AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   28 / 52

81K to 84K   out of 155.4K words

mata harara, "ni fa saboda wutar da Yayanki ya hada min yan kwanakin nan, kwalwata bata gane maganganu masu baki biyu. Don haka ki daina bani a dunkule kawai ki fito ki min magana kai tsaye don bana fahimtarki".

Itama ta harareni, tace "shi wanda kike likewa din, kina da tabbacin zai rike ki kamar yadda kike hange ne? Kin kuwa san waye Dr. Na Abba? Shekarunshi talatin da biyar, aurenshi bakwai Na'ilah! Aure bakwai! Amma yanzu bashi tare da mata ko guda daya sai 'ya'ya kashi-kashi dake gaban mahaifiyarshi wadanda matanshi suke ajiyewa idan suka rabu. Kin san me yake hada shi da matan har su rabu? Kika sani ko yana da wasu halaye da basu dace bane shi yasa? Kina da tabbacin ke idan kika aure shi a hakan, zaki zauna a gidanshi ne? Wallahi ina jiye miki yin dana sani Na'ilah".

Nace "na farko ba ni na like mishi ba, idan da wanda ya likewa wani a cikinmu to shine. Sannan nasan da labarin hakan ai, kawai mutane ne da basu rabuwa da tashin zaune-tsaye. Kika sani ko matan nashi ne masu halaye marasa kyau? Idan ma ba hakan bane, wai meye ruwan mutane ne da rayuwarshi iye?".

Janan ta daga baki cike da mamakina, tace "wai lafiyarki lau kuwa? Kin ma san abinda kike fada ne? Auren mutumin wannan da zaki yi sunan shi gudun gara, kin guji auren mai mata kin fada gidan mai 'ya'ya. Yo ba gwara auren mai matar da kika sani ba sau dubu akan wanda baki sani ba? Kodayake, rayuwarki ce ai. Kiyi duk yadda kike so da ita. Daga yau na daina yi miki magana game da Yaya Bilal in Allah ya yarda. Kiyi duk abinda kike ganin shine daidai a wajenki, jiki magayi!".

Ta juya ta wuce abinta, ni kuma na bita da kallo na wasu lokuta, kafin na bi bayanta da sauri ina kwala mata kira.

Da yamma Yaya Mudatthir ya kirani, Anty Sailu ta haifo yaranta maza biyu.







🙏🙏🙏🙏










*☆⋆29⋆☆*





"Yanzu yaushe kike tunanin zamu tafi wajen sunan ne? Ina ganin kamar mu tafi Talata ko? Ya kike gani?".
Janan take tambayata a washegarin ranar da aka yi haka, bayan mun dawo daga masallaci.

Nace "zaki je ne?".
Ta dan yamutsa fuska cikin nuna alamun rashin jin dadi, "ban gane ba? Kina tunanin ba zan je bane ko me?".
Nace "kinga, ni fa ba cewa nayi ki hayayyako min bane. Nasan Yayanki da protectiveness dinshi, ban sani ko zai barki kije bane, shi yasa".

"Wannan kuma matsalar mu ce ni dashi, don't you think? Kawai ki fada min lokacin da kike ganin yakamata mu tafi!". Ta fada a dan zafafe, har sai dana kara kallonta cikin mamaki.

Naja tunga na juya ina kallonta tare da kama kugu, nace "ni fa na kasa gane miki ne, tun da kika zo yau kike hade min girar sama data kasa. Na miki wani abu ne?". Duk yadda naso inyi masking damuwar data lullubeni, na kasa. Janan ita ce mutum daya kacal da duk duniya nake ganinta kamar jinina, kai wasu lokutan ma fiye da jinina. Ita ce kuma kadai nake ganin duk duniya, babu abinda ba zan iya sadaukar mata ba. Sai dai banyi tunanin sadaukarwa zata zo da consequences kamar wannan ba, wannan shine abu dayan da ba zan taba iya sadaukarwa ba. Don haka nake iyaka bakin kokarina wajen ganin cewa ban biye mata mun raba kai a tsakiyar titi ba, nasan cewa zuciyarta cike take da haushina dankar. Amma na fara kaiwa bango.

Tayi ajiyar zuciya, kanta yayi kasa cike da nuna nadama, "am sorry... Kawai na kasa wrapping kaina akan abubuwan da kike yi ne. Kin san cewa na damu dake, bana so ki aikata abinda zai zo ya zame miki dana sani daga baya wallahi. Why not Yaya Bilal kam? Kinga bayan mun bar nan, babu ruwanmu da tunanin rabuwa, zamu sake zama tif da taya, mu zama yan uwa na hakika".

Na dan sosa saman hancina cikin nuna alamun gajiya da zancen wannan, kamar ba ita bace take ihun maganar wannan ba zata sake hada mu ba jiya-jiyan nan.
Nace "Janan kenan! Wai ke a tunaninki zan iya jera kafada ne da matan Yaya Bilal muyi kishi dasu? Ki dube su fa ki dube ni, me zan nuna musu bayan bakar fata da tsaurin ido? Yadda yake da mata fararen nan tubarkallah, kamar ka taba jini ya fito, ban san me yake nema a wajena ba".

Janan ta kwashe da dariya, tace "babe! Wani lokacin shirmen ki dariya yake bani wallahi. You are very shallow, God! To an fada miki farin fata shine auren? Shi kanshi Yayan idan zan iya tunawa, ai ba fari bane. Allah wallahi ina shawartarki ni dai, ki sake zama kiyi tunani. Har ga Allah ba wai don Yaya yana Yayana bane, amma da ace shi wanda kika kafewa din kina son shi, kuma zai iya rike ki cikin mutunci, wallahi da baki kara jin bakina cikin maganar nan ba. Saboda ba karamin bata min rai kika yi jiyan nan ba".

Nace "kiyi hakuri", cikin sanyin murya. Jiyan yini nayi cike da damuwar bacin ran dana haddasa mata. Sai dai hakan fa bai yi kusa daya sanyayar min da gwiwa ba. "Amma wa yace miki bana son Dr. ne? Kina tunanin zan iya amincewa da auren wani bayan bana son shi? Kawai zama da kishiya ne baya cikin abubuwan da zan iya yarda Jan".



"Ke dai kawai ki ce, tsoron matan Yaya kike yi. Kina tsoron kiyi hadaka dasu, ki dinga challenging dinsu, suna challenging dinki, kina tsoron may be, you'll lose...". Ta fada cike da confidence, kamar tana da tabbacin abinda yasa nake gudun auren Yaya Bilal din kenan.

Nayi dariya da daga jin ta kasan bata kai zuci ba, nace "Jan kenan. Kin sanni sarai da tarar aradu da ka, sai dai wannan aradun tafi karfina, idan na dauketa tarwatsa ni zata yi. Maganin kada ayi, kada a fara. Gwanda in zauna a inda Allah Ya ajiye ni, kada in kai kaina inda zan hallaka!".

Da alamun ta fara gajiya da kokarin sanya ni fahimta da take ta kokarin yi tunda zancen wannan ya taso, tayi kwafa, "shi yasa zaki gwammace ki cuci kanki kenan akan ki bi zuciyarki? 'Cause let's face it, kina son Yaya Hilal, ni nasan wannan. Yanzu kin gwammace akan wani dalili naki na daban, wanda ba na Allah da Annabi ba, ki tauye zuciyarki da rayuwarki?".

Na daga kai na kalleta sosai, cikin girgiza kai, "baki san abinda na gani ba Jan, baki kuma dandana abinda na dandana ba, ba zaki taba fahimta ba... Ina kallo kiri-kiri ba zan jefa kaina inda nasan takaicin miji ko kuma na matansa ne zai kashe ni ba, ko kuma duka. Ba zan iya ba!!". Na kara maimaita mata, don tasan cewa da gaske nake, kuma ba zan canza maganata ba.

"To amma idan fa shi wanda kika kafe zaki aura din, shima yazo zai kara aure daga baya?".

Nayi shiru cikin tunani, lokaci zuwa lokaci ina irin wannan tunanin, sai dai har yau akan mafita daya nake sauka, "sai ya zaba ko ni, ko ita!".
Maganar ta fito tun daga kasan zuciyata har cikin bakina, babu wata tantama ko fargaba.

Ta zare ido cikin mamaki, ta daga baki zata yi magana, nayi gaggawar katseta, "na san abinda kike kokarin yi Jan, maganar gaskiya zan fada miki, itace ki daina bata yawun bakinki. So kike yi kiyi provoking dina, ko kiyi convincing dina, koma dai wannene daga ciki ba zai yi aiki a kaina ba. Kin san hali na sarai. Zama da kishiya daya ma bai cikin tsarina, Allah ya gani, balle kuma mai mata har biyu? Not a chance! Ba wai ba zan yi bane, ba zan iya ba! Don haka gwanda ma kiyi hakuri kawai, mu canza magana, kafin rayukanmu su zo su baci a banza!".

Maganar da nayi ta sosa mata rai, sai dai tasan kamar yadda nace, idan ta kafe akan wannan maganar, lallai rayukanmu zasu baci. Don haka ta girgiza kai kawai, "Allah ya ganar dake" kadai ta iya furtawa.
Nayi murmushi ina kai gorar yoghurt din dake hannuna baki, "Ameen".
Ban nuna mata na kula da kallon da take min ba na takaici da ban haushi, abu daya na sani, ba zan taba canza magana, ra'ayi, ko tsari na ba. Ba zan taba zama da kishiya ba!!.

Janan ta juya taci gaba da tunkarar pediatric ward bayan wannan, na bi bayanta da sauri tare da sankala hannuna bayan wuyanta, ina kallonta cikin kokarin ganin na dan yi lifting din mood dinta.
"Come now Jan, kada ki bari wannan maganar ta shiga tsakaninmu mana, shi yasa seriously maganar nan does not appeal to me that much. Haka kike so inje in auri yayan naki, idan muka yi fada ki dinga goyon bayanshi?".
Na fada cike da tsokana.

Janan tayi dan murmushi kawai, "Na'ilah kenan. Ni nasan ko hakan ta faru babu ta yadda za ayi in juya miki baya, ko mai zai faru kuwa... Yanzu mu bar wannan maganar, yaushe kike ganin yakamata mu tafi?".

Na dan sauke ajiyar zuciya cike da jindadin ta bar maganar, nace "kin san fa da kyar ne su bari mu tafi har na kwana hudu Janan".

Tayi yar dariya, daidai lokacin da muka shiga cikin ward dinmu muka wuce nursing station kai tsaye, tace "mu masu uwa a gindin murhu? Ango guda fa garemu a cikin wajennan, Allah na tuba ko wata ne ai ba zamu samu wata matsala ba".

Na jefa mata harara cikin wasa, nace "amma kinsan bana using mutane to my advantage ko?".

Tana shirin bani amsa, muka ji gyaran murya a gefenmu, muka daga kai. Dan halas dinne a tsaye a gefenmu, ni da Janan muka gaida shi ya amsa da murmushi akan fuskarshi from ear to ear, idanunshi a kaina yace "amaryata!".

Yadda kasan saukar aradu haka naji kalmar, wani irin vile feeling dana ji ya taso min daga can cikin cikina ya makale min a makoshi, yadda kasan zanyi amai. Na daure na hadiye shi, na kakaro murmushi duk da ni a karan kaina ban ji alamun murmushin ba. Nace "Dakta!".

Ya dan girgiza kai, "gaskiya zamu zauna muyi magana akan wannan sunan Na'ilah dear. Amma wannan zama zamu yi na musamman, ya kike?".

Na amsa a tausashe, duk da cewa can kasan zuciyata ji nake kamar ana tafasa min ita. Lallai idan aka cigaba da tafiya a haka, akwai matsala.

Ya jima anan muna yar hira dashi, Janan tashi tayi ta bamu waje. Rabin hirar sama-sama muka yi ta saboda hankalina baya tare da ni. Har sai daya kai ga tambayata lafiya? Na mishi karyar kaina ne yake ciwo. Nan da nan ya rikice, ya fara watso min tambayar ina bukatar ganin likita ne? Nace mishi a'ah, nagode.
Ranar da wuri muka tashi saboda ciwon kan da nace mishi ina yi, hasalima a motar shi ya kaini har gaban hostel dinmu, ya hado ni da tulin magunguna da yoghurts. Sai dai duk abinnan da rawar jikin nan da yake yi, ban ji wannan so da kaunar da nake ji ba a duk lokacin da Yaya ya nuna min kulawarshi ba.


Da kyar muka samu suka barmu zamu tafi ranar Laraba, shima sai da Dr. Na Abba ya sanya baki sannan.

Ranar larabar, da kanshi ya kaini har tasha inda zamu hau mota, muna zuwa muka hadu da Janan itama zuwanta kenan.
Muka yi sallama da Dakta, ya hada ni da dubu ashirin, goma muyi kudin mota, goma kuma in ba maijego ta sai wa yara kwalli. Da kyar ma dai na amshi kudin sai daya fara nuna alamun bacin ranshi sannan na amsa na mishi godiya. Muka hau mota muka tafi.

Motarmu ta samu matsala can wajejen Hadejia, gyaran da aka tsaya akan yi yasa bamu isa cikin garin Gashua ba sai karfe tara na dare. Yaya Mudatthir ne da kanshi yaje ya dauko mu daga tasha kamar yadda ya saba a yawancin lokuta. A gidan Malam muka sauka.

A gurguje muka yi wanka muka dan ci abinda aka ajiye mana, daga haka muka bi lafiyar katifa.

Washegari muka yiwa gidan suna tsinke. Yara sun ci sunan Malam da sunan Mahaifin Sailuba din.
Yinin nan cur haka muka yi shi cikin kujiba-kujiba, da kai da kawowa. Mutane ne mu na dangi, wadanda suke da son zumunci da karah. Taron da sunan Sailuba yayi, da irin alkhairan da suka samu ita da 'ya'yanta kadai ya isa ya tabbatar maka da hakan. A gidanta muka kwana ranar, saboda bayan watsewar yan taron suna, mun zauna gyara mata gidan har zuwa tsakiyar dare. Sai hakura ma muka yi muka bar wasu ayyukan zuwa washegari.












*☆⋆30⋆☆*




Dogon salatin da Fatsu ta ja ne ya tashe ni daga dan barcin daya fara daukata. Sai da daren nan muka dawo daga gidan sunan, bayan mun ci abinci mun dan kimtsa, muka yi sallah. Muna gamawa Janan ta fita waje inda Fatsu take zaune tana sak'arta, ni kuwa na kwanta akan abin sallar muna waya da ango na to be, wanda bamu jima akan wayar ba muka yi sallama saboda ciwon kai, gajiya, da barci da suka lullube ni (don dai kawai ya kyale ni). Ban san ma barci ya daukeni ba sai da naji wannan salati.

Na zabura nayi waje a sukwane, dankwali a hannu. A tsakar gida na samesu zaune akan tabarma, hasken wuta da aka kawo da yammacin nan ya haskake wajen. Na kallesu a rikice, nace "lafiya, me yake faruwa ne?!".

Fatsu da take tafa hannuwa, cikin salati har yanzu ta kalleni kamar na bullo wasu kawuna daga jikina. Na bisu da kallo ita da Janan cike da mamaki.

Sai data gama salatinta da sallallami sannan ta dakata, ta kama haba tana girgiza kai, tace "oh ni jikar su! Na'ilah wace irin shiririta ce nake ji haka? Kanki daya kuwa?".

Na fara raba kallo tsakaninta da Janan, fuska na bayyana tsananin mamaki da nake ciki. Nace "wai me yake faruwa ne? Kin sanya ni a duhu!".

Ta min dakuwa da hannuwanta biyu, "amshi nan ja'irar kawai! Ke dai wallahi baki ji dadin halinki ba. Dama wannan dan banzan ra'ayin rikau din naki yana nan? Nayi zaton duk yarinta ce ta janyo haka. To wallahi bari kiji, ba dani za ayi wannan haukan ba. Ina Yayan naki yake ne? Bari yanzu a kira min shi yazo!".

Ta fara neman wayarta tana cigaba da mitar dana kasa fahimtar abinda take cewa.
Na daura dankwalina tare da zama a gefen Janan da tayi tsumu-tsumu.
Nace "wai ni akan menene kike ta wannan fada ne kam, Fatsu na?".

Ta hararoni da duka idanuwanta, dama gasu tubarkallah, manya ne. Tace "gidanku nace! Wato ma baki san akan menene nake miki magana bane? To akan wannan yaro Yayan wannan yarinya da yake nemanki ne, kika badawa idanunki toka wai ke baki auren mai mata. Ba'a auren aka auri uwaki? Ko a gidanku don iyayenki mata nawa ne a ciki? To bari kiji in gaya miki, tun ma kafin tafiya tayi nisa, ki sallami wannan dan dukurkushin yaron da yazo nan. Ni dama tunda na ganshi naji raina bai kwanta dashi ba".

Duk da haushin Janan da naji ya ciko ni, hakan bai hana ni kwashewa da dariya ba, itama Janan ina ji ta saki dariyar. Nace "ji Fatsu don Allah, wai dan dukurkushi. Idan baki son mutum bai kamata ki bata mishi suna ba wallahi".

Ta dauki zaren da take saka dashi ta jefe ni dashi, "gidanku! Wato ke abin dariya ma ya baki kenan? Bari dai ki ga...", ta komawa neman wayarta, tana ganinta ta mikawa Janan ita, "yauwa yar nan lalubo min Mudan ki kira shi, ce mishi yazo yanzu-yanzu".

Dan halas din, kafin Janan ta ma lalubo lambar shi, sai gashi ya kwaro sallama ya shigo. Fatsu ta ware hannuwa kamar wadda zata rungume shi, na hau danne dariyar data taso min despite haushi da tsoron abinda zai je ya dawo daya cika min ciki. Fatsu ta harareni, ni kuma na harari Janan. A raina ina saka kalar rashin kirkin da zan mata idan muka samu muka kebe. Wato da biyu tazo Gashua kenan? Zata yi bayani ne.

Yaya ya samu waje ya zauna, shima dai cike da murmushi da kuma mamakin dabiar Fatsu a daidai wannan lokacin.
Yace "me yake faruwa ne anan?".

Fatsu ta gyara zama, "dama kiran ka nake kokarin yi yanzu. Kaji-kaji abinda yake faruwa".

Ta zauna ta zayyane mishi magana da halin da muke ciki da Yaya Bilal yanzu, babu ragi babu kari. Yaya bai ce komi ba tunda ta fara maganar, har ta direta.

Sannan yace, "ni dama nasan da walakin wai goro a miya, nasan tunda ta turo wani akan yazo ya ganmu kamar daga sama, nasan da wata a kasa. Ke yanzu a tunaninki hakan shine daidai a gareki? Ba zaki yi tunani wanda zai fissheki ba Na'ilah?".

Na turo baki gaba, "to ni Yaya wai nace muku ina son shi ne? Abun ai sai yayi min yawa, wai shege da hauka. Da wanne zan ji ne? Da rashin so ko kuma zama da kishiyoyi?".

Yaya ya kama baki, "ni kike fadawa haka Na'ilah? Lallai wuyanki yayi kauri da yawa. To bari kiji in gaya miki, idan ke idanunki a rufe suke, mu namu a bude suke tar, kuma babu ta yadda za ayi muna kallonki ki bi hanyar da bata dace ba kin ji na fada miki...".
Ya hau fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, daga karshe dai ya kare da, ".. don haka tun ma kafin magana tayi nisa, ki sallami mutumin nan. Mu dukanmu hankulanmu basu kwanta dashi ba, balle me ma zaki yi da mutum mai auri saki? Kina da tabbacin zai tsaya ne a kanki? Ga responsible mutum irin Bilal? Dan gidan mutunci da karamci, wanda kuma muka sansu suma suka sanmu?".

Gabadaya haushi yazo ya dabaibayeni wai me yasa ni ba zasu duba dalilina ba, zasu dinga concluding rayuwata kamar idan nayi auren su ne zasu yi min zaman auren ba ni ba? Na tashi

28 / 52