Author : King Boy Isa Category : My Hausa Novels
duhun Dake cikin dakin ya washe Sama da kasa na nemi Su marsiyya na Rasa. Gefe na juya Ashe Zainab ce ta farfado ta tuno da Ayatul Qursiyyu Ta fara Karantowa shi yasa suka Gudu.
Dakatawa tayi da karatun da Gudu ta tashi ta nufi Yasmeen da ta hanga can gefe kanta Jini na Zuba. Al amern Kuwa wani Masifafan ciwon kai ne ya zo mishi a lokacin A wahale ya tashi kanshi a dafe jiri na debansa ya tashi ya nufi Gurin su Yasmeen din. Da sauri Zainab ta cire Dan kwalinta ta daurewa Yasmeen kanta. A haka al ameen ya kama Ma Zee Suka taho da ita waje. Da sauri su idiris driver suka taso suka taimaka da bude motar aka saka Yasmeen suma suka shiga driver yaja mota Sai G . N . H . hospital.
Nan suka bar M. lawal a gurin Yana tunanin me ya faru a gidan domin shi kanshi Ya daure yasan dai idan fadan kishi ne akayi To Zainab bazata taimaka a fito Da yasmeen din ba.
( Ni kuwa nace. wannan Fadan na kishi ne amma fa da Aljana. lolz)
Su husaini ne suka karbi Yasmeen da Sauri aka nufi Emergency da ita. Dake ba bangaran shi bane ya fito ya bar Sauran likitocin a ciki domin huruminsu ne. Wajen su zee ya dawo a rikice yana tambaya me ya faru domin Shima abun ya Daure mishi kai. Zee tace yah yanzu dai a kirawo iyayen ta ya kamata a sheda musu halin da yarsu ke ciki shi yafi mahimmanci.
Husaini ya juya ga Al ameen wanda tunda aka zo ya sama waje ya zauna kanshi rike sai Zufa yake. Domin kanshi yake ji kamar Zai tsage. Husaini yace. "kai lafiya kuwa kazo ka sama waje ka zauna Kira wo iyayen Yasmeen mana a sheda musu."
"wllh kaina ne ke masifar ciwo kamar Zai tsage nake ji. ga wayar kira su". ya mikawa Usaini wayar. Husaini ya lalubo number Hajara ya sheda mata halin da Yasmeen din ciki. A Rude itama ta nufi gurin umma ta gaya mata.
Lokaci Daya naga idanun Al ameen sun wani canza kala Tsaye ya mike yake magana irin ta mata. Al ameen bazan taba Rabuwa da kai ba tunda na samu nasarar Shiga jikinka duk rintsi Duk wuyi bazan fita ba sai na dandana maka azaba.........................................................
๐๐ป๐๐ปAL AMEEN YA SHIGA UKU ASHE TANA JIKINSA๐๐ปโโ๐๐ปโโ๐ฐ
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
โ๐ผAutan marubuta โ๐ผ
๐King boy๐
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 138 - 139
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐ZAMANI APR 2017 ๐
|_________________________|
***** zamani *****
๐ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉZ.W.A
***** zamani *****
. _*DEDICATED TO UR|โ> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐๐ฝ *Na gaida ki kyauta na gode da kulawar da kike bani hakika kece lamba daya a fagen kaunar wannan littafin*.๐๐ฝ๐
๐ณ Husaini da zee hada ido sukayi a tare domin sunji al ameen na magana saidai basu ji ko me yake cewa ba hakan yasa husaini yace,
"me kaki cewa wai?" cikin 1 second tuni kursiyya ta bar jikinsa Al ameen yaji tambayar tazo mishi wani banbarakwai. " Yace ni me kuwa nace nace nayi kawai kaina ke ciwo."
A lokacin ne hajara da su mmn yasmeen har dady suka karaso duk a Rikice suke cikin tashin hankali suka fara Tambayar Al ameen me ya faru da yar su.
Al ameen in'ina ya kamayi Domin ya rasa ma abunda Zai gaya musu Shin wace amsa ma Zai basu yace Aljana ta Raunata ta kenan?. kai gaskiya bazan fada ba mmn yasmeen ta rikice sai tambaya take ina Yasmeen lokacin wani doctor ya fito da Sauri su husaini suka tarye shi suna Tambayar ya jikin nata.
yace Jikin nata alhmdulilah da sauki tama dan Sama barci ne nan da Rabin awa zata iya farkawa in yaso lokacin Dazu iya shiga ku ganta. Su al ameen suka ce Alhamdulilah" gaba daya. Al ameen ya biyo doctor yana Tambayarsa ko sun duba cikin da ke jikinta bai samu matsala ba. Doctor yace, "Eh gaskiya ba wani matsala a ta nan bangaran ma. godiya Al ameen yawa allah ya koma gurin su abba wanda duk sun Sama waje sun zauna umma da hajara har yanzu hankalin su bai kwanta ba sun matsu suji me ya sama yasmeen.
Bayan al ameen ya isa gurin ne Dady yace, "Al ameen gaya mana me ke faruwa ne i hope dai ba fada bane Tsakaninta da amaryarka Domin naji an ce min kayi aure.
Al ameen yace. "Aa dady ba tsakanin su ba domin ga Amaryar nan ma tare muke da ita kuma badan itaba da tuni Aljanar Ta kashe mu gaba daya. daga ni har yasmeen din. da sauri Zainab tayi magana. " Wannan bayi na bane yin Allah ne shine ya cece mu daga gare ta kuma ni a tunanina Sakacin da kuke da addu'a ne ya jawo haka domin na lura daga kai har Yasmeen din ba mai ilimin Addini."
dady ne ya dakatar da wannan shafin domin yaji Zainab ta dago shafin Laifinsu
"Al ameen aljana fa kace to miye hadin ka da Al jana ni fa banma wani karasa Yarda da wannan aljanun da ake fada ba. kawai daga mutun ya kamu da Zazabi mai Zafi ya fara surutai sai ace wai aljanune to kuma koma al janine ai bazai taba ya' ta ba ko shi waye dan uban sa aljanin banza.
zee tace dady kayi hakuri amma ai dole mu yarda aljanu domin ga ayoyi nan da dama cikin Al qura'ani mai girma wanda suka bayyana mana ceww tabbas akwai aljanu kuma suma suna Rayuwa ne a doran kasa kamar yanda muke yi. suma cikin su akwai Musulmi akwai kafurai akwai mugu akwai kuma wanda ba mugun ba...."
Maganar wata nurse ce ta dakatar da zee. tace zaku iya shigowa kuganta. Da sauri su umma suka shiga gurin.
"
Yasmeen ji tayi kawai kanta nayi mata wani masifar zafi lalubawa tayi taji Alamun bande ji a gun kokarin tuna abunda ya faru da ita ta fara yi. ai kuwa ta tuno duk abunda ya faru. momy ce ta karaso gun tana mata sannu. ita kuna kofa take kallo cikin masu shigowa ko zataga Al ameen dinta shiru bata Gansa ba.
Tambaya ta farayi ina Al ameen zee tace yana waje Tare muke da shi. wata kallar harara yasmeen ta aikawa da zee.
( wato kishin ne har yanzu) Zee kuwa ko a kanta domin tasan halinsu su mata game da kishi. Cikin kuka Yasmeen din take magana. "momy ina Al ameen ku gaya min mana yana ina Allah yasa dai bata kashe min shi ba."
mum ta dafata. "Yasmeen lafiyanki kuwa wacece zata kashe shi kuma, to al ameen lafiyansa lau kanshi ne ke ciwo shine ya tafi karban magana but yanzu Zai dawo ki kwantar da hankalinki kinji." Gyada kai yasmeen tayi amma har yanzu zuciyarta bata gamsu ba tunaninta Al ameen ya mutu ne shine ake boye mata domin taga kowa a gurin amma babu shi. Sauran mutanan gurin ne suka fara mata sannu ya jiki tana Amsawa amma da zee tace ya jiki banza tayi da ita ko kallanta bataiyi ba. kowa yayi tunanin wani abu a gurin amma ba wanda ya nuna.
'Ana faman dubiya ita kuwa nuratu kokarin hawa kan gadan da Yasmeen take takeyi da gyar ta samu ta hau. ta kalli yasmeen. " aunty nazo ki karasa min Labarin ALJANAR FATIMA domin kullum sai nayi mafarkin fatima da yar babynta shi yasa nake so inji yabayin. yasmeen tace. " To naji zan karasa miki amma ba yanzu ba tukun sai ranar da kika zo gidana Zan miki labarin har karshe amma kinga nan asbiti ne kuma bani da Lafiya... (keeeeeeyy!) karan bude kofa. kofar take kallo ganin waye zai shigo. wani mugun kara Yasmeen din ta saki hade da makalkale umma sosai tana fadin ku boye ni gata nan zata kashe ni momy wallh kashe ni zatayi bana so in mutu yanzu ku boye ni. kowa ya tsorata sosai a gun tambayarta aka shiga yi "wacece wacece" domin su basu ga kowa ya shigo ba bayan Al ameen. juyawa tayi da hannunta take nuna saitin al ameen din tana cewa "gatan nan mum karku bari ta karaso kashe ni zatayi ku ceceni.
lokacin Al ameen ya karasa gurin yana cewa "yasmeen lafiya kuwa me ya same ki ya jikin naki" a yayin da ita kuma kursiyya take gani a maimakon shi din ji tayi tana cewa "Yasmeen kin tsalake Rijiya da bayq da kika samu kika tsira da rayuwarki dazun amma yanzu bazan barki a raye ba yar yasmeme kina tunanin wai zan barki ne hahahaha to ki chanza tunani" hannu al ameen ya mika zai taba fuskar Yasmeen din yayin da ita kuma take ganin kursiyya ta miko hunnan wani ihuuu tayi hade da tsillo daga kan gadon Sauran kadan ta fado badan su hajara sun Riketa ba. da sauri su Zee suka kira doctor Allurar barci aka yi mata sannan ta sulale ta kama barci.
har Magariba ta gabato suna asbitin ganin dare ya farayi abba yace to mu tafiya zamuyi ya kalli su al ameen yace suma su tafi gida in yaso sai a bar hajara a nan ta kwana. haka kuwa akayi gaba daya suka tafi sai hajara sai yasmeen dake barci aka bari. karfe 8 su al ameen suka dawo asbitin suka kawo abinci amma har lokacin Yasmeen bata farka ba. sun dade a asbitin sai wajen karfe 11 suka koma gidan da zasu tafi zee ta tofawa Yasmeen addu'a. yau kam ko zee din ta kasa gane wa Al ameen domin gaba daya ya chanza shiru shiru yake kuma bai fiye shiga mutane ba.
ayatul qursiyya ta fara karantawa tana tofawa a dakin kamar yanda ta saba yi ko a gida. Tsawa ya daka mata yace ta daina baya so tace ai addu'a ce domin kariya. karayi tayi ta tofa Ai kuwa da gudu kamar wqnda aka kora ya fito ya bar dakin. abun ya daure mata kai daga baya kuma sai tayi tunanin ko barkwanci ne irin nasa da ya saba yi.
A gidan su Yasmeen jarfe 12:30
Dady ne zaune a parllo duk daren nan amma shi fim yake kallo hannunsa rike da Jarida kuma yana karantawa. umma kam tuni taje ta kwanta. yana zaune ya fara jin kuka a tsakar gidan " kuwwwwwwwwww,wooooooo" haka yata jin kukan na karuwa kuma yana kara kusanto dakin. ta ji yayi gen ya mutu dakin yayi duhu rudum ya lalubo wayarsa ya danna switch ba charji. abun ya bashi mamaki domin a full take. daga waje kasa yaji ana tada gen. bayan kuma yasan ba wanda ya bari a maimakon mai gadin su da yayi tafiya. karan tada gen. yake ji can kuma sai yaji surutu yan-. yan. haya- haya. sai hayaniya ake surutun ba na mutun daya ba bana biyu ba. a hankali ya nufi saitin window da yake dan ganin haske ta wajensa domin duhu yayi yawa kuma gashi yana upstairs a Tsorace yake tafiya cikin sando domin hayaniyar ta yawaita. karasawq yayi ya leka. don Tsoro ji yayi kamar zai fada kasa daga kan benan wasu halitu ne wanda bai taba ganin kalarsu ba sai hidima suke a tsakar gidan kamar dai gidan biki. halittun da yawansu basu karasa girman mutum ba, suna da bindi dogo ko wanne yana da zallakeken hakori a gaba dogo wanda ya fito daga cikin dogon bakin fatar jikinsu dark Green ce mai walkiya. can ya hangi wata Tsohuwa tsohuwa a cikin su tana bugon mai tada generator di tana cewa. "kai kumudu baka jin magana yanzu gashi ka kashe mana inji ga mai gidan baya nan balle ya zo ya tada mana So kake muyi party a cikin duhu ko?." kumudu ne ya dago kai da jajayen idanunsa suka hada ido biyu da abba sai da fitsari ya kusan fitowa abba a wando dan tsorata da yayi na ganin mumunar fuskar aljanin nan. da sauri kumudu yace " lah ga mai gidan can saman shigifa" da wata irin murya marar dadi. gaba daya Aljanun naga sun daga kai suna kallon abb.......................... . ..............................
Lalai abba zaisan akwai aljanu ashe daga today.lolz
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
โ๐ผAutan marubuta โ๐ผ
๐King boy๐
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 140 - 141
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐ZAMANI APR 2017 ๐
|_________________________|
***** zamani *****
๐ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉZ.W.A
***** zamani *****
๐Kuyi hakuri fa na fiki matsuwa da inga na kamala book dinan amma ayuka ne sunyi over ynz ma bikin abokina ake mune angona ๐ dan haka in kunji shiru kuyi uziri kawai. king na san duk mai sanshi ๐ love u all ma๐
dady jin an ambaci haka a Rude yayo baya domin ya gudu. juyawarsa keda wuya yayi karo da kalar aljanun nan guda biyu kafin yayi wani yunkur'i suka sunkuce shi sukayi sama da shi yana ihuu! yana wuntsile-wuntsile suka bace da shi basu bullo ko'ina ba sai gurin gen. tsakar gida kenan tsakiyar aljanun abba suma ne kawai baiba dan Tsoro. haka suka ce
ya tayar musu da gen. a tsorace hannun na karkarwa ya fara jan gen. din ja biyu yayi gen. din ya tashi gaba dayan gun ya dau wani kara da shewa na ajlanu sai jin dadi suke suna tafawa. abba kam sai karkarwa yake suma ne kawai baiyi ba. ganin hankalinsu yayi wani gun a hankali ya zame jikinsa ya tsere daki. yana shiga parloon wata dariya yaji anayi dariyar mace. daga jikin bango wata aljana mununa ta bayyana tana yin dariya. tace ba kai ne mai zagin mu ba kana cewa ba aljanu to yanzu ka gane akwai mu ko. mu ba bugo ba zagi kawai shagalin biki ne zamuyi na wata biyu kullum cikin dare kaima dole ka dinga fitowa walima kajj ko?.
ciki kaduwa ya gir-giza kai alamun eh zai yi Dariya ta karayi hahahahaha maza ka wuce. da gudu ya tashi har yana tun-tube ya shiga dakin da gudu kamar an koro shi. can ya fada kan umma baima lua da ita ba shi wajen buya kawai yake nema.
Farkawa tayi tana murje-murje Alhji lafiya kuwa?. cikin Rada yake ce mata "kiyi shiru, kiyi shiru kar suji mu"
"suwa" ta fada da dan karfi, da sauri yasa hannunsa ya toshe mata baki. shiru sai da aka dan dade tukun ya sake ta. shiru yayi cikin blanket ko motsin kirki baya yi. har safe.
tun da sasafe abba ya Rikice wai aje a nemo mishi malamai suzo suyi karatu Aljanu sun cika mishi gida
abun dariyama yabawa umma tace alhj inace kaine kace ba aljani ma jiya. " pls yi shiru karsu ji mu nasan suna nan kasa suna bidirinsu bari ma in leka inga".
a hankali yake tafiyar har ya karasa wajen window ya leka wayam ba komai a gurin kamar ma sam wasu halittu basuyi shagali a gun ba. lokacin itama umma tazo ta leko bata ga komai ba tace. " wai ni alhj me ke faruwa ne ina ce kace ba wani aljani a duniya duk karya ce to ka kwantar da hankalinka tunda babu" bai karasa jin me umma ke fada ba yaji magana ta kasa ana cewa. "alhji mun gode fa sosai da aran gidan da ka bamu jiya mukayi sarkin aljanu day. gobe waziri day. jibi fadawa day. a haka har sai anzo su hakimi da sauran tarkace sannan azo kan uwayen amarya day. alhji bai ko iya lekawa ba sai karkarwa da yake yi. yana fadin. "kinji ta ko-kinji ko shikenan na kwaso wa kaina bala'i aljanar ce fa wannan ke magana" A cikin kunne yake wa umma Radah.
Umma tace "wai ni miye haka Dr gashi na leka banga komai ba Dr lafiyanka kuwa"....
"A saboda wannan abu da kayi mana zan baka Aljanu guda biyu masu Tsaran lafiyarka. zasu dinga binka ko'ina don tabbatarda Tsaro." da sauri abba ya leka "A'a wllh na yafe bana so na gode kuzo kuyi duk abunda zakuyi amma ki bar tsaron na gode". Ba saitin aljanar yake kallo ba domin tun kallon Farko da yayi mata yaji hantar cikinsa ta kada.
*hahahahaha* dariya tayi. "mun yanke hukunci ba mai ketare wa in na ajiye kara ko cikin aljanu bare kai kace zaka min gardama karya kaka" ta bacce batt!
Dr na juyawa yaga wasu yan kananun halita da basu wuce mage ba sai dai ba magen bace a tsaye suke tafiya idan ka kalle su dan muninsu da ban tsoro baza ka sake kallo ba. Abba yace "Na shiga uku"
"Alhj me ke Faruwa kuma?" bai tsaya bata amsa ba ya nufi daki da gudu yan aljanun kuma suka bishi a guje. har ma sun fishi gudu da kyar ya samu ya Riga shiga dakin ya Rufo kyauran da kadan ya datse kafar wani daga ciki.
umma tazo tana kwankwasawa. "Alhj bude mana me ke faruwa ne" Domin ita bata ganin komai ko maganar aljanar bata ji ba. daga cikin dakin Alhj yace "wai ke bakya ganin su ne. wallahi aljanune gasu nan wai gadina zasuyi dan allah Taimaka ki kirawo malam mujitafa wata kil shi yasan yanda zaiyi ya kore su"
"Hmm alhj kenan yanda ka dauki malam mujitafa ba abakin komai ba yau har kaine kuma kake neman taimakon sa. hmm ruwa baya Tsami banza kenan yanzu sai ka gane ko wane mutun akwai ranarsa Maganar da nake ta faman fada maka kenan amma sai kace bazaka taba neman taimako a gurin su ba To yau ga Ranar sa Allah ya kawo ji dakai da tamakar kai dan boko ne mai.. . "
"ke wai ni zaki tafi ne ko kuma zuba zaki tsaya kina tayi kamar Rariyar Garara." "yi hakuri Alhji bari inje to allah yasa ya Zo.
Ta