Author : King Boy Isa Category : My Hausa Novels
yace tabb yaufa ake yinta amma bari kigaji ai idan kinsan wata baki san wataba.
ya juya ya kalli hauwa yace maza jeki ki samo min garwashi yi sauri yau zan fitar mata da taurin kanta tunda ta nuna min ita taka diriyace.............
nida nasmat da muke labe muna kallan fidda aljana muka kama baki nace tabb wannan aljanar fa tacika taurin kai ta baya naji an dan dake ni a firgice na juya inace aljanar ce sai naga ashe zeesa ce.lolz
i invited u to like my page follow this line below
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarks
naku har kullum kingboy little of writer's
for continue follow me 08096831009
🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿
page 37 - 38
|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|
***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©5SWA
***** 5 star *****
😘this page in dedicated to you
❤didje ❤
❤ ..... no name😜 ❤
❤zainab abdullahi ❤
❤fatima❤
❤ rukkaya alhaji❤
❤aminu tajudeen❤
❤ isah.❤
❤aisha hassan❤
and others fans 😉
da sauri hauwa ta tashi dake babu wata a gidan a makwabta ta samo garwashin tana kawowa malam ya karba ita kuwa ta koma mazaunin ta.
addu'a ya farayi yana tofawa a cikin garwashin haba wani irin ihoo da marsiyya ta dingayi. hakan yasa har saida makwabta suka fara lekowa wasu ta katanga wasu kuma ta kofa.
malam kuwa yaci gaba da toyata tana ihoo. tafara cewa wllh ynz zanyi mgn zanyi malam zanyi. sannan ya dan saurareta yace to fada mana ke wacece ke musulma ce ko kafura.
' ni ba musulma bace ta fada lokacin da bakin basmah ke mutsi. to me yasa kika shiga jikin wannan baiwar allah me tayi miki. "malam itace taja na shiga jikinta kuma bazan fita ba saboda na aure ta ta fada cikin wata iriyar murya.
malam yace ko a ku aljanu kin taba ganin mace ta auri mace ne. tace aa amma nidai na aure ta kuma ba wanda ya isa ya rabamu da ita. malam yace karya kike azzaluma ayar allah zata rabaki da ita shin zaki fita ko bazaki fita ba.
bazan fitaba sbd itace ta koya min santa koma na aure ta dan hk baka isa kasa ni in fita a jikinta ba.
malam yace gaya min garin yaya ne ta koya miki santa fadi muji.
bazan fada ba amma ina so ka sani ni ba yar iska bace amma ta maidani yar iska yar lesbian kuma ni na riga na aure ta dan hk dole ku bar min ita.
malam yace inalilahi wa'ina ilaihiraji'un. yayi ajiyar nunfashi tukun ya kalli umma yace ko zaki iya gaya mini meya jefa yarki cikin wannan mumunan abun abunda allah baya so kuma ya tsinewa maiyi.
umma tac wllh tallahi malam basmah yarinyar kirki ce mai kula da addini bata ma cika kula kawaye ba domin a halin ynz ma kawarta 1 tillo amma ban sani ba ko a can Borden din ta hadu da miyagun kawaye bata gari.
malam ya juya ya kalle basmah yace ynz dai abunda muke so kiyi hkr ki fita daga jikin yarinyar nan. marsiyya kuwa taki fur wai ita bazata futa ba. malam ya dauko kwano mai ruwa ya fara addu'a yana tofa mata. ba abunda kake ji sai iho.
zaki fita ko baraki fita ba. kai tsaye take cewa bazan fita ba. ai kuwa yaci gaba da jawo ayoyi masu zafi na ruk-yah ya dinga watsa ma basmah a fuska. ya dade yana hk ita kuwa tana iho tukun ta fara fadin cewa zan fita zanfita.
malam bai sauraretaba domin yasan halinta taurin kanta. saida ta fara cewa allah zan fita. da karfi take fadi zan fita. tukun malam ya dan saurara yace to fito ta ina zaki fita.
tace ta hanci zan fita malam yace bamu yarda ba. tace to ta ido. nan ma yace bamu yarda ba. nanfa tata zano guri guri mahalaka malam nacewq aa. har saida tace baki tukun ya ce to ta fito.
hangame baki naga basmah tayi wani irin bakin hayaki ya dinga fita. saida ya fita baki daya tukun tayi atisha'wa har sau uku. nan fa ta hau waige waige tana kalan mutane kowq na ganin haka duk suka ce alhamdulilah gaba dayan su.
basmah kuwa tambayarsu tashiga yi me ya kawo ta nan me ya faru ita da take makaranta ya akayi ta ganta a nan. umma ta fara yi mata mgn tace basmah ki kwantar da hankalin ki ba abunda ya faru. ta kalli hauwa tace tashi ki rakata ban daki tayi wanka ta canza kayi.
hauwa tace to umma ta tashi itq har a lokacin a tsorace take saida ta gwada ta wai taga ko ta dawo nml. garwashin dake cikin kasko ta mika mata tace dauki daya. basmah ta harare ta tace waye zai daukar miki wuta . dajin hk hauwa tace ah lalai kin samu. ta je da sauri ta kamata suka nufi bandakin.
malam ya juyo ya kalli umma da take faman yi masa godiya yace garin yaya hk ta faru me yasa kuka kaita borden yarinya hk mai natsuwa bayan kinsan da yawa tarbiyar yara na tabarbarewa a borden in basu hadu da kawayen kwarai ba.
umma da take ta faman sharar hawaye tace hk ne malam amma ni banyi tunanin tarbiyar basmah zata tabarbare sanadin borden ba ba yanda kanin mahai finsu baiyi ba a kan karda a kai basmah borden amma naki domin ni shawarar kawata na dauka tace basmah zatafi yin karatu a borden..
malan yace to allah ya kyauta ai ynz kinga kadan daga cikin sharrin mkrnt borden din ko nan dai suka danyi hira yaja mata kunne sosai a kan borden din tukun ta bashi abun saraka tana ta godiya malan ya tashi nuhu ya raka shi.
a daki ta iske basmah ta gama wanka har ma tasaka kayanta kwaliya ne batayi ba. waje ta samu ta zauna a gefan dan tsohon gadan nata ta kalli basmah da itama kallan ta take.
tace basmah zo ki zauna ina san magana dake. ta nuna mata gu ba gardama kuwa tazo ta zauna kusa da ita. umma ta kalle ta tace basmah nasan ki nasan tarbiyar dana baki ban baki tarbiya ta banxa ba ko a cikin anguwar nan ana kwatan cen ki saboda tarbiyar ki da kamun kanki kinsan da hk ko. kai ta daga alamun eh
basmah me yasa kika biyewa kawaye na banza me yasa zaki zubar da duk tarbiyar da na baki hb basmah ban taba tunanin zakiyi hk ba.
kuka basmah ta shigayi wiiwii. ba kuka zakiyi ba bayani zakiyi min garin yayi kika je kika biye wa abokan banza. share hawaye tayi ta shiga ba bada labari.
umma a ranar da..................................
juyawa nayi na kalli nasmat nace anyi shegiyar aljana mai taurin kai a nan. rugawa tayi da gudu na tambaye ta ina zuwa wai tace dataje ta gayawa marsiyya ina zagin ta. habawa da gudu na yarda paper da pen na bita ina bata hkr. friends ko kunga laifina? lolx
🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿
page 39 - 40
|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|
***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©5SWA
***** 5 star *****
😘 in dedicated to u my heart Repel with u fans 😉
❤ hafiz adam ❤
❤ hauwa yusuf ado❤
❤ fatima usman❤
❤ Real Saleem Uztaxu ❤
❤ Umaima Abdullahi ❤
❤umar d um❤
❤ Raveeat B Suleam ❤
thaks d love and support mijin aljana 🤝 i luv u all fans 😘
🤔 readers gaskiya kun bani mamaki duk kuna ina nasmat taje ta hadani da marsiyya in kukaga dajin data daure ni hmm sai ku kama baki badan ni jarumi bane ai da ynz ban kwabto ba shi isa baku ganni bama yau 😜
a ranar da muka je school din naga tsare2 kala2 abubuwa da yawa sun faru tun a ranar wanda ban saba gani ba. a dakin mu a kwai yan iska da yawa mata. kinsan irin bed din can mai hawa biyu ne sama da kasa to ni ina kasa wata yarinya da ake ce mata sadiya kaleed senior ce tantiriya ce ita aka sa a sama wato gadan sama.
tun a ranar ta fara neman mu kulla kawance da ita amma fur naki domin naga tamu bata zo daya ba. da safe ma hk taita nuna kulawa gare ni sai dai wai ita abuda take so wai in cire hijab dina wato ni taga tunda naje ban cire hijab ba. sabanin su da wani lokacin ko dankwali basa ma sakawa.
sadiya taci gaba da jana jiki ni kuma ina basarwa nayi kusan sati uku a makarantar amma bni da kawa ko ina ka ganni a nutse nake. kasancewar babu abunda nake a wajen da nake a zaune kuma na gaji da zaman kadaici hk yasa na koma ciki
tsayawa nayi cik ganin abunda siniyoyin ke aikatawa layi layi su sadiya suke bi ana taba Breast din kowa wai aji wanda yafi taushi idan ma baki tsaya dan allah sun taba ba to wllh da karfin tsiya za'a ririke ki a taba. nan fa jikina yq hau rawa na fara kyarma ina fadin wannan wane irin bala'i ne
juyawa nayi da niyar in gudu habawa ashe sun ganni wasu yan mata ne su uku karti aka sa su kamoni ai kuwa banje ko'ina ba suka isko ni kamar yarinya haka suka dauko ni suka kawo ni gaban sadiya.sai wani karkarwa nake na tsoro sa'adiya ta kalle ni ta wani kece da dariya gaba daya yan dakin ma suka rufa mata baya dariya suke. ta kalle ni tace ke wa kika fi a nan da bazaki bari a taba aji ba ko kuma wa kike jin kunya a nan. ta daga hannun ta wani zagaye dakin tace gabaki dayan mu nan mata ne ba namiji ko daya to dan haka kima saki ranki ki cire kunya ki ajiye gefe.
dayar senior din tace taba mana muji da alamu dai taushi gare shi shi yasa take rowa. sadiya naga ta miko hannu da niyar taba breast dina a'uzubillah na fara furtawa tukun na kabe hannun. kallan wannan yan matan tayi tace ku rike min ita mana nace. nan fa suka hada hannuwa na suka rike gam na kasa ko motsawa. gabana kuma ya wani kara firfitowa.
sadiya naga tana kallan kirjina tana wani lashe harshe tana wani lashe harshe tana wani lashe harshe kamar mayya taga .... ba riga😜
abun ya kara tsorata ni su kuwa sauran students duk sai na mujiya suka zobo mana hannu naga ta zuro zata kama kirjina nan fa na shiga kokarin kwafcewa amma ina nasha mugun riko ba yanda na iya. hannun takai tana ta mamatsamin tana dariya tana cewa shegiyar yarinyar nan ashe tasan abun taushe ke gareshi shine take neman yi mana rowa.
haba nan fa sauran seniyoyi ma suka zo suka shiga tataba ni ni kuwa hawaye kawai nake ba yanda na iya kusan duk wanda yake ji da kansa saida yazo ya lalaguda min Brest nasha kuka na har na gaji a nan suka barni suka yi ficewarsu.
abun ya kara tsorata ni su kuwa sauran students duk sai na mujiya suka zobo mana hannu naga ta zuro zata kama kirjina nan fa na shiga kokarin kwafcewa amma ina nasha mugun riko ba yanda na iya. hannun takai tana ta mamatsamin tana dariya tana cewa shegiyar yarinyar nan ashe tasan abun taushe ke gareshi shine take neman yi mana rowa.
haba nan fa sauran seniyoyi ma suka zo suka shiga tataba ni ni kuwa hawaye kawai nake ba yanda na iya kusan duk wanda yake ji da kansa saida yazo ya lalaguda min Brest nasha kuka na har na gaji a nan suka barni suka yi ficewarsu.
wata yarinya da ake kira naja'atu kabir itace taxo ta durkusa take gabaña ta rike hannuna tace sis kiyi hkr allah ne ya hadamu da seniors mugaye kuma marar tsoran allah gasu yan iska wannan abunda sukayi miki ynz haka sukewa duk wata bakuwa da tazo makarantar nan idan taki basu hadin kai.
dagowa nayi cikin hawaye nace ni kuma wllh sai na gayawa teacher abunda sukayi min domin wannan ba karamin cin mutunci na bane sukayi.
naja'atu ta dafani tace sis karma ki fara domin hakan bata lokacin kine ma zakiyi a banza domin ba malamin da zai saurare ki da yawa sun kai karar hakan amma a banzac aka dauki maganar. nan dai muka dan taba hira nida naja'atu ta gaya min sunanta nima na gaya mata nawa.
washe gari bayan an fito daga makaranta nida naja'atu tafiya muke muna hira domin kuwa tuni har mun dan saba da ita munje wucewa ne muka ji ance kai kuzo nan. juyawa mukayi muka kalli gurin da kiran ya fito sadiya ce gefe guda ta wani murtuke fuska hannunta na dama kuwa wata seniyo dince mai suna khadija.
mukaje muka tsatsaya gabanta. hararan mu naga tayi da sauri naga naja'tu ta durkusa rigata ta dinga jijigawa alamun nima in yi yadda tayi habawa ni kam ban fahimta ba ban ankara ba naji an wani kwalfe kafafuna na fadi kasa............................
.
.
.
.
friends i need u dua'a i'm sick bt da sauki ynz
🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿
page 41 - 42
|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|
***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©5SWA
***** 5 star *****
ta kwalfe kafafuna na fadi.
ke wato na lura da cewa kin fiye jiji da kai kina nuna ke wai ga ustaziya ta wani yatsine fuska to wllh ku sani cewa nan ba wajen wani ustazanci bane ku bari sai kun koma gida kwayi daga yau kar wacce na kara gani da hijab a cikin ku idan kuma kunki ji to bazaku ki gani ba.
na daga baki zanyi magana kafin in furta maganar naji an kwashe ni da mari ke marar kunyar banza wannan umarnine ba wai shawara muke baku ba ta kama hijab din tace cire maza cire. naja'atu ma da sauri ta cire. nan fa na cire dan guntun hijab din duk sai naji ba dadi na fara matse matse domin ni hijab din makarantar ma ji nakeyi kamae tsirara nake balle ace in cire ta.
kuka na fara yi dan allah kiyi hkr wllh bazan iya zama ba hijab ba kiyi hkr ki bani hijab dina. sadiya ta kalle ni tayi wata yar dariya tace hijab ko hijab kindai ganta ta dago ta tace to keda ita kunyi bankwana kenan baza ki kara sakata a cikin school din nan ba.
haba sadiya kiyi mana adalci mana hakan fa ba tarbiya bace yawo ba hijab ke kinsan fa makarantar burden bata rabuwa da iskokai domin kuwa nan a dokar daji muke naja'atu ce kw fadin hka. tabe baki tayi tace iyeee lalai yarinyar nan wuyanki yayi kwari inji sadeeya wato sunana kike fadi waka gatsar ba wani aunty ko senior ko to wllh kinja wa kanku kuzo kinja muku dama kayana sunyi datti muje in kwaso muku sai kun wanke su. khadija dake gefe tana wani hararen mu tace nima akwai kayana da sukayi datti muje in hada musu da su.
tashi mukayi sumi sumi muka bi bayansu muna yayatsine fuska naja'atu kuma har gwalo take yiwa sadiya ta baya. saida muka tsorata ganin uwayen kayan da suka tila mana. nan fa muka shiga basu hkr su biyun a kan su taimaka su rage kayan. suka ce ai fa ina wllh sai mun wanke su.
rokon su na shigayi domin ni kam ban saba da wanki ba ko a gida wankau ake kaiwa. sadiya ta karo bakinta wajen kunne na cikin rada tace min idan kinga dama zaki iya fansar kanki kinada abunda zaki iya cire kanki. cicira ido na shiga yi domin ni ban gane me take nufi ba abunda na sani dai ita ba namiji bace balle in yi zargin wani abu game da mgnrta na fansarkai.
raba idan da nake yi ne ta fahimci ban gane me take nufi ba shi yasa tace khadija yi mata bayani fala fala domin naga yarinyar ba wayaya ce ba. naja'atu dai kallan mu takeyi ta fahinci me suke nufi amma bata ce komai ba tana tsoro.
khadija ta jani gefe muna tafiya na waigo gani nayi naja'atu na girgiza min kai kuma tana mallake min kafada alamun aa kar in amince. nidai gaba nayi nabi bayan khadija.
saida muka dan koma gefe khadija ta kalle ni sama da kasa tace ke gaki kmr wayya amma naga ko kadan baki waye ba ina nufin ki bamu hadin kai kinga mu ba maza bane ba abunda zai faru dake.
dafe kirji nayi cikin kaduwa nace subuhanallah kina nufin les kenan. allah ya kare ni wllh bqzan taba amincewa ba kuwa.
khadija ta wani harareni tace kaji banxa wawaya karki amince din kece ai zaki shawuya. wa'azi na shiga yi mata haba aunty ynz ke tsakaninki da allah hakan daidai ne ki sani fa cewa da lesbian da kuma ludu duk laifin daya na domin ba banbanci kuma kinsan irin abunda ya faru ga mutanan annabi luw 'd Acikin Suratu Huud (as) Allah yace:
"YAYIN DA AL'AMARINMU YAZO, SAI MUKA SANYA
SAMAN BIRNIN YA ZAMA KASANTA, (WATO MUKA
KIFAR DA BIRNIN) SANNAN MUKAYI MUSU RUWAN
DUWATSUN WUTA NA SIJJEEL".
Kamar yadda Allah (SWT) yake cewa :
"SAI MUKAYI RUWAN (DUWATSUN AZABA)
AKANSU, LALLAI RUWAN DUWATSUN AZABAR NAN
TA WADANDA AKAYI MUSU GARGADI YAYI MUNI
KWARAI"
(suratun Namli ayah ta 58).
Saboda tsananin bala'in da yake cikin wannan aika-
aikar, Manzon Allah (saww) yace:
"MAFI GIRMAN ABINDA NAKE TSORACE MA
AL'UMMAH-TA, SHINE IRIN AIKIN MUTANEN
ANNABI LUUT".
(Tirmizy ya ruwaitoshi acikin Sunanu, hadisi na
1,457. Ibnu Maajah acikin Sunanu, hadisi na 2,563).
mari naji tas!! tace ni zakiyiwa wa'azi to bana so kije masalaci ko an gaya miki nima bansan duk wannan bane. nima kaina da kika ganni nan a ustaziyata nazo mkrtar nan daga baya ne na dawo kuma kema muna nan dake sai kin ajiye wannan ustazancin naki kinbi sahun mu.
na dafe kunci na nace allah ya isa wllh ban yafe ba yan iska kawai masu jawo mana bala'i da karancin ruwa.
su sadiya dake gefe nufo mu tayi domin taji abunda ke faruwa tana zuwa ta tambayi khadija me ke faruwa.