Author : King Boy Isa Category : My Hausa Novels
A kasa. Bata ganin mai jan nata.
Tayi kokari iya kokari ta kwace amma hakan ya gagara.
Sakamakon bata ganin mai jan natama balle ta san taya zata kankare. Ihuu kawai take tana kara. Basu gushe ba sai a cikin wani dan rami ma dai-daici wanda yake cike da jini. Aciki aka jefa ta. Nan fa ta fara facal niya tana kokarin fita. Garin kokarin fita taji ta tabo wani abu kamar jariri a kasar ruwan jinin nan hakan yasata dago dashi sama.
Wani mumunan jaririn๐ถ๐ฟ aljani ne mai matukar ban tsoro. bakin. Suna hada ido ya wangale baki yayi mata magana. Mayaba mayaba namanmu. Dama yunwa nakeji da ayamu kuwa zakiyi dadi ya wani fiddo wani harshen shi ja talabebe dashi ya lashi lips dinsa dashi.
Habawa hajara wulli tayi dashi da iya karfinta. Ta kwalla ihuu. Ta fito da gudu. Ta nufi hanya. Kuka taji kamar ana binta dashi hakan yasata juyowa dan jaririn ne ke binta da masifar gudu yana fadar mama. Mama data gudu. Nan fa ta kara wuta.
Tana cikin gudu naga taja wani uban birkiWanda yasa har saida ta fadi kasa. Sakamakon ganin wasu samudawan yan matan aljanu guda biyu ko wacce idan ka kalleta bazaka sake marmarin kallo ba. Domin fuskokin su abun kyama ne. Rabi na mutun rabi kuma baka ganin komai sai tsutsotsi manya-manya cike da gun sai wutsil wutsiltu suke yi.
Dayar ce ta kama kafar hajara daya ta dauke ta da hannu daya kamar mage. ta dagota saitin fuskarta tace ke wai ke kike tunanin zaki ja da marsiyya๐บ to karyarki tasha karya baki isa ba bazaki iya ba mun riga mun wuce sanin ki munsan lagon ki ke kuwa kin kasa gane namu.
Hajara kafafunta a sama kanta a kasa tana reto tuni ta gama kidimewa ta tsorace da jin furucin wannan aljanar.
Aljanar tace yanzu zamu gama dake zamu yagaki gida biyu mubawa jariran aljanu su shanye jininki. Aljanar ta juya ta kalli dayar basamudiyar aljana wacce nake zatan itace kursiyya.
Tace " aunty kama kan mu yagataGida biyu gobe sai muga wanda zatawa rashin kunya. Bata ce komai ba ta kama kan. Suka fara ja. Hajara na ihuu. Fets naji jini ya fantseni. sun cirata gida biyu kafafun daban kugu abun da yayi sama daban jini sai tsartuwa yake yi.
Firgigit. Ta farka ๐ฐ daga barcin da take yi. Wash! wash! wash! take fadi wannan wane irin mumunan mafarki ne nayi haka.? Take tambayar kanta. Hmm amma nasan abunyi. Mike wa tayi.
Cikin hanzari ta mike ta nufo parllo ta dauki handbag dinta dake kan tv . budewa tayi ta dauko wasu layoyi ta rata a wuya ta dauki wani farin abu dake cikin wata yar roba karama ta shaka a hanci.
( dariya nayi nace tofa nasmat zamu sha kallo yau za'ayi ta kenan kinga yar gado ko๐)....................................................................
GOOD MORNING
Little of writters
King boy
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 81 - 82
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐5STAR APR 2017 ๐
|_________________________|
***** 5 star *****
๐5โฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉ5SWA
***** 5 star *****
๐๐ _*FRIENDS INA ROKON ADDU'A KU BISA WANI ABU DA NAKE NEMAN ZABI A KAN ALLAH YA ZABA MIN MAFI ALKHAIRI --- allah kayi mana zabi mafi al khairi*_ ๐๐ฝ
Tana gama shafawa ta fiddo wani bakin abu a leda tace kashh! Ga turare amma ba garwashi ko dan ai akwai na ruwa.wata yar kwalbar turare naga ta fiddo sannan ta mike ta koma dakin. Da shigarta ta bude kwalbar turaren tafara bin kusurwoyin dakin tana zubawa sannan tazo ta kara zubawa a kan gadon. Su marsiyya ido kawai suke binta da shi.
Sanda ta gama tukun ta haye gadon tace ai nayi maganin ku kuma inma mayu ne in fatalwa ce kai inma aljanu ne sai mu gani. Yace ko layin nan nasan basu isa su ketaro ba balle ma ace sun zo gidan nan ba har su shigo dakinan domin na riga na daure su tsaff.
_na kalli nasmat nace bata san akwai wasu ma a cikin dakin ba_๐
Bayan ta gama surutanta taja blanket dinta ta rufa. _Marsiyya tace ai kuwa bake ba barci_ Ba'a dade ba taji an fara kwankwasa kofa. Tace yasmeen! yasmeen! Shiru. Can an dan jima kuma sai ta dinga jin ana taba bargon ana dan ja sama kadan. Da sauri ta bude ta duba bataga komai ba.
Ta kara jan bargo ta rufa _kachau!- kachau!_ ta dinga ji a saman dakin Kamar ana kada karau-rawa. Tashi tayi zaune abun ya fara bata tsoro fa miye haka bayan kuwa kawu yace mata idan ta fesa turaren nan ba aljani ba zuwa ko kusa da inda aka fesa turaren nan. To ya akayi hk ko dai jabu ya bani ne.
Shiru taji an daina kada karau-rawar can jimawa kadan tana zaune kuma taji kara a ban daki kamar ana wanka. _*Shaaaa!* Karin zubar ruwa_
๐ shiru ta zubawa kofar ban dakin ido tana sake-sake a xuciyarta ta tashi ta leko ko kuwa ta kudun dune abunta a gado.
_(ni kuwa nace wllh dama kin kwanta abunki domin abun yafi karfin ki keda kawun naki)_
Kwantawa tayi taja bargo ta kudundune Tayi shiru ko motsin kirki bata yadda tayi. Shiru taji anyi. Kuma sai ta fara jin kukan jarirai da yawa ma ba daya ba.
_*inyarrr-inyarr* kukan jarirai_
Ya cika mata kunne saida ta toshe kunnuwanta da yatsa. a hankali ta cire hannun. Dariyar garada taji anayi a gaba dayan dakin.
_*hahahuhuhoho* dariyar garada_
Wani mugun tsoro ne ya shige ta domin an kure iya saninta layar da ke jikinta da kuma turarikan dama ita su take takama dasu karkarwa ta farayi. Domin tsoratatan da ake yi yayi yawa.
_(nasmat tace irin su kursiyya ai basa jin tsafin boka domin suma shedanun ne. Qur'an kadai zai fatatake su)_
Wani lokacin ma ji take yi kamar ana jan bargon sai ta ririke. Ji tayi ana girgiza kofar dakin kamar za'a ballata. Itadai batayi magana ba kuma bata dago kai ba. Can jimawa kuma ta fara jin wani iska mai karfi na busawa.
_*Fuuhhhh* karar fitar iskan mai kama da guguwa_ hade da wata dariya a cikinsa.
Da sauri ta tashi ta yace bargon. Ihuu ta kwalla sakamakon abunda ta gani. Gadan da take a kwance ne a sama wata rabe yake da kasa. Ga kuma wata guguwa da ke zaza gaya ta.
Kamar wacce aka ce ta kalli gefan ta na hagun.
_Wohuhu_
Wata muguwar hallita ce ta gani mai kawuna uku ko wanne kai kuma yana da idanu sunkai biyar. Da tana ganin nisan wajen saman da gadan yayi. Amma bata san lokacin da ta duro ba. A zaune tazo kamar ba ita ta fado ba. Ta tashi ta zungura a guje. Ta bude kofar ta nufi.dakin yasmeen.
Yasmeen na barci taji ana kwankwasa mata kofa. Hakan yasa ta tashi cikin barci ta fara tambayar waye?. Waye ne?
Cikin wata murya dake nuna mutun a razane yake anty hajara ke magana. Nice yi sauri ki bude pls yasmeen yi sauri ki taimaka kiyi sauri ki bude. Tana maganar tana waiga baya tana kallan dakin.
Yasmeen ta taso tazo kofar dakin ta kuma tambaya kece. Wa?. Daidai lokacin ne anty hajara ta hangi wani baki kirin din abu ya durfafo inda take.
Habawa kara rikicewa tayi ta ke bugwan kyauran nace miki nice hajara ke dawaye a cikin gidan in ba niba. Yasmeen bata bude ba tace au aunty hajara me kika taso yi a cikin daran nan yanzu around 2:30 o'clock fa ๐๐ฝ
Anty hajara ta kara juyawa taga abun gadan gadan ita ya nufo. "Na shiga uku ta fadi kmr mai shirin yin kuka yasmeen yanzu ba lokacin tambayoyi bane pls bude min kofa pls yasmeen. Yasmeen tace to anty key din ne ya makale yaki murduwa.
Hajara tace kash! Ta juya domin ganin nisan inda abun yake. Ashe ma bata ga abun tsoro ba saida abun ya kara matsowa gare ta. Taga fuskan nan fa ta fara buga kafa tana wani makewa jikin kyauran tana bugawa kamar ta fashe da kuka ๐ซ wata irin haliita ce sanye da bakaken kasa ga kusunbi a baya. Idanunta jawur hakoran dogaye sunfi tsayin babban dan yatsa ga wani irin hanci kmr na alade๐ฝ saidai shi baki ne.
Abun tafiyar fatalwa yake hannu a waware ga yatsotsin wasu mugayan farata ne zako-zako . anty hajara kamar ta sร ki ihuu sai dai kuma tana tsoran yasmeen ta rainata.badan abun na tafiya a hankali ba da tuni ya iso gare ta.
Kara tsurewa tayi ganin abun ya kara sauri yana tahowa wani tagal-tagal zai kamata kiris ya rage saura baifi taku biyu ba ya karaso taji kofa ta bude. Ta wani fada kan yasmeen yasmeen da sauri ta mayarda kofar ta rufe tana tambayar lafiya kuwa anty. Ya na ganki ma duk wani iri kamar a tsorace kike.
Aunty hajara da ta tabbatar ta tsira kuma taga alamu yasmeen bata ga abunda ta gani ba. " tace wllh cikinane ya murda. Ta dafe cikin tana yamutse fuska. Shine nazo in dan shiga toilet.
Yasmeen ta kalle ta tace " sannu aunty ya cikin fatan dai da sauki kash! Gashi ba maganin ciwan ciki a guna. Amma anty toilet ai akwai toilet a cikin dakin da kike. Jubi ne ya fara ketowa hajara domin ta rasa karyar da zatayi.............................................................
๐ *nace nasmat rike bairon nan da paper kici gaba da rubutun domin ni dariya taci karfina. Su yar gado an sambado kar......*๐
Little of writer's
King boy
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 83 - 84
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐5STAR APR 2017 ๐
|_________________________|
***** 5 star *****
๐5โฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉ5SWA
***** 5 star *****
_*NOTE* kawayen yasmeen ina so kuyi hakuri ku barni in cigaba da rubutuna hankali kwance kmr yanda na tsara๐ ko dan tun farko laifi nane da ban fadi muku asalin yasmeen ba kuma ban fadi muku yanda suke da hajara ba. Da kuma yanda sukayi facali da addinin su muje zuwa dai in kukayi hkr zaku ji komai๐_ *luv u all fans wanda na sani dama wanda allah bai sada mu ni da shi ba.ina muku fatan alkhairi kamar yanda kuke min*
Anty hajara tace ni ai nama manta da cewa a kwai bandaki a cikine. Bata jira yasmeen tayi magana ba ta nufi ban dakin da sauri tana yan noke-noke yasmeen kallo kawai ta bita dashi bata kawo komai a zuciyarta ba ta hau gado abunta ta kwanta.
Anty hajara ta shiga toilet ta zauna kamar wacce datayi kashin da gaske. Sake-sake kawai take a zuciyarta wai kawu ya bata laya marar kyau. Ta dan jima a toilet din shiru tana zaune tana tsoran ta fito da wuri yasmeen ta gane ba kashin tayi ba hakan yasata yanke hukuncin tsayawa a ciki har sai ta dai-daici lokacin da yasmeen din tayi barci tukun sai ta fito.
A wannan shawarar ta kafu. Tana nan zaune ita kadai kan toilet kamar wace akasa dole sai raba ido take. Wani kyankyaso ne ya fado daga sama. _*diff*karar fadowar kyankyasan a kan tias_
Wata irin zabura tayi hade da yar kara bamai yawa ba. Saida ta lura da kadangaran ne kuma ta waiwaiga bataga komai ba tukun ta dan sama natsuwa.
Ji tayi ana shafar gashin kanta dake daure da ribon dake kan nata ba dan kwali dama hulace kuma ta baro ta a dakin umma. Da sauri ta waiga. Shiru bata ga komai ba. Juyowarta keda wuya wasu kyankyasan guda biyu suka fado _*tim*_ da masifan gudu tayo waje ko pant dinta bata ja sama ba. Sai a wajen. Allah yasa lokacin yasmeen barci ya fara debanta.
Anty hajara tayi ajiyan zuciya taje ta haye kan gadan yasmeen.nan ta dan tabo yasmeen lokacin ta tashi taga anty hajara na niyan kwanciya. Yasmeen tace ah aunty hajara ai dama saida nace miki tun farko ki dawo nan mu kwanta kika ki yan......
"Bata karasa maganar ba" aunty hajara tace ai ni badan komai na dawo nan ba sai dan zafin da ya dame ni amma da acan zan koma in kwana ai.
("ni kuwa nace in ba tsoro ba a koma mana. Lolz)
Yasmeen tace ai akwai ac. Eh naji akwai ac ai wutar dakin ce ta dauke baki daya. Kinga yanzu dai ba wannan ba ni barci nake ji. Ta juya baya ta rufe idanu.
Yasmeen tace ayi barci lafiya itama ta juya ta kama barcinta.
Su kursiyya parloo suka dawo suka cika shi da dariya irin tasu ta shedanu.
_*Hahahahuhuhhehehehekyalkyalkyalkyalkyakyakyakya* dariyar su kursiyya.lolz_
Kursiyya tace sister naji dadin zuwan ki gidan nan gaskiya gashi yanzu kinyi maganin wannan hajarar. Marsiyya tace wai ni waye kawunta ne boka ne kenan.
Kursiyta tace kwarai kawunta boka ne amma karamin boka. Dan Karya tafi yawa a lamarinsa.
Marsiyya tace ba kawunsu daya da yasmeen ba kenan?
Kwarai kuwa. Domin nasan asalinsu nayi bincike a kan yasmeen kwanaki domin in gano asalinta dan naga rashin addu'ar ta yayi yawa ba ruwanta da sallah balle xikiri yanzu dai bari in gaya miki yanda suke.
_maman yasmeen wato ramma wace suke kirada umma a baya ta taba aure kafin ta auri baban yasmeen Auren ta na farko wanda a shine ta haifi hajara din mahaifin hajara garinsu daya da umma can wani kauye ne a 9ja duk da garin musulmai ne amma tsafin su yayi yawa gasu da rashin imani_
Boka mai tabargaza baban boka ne a kauyen yanada yara biyu maza. Yayinda yaga mutuwa ta fara kusanto shi sai ya fara koya musu harkokinsa na bokanci. Babban dansa wato mujabir yafi dan uwansa kasumu ilimi da kwakwalwa. Domin shi yana daukar abubuwan da ake koya musu din sosai ba kamar kasumu ba da shi abun bai dame shi.
Boka mai tabargaza yana yawan gaya musu cewa su rike wannan harkar karsu bari ta kubuce musu. Sannan ya gaya musu cewa basu ba aure ba kuma kusantar mace yin hakan kuskure ne domin ko ku kafin in fara harkar nan na hafe ku. Nan dai suka kasance cikin daukar training a kullum.
Ranar wata asabar boka mai tabargaza ya mutu hakan yasa mujabir ya hau karagar mahaifinsa ta bokanci. Wata rana da yamma ya tafi neman wasu ganyayaki da kasar tururuwa a cikin daji.
Yana cikin tafiya can ya hangi wata kyakyawar yarinya ta nufo shi tana iho. Hakan yasa ya tsaya cik inda yake. Tana zuwa ta wani shige bayansa ta makalkale shi tana fadin ka taimake ni ka taimaka min macijine.
Shiru yayi ya dage kai sama wani dadi da dimin jikinta yana ratsa shi. Yace a zuciyarsa au ashe haka abun yake haka ake ji ashe in aka taba mace. Ashe dai mata da baba ya hanamu taba su haka ake jin dadi idan aka taba su.
Nan fa ya kudurci niyar sai yayi aure saidai in duk ya watsar da harkokin nan domin shi tun can farko dama mutun ne mai san yara nashi na kansa. Sai kuma gashi babansa ya sa musu iyaka da mata.
Yarinyar da take makalkale da shi wacce duk a tsorace take. A tunaninta macijin ya iso gare su har yayi wa mutumin illah.jin shiru yayi yawa yasa ta dago da kanta hade da sakin mujabir din.
Shi kuwa abunda bai so ba kenan domin bai ki su kwana a haka ba tana rungume da shi.
Yarinyar ta fara tambayars baiga maciji ba ina macijinda ya biyo ni.? Kyakyawar fuskarta kawai yake kallo yana Murmushi wai shin wannan Yarinyar yar nan garin ce.? Yake tambayar kansa.
Ke yar nan garin ce? Ya tambaye ta. Eh ni yar nan ce mana a nan aka haife ni. Ya sunanki.? Sunana ramma. Kaifa. Ni sunana mujabir ya fada lokacin da yake Murmushi.
Mujabir? mujabir? Ni kuwa ina ma nasan mujabir ta dan sa yatsa a kumatu ta alamun tunani. Au mujabir sarkin bakaye na garin nan ko. Murmushi yayi yace kwarai kuwa nine mujabir dan boka mai tabargaza. Ramma tace bakaga macijin da ya biyu ne bane?
Yace na ganshi mana gashi can. Ya nuna mata wani bangare a gefe. Macijin ne a saman iska shi ba sama ba shi ba a kasa ba. Yana ci da wuta.ramma sai da tayi yar kara. Taja da baya Tana fadin bana so bana so. Ya kalle ta miye bakya so.?
A nutse ta kalle shi tace kwata-kwata bana san tsafi shine abunda nafi tsana ma a rayuwata.
โ๐ผLittle of writer'sโ๐ผ
๐King boy๐
From comment
08096831009
Number marsyyy ๐
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 85 - 86
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐5STAR APR 2017 ๐
|_________________________|
***** 5 star *****
๐5โฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉ5SWA
***** 5 star *****
๐ท๐ทASSALAMU ALAIKUM BARKAKU DA SAFIYA FATAN KOWA YA TASHI LAFIYA KUYI HAKURI DA PAGE NAN DAI DOMIN IT'S VERY SHORT
๐๐ love u all my fans
Mujabir yayi shiru na yan wasu lokutan tukun ya dago kai ya kalle ta yace ina ne gidan ku?. Nan tayi mai kwatance wanda zai gane. Yace to shikenan sai kin ganni. Sukayi ban kwana tayi mishi godiya bisa taimakonta da yayi.
Har ta bace yana binta kallo wanda itama wasu lokutan tana juyowa in sun hada ido kuwa sai suwa juna Murmushi. To bayan mujabir ya cire abubuwan da yake so ya koma gida. Ya kira kaninsa wato kasumu yace mishi to shifa zai bar wannan harka domin kuwa aure zaiyi kuma baban su yace ba dama mutun ya rike mukami nan kuma yayi aure dan haka nidai ajiye wa zanyi idan zaka iya to.
Kasumu baiji haushi ba sai ma farin ciki da ya lulube shi domin dama yanzu yana san abun sosai.yace to yaya ba komai zanci gaba da yi ni. Nan mujabir yaci gaba da koya mishi surukan tsafi da wasu abubuwan na bokan ci. Bayan sati daya mujabir ya damka kambun sarautar bokanci a hannun dan uwansa wato kasumu.
A ranar yaje gidan su ramma inda ta kwatanta mishi tabbas ba karya yayi ba. Dake su al adar su lokacin idan kaje hira gun budurwa