Author : King Boy Isa Category : My Hausa Novels
ya ambaci sujjada. a fusace ya daga kai sama ya kalle sa yace.
" na tuba bazan kuma yiwa wani aljani ko shedani sujjada ba. Wanda nayi muku a bayama. Allah zan roka ya yafe min. Shedanu kawai mugaye azzalumai. Allah yafi karfin ku ai kuma na fita daga bokancin inga wanda ya isa ya mayardani. Wani alh. Da ke wucewa a hanya. Naga ya tsaya sai kallan kasumu yake dake duk maganar da yakeyi a bayyane take. Ana ji. Mutumin kuma yaji duk abunda kasumun ya fada. Da sauri alhj. ya karasa gurin. Ya fara tambaya bawan allah lafiya. Lafiya kuwa. Kasumu kuwa sai huci yake kamar wanda yasha dan karan gudu. Abun mamaki mutumin na zuwa wajen kasumu ya bar ganin aljanin.
Alhj ya tambaye shi lfy kuwa. Bai boye mishi ko mai ba saida ya gaya mishi duk abunda ke faruwa da yake yana bukatar taimako. Alhj yace. Ba damuwa ka iya ayyatul qursiyya? Kasumu yace miye haka din? Alhj. Ya kama baki yace dan kari! Ah dole aljanu su takura maka. To da yake dai tana da dan tsawo baza ka iya rike ta duk a yanzu ba. Abun da nake so dakai yanzu shine kata fadar استغفرلله واعتب علك sanda aka sha fama tukun ya iya istigfarin. Mutumin yace yanzu ina zaka?.
Kasumu yace shi kam yanzu baima san ina ya nufa ba. Domin bazai taba komawq kauyen can ba. Idan ya koma yasan kara fadawa cikin kafurci zaiyi. Alhj yace tashi biyo ni muje gidana. Ba gardama ya bishi. Har a lokacin kasumu na fadar astag'firullah.
Karfe hudu na yamma abba ya dawo daga gun aiki yayi mamaki da ya ga su yasmeen a gidan amma bai nuna ba. Bayan su gaishe shi hade dayi mishi sannu da zuwa. Umma ce ta karfi jakan ta shiga gaba ya bita baya har suka kai dakin sa. Da suka shiga yake tambayar umma.me ya kawo yasmeen gida. In ma ziyara ne ai ynz dare ya farayi. Umma ta fiddo takarda ta mika mishi. Ya karanta ( what ya sake ta) cos o what? A kan me al ameen zai sake ta. Umma tace nima dai ban sani ba kuma nasan al ameen bazai aikata wannan mumunan aiki a hakanan ba. Domin yaran peace-loving ne kaima ka sani kaga dai tun da akayi auran nan har ynz ba' wata matsala data taba shigowa a tsakaninsu.
Nima hkn na gani domin al ameen is fair minded. But kirawo min ita. Umma ta fita ta kirawo yasmeen yare suka shigo. Dady ne ya zare mata ido yace gaya min me kika yi mishi ya sake ki. Dady wllh ba abunda nayi masa. No! Hakan bazai yoyu ba. Dole akwai abunda kika yi masa. Yayi yayi da ita taki fada. Hajara ce kamar wacce aka wullo daga sama ta shigo dakin. Haba yasmeen ki fada musu gaskiyar abun da ya faru mn. Tunda kinsan baki da laifi kuma nima shaida ce. Nan hajara ta fara basu labarin duk abunda ya faru tun daga kiranta da yasmeen tayi har kawo yau.
Abba yayi ajiyar zuciya. Yace to kinji ba. Ga gaskiya ai. To waye zaiga kato a gidan sa. Kuma baya nan kuma yaki zarginki. Ai ni abunda yayi yamin daidai kuma ko nine hakan zanyi. Kuka yasmeen ta farayi. Yace kukan me kuma kike tashi ki bani guri ni. Kuma ki sani nidai bazan dauki kafata inje in basa hakuri ba. Da wane ido zan kalle sa?. Ga gidan nan sai kita zama idan yaga dama yaxo ya nemi ki koma dakin ki to babu laifi idan kuma baizo ba to nidai bazan je bada hkr ba domin tsuntsun da ya jawo ruwa?.
Gida ya zama na su kursiyya kwana biyun nan sharholiyarsu kawai suka sha. Ga mugun kazamta cikin su ba mai shara ko goge..................................................................
♥ HAPPY ♥
JUMA'AH MUBARAK
♥ ♥
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
✍🏼Autan marubuta ✍🏼
👑King boy👑
🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿
page 109 - 110
|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟ZAMANI APR 2017 🌟
|_________________________|
***** zamani *****
🌟ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©Z.W.A
***** zamani *****
😇 ASSALAM.BARKANKU DA SAFIYA TO ALHAMDULILAH NA SAMA LAFIYA TUN KWANA BIYU DA SUKA WUCE JIKINA YA WARWARE. INAYIWA DUK MASOYANA MASU KIRANA DA MASU AIKA TEXT GODIYA. KUMA ISHA"ALLAH KAMAR YANDA NAYI ALKAWARI TO ZAN KWATANTA HAKAN WATO POSTS UKU A RANA. MUJE ZUWA. LOVE YOU ALL MY FANS ♥
🌷🌷IN DEDICATED TO UR MY BEST AUNTY. MMN ALI.
bakina bazai iya burta godiya a gare ki ba. Badan komai ba sai dan ya rasa kalar wacce zaiyi din a gare ki 👏🏼 na gode da kulawa allah ya baki abunda kike so duniya wa lakhirah ☺ na gode da kulawa. Love u too much my aunty
(_*After 3days. Da sakin yasmeen*_)
Zaune suke a falo kursiyya ce cikin shigar Yasmeen ba banbanci ko kadan. Marsiyya kuwa na zaune a kusa da ita suna hira.
Salamar da sukaji ne yasa marsiyya ta bace da sauri. Kursiyya kuwa ta tashi ta nufi kofa tana tambaya waye. Cikin wata murya a shagwabe take maganar. Yasmyy nice.
.
Ke wa? Hmm kina so kice kin manta da muryana ko yasmeyy?. Kursiyya tama rasa yanda zatayi domin kuwa idan ta bude matar zata gane ba Yasmeen bace. Muddin in bata san sunanta ba. Matar ta dade a kofa tana bin kan Yasmeen ta bude kofar amma taki. Yasmeen tayi rantsuwa tace wllh indai baki fadi sunanki ba to saidai ki koma ni kuwa bazan bude ba.
Dadai taga lalai Yasmeen da gaske take bazata bude ba tace. Haba yasmeen asiya ce fa. Kawarki wace kuka karasa makaranta tare. Ohh asiya wa? Hmm asiya Muhammad(Reality) da sauri kursiyya ta fuske ta bude kofar tace yar rainin wayo ai naso ace kinyi min gardama da sai na bari kin juya tukun in bude. Amma tun farko ina sane na kuma gane ki. Kawai dai yau tsokala nake ji. Asiya ta wani murgude baki. Tace ni kuwa wllh har nayi fushi da tafiya ma zanyi abuna.
Ohh! Srry sister wasa fa nake miki. Ta jawo hannunta shigo mn. A shagwabance ta shigo tana kunbure baki tana tatokarewa. Marsiyya kuwa tana gefe sai hararen ta take. Dake ita bata ganin Marsiyya.
( ni kuwa nace indai su Marsiyya ne ai da gudu zaki fita a gidan😀)
Bayan ta zauna Yasmeen ta tafi domin hado mata juice🍷 ita kadai a falo sai raba ido take. Ji tayi anja gashin kanta da dan karfi daga baya. Tace haba Yasmeen miye hk ko so kike ki tsinka min gashi. Shiru din dataji yasa ta waiga bata ga komai ba wajen wayam. Bata damuba ta juyo abunta.
Taci gaba da harkokin gabanta. Ba'a jimaba wani katan kadangare ya dilko a gabanta tim!! Ta saman kujera tabi a tsoraci. Ta kwalla ihuu. Tabi yasmeen har kitchen. Tana haki. Yasmeen ta tambaya lafiya? Me ya faru ne asia?. Kadan gare. Yasmeen din dariya ta hau yi mata. Wai wannan uban ihun duk sbd kadan gare ne.
Asiya tace ahh. Kiji yar rainin wayo dama ace kema din bansan ki da mugun tsoran kadan garen bane. To amma dadin abun da duk mota daya ce ta kwaso mu. Lokacin yasmeen ta gama hada lemon a kofi biyu ta zuba. Tace muje parllo. To uwar tsoro. Bayan sunzo sun zauna Yasmeen ta mikawa asiya kofi daya na juice din wanda aka zubawa kankarq yayi sanyi. Asiya ta karba ta dan kurba tukun ta ajiye. Tace yauwa dama nazo ne a kan maganar nan da mukayi ranar. Yasmeen tace wace magana fa? Na manta tuna min. Asiya ta harare ta. Ji yar air ko kina mance komqi ai baza ki manta wannan ba. Kawai dai raina min wayo zakiyi. Kuma kin san dai halina sarai bana daukar raini . ehhy!
Kursiyya ta rasa ya zatayi domin bata san maganar da sukayi da Yasmeen din ba. Da taga dai ba mafiyata. Sai ta juya ta kalli marsiyya cikin magana irin tasu wacce ko bakinta ba'a ganin motsawarsa. Tace sister kiyi wani abu mana. Marsiyya kuwa dama kamar haka take jira ayi. Tufe bakin Yasmeen keda wuya Marsiyya ta bace. Asiya tace ke kiyi dani kin wani tsaya kina jamin aji. Ina sauraren ki miye abunyi?. Yasmeen tace kedai sha lemo tukun. Rufe bakin ta keda wuya suka dinga jin wani irin kararaki na fitowa daga dakin umma can kuma suka dinga ganin hayaki na fitowa tururu. ..
.asiya a tsorace take tambaya Yasmeen miye wannan?. Miye wannan Yasmeen. Kafin Yasmeen tayi magana. Kofar suka ji an buga ta balle ta fadi a kasa tum! Saida yan hanjin cikin asiya ya kada sakamakon idanunta da sukayi tozali da wani narkeken aljani mumuna a tsaye a kofa. Duk jikinsa a yayanke yake jini na futa kamar ankunna famfo. Fuskarsa kuwa ba kyan gani. Ihu asiyya tayi hade da makalkale Yasmeen ita ma din ihun take. Asiya da taga abun bazai yuyuba. Yashi tayi cikin rudu da gudu ta nufi kofar fita ko jakarta bata tsaya dauka ba da niyar ta fita ta tsere. Habawa. Kafin ta karasa Kofar wani jaki ne marar kai ya bayyan. A gabanta. Yace asiya yan mata ina zaki ne keda kika kawo mn ziyara. Cikin murya irin ta mata yayi maganar.
Asiya sulalewa tayi a gurin sumamiya. Daga ganin hakq yasmeen ta taso tana dariya. Tace maganinki kenan. Ai gobe ma ki kawo mn ziyara. Asiya da ta tashi falkawa sai kawai ta tsinci kanta a kan gadan ta. Cikin dakinta. Abun ya daure mata kai...
***********
Yan kwanan nakin nan da al ameen yayi a S.A. duk ya rame ya wani lalace kallo daya zaka mishi ka gane hakan indai ka sanshi can dama. Ba wani abu bane yasa shi cikin wannan halin illa barazanar da dursum keta yi mishi da kuma kashedi ga yawan bashi tsoro da ake. Sai yaji shi duk ya tsani kasar ma ba abunda yake so illah ya sauka a gida Nigeria. Kamar kullum. Yauma yanq chat a imo sai yaga an kirashi video call. Da watq bakuwar number. Bayi wata-wata ba ya daga kira don ganin waye ke mgn. Gabansa ne yayi mumunan faduwa ...............................................
🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿
page 112 - 113
|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟ZAMANI APR 2017 🌟
|_________________________|
***** zamani *****
🌟ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©Z.W.A
***** zamani *****
Zainab tace yaya dama.. Dama me?. Fada inaji. Dama ba... Al ameen da yagano zainab bata so ta fadi maganar ne yace kaga malam kawar matata ce. Shi yasa na santa. Da sauri Zainab tace aa yaya al ameen. Gwara kawai mu fada mishi gaskiya domin ramin karya kasan kurare ne. Duk zurfin sa kuwa. Inji husaini. Zainab tace yaya hussaini kayi hakura. A chat muka hadu. What a chating ya fada zainab har saida ta zabura sakamakon mgnr da yayi a wani razane. Al ameen yace of course a whatsapp ma muka hadu. Amma karka yi mata mumunan zata domin a wani group na Whatsapp mai suna hayatul islam muka hadu. Nima garin biye biyen Link dina na shige sa a ciki na ganta kuma kasan dai halin mutumin naka da... Husaini a lokacin ya saki fuska yayi Murmushi idasa mana. Ka fara magana ka tsaya. Karasa mn kowa yaji. A daidai lokacin wayar husaini tayi kara yana duba screen din yaga mai call din sai ya tashi da sauri ya nufi dakinsa yana waya. Nan aka bar al ameen da Zainab a parllo. Hira suka hau yi suna dariya. Can al ameen yace wai ni kam laifin me nayi miki ne kikayi block dina. Ni sai kwanaki ma na lura da haka da na dauka ba kya hawane ashe blockdina kikayi.
Zainab tace kaine fa ka kirani kace gaskiya zaka fada min ba sona kake ba yaudarana zakayi miye-da-miye kace inyi block dinka da kanka kai ka fada min haka. Al ameen yayi shiru yana tunani. Shidai yasan bai taba aikata haka ba domin shi inma ya gaji dake saidai yayi block dinki badai yace kiyi nasa ba. Yace aa kin manta dai tuno dai wata kila wani ne zai gaya miki haka ke kuma sai ki saba layi kiyi block dina. Zainab har zata musa kuma sai ta tuno zuwan kursiyya. A zuciyarta tace tabbas wannan itace zatayi wannan aiki ba wani ba. Nan tayi yanda zata basar da zancen tace wai kana aminin yayana amma ace baka taba zuwa gidan nan ba. Gaskiya badan badan ba da nace baka da. Murmushi yayi yace karasa mana nasan cewa zakiyi bani da kirki ko?. Kuma ba haka bane duk laifin yayanki ne... Sun dade suna hira daga karshe dai ya karbi wayarta da kansa yayi unblock din kansa. Tukun ya bata wayar. Lokacin husaini ya fito yace kai uban surutu tashi mu tafi in rakaka gida ko in barks a nan ne.? Al ameen yace ai hakan ma yayi jeka abunka ka bamu waje muna hira ni da kanwata. Husaini ya rike baki yace au allah. Kai dallah malam tashi mu tafi. Juyawa yayi ya sai surutu al ameen yake ta zubawa zainab. Dadai yaga al ameen bayada niyar tasowa hannunsa yaje ya kama yace kaga malam taso mu tafi karka koyawa kanwata wannan shegen surutun irin naka. Al ameen ya mike badan yaso ba yace kanwata kinga wannan yayan naki korata yake a gidan naku ko. Wannan shi zai tabbatar miki da cewa baya so in zo gidan. Zainab tayi Murmushi tace aa ba haka bane wata kila baya so in kaje gida madam ta maka fada ne shi yasa. a'ah wato dai kema goyan bayansa kike ko tare dake ake korata. Lokacin umma ta fito tana Murmushi ganin su da tayi a tsai-tsaye tace ah har zaku tafi. Al ameen a kunyace ya sadda kai eh wllh umma zan tafi.
To madallah a gaida yan gidan. Yace to zasuji. Umma tace kuma sai yaushe?. Al ameen yace umma ai yanzu tunda nasan gidan zan dinga lekowa muna gaisawa. Ko ni daya ne. Dama can baya rashin sanin gidan yajawo haka. Nan sukayi bankwana da umma. Zainab kuwa har mota ta rakosu sukayi bankwana tukun ta juya su kuma suka tada muta suka tafi.
Su kursiyya a parllo sun tada sautin kida har daga waje ana jiyowa. Su mai gadi kam abun yafi karfinsu karar tayi yawa hakan yasa suka dawo kofar gidan suna ta masifa. Wacce bata da amfani. gidan sai wari da tsami yake tashi. Ba yanda za'ayi mai tsantsani ya iya zama na 10mints a ciki. kaya kaca-kaca ko'ina duk sun warwatsa. Su kuwa sai rawar su suke tikawa. Ita da marsiyya. Su al ameen suka karyo kwana suma tun a farkon layin suke jin kida kamar casu ake a layin. Husaini yace al ameen wai biki ake yi ne a layin naku. Shi kuwa al ameen dake yasan halin kayansa yace. Aa wllh ba biki bane Yasmeen ce. Yarinyar bata jin magana ne wllh na hanata- na hanata amma taki ta bari. Nace matq in ma waka take san ji ta dinga sasauta volume din amma a haka ai volume yayi yawa tana takurawa yan anguwa.
Husaini yace ah lalai wato ma da daurin gindinka take yi bama ka hanata ba saidai kace ta rage volume ko. To yayi kyau amma kasan irin wannan ba kyau ko. To ai ko ba komai ma kasani duk gidan da irin wannan sautin wakar ke tashi kai koma baikai haka kara ba to mala'ikun rahama baxa su sauka a gidan ba. Kuma bayan haka yana janyo aljanu. Shedanun aljanu suna san kade-kade da wak'e-wak'e kaga kenan gidan ka ne club din aljanu kenan kaga kenan yanzu haka ma suna can sun cika maka gida sai tikar rawa suke.
(Nayi dariya nace ka canka daidai ml husaini)
Al ameen ya dan bata rai yace ni fa kaji matsalana da kai kenan wllh. Kai baka waye ba abu kadan sai ka jawo wa mutun aya ko hadisi to ni bana san haka gaskiya. Idan zakayi wa'azi to ga masalaci can ko kuma kaje kasuwa i no need. Kaji mutun to shikenan sai in hanata ta shakata. Bayan kuma kasan ita din babbar yarinyar ce. Husaini ya jinjina kai yace ah lalai. Bazan hanata ba.allah ya baka hakuri kaji muje. Al ameen yace ameen yaja mota sukayi gaba. A kofar gida suka iske su idi da lawal mai gadi. Da sauri lawal ya tashi ya bude musu gate. Nan al ameen yake tambayar idi me yasa baije dauko saba a airport. Idi yace wllh motar ce ta dan sama matsala saida aka gyara kuma wayata ba charji. Al amee yace ok ba matsla. Ya shige.
Ta glass din window marsiyya ta hangi su al ameen na fitowa daga kofar mota. Da sauri ta juya ta sanarwa kursiyyya. Kursiyya ta juya baya ta kalli dakin kaca-kaca kuma ga wari. Da sauri tace marsiyya ta gyara parllo kafin su shigo ita kuma zata kwashe kayan wanke -wanke ta wanke. Kafin kace me marsiyya ta fara kimtsa dakin tana shashare ko'ina. Ita kuma kursiyya tuni ta kwashe kayan ta shiga kitchen tana wankewa a cikin sauri irin nasu na aljanu shaf-shaf ta gama ta shirya su. ta fito ta tarar da marsiyya ma ta gama. Kursiyya naga ta bace bat. Kafin kace me sai gata ta dawo hannunta dauke da kaskon turaren kamshi. Bullowarta keda wuya su al ameen suka fara kwankwasa kofa.marsiyya najin haka tq bace. Ita kuma kursiyya ta koma Yasmeen cikin wata kafurar shiga. Yar guntuwar riga figil kadan ta wuce cibiyarta.sai kuma jeans wanda ya dame jikinta ya tsuketa sosai komai na jikinta a bayyane yake.
Tafiya take tana karye-karye irin na wanda kunya bata ishesu ba. Tana bude kofar taga su al ameen ne. Rungume shi tayi. Tana oyoyo-oyoyo babyna shi kuma duk kunya ce ta rufe shi kokarin ture tama yake yi. Husaini kuwa tunda yayi mata kallo daya ya kauda kai bai sake kallan inda take ba domin mumunar shiga ce tayi wacce ko wasu arnan ma