yace au srry fa wslm. gidan ku ne wslm din baraka amsa min sallama cikaka ba wato chat ya bata ka baki daya ko al ameen. dariya al ameen yayi.




kuma nace ma ka daina cemin ustaz din nan karma mutani suji su zata ni din wani malami ne ku dama mutanan nan daga fadin gaskiya sai ku fara cewa mutun ustaz shehu miye da miye.






al ameen yace ynz dai ba wannan ba dama ina so in baka wani labari baka san nayi saban kamu ba ko. usaini ya kalle shi cikin rashin fahimta yace ban gane ba me kake nufi.





al ameen yace bazaka gane ba kai kam ai shekaran jiya nayi sabuwar budurwa galeliya har a ledan ta. usaini yace hmm budurwa kuma ai ni har nagaji da ji indai a gunka ne domin kusan kullum idan muka hadu sai ka fadan kayi sabuwa.






kai wannan fa ta daban ce karkaso kaga yanda ta damu dani al ameen yayi murmishi yace wai kasan wani abu irin auren whatsapp din nan mukayi amma da ango take kirana.




usaini yace uhm lalai tsageran cin yayi yawa wato har wasa da aure kuka a whatsapp din ko to wllh zai iya dauruwa da gaske indai kunbi ka'ida


kai dallah share duk shirme ne ba wani gaske ba. messages din photos yagani a number kursiyya yauwa yar albarka ashe ma ta turo pics din ya kalle usaini yace matso kusa ka ga matan manya domin nadan babbar yarinya ce.






usaini ya matsa yana murmushi. me zasu gani kuwa inba photan................................. kuyi hkr fa sis nasmat nace ta leko min pics din taki amma bari in leka da kaina.

shiga nan kayi like din page din mu domin karanta sauran labarin

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarks

king boy












πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 23 - 24


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****

...
.




*wannan page din naku ne yan samari facebook luv kursiyya tace in gaida ku. lolz*







(ina lekawa nayo baya da gudu. nasmat tayi dariya tace
me zan gani hk kaifa namiji ne. kardai ace duk abunda kake fada cika baki ne. hararenta nayi nace da kinga pic din ba kyan gani abun tsoro bari dai in dawo in baki lbr na juya na koma )






al ameen da husaini kallo daya sukawa pic din suma basu yarda sun kara ba.


pic din wata halita ce mace amma bakikirin da ita kamar gawayi ba abunda kake gani a jikinta sai wasu jajayen idanu chaka-chaka a jikinta tana da bindi ( hutsiya) bakin ta wani wakeke ne idan kasa jariri zai shige. kafafun doki ne da ita hannuwa ma kofato ne.







kana iya ganin abubuwan cikin kanta su kwalwa ne da sauran su. bayan al ameen ya goge pic din yayi tsaki mwtseew data tsorata mutane hk kurum.







husaini da shima kansa ya tsorata sai kuma abun ya bashi dariya ganin yadda al ameen din ya tsorata. dariya yake kyakyala masa. hada rike ciki al ameen ya harare shi. malam ya isa haka.




husaini ya dan sasauta dariyar yana mgn cikin dariya- dariya toh toh shikenan. kallan al ameen yayi yace _MIJIN ALJANAH_ ya kuma kyalkyale wa da sabuwar dariya. husaini kaga ni fa bana san wannan abun miye kuma na dariya hada ce min wani _MIJIN ALJANAH_ toh ni allah ma ya shiga tsakanina da su ni fa ka sani duk gidan mu ma aljanu tsoran su suke because ba wanda aljani ya taba shiga. aha.








to naji usaini ya fada lokacin ds ya dakata da dariyar yace ba wanda aljani ya taba shiga amma inaga ai kai ka kwaso ta domin ni ko a fim din horror ban taba ganin kalan hallita mai ban tsoro irin wannan ba.





al ameen yayi yar dariya yace kaji matsoraci kawai inaga tayi ne dan ta tsorata ni kuma gashin ban tsorata ba sai kai.





hmm muka tsorata dai in baka tsorata ba kai miye yasa ka gogewa kaji mutun. al amern wllh ina gayama ka kula domin ynz al jannun ma chat suke sosai sai su shigo cikin mutane atayin harka da su kuma bazaka taba ganewa ba.






al ameen dariya yayi sosai yace amma gaye ban san kai mugun matsoraci ne ba sai yau wato dan kaji ana cewa wai aljanu na chat har ka wani dauka to ya za'ayi ma aljani yayi amfani da waya bayan ba ganin su ake yi ba kuma su iska ne.







husaini yayi murmushi yace to naji amma kasan cewa aljani yana iya rikidewa ya zama mutun ko wata hallitar ko. al ameen zaiyi wata mgnr husain ya daga mai hannu kaga bani amsa eh ko aa.





eh hk aka ce amma ni sam ban yarda ba. husain yayi murmushi yace to kar allah yasa ka yarda amma tunda suke iya zama mutun kuma suna ci suna sha to kaga kuwa dan su sayi waya suyi chat ba wani abu bane kadai kawai ka kula ka rage yaudarar yaran mutane .






al ameen yayi dariya yace ai gaye ba abunda za'a fasa kaga wannan yarinyar. ya nuna mai number da aka rubuta yar wahala. husai ni yace ai yar wahala aka rubuta.




eh sunanta fauziya tun da na tura mata pic dina ta rikice ni kuma wllh yarinyar bata min ba ko kadan dan karka so ka ganta wata black.





husaini yaja tsaki mtseeww to uban wa yasa kace kana santa da farko ai dai nasan ba ita ce zata fara cewa tana sanka ba dan hkn abu mai wuya ne.





al ameen yace gaye karka so kaji muryar yarinyar it ix very sweet but her face ix bad 4 me.




allah ya sawake ma yasa ka gane kuma. al ameen yace ba amin ba domin ina nishadi sosai inga budurwoyina 5 ko sama da hk a online ko wacce kuma bana bari tayi chat da wani ko wata sai ni in dai ina on gaye ka shigo harkar nan fa zan baka number yarinya 20 domin ni sunyi expired a gare ni dan ni delet dinsu ma zqnyi.





allah ya kiyaye min wllh ba dani ba kaga bari in koma office dina nima naga ba aiki ne nayo nan. husai ya juya yayi hanyar fita. al ameen yace to matsoraci sai ka dawo husaini yace matsorata dai ya fita yana dariya.


husaini bai dade da fita ba wayar Yasmeen ta shigo. dauka yayi yace hello my dear gaskiya abincin ki na yauma yayi min dadi sosai.





Yasmeen tace ai mun bata da kai yau fushi nake da kai.




cikin wata irin murya yace haba my sweet wife me kuma nayi da za'a bata dani laifin me nayi?






Yasmeen tace ai laifi ba daya kayi ba har biyu ma .






na shiga uku na. ya fada cikin zolaya ni din ?


Yasmeen ta danyi gungunin kuka cikin shagwaba tace. " shine zaka ci abinci

3 / 26