Author : Jeedderh Lawals Category : New Hausa Novels 2026
daya dinga jefa min ranar nan da nayi rashin lafiyar nan, har na dinga tunanin zafin zazzabi ne yasa nake ganin hakan, dama da gaske ne? Dama duk wannan lokacin, kallona kawai yake yi a dage, yana min kallon wata sakara wadda bata san abinda take yi ba? Da kuma maganganun daya dinga min a jiya, ba karamin godewa Allah nayi ba da bai sa giyar soyayya ta kwasheni na dauki alkawarin da ba zan taba cikawa ba. Yanzu da na amince mishi fa aka sa mana aure ko aka daura ba tare dana taba ganinshi ba? Nasan mutuwata ce tazo kawai.
Hankalina ya kasa kwanciya, duk inda na juya idanun Yaya Bilal kawai nake gani a cikin dakin, haunting me. Naji na fara damben warto numfashina da naji ya fara guduwa, ina warto shi da kyar.
Ban san lokacin dana rarumi wayata ba na dannawa Janan kira.
Ta dauka cheerily, murya cike da tsokana, "hey.., har Muhammadun naki ya tafi ne?!".
A rikice na hau kiran sunanta ina maimaitawa kamar karatu, "Janan... Janan...!!".
Nan da nan ta rikice, tace "subhanallahi, Na'ilah me ya faru ne?".
Nace "Yaya ne! Yaya Bilal ne... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yau ya zanyi da rayuwata? Hasbunallahu wa ni'imal wakil!!".
Ai sai na kara rikitata, naji alamun motsa kaya daga can inda take, "me ya samu Yayan? Kun hadu dashi ne? Wai meke faruwa ne? Kiyi min bayani please!".
Na daga baki da niyar yin magana, amma sautin komi ya kasa fita.
"gani nan" kawai tace, kafin inji ta kashe wayar. Na koma na jingina da bango ina lumshe idanuna.
Abin kamar a almara haka nake jin shi. Yau da safe dana tashi, mafarki na farko dana fara tunawa wanda nayi ne akan Yaya Bilal. Maimakon abin ya bani mamaki, sai ma ya bani dariya. A tunanina meye hadin kifi da kaska? Tunanin Yaya Bilal da ni a waje daya, abu ne da bai taba, ina nufin koda wasa bai taba gittawa ta cikin raina ba, ko a mafarki ban taba ganin hakan ba sai a yau din. Shi yasa ko a dazun abin ya matukar bani dariya, saboda babu wani abu daya kamata inyi a wannan lokacin da yafi inyi dariyar.
Amma yanzu da naga abin yana shirin ya zama gaskiya, sai kuma abin yake shirin ya sanya ni kuka.
A yadda nake dinnan, a haka Janan tazo ta sameni. Ta tattagoni jikinta cikin tsananin nuna damuwa, ko bata furta ba fuskarta da idanuwanta sun nuna min hakan baro-baro. Hakan yasa naji jikina yana relaxing, na kwantar da kaina akan kafadarta, totally vulnerable.
Kusan mintunanmu biyar a hakan, kafin ta dago kaina daga jikinta, murya a tausashe, kamar wadda take tsoron idan ta dan kara daga muryarta zata saka ni kuka. Kodayake, hakan ne, ni nasan a yadda nake jina dinnan, zuciyata a wuya, to abu kadan da bai gamshe ni ba a yansu zai iya sa ni fashewa da kuka.
Tace "me ya faru ne? Wani abu ya faru da Muhammad dinne? Me kuma ya jefo Yaya Bilal cikin wannan magana?".
Na daga baki nace "Janan, Muhammad... Shi.. Yaya Bilal...". Nan da nan na fara hargitsewa. Tayi saurin taba kafadata, tace "kinga, nutsu kin gane? Yauwa, just calm down. Everything's good, ok?".
Na gyada mata kai a hankali, na fara jan numfashi ina saukewa a hankali har naji bugun zuciyata ya daidaita. A hankali na bude baki nace "Muhammad, Yaya Bilal ne! Yaya Bilal ne Muhammad Janan!!".
Naji wata zazzafar kwalla ta ciko min idanu, nayi saurin kokarin maida ta. Sai da na fadi maganar da karfi ta shiga kunnuwana, sannan naji gaskiyar lamarin yana shigata.
Janan ta zuba min idanu tana kallo, kamar wadda take jira in ce mata tsokanarta nake. To ai ni kaina jin abin nake kamar a mafarki ko a almara. Ni kaina na kasa yarda wai hakan ta faru.
Zuwa can tace "ta yaya?".
Nan na gyara zama na fede mata biri har wutsiya, ban rage mata komi ba. Tun daga fitata daga hostel, maganar da muka yi dashi har gudowar da nayi. Ban san cewa hawaye nake ba, sai dana sauke aya. Naja numfashi na ajiye, sannan naji lema tana bin kumatuna. Na sa hannu na share, amma ina dauketa wata ta sake gangarowa.
Na dora da, "Me yasa ni? Me yasa Yaya zai yi min haka? Me yasa hakan zata faru dani? Janan ya zanyi?".
Tace "mafita daya ce, kiyi hakuri ki danne zuciyarki, ki saurareshi kiji abinda zai ce".
Na tabe baki ina jinjina kai, "tab, lallai ma! In saurareshi ince mishi me? In gaya miki gaskiya ni da Yaya yanzu sai dai hange daga nesa, kai ko daga nesar na hango shi, zan canza hanya ne a sukwane ba tare da bata lokaci ba!".
Tace "amma kuma hakan ba mafita bace Na'ilah. Kika san ko yana da wani kwakkwaran dalili da yasa yayi hakan ne? Kada fa ki yanke hukunci cikin fushi Na'ilah, daga baya kuma ki zo kiyi dana sani!".
Nayi wata yar dariya da daga jinta babu digo ko alama ta farinciki a cikinta, sai akasin sa. Nace "wane dalili ne daya wuce ya muzanta ni, ya maida ni sakara? Da ba don nasan Yaya ba sosai, da sai ince baki ya hada da Umar ko wani akan suyi wasa da hankalina. Kodayake, ban san shi ba yanzu anymore!".
Janan ta kalleni, frowning. Tace "Ni nasan Yaya Bilal sosai, ba zai taba stooping that low to do something like this ba. Kamar yadda nace, da ace baya da kwakkwaran dalili, to ina mai tabbatar miki da cewa da ba zai taba ma bata lokacin shi tsawon lokutan nan ba!".
Na turo baki, "yanzu kuma kina bin bayan Yayanki ne, zaki yace min baya?".
Ta matso kusa dani da sauri, "koda wasa wallahi, haba, akan me zan miki haka? Ni fa shawarar da nake gani zata fissheki ce naki baki ba wani abu ba".
Na tashi tsaye, "whatever dai, ni dai an gama min wasa da hankalina, bana kuma tunanin zan iya tsayawa in sake sauraron shi".
Janan bata ce komi ba, ta zuba min idanu. Ni kuma na fara cire kayan jikina.
Idan da ace wani zai gaya min cewa a haka yinin na yau assabar zai kare min, da tuni zan karyata shi. Idan ma raina ya baci sosai, in kara da fada mishi bakar magana. Yau dana tashi da safe, ba haka na hango ni ba, ban taba tunanin akwai wani abu da zai zo yayi ruining yinin nawa na yau ba, sai gashi tun ba'a je ko'ina ba, yinin yayi bacin da ban taba tunani ba.
Na kalli kayan jikina dana cire, naji wani makokon takaici ya kawo ni wuya, ko linke su banyi ba na cukuikuyesu na jefa cikin kayana. Na dauki towel babba na daura a jikina. Ban cewa Janan komi ba, na dauki bokiti na sauka kasa na tari ruwa naje na watsa ruwa a jikina haka nan.
Ina cikin yin wankan naji an kira sallar magriba, don haka na daura alwala na koma sama.
Ina shiga dakin naci karo da Esther a zaune, da kayan dana baro a inda na ajiye. Ni na ma manta dasu. Daga ita har Janan suka bini da kallo.
Esther ce ta fara magana, ban san me Janan tace mata ba, amma naji bata tado min zancen dazu ba. Na dai ji ta tana mitar, "Ni wallahi nayi zaton ko accident ne suka yi ko wani abu a dazun, har na tsorata. Daga yace wani abu na gaggawa ya taso, sai ki wani rikice har haka? Lallai kina da babban aiki kuwa yarinya!". Ni dai na shareta ban ce komi ba.
Kayan dana ke sanyawa na shan iska na sa, na tada sallah nayi. Ina gamawa itama Janan ta shigo dakin, don haka na koma gefe na bata waje itama tayi. Tana gamawa Esther ta kallemu, tace "ni fa yunwa nake ji, kuma na rantse ba zanyi wani girki ba alhalin ga abinci nan ina gani a gabana. Idan ba zaki ci wannan abun ba, ki bani inci don ba zan so ayi asarar su ba gaskiya".
Nace "gashi nan kiyi ta ci".
Tayi tsalle ta rarumo kayan, Ina ji Janan tana itama a ajiye mata bari tayi sallah ta zo taci, nayi banza dasu su duka.
Ana kiran sallah na tashi nayi. Janan ma tana gama nata, ta zauna ta tada meat pie din da Esther ta rage mata da sauran drinks din. Dama guda biyar ne nayi babu yawa. Janan tana gamawa ta kalli agogo, tace "bari in tashi in tafi kafin Yaya ya dawo, yayi fada".
Ai jin an ambaci sunan Yaya, sai naji raina ya kara dagulewa. Na koma kan katifa na zauna, na harde hannuwa a kirji ina turo baki ina kallon Janan tana gyara zaman hijabin jikinta a wuyanta, ta gama ta juyo tana kallona, "mai kike jira ne, ba zaki raka ni ba?".
Na kara turo baki, "a'ah, ki gaida mutan gida!".
Ta daga hannuwa sama in mocking surrender, cam cikin idanunta alamun dariyar da take ta kokarin boyewa ne. Na harareta, ta kara yin murmushi, tace "yi hakuri ki maida wukar, ba ni na kar zomon ba kin gane? Bari in karasa gida ni kam. Don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, kada ki bari wannan abin ya taba zuciyarki kinji?".
Na kalleta kawai, sanya abu a cikin rai na nawa kuma?
A haka dai ta mana sallama ta tafi.
Ina zaune ina kallon Esther data tashi tana hada kayan, tana cewa ita dai ba zata yi wanke-wanke ba fa, "Sai dai idan kin tashi gobe ki wanke kayanki amma ba zan iya ba".
Ta dai gaji da mitar ta tayi shiru ganin ban tanka mata ba. Tana gama abinda zata yi, tace min ta tafi class. Exam dinmu ranar monday ne, amma nasan ko giyar wake na sha ba zan iya yin karatu ba yanzu. Don haka na kwanta kawai ina ta faman saka da warwara a cikin raina.
Har wajen karfe goma sha daya na dare idanuna biyu kyar, babu alamun barci a cikinsu. Juyi kawai nake yi, ba tare da takamaiman wani abu da nake tunani a kai ba. Wayata ta fara kara, daga farko cak nayi a zaune, hatta da numfashina sai daya tsaya sakamakon jin kalar karan. A hankali na juya na kalli wayar, babu shakka sunan Muhammad ne, ko kuwa Yaya Bilal zan ce? Yake yawo akan wayata.
Ban iya motsawa ba har ta katse, tana katsewar aka sake kira. Na hau gyada kai ina kara girgizawa cikin tsananin mamaki, yanzu har Yaya yana da sauran kunyar da zai iya kirana a waya dama? Oh duniya ina zaki damu?!.
Na dauko wayar da niyar kasheta, hannuna ya silale ya taba answer and speaker button ba tare dana kula ba, sai dana ji muryar shi radam kamar a cikin dakin yake yana magana, "hello? Oh thank God! Baby kina ji na? Baby...?!".
Da sauri na danne wayar har ta mutu, na dafe saitin zuciyata data hau bugawa da sauri kuma da karfi. Jin muryar shi a yanzu, sai naji kamar an tado min wani tsumi. Ko ba'a fada ba, nasan yau munyi baram-baram ni da barci.
Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe don Allah. Jiya sai dana yi typing, nayi zaton na turo na goge, sai daga baya naga ashe ban turo ba.
*☆⋆23⋆☆*
Washegari na tashi da wani azababben ciwon kai wanda ban taba zaton wani mahaluki zai taba yin kamar sa ba sai a ranar. Ni dama nasan za'a rina, yadda jiya na kwana ina sake-sake, barci ma sai gab da sallar asubahi sannan ya daukeni. Dalili kenan da yasa na so in makara sallah yau. Ina yin sallar kuma dana koma barci ma, kasa komawa nayi, sai can rana har ta ma fara fitowa sannan nayi barcin.
Yanzu kam zaune nake akan katifata da misalin karfe goma da rabi, kaina da yake bugawa kamar ana kwankwasa guduma tallabe cikin hannuwana guda biyu. Dakin babu kowa, Esther ta tafi church, Maimuna kuwa dama rabona da ita tun ranar juma'ah da safe da zan bar daki, ban kara ganinta ba.
Na samu na lallaba da dafa bango na tashi na fita. Ruwan wanka na jona a jikin heater, kasancewar ruwan da aka yi yau da asuba, yasa har yanzu garin sanyi garai. Yana dan yin zafi na je nayi wanka, nayi brush hadi da dauro alwala. Sai dana fara yin sallar walaha sannan na sake dafa wani ruwan a cikin kofi karami, na hada hot chocolate shi kadai na sha. Bayan na sha na balli paracetamol guda biyu na afa a baki na kora da ruwa.
Bayan na gama kin komawa in kwanta nayi, na kuma ki zama in saka tunanin Yaya Bilal da al'amuranshi a cikin raina. Sai kawai na dauki wayata na jona ta a jikin caji ba tare dana kunnata ba, na hada kan kayan wanke-wanke na kulle dakin na sauka kasa nayi.
Bayan na gama na koma dakin, ciwon kan ya dan sauka kadan, amma jifa-jifa na kan ji ya sara min har yanzu. Na bude dakin na shiga tare da maida kofar dakin na rufe. Kasancewar yau students suna ta hutawa kuma safiya ce, wasu kuma sun tafi gida, yasa hostel din yayi shiru babu hayaniya, yadda kasan ma babu kowa.
Na fara da kunna wayata. nasan dai ba zan dawwama a haka ba, komi daren dadewa nasan dole in fuskanci wannan chakwakiya. Ban shirya ba, amma nasan dole ne. Don haka naga gara in fara tun yanzu, the earlier, the better.
Ko minti goma cikakke banyi da kunna wayar ba, ta hau kara. Na saurara da goge-gogen da nake yi tare da tsayar da kira'ar Sheik Minshawi da dan yaro a cikin suratul-Mulk dake tashi daga cikin laptop dina, na dauki wayar. Ganin sunan Yaya Mudatthir na daga da sauri, cike da tunanin ko Anty Sailu ce ta sauka. Sai dai ina dagawa, tun ma kafin inyi magana ya riga ni, yace "wai ni Illo don Allah menene amfanin wayarki ne? Ke kullum aka kira wayarki a kashe? Me yasa ba zaki ajiye wayar kawai ki cire komi nata ba kowa yasan baki amfani da waya?".
Nayi dan murmushi, "Yaya, nasan amfanin wayata ni fa, wasu lokutan rashin caji ne yake sawa idan kun kira kuke ji a kashe".
Yace "kwarai kuwa, ai da yake duk Nigeria baby garin da ake wa kwauron wutar lantarki kamar nan ko?".
Nayi yar dariya, "ni ban ce haka ba. Anty Sailu ta sauka ne?".
Yace "tukuna dai, yanzu haka muna asibiti ma".
Nan da nan naji gabana ya fadi, nace "lafiya? Jikin ne ya motsa?".
Yace "a'ah, amma likitocin sun ce tana bukatar zama a asibitin zuwa lokacin da zata haihu domin su dinga monitoring dinsu ita da babyn. Amma so far dai komi lafiya lau".
Na dan sauke ajiyar zuciya, "Masha Allah, Allah ya sauketa lafiya. Amma nayi fatan ace ina nan yanzu tare daku wallahi".
Yaya yace "to ya zaki yi? Haka karatun ya gada ai. Ina fata dai idan ta haihu zaki zo ko?".
Nace "sosai ma! Ai ko muna exams sai na kansileta nazo!".
Yaya ya saki yar dariya, "ba wani nan. Ke dai kawai kiyi fatan kina free lokacin".
Nace "to shikenan. Ya su Inna? Kwana biyu ma bamu gaisa dasu ba".
Yace "a asibiti na baro ta, ni na dan fito yanzu. Amma idan na koma zan kira ki sai ku gaisa dasu".
Nace "to shikenan, sai ka dawo din".
Yace "babu dai wata matsala ko?".
Nayi dan murmushi a hankali, nace "babu Yaya. Sai anjima". Muka yi bankwana na ajiye wayar.
Aikin da nake yi na komawa, ina yi ina bin kira'ar har na gama. Ina gamawa na fara gyaran wajen da nake. A takaice sai wajen karfe daya na gama komi.
Bayan nayi sallah na fita waje can wajen yar kasuwar su na siyo kayan miya na dawo daki na hada miya na dafa farar shinkafa na ci.
Na dauki system dina na fara aiki akan project din da nake to har zuwa lokacin da Janan ta kira ni, sannan na dakatar da aikin na dauki wayar. Bayan mun gaisa ta watso min tambayar lafiya ta lau dai ko? Na kada idanu kamar ina ganinta, "ehh, ga wanda ya kwana ya wuni cikin tashin hankali da damuwa da rashin barci har da karin ciwon kai, lafiyata lau Jan. Ina fata kinyi kin tashi kin kuwa wuni cikin koshin lafiyata?".
Janan tayi yar dariya, "ai daga ji ma babu tambaya lafiyarki lau, ba sai kin janyo min wani dogon bayani ba. Ya karatu, ina fata dai kinyi ko?".
Na dan saci kallon tulin jotters da textbooks dana fiddo dazu wadanda suke jiran in daga su, tare da sauke ajiyar zuciya lokacin dana tuna akwai fa sauran gingimemen aiki a gabana. Nace "ban fara ba wallahi, amma anjima da yardar Allah zan fara tunda dama revising ne kawai zan yi".
Tace "hummm, nima hakan take. Allah dai ya bamu sa'a". Nace "ameen".
Tayi shiru, hesitating, banyi kokarin katseta ba ko tambayar lafiya, nasan tunda naji haka akwai magana da take son muyi, wadda kuma bata wuce ta mutum daya. Sai da tayi radin kanta tace "me zai hana ba zaki saurari Yaya ba don Allah? Ko sau daya ne Janan, ya cancanci wannan damar daga gareki".
Nayi shiru ina sauraronta, sai data dire aya sannan nace a hankali, "dalilin kenan da yasa kika kira ni dama? Saboda Yaya?".
Itama ta danyi shiru kafin tace "wai me yasa kike cewa haka ne Na'ilah? Ke kinsan cewa tsakanina dake ai babu wannan abin, wallahi jin ki nake kamar yar uwata ta jini, sai dai shima Yayan ina jin shi a cikin jinin jikina. I just want what's best for you Na'ilah, shine kawai!".
Na san duk abinda ta fada hakan take, idan kuma da kunya da kara, bai kamata in watsawa dan uwanta kasa a ido ba, sai dai bana tunanin zan taba iya wannan abu da Janan take kokarin sanyowa, ba zan iya yin wannan karar ba.
Nayi kasa da murya, cikin tsananin son yi bayanin da zata fahimta, wanda kuma ba zata kullace ni ba, nace "Janan... Ke kinsan abinda yake damuna, kin kuma fi kowa sanin yadda nake kin wannan akidar, don haka don Allah don Annabi Jan, ki taimake mu ki daina sako wannan maganar. Kince