Author : King Boy Isa Category : My Hausa Novels
da wata biyar ma aljani bai isa ya tako kafarsa cikin gidan nan ba.
Zan bar wannan shi kuma a nan fallo shima saboda tsaro. Kuje kuyi harkokin gaban ku kawai baku da matsala. Da Murmushi a fuskarsu suka tashi cike da farin ciki wai anyi maganin aljanu. Kawu ya shiga daki ya ajiye karikitan sa gefe guda. Tukun ya dawo ya kalli yamma yayi tafi! Raf! raf! Sai ga aljanun nan su biyu sun bayyana wato kibru-kibsu. Zubewa kasa yayi ya gaishe su tukun ya mika kokon bararsa a gunsu.wai a kan su taimake shi. A bisa karyar da ya tafka. Su kuwa suka ce sam bazasu sake taimakon sa ba tunda ya karya musu dokoki yake amfani da mata bayan kuma sun hanashi.
Hakuri ya shiga basu yace bazai karaba idan dai har suka taimake shi. Idan kuma ya kara to suyi mishi duk abunda suka ga dama. A haka suka yarda bayan da suka saka shi yayi musu sujada.
(Wa'iyazubillah! Allah yayi mana tsari da bokanci dama zuwa gurin bokan masu zuwa ma allah yasa su gane. Su kuma koyi hakuri da juriya. Domin rashin hakuri ne ke kai mutun ga zuwa wajen boka. Bayan shi boka bai isa yayi abunda allah bai nufa ba. Allah yasa mu dace. Ameen)
Nan ya tambaye su shin da gaske akwai aljanu a gidan nan ku kuwa dai tsoransu ne irin na mata. Aljanun suka ce tabbas akwai aljanu domin nan a dakinsu ma kake sai dai mu bamu san ko suwaye ba tukun sai sunzo. Kuma zamu baka tsaro da kariya kaida duk sauran yan gidan nan. Boka yayi godiya nan suka bace batt. Shi kuma ya tashi ya nufi falo yaci abinci tukun ya dawo dakin kursiyya a gadanta ya bingire sai barci.lolz
Su yasmeen yau an saki jiki sosai domin cqn na hange ta rike da waya sai suburbuda dariya take. Ba wani abu take wa dariya ba. Sai chat din da suke ita da kawayen ta. Haka itama aunty hajara. Sai faman chat ake cikin nishadi da walwala.
Karfe 11:00pm su kursiyya ne suka nufo gidan a kan iska sai dariya take mai karfi irin tasu ta aljanu. Ba wani abu take wa dariya ba. Illah muguntar da marsiyya tayi a yau. Domin yau ta karasa yarda yar uwar tata azzaluma ce. Dan sai suna tafiya. Taje ta tadewa wancan kafa. Tasawa wannan dutse a wanya yayi tuntube. Ta tsorata waccan.
Yau har akwai wanda ta jefa rijiya. Da kyar aka ceto rayuwarsa. Gidan suka nufo.marsiyya tace kai! Aunty a rage dariyar mana. Ke abu baya wucewa a wajenki?. Kursiyya tace kedai bari ai yau nasha dariya. Har na gaji. Daga nesa marsiyya ta hangi hayaki na tashi a gidan. Tace aunty ji wani hayaki. Dake tashi. Kursiyya tace yi sauri muje mu gani. Batt! Suka bace sai gasu sun bullo a cikin gidan. Marsiyya ta duka gaban kaskon tace aunty wannan ai turaren mayu ne. Kuma nasan dai saboda mu aka sashi.
Kursiyya ta kyalkyale da dariya kuma sai ta bata rai. Nan take naga wasu bakaken gashi dogaye na fitowa a jikinta bakinta ya wani koma dogo kamar na alade. Kanta kuwa haka ya koma rusheshe ba ko gashi daya a jiki. Marsiyya na ganin haka itama sai ta fara canza suffarta. Itama ta koma wata dudanniya. Mai ban tsoro.
turaren mayu kuma saboda mu. To waye zai aikata haka. Ko dai boka suka dauko. Hmm ai kuwa da yaci ubansa indai boka ne. Kinga taso mu shiga cikin gidan.
Bacewa sukayi sai gasu sun bullo a cikin parlo. Nan ma sukaga kaskon wutar. Dakin yasmeen suka bullo. Nan suka iske su yasmeen tuni sunyi barci. Marsiyya tace inaga fa ba wani abu sune da haukansu kawai suka kunna wancan hayakin..............................................................................
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
โ๐ผAutan marubuta โ๐ผ
๐King boy๐
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 103 - 104
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐5STAR APR 2017 ๐
|_________________________|
***** 5 star *****
๐5โฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉ5SWA
***** 5 star *****
Dakin umma suka nufa. Dakin a kulle suka ratsa ta jikin bango suka wuce. Mamaki ne ya mugun kamasu. Ganin kasumu mashe-mashe sai barci yake a kan gadan kursiyya. A gefan sa kuwa wannan yan guntayen aljannun ne. Suna gadinsa. Marsiyya ce ta daka musu tsawa kaii! Me kuke yi a nan. Wata muguwar zabura sukayi. Bama da suka juyo suka ga marsiyya ce. Sunsanta sarai. Yar sarkinsu ce. Gaisuwa suka fara kwasa suna tuba. Dai-dai lokacin boka ya farka yana jinsu amma ya lumshe ido kamar me barci. Koma yaki yarda yayi motsi ko kadan.
Kursiyya tace. Wannan kuma da kuke tsaro shi din wayene?. Daya daga cikinsu yace shi din uban gidan mu ne a karkashin sa muke aiki. To me ya kawo shi gidan nan?. Eh zuwa akayi aka dauko shi wai domin yazo ya fitar da aljannun gidan nan. Hahahahahahaha. Marsiyya tayi dariya tukukun ta murtuke fuska. Ta harari boka dake kwance. Da jajayen idanta tace. Au wai shi wannan dan bashi da kunya mu yazo ya kora. To bari in shekaka lahira kafin ka fitar damu. Din. Karkarwa boka ya farayi a cikin bargo kamar ya kwalla ihoo. Dan tsoro.
Hannu ta dan mika sama. Sai ga wata sharbebiyar wuka sai kyalli take ta bayyana a hannun. Dagawa tayi da niyar ta cakawa boka a makogwaro. Cikin hanzari ya mike yana nishi day-daya ya daga hannu biyu yana rokonsu. Dan allah kuyi min rai ni ba bokan gaskiya bane.ni makaryaci ne. Kawai kasuwanci na mayarda abun. Yana maganar kamar wanda zaiyi kuka. Dariya sukayi su biyun gaba daya. Hahahaha-hahahah saida sukayi mai isarsu. Tukun. Shidai kallansu kawai yakeyi.
Marsiyya ta kara bakinta gurin kunnusa ta dade tana gaya mishi wani abu. Saidai duk yanda na matsa domin inji me take fada. Banji ba. Dole sai hakura nayi. Bayan ta gama gaya mishi maganar naga boka yayi likis. Zuwa can kuma ya dago kai yace idan akayi haka zadai ku barni in tafi ai ko?. Kursiyya tace karkaji komai zamu barka ka tafi. Kaida yan komatsan ka. Yanzu dai sauko daga kan gadan nan. Hawa kan gadan ma da kayi sai nayi maka hukunci. Miko min hannunka. Da sauri ya mika. Dogon farcin ta mai tsini tasa ta dan yanke sa. Jini ya fara fita. Da sauri ya matse gurin. Maza ka koma falo. Da sauri boka ya tashi ya fita a dakin falo ya dawo yana ajiyar zuciya. Sannan kuma sai tunane-tunane yake yi na maganar da marsiyya ta gaya mishi.
Washe gari tunda sasafe. Su Yasmeen suka tashi sukayi wanka sannan suka fito suka nufi kitchen domin hada dinner. Sunsha mamaki da suka tarar da kawu a daki. Da sauri hajara ta karasa. Gurinsa ta tashe she shi tana tambaya lafiya kuwa kawu muka ganka a falo.? Boka ya tashi yana yan waige-waige tukun yace uhmm da kinsan uban artabun da mukasha da aljanu jiya da dare. Da sai kin jinjina min.
Ashe dai aljanun gidan nan naku sun wuce adadi.kuma ni ban taba ganin tsagerun aljanu masu taurin kai ba sai jiya. Kinsan ance sarkin yawa yafi sarkin karfi. To jiya sarki yayi iya bakin kokarin sa na yaga ya fitarda su daga gidan nan amma abun yaci tura. Har saida ya gaji ya barni dasu. Nan fa na nuna musu cewa ni dan gado ne. Kinga wannan ciwan kadai suka sama nasarar yi min. Da sauri hajara ta kamma hannun tana dubawa ayya sannu kawu. Nake ganin ma wannan ai kamar sawun farce ne?.
Eh mn farcen wata yar.... Bai karasa ba yaga marsiyya ta bullo a bango tana hararen shi. Hakan yasa yayi kwana. Yace farcen wata yar sarkin aljanu ce. Lokacin Yasmeen tace to kawu fatan dai anyi nasara? An kore su?. Yayi murmushi yace ai ynz gidan nan ba aljani ko daya. Domin gabaki daya na kore su jiya. Dan haka ku kwantar da hankalinku. Kuma zan tsaya inyi kwana biyu a nan dan tabbatar da tsaro. Yasmeen cike da murna harda dan tsalle na jin dadi. Tace mun gode-mun gode kawu. Bari mu shiga mu hado kayan kari..
Misalin karfe biyu naga motar al ameen. Ta shawo kwana a guje. Yazo daidai gate. Yayi oda. Da sauri M. Lawal ya zo ya bude. Bayan ya bude ne. al ameen ya shigo yayi park. Yace kai M.lawal zo nan. Da sauri m.lawal yaje ya duka yanayi mishi sannu da dawowa. Tsawa al ameen din ya daka mishi. Cikin tsiwa kuma ya haushi da fada. Wai yana jin mutun nayin hurn amma yaki zuwa ya bude kofa da wuri. Saida yayi mishi fada sosai shidai M.lawal hakuri yake ta faman badawa. Yana kuma tunanin yanda mai gidan nasu ya canza haka. Domin bai taba yi mishi abu makamancin wannan ba.
Al ameen ya juya a fusace ya shiga cikin gida. A falo ya tarar da . Yasmeen ita kadai zaune take tana chat tayi wanka. Tasa ka wata hadadiyar yellow atampa mai kwaliyar flaws. Dinkin riga da sket sunyi mata kyau sosai sun kama jikinta. Tsayawa yayi a bakin kofar yana kallanta yana murmushi. Ita kuwa hankalinta yana kan waya sai murmushi take ita kadai. .
Da dai yaga bata da alamar tasowa. Sai yayi gyran murya. A'ehhm! Da sauri ta dago kai. Idanunta basu sauka a kan kowa ba sai al'ameen. Wulli tayi da wayar ta saka yar kara ta nufo kanshi tana oyoyo-oyoyo taje ta wani rungume shi. Kamar wacce data shige jikinsa. Nan fa ta shiga. Kukan shagwaba. Um! uhm! um! A shagwabance take magana shine zaka tafi ka barni har na tsawon kwana biyu ko?. Jin yayi shiru kuma ya kame kamar gunki. yasa ta dago ta kalle sa domin taga me ke faruwa.
Lokacin data kallesa ta lura da wani waje ne ya zubawa ido hakan yasa ta juya baya domin taga me ke faruwa. Gabanta ne yayi mumunar faduwa. Kawu ne a zigidir daga shi sai gajeran wando yana yan matse-matse irin na muna hicci. Kuma shi al ameen yake kallo............. ....... . ........................ . .............................................
Turkashi!!!!!!! Me yake faruwa ne. Na tambayi nasmat??????
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
โ๐ผAutan marubuta โ๐ผ
๐King boy๐
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 105 - 106
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐5STAR APR 2017 ๐
|_________________________|
***** 5 star *****
๐5โฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉ5SWA
***** 5 star *****
allah ya baki lafiya sister *๐ซibrahim Fatima*๐ซ ku taya ta da addu'a yan uwa
al ameen ya nunasa da yatsa yace yasmeen waye wannan. zatayi magana ya daga mata hannu hade da yi mata tsawa. dakata yasmeen dama cin amanata kike yi idan bananan kin cuce ni yasmeen. Yasmeen me kika nema a gurina kika rasa?. kuka ta fara tana so tayi mishi magana amma ina kuka yaci karfinta.
.daidai lokacin anty hajara ta shigo falo din. tsayawa tayi cik ganin abunda yake faruwa. ta kalli. kawu dake faman raba ido.tace kawu miye haka kake yi lafiyan ka lau kuwa?. Sannan ta juya da murmushi ah al ameen yanzu ka dawo?. Yasmeen me ke faruwq ne. Naga kina kuka! Wani abu ne ya faru. .
Al ameen bai saurare ta ba. Karasawa yayi gaf da kawu. Boka kuwa sai wani makyarkyata yake yi. Waye kai me ya kawoka gidana. Tambayar da ta fito daga bakin al ameen din kenan.
Kawu ya tsaya inda-inda ganin hakan yasa al ameen ya daga hannu ya sharara mishi mari. Hade da cewa fada min kai waye.. Zan fada zan fada. Su Yasmeen kuwa kallo ne kawai nasu. Boka yace ni sunana tasi kuma ni tsohon saurayin Yasmeen ne. Tana sona ina santa hakan yasa duk lokacin da baka gida. Take gayyato ni domin har ynz tana sona. Idan nazo wuni nake a gidan nan muna soyewa.
Wani marin al ameen ya kara kai mishi hade da cewa tsohon banza kawai kai ko kunya baka ji ba?. Wannan yarinyar baka haifeta ba?. Su hajara kuwa mamaki ne ya cika su. Shin me ya samu kawu anya kuwa lafiyarsa. Yasan abunda yake shirin aikatawa kuwa?. Yasmeen. Kasa ta zube da gwiwoyinta. Tana kuka tana fadin wllh karya yake. Al ameen. Wllh kawun hajara ne. Kuma magani yake bayarwa mun dauko sa ne domin ya fitar mn da aljanun dake cikin gidan nan. Kum...... Bata idasaba ya daka mata tsawa me zaki gaya min.
Kin dai riga kinci amanata ban taba tunanin zaki min haka ba Yasmeen kin dade ashe kina cin amanata ke da wannan.ya kamo kwalar rigar kawu ya jijiga. Yace amma sai yau allah ya toni asirin ki dama ance rana dubu ta barawo daya tall ta mai kaya. Kuma shi ramin karya kurare ne. Dan haka yasmeen kije na sakeki saki 1 ki tatara kayanki ki bar min gida yanzun nan.
Juyawa yayi ya kalli bokaTukun yace me kaka jira a nan bazaka bace ba ko so kake in hadaka da hukuma ne? Da sauri boka ya tatara nashi ya nashi ya fita a guje. Har yana tuntube. Yasmeen kuwa ita da anty hajara magiya suka shiga yiwa al ameen yayi hakuri ya saurare su amma ina banxa yayi dasu. Dadai suka ga abun nashi ba alamar zai yi hakuri sai suka tashi. Yasmeen ta dauko kayanta.
Tana tafiya tana waigowa tana kallansa tana zubda hawaye. Shi kuwa gogan naku ko kula ma baiba.
Haka suka fita. Basu hau motar gidan ba napep suka tara suka hau cikinsu kowacce da abunda take tunani. Can Yasmeen tace aunty hajara kinga abunda kika jawo mn ko. Kinga abunda kawu yayi mn ko.? Laifin me nayi wa kawu ne. Ta fada cikin kuka. Cike da tausayi hajara ta juya ta dafata. Kiyi hakuri Yasmeen haka allah ya tsara amma koni nayi mamaki sosai abunda kawu ya aikata mn kamar wanda aka sashi dai wannan sharrin ai yayi yawq. Gaskiya al amarin nan abun a duba ne.
Dai-dai lokacin suka karasa kofar gidansu. Bayan sun biya mai napep suka shige ciki. Yasmeen na hada ido da umma ta fashe da kuka ta ruga da gudu ta fada jikinta. Umma ta fara tambaya lafiya?. Lafiya?. Lokacin hajara ta karaso gurin jiki ba kwari kamar kazarda kwai ya macewa a ciki. Umma da taga dai Yasmeen bata da niyar yi mata magana. Sai ta juya ga hajara tana tambaya minene?. Lafiya ku fadamin mana. Duk ta wani rikice. Anty hajara tafiddo farar takardar ta mika mata. Gabanta ne ya fadi. Hajara ta miye kuma wannan takardar miye. Yasmeen cikin kuka tace umma ya sake ni. Dumm!" Gaban umma ya fadi ta dafe kirji saki saki fa kika ce?.
To me kika mishi da ya sake ki bayan baku taba ko samun sabani a tsakanin ku ba to taya zai sake ki. Me kika yi mishi?. Yasmeen tace ban mishi komai ba. Aa ba wannan zancen shi mahaukaci ne da zai sakeki ba laifin fari balle baki? Kudai fadi min gaskiya. Su Yasmeen raba ido suka shiga yi.
Tayi tayi dasu amma fur! Suka ki su gaya mata abunda ya faru. Tace to shikenan bari babanku ya dawo tunda kun rainani ai shi kwa gaya mai...............................
FRIENDS KUYI HAKURI DA WANNAN DAN KARAMIN PAGE DIN GOOD NIGHT.
*SHIN ME KUKA FAHIMTA A CIKIN AL'AMARIN NAN?*
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 107 - 108
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐ZAMANI APR 2017 ๐
|_________________________|
***** zamani *****
๐ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉZ.W.A
***** zamani *****
su yasmeen na fita daga gidan al ameen ya fashr da wata mahaukaciyar dariya. hahahahah- hahahahaha- hahahahaha. nan take naga kursiyya ta bullo. itama dariyar take. zuwa tayi ta rungumi al ameen din. cikin murna da farinciki. tace sis tsarin ki yayi ina ji dake ina sanki ina kaunarki miye tsari na gaba?.
fatar al ameen din naga tana banbarewa. abun mamaki jikin marsiyya ke bayyana. ( kadan ta hana in sume. a gun. har sai bayan one week in farfado.lolz) bayan ta gama juyewa ta dawo asalin marsiyyarta tace. yanzu gida ya dawo hannunki aunty ke zaki dinga tafiyarda komai. yanzu Yasmeen zaki dawo. bata rufe baki ba naga kursiyya tayi juyi ta dawo Yasmeen sak ba wani banbanci. good aunty yanzu sai musha shagalin mu a gidan nan kafin al ameen ya dawo. ko ya kika ce. kursiyya tace haka ne fa kuma hegiyan yarinya akwai kwanya hiyasa nake sanki.
kasumu zaune yake yayi tagumi duk abun duniya ya ishe shi. wannan wace irin rayuwa ce. haka shidai tunda ya taso har yanxu bai aikata wani aikin alheri ba.abunda ya aikata yau yake tunawa. tabbas ya aikata babban kuskure. amma ya zaiyi. yasan idan baiyi hakan ba tabbas sai sun haukata shi tunda suka umarceshi da yayi din. to amma da wane ido zan kalli Yasmeen da hajara?.
wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo a fuskarsa.
yanzu kam cike yake da nadama. shi harkar bokan cin ma ji yayi kwata-kwata ya tsane ta. kallo daya zakayi mishi kasan yana cikin damu. wani shago dake kusa dashi yaje ya sayo ashana yazo ya cinnawa. kayan bokan cin nasa. ya koma gefe yana kuka domin shi yanzu baisan abunda zaiyi bama allah ya yafe mishi. domin ya kashe mutun yafi a kirga ya haukata wasu kuma yayi zina da matan aure ma. banda yan matan da yayi dasu masu zuwa gurinsa neman wata bukatar. durkushewa yayi a gurin yana kuka.
hahahaha-hahahaha. mahaukaciyar dariya yaji a saman kansa. daga kai sama yayi. wani makeken dodone. kamar video haka ya cika fadin saman. a tsorace ya dinga jan gindi yana neman wajen labewa.kasumu kenan bazaka taba samun damar fita a bokancin nan ba tunda ka yarda ka shigo ka shiga kenan. hahahaha. hahaha. cikin wata katuwar murya ake maganar mai fitowa da karfi hakan yasa saida ya toshe kunnuwa. kasumu! kasumu! ka dawo sana'ar ka indai mata ne ko dukiya ke tsone ma ido ta zamu baka su. muddin zaka dinga yi mana sujjada kamar yanda ake yiwa allah. (wa'iyazubillah) kasumu har ya fara amijcewa da zancen da yaji shedanin nan