Author : Jeedderh Lawals Category : New Hausa Novels 2026
"come on mana, nasan dana baki wayar nan daga tashinki daga barci, ba lallai kici abincin nan da wuri ba. Ko baki ga kokarina bane?".
Na daga baki zan bata amsa, aka amsa kiran dana dannawa wayar Dr., don haka na rufe bakina tare da kara wayar a kunne.
Tun kafin inyi magana ya riga ni, daga jin shi cike yake da doki da farinciki, "hey, guess what?".
Yanayin yadda yayi maganar kanshi ma, kasan cewa wani abu ne babba kuma muhimmi ya same shi, don haka naji na saki murmushi ba tare dana shiryawa hakan ba, nace "me ya faru ne?".
"Tafiyar nan fa ta samu, nan da sati biyu! Oh God!! I can't really believe this is happening!!". Ya karasa fada cikin karajin murya.
Naji na balle da murmushi nima kamar lebuna na zasu rabe biyu. Wani course ne asibitin zasu tura manyan doctors na department din su biyar kasar London duk bayan shekaru biyu, course ne na shekara biyu. Yace idan kaci sa'a, idan can asibitin da kaje yin course din suka ga kwazon ka, zasu iya daukar ka aiki kamar yadda suka dauki likitocinsu biyu aiki wadanda suka je waccan shekarar. Idan kuma baka samu aikin a can ba, idan ka dawo, zasu kara maka matsayi da kuma albashi anan. Wannan ba ma shine abin birgewar kadai ba, idan ka tafi can asibitin zasu dinga biyanka albashinka, su baka wajen zama, haka babu ruwanka da biyan kudin makaranta idan kaje. Tsarin shine, idan ka tafi yanzu, zaka yi wata takwas a makaranta kana daukar darasi abinka, a hakan ma kana da albashinka a hannu, bayan ka gama da nan zaka koma asibitin kayi aiki dasu na watanni goma sha biyu. Daga nan kuma sai su yanke shawarar yadda zasu yi da kai.
Yace min yanzu sau uku kenan yana applying ana hana shi, wannan karon ma kwata-kwata ya cire ranshi daga samu, sai kuma gashi yanzu babu zato babu tsammani, ya samu din.
Nace "Masha Allah, Alhamdulillah! Kai amma naji dadi wallahi, Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah ya albarkaci aikin wannan".
Yace "ameen ameen amaryata. Ni har na rasa wace kalar murna ma yakamata inyi, ji nake kamar mafarki nake yi!".
Na saki yar dariya, "right! Kawai ka kalli alkibla yanzu, ta nan kadai zaka nunawa Allah godiyarka. Idan ka bar nan kuma, sai kayi sadaka".
Yace "haka ne, nagode dear. Bari in tafi yanzu".
Na girgiza kai fondly, wani lokacin kamar yaro haka yake gudanar da dabi'un shi, wasu lokutan ya baka dariya, watarana kuma takaicinshi ya cika maka ciki kamar kayi me.
Wani tunani ya darsu a raina, nace "to amma ya zamu yi ne? Bikin ma nan da sati biyu ne, kenan hakan yana nufin tare zamu tafi kenan?".
Ya danyi jim, zuwa can yace "har yanzu ina kan wannan tunanin ne. Yanzu zan shiga gida in sanar dasu, zan kira ki zuwa anjima". Nace mishi "to ka gaishe dasu Hajiya". Yace "zasu ji", ya kashe wayar.
Na bi wayar da kallo, ko menene abin yin tunani a cikin wannan maganar? Na tabe baki tare da daga kafada.
Su Janan da tunda muka fara wayar suka katse hirarsu suke kallona jifa-jifa, suka zubo min idanu, na kallesu cikin murmushi, "dudes, London ta kira mu yanzun nan!".
Habawa, suka saki ihu da shewa tare da fadowa kaina, sai da muka fadi kasa.
Janan tace "da gaske?!".
Esther kam, "Oh my God!" Kawai take fada tana nanatawa.
Sai da suka gama ihun murnarsu sannan Esther ta tashi zaune, muma muka tashi. Janan ta sake sarkafo hannunta ta rungumo ni, "Na taya ki murna wallahi dear... Allah yasa hakan shi yafi alkhairi. Yanzu sai kiyi tafiyarki ki barni?".
Nayi dariya, "sis, maganar fa bata tabbata ba. Ni fa ina assuming abubuwa ne kawai".
Ta kai min duka a kafada, "maganar banza kenan! Ke yanzu kina tunanin zai tafi ya barki anan har na tsawon shekaru biyu? Wasa kenan. Balle ma, su da ana basu gidajensu acan, ai babu ma wani dalili da zai hana mu zuwa kai amarya kasar London". Ta kyalkyale da dariya bayan ta gama fadin haka, ni da Esther muna taya ta.
Sai wajen karfe biyar na yamma sannan muka fita zuwa amsar dinkin. Har Esther muka tafi. A hanya Janan take tambayata, "su fa kayan lefen da ba'a kawo ba har yanzu, ya za ayi dasu?".
Na kalleta, "ke da kika san zamani ya canza, yanzu lefe da zaki ga har ana saura kwana biyar daurin aure ba'a kai ba. Balle shi fa yace kamar haka al'adar gidansu take, sai bayan aure ake kai kayan lefe".
Janan ta jinjina kai, "haka ne. Mu dai ya taimaka ya kawo kafin mu kaiki, idan haka ne, bamu da damar daukar turamenmu kenan".
Na kai mata duka ina dariya, "ke fa baki da M wallahi, wawashe min kayan zaku yi kenan?".
Muna wannan hirar har muka fita waje, muka hau bus zuwa inda muka kai dinki.
Dancing Banana, nan ne wajen da muka kai dinki. Duk da wasu kayayyakin suna can Katsina, Maryam ta kai min su, kai wasu ma suna Kaduna. Wadannan wadanda Ummahn su Janan ne ta bamu, manyan atamfofi guda biyu iri daya, da wani lafiyayyayen yadi ni da Janan din. Da kanta ta kai dinkin, namu kawai tura measurement dinmu ne.
Wadanda muka kawo nan, wanda angon ne ya kawo, tunda ba'a riga an kai lefe ba. Na Katsina kuma, wanda muka fitar ne a matsayin anko.
Kai tsaye wajen wanda yake mana dinkin muka wuce, muka samu ya dinka kala na mutum daya, na dayan kuma ya yanka bai dinka ba. Esther ta fara fuming, dama ita ta hada mu dashi, "yanzu kana nufin kusan sati biyu wai har yanzu baka gama mana dinkin ba? Mike meye hakan wai?".
Yace "na fa yi kokari, yanzu haka aikin wata na maida gefe nayi wannan din fa. Nayi alkawarin nan da kwana biyu zan gama muku, kin san bama yin haka dake Esther".
Muna nan tsaye, sai ga Haleemo a gabanmu. Bata ko yi acknowledging dinmu ba, ta hau zazzagawa mai dinki masifa. Apparently, ita ce wadda ya ture dinkinta dake kan layi ya mana namu. Tun yana bata hakuri, har shima ya hau sama ya fara zuba mata tata kalar masifa, mu kam muka koma gefe muna kallonsu.
Ta ja tsaki, "matsalarku kenan dama wallahi, ku kwata-kwata baku san mutumci ba. Su waye suka fito da martabar wannan shagon idan ba mu ba?".
Yace "ke kada fa ki kawo min rainin wayau nan wajen. Kada ki manta ko wancan dinkin dana miki, baki cika min kudina ba. Wannan ma kika wani ciccibo kaya kika kawo min babu ko sisi, an gaya miki ni din bawanki ne wai?".
Sai lokacin ta kallomu, ta fara borin kunya, "to ni nace ba zan baka kudin ka bane? Kada ka wulakanta ni a gaban mutane mana!".
Ni da Janan muka danne dariyar data ke neman subuce mana.
Shi kuwa Mike yayi dan tsaki, "whatever, kin san ni bana irin wadannan tone-tonen. Su ma don dinkin aure ne shi yasa ma na ajiye nakin gefe guda".
Ta kallemu ido a zare, "aure zaku yi?".
Nayi murmushi nace "eh".
Tare da bude jakata na dauko iv na mika mata, ta amsa ta karanta. Tace "to Allah ya sanya alkhairi". Muka ce ameen.
Bayan mun tabbatar da cewa zuwa jibi zamu dawo mu amshi dinkin mu, muka tafi muka bar su suna cigaba da sa'insar su.
A kofar wajen, muka samu Umar tsaye a jikin motar shi, da alama budurwar tashi yake jira. Muka yi kallon-kallo dashi, muka zagaye shi muka wuce abinmu ba tare da wani yayi magana ba. Janan gida ta wuce, ni da Esther kuma muka koma cikin asibiti.
Muna shiga daki sai ga kiran wayar Janan, wai Anty Sarah tayi yar diyarta kamar Mimah. Na mata fatan samun sauki da barka muka yi sallama.
Ranar juma'ah muka yi induction dinmu, bayan an rantsar damu, mun karbi nursing license dinmu, aka shiga shagalin ciye-ciye da shaye-shaye. Allah kadai yasan irin farincikin da muke ciki a wannan ranar. Duk da cewa convocation dinmu nan da satika biyu ne, amma kuma induction ya ma fi muhimmanci ga nurses nesa ba kusa ba. Yinin ranar guda, kira ne kawai yake shiga yana fita daga wayata, sakonni na taya murna daga yan uwa da abokan arziki.
Da yamma bayan mun gama shagalin, ni da Janan muka dauki hanya zuwa barka. Kasancewar gobe asabar zan wuce gida. Gashua zan fara zuwa inyi kwana biyu, sallama da yan uwa da abokan arziki, sai in wuce Katsina daga can.
Napep din da muka hayo daga bakina titi yayi parking a kofar gidan, muka biya shi, sannan muka fita daga ciki.
Na daga kai na kalli gidan da kallo, yan kadan daga cikin memories dana tara a gidan, suka dinga flooding suna shiga cikin kwakwalwata. Na girgiza kai a hankali, ina kokarin shaking din komi daga cikin kaina.
Ni da Janan muka shiga gidan, bayan mun gaisa da maigadin gidan. Kai tsaye dakin Anty Sarah muka wuce. Da yake yamma ce, babu cunkuson mutane sosai. Muka gaisa na mata barka, ta amsa tare da min godiya. Yanayin yadda take fara'a da tambayata bayan rabuwa, sai kayi tunanin irin mun saba sosai dinnan ne.
Aka miko min diya na amsa, kamar yadda Janan tace, kamar su daya da Mimah babu banbanci. Na kura mata idanu ina kallo kamar in sude ta saboda birgewa. Yadda ta nade cikin towel din da aka nadeta a ciki, kamar irin magen nan sabin haihuwa, very adorable.
Mun jima sosai dasu ana yar hira, ba karamin mamakinta ta nuna ba akan maganar aurena da taji ba. Musamman ma da wani, ba... Bata karasa ba, naji Janan tayi saurin ta katse mata maganar. Na bisu da kallon mamaki, ban tsaya tambayarta wa take nufi ba, duk nayi zaton da Umar take, don haka na share maganar don nima bana son tuni akan irin rayuwarmu da Umar, da irin cin amanar da yayi min.
Ina shirin tashi da niyar yi musu sallama in tafi, kawai naji tashin sautin muryar data matukar rikitar dani. Da sauri na koma cikin kujerar dana fara tashi dabas, wata irin rawar jiki ta ziyarce ni. Ba shiri na fara janyo salati da hailala ina ja ina karawa a cikin raina.
Yaya Bilal da Yaya Jameel suka shigo cikin falon. Yaya Jameel sanye da casual jeans and T-shirt, yayin da kamar kodayaushe, Yaya Bilal yake sanye da shadda ruwan sararin samaniya, rataye a kafadarshi ta dama, brief case dinshi ce, da alamu dawowarshi kenan daga wajen aiki.
Suka samu waje suka zauna, kallon nan daya dana musu, ban sake daga kai na kallesu ba. Falon daga mu, maijegon, sai kuwa wata makociyarsu Ikilima data shigo bayan mun shigo muma.
Ina jin tashin muryarsu suna gaisawa da mutanen falon, nasan nima dole ne in gaida su.
Na daga baki da kyar na gaida su, ba tare dana iya daga kai na kallesu ba. Tashin muryar Yaya Jameel kadai naji ya amsa, hakan yasa naji jikina ya kara yin sanyi.
Ko lokacin da Janan ta karbi diyar daga hannuna da niyar mika musu, ban iya daga kaina ba.
Na yan wasu lokuta, dakin ya dauki shiru, babu motsin abinda kake ji, sai tashin muryar Yaya Bilal kawai da kake ji yana tashi, yana yiwa jaririyar addu'o'in tsari da kariya kala-kala.
A lokacin ne na samu na iya daga kaina a hankali, na saci kallon inda Yaya Bilal din yake zaune dauke da yarinyar. Rabon da in saka shi a cikin idanuna ko kuma inji muryarshi, run rana daya tsare ni a hanya a asibiti da kuma lokacin da muka yi waya dashi ta karshe.
A yanzu da nake kallonshi, yadda ya rike yarinyar nan a hannunshi kan-kam, kamar wanda yake tsoron wani abu ya faru da ita. Tsananin soyayya da zaka gani a cikin idanunshi, tsantsar adoration da wani irin hope, hope wanda ya kasa boyuwa a cikin kwayar idanunshi, ya sanya naji wani matsi a cikin zuciyata har sai da naji kwalla ta cika min idanu. Ba zan iya jurar wannan abu ba, na zabura na tashi tsaye da sauri, har wayata da take kan cinyata ta fadi. Nayi sauri na wawureta tare da sungumar jakata na rataya, na kalli Janan da Anty Sarah da suka bini da kallo cike da mamaki.
Nace "zan tafi ne, Anty Allah ya raya baby, Janan, sai mun hadu ko?". Anty ta amsa da ameen, Janan kuma ta matso kusa dani da niyar taka min zuwa waje.
Ina tunanin sai lokacin Yaya Jameel ya kula da nice a cikin falon, yace "a'ah! Wai dama Na'ilah ce?".
Na daga kai a hankali ba tare dana kalli inda yake ba.
Yace "ke kuma sai kawai muji labarin aurenki daga sama babu sanarwa kamar saukar aradu?". Mutanen falom suka saki dariya da jin haka, nima sai dana dan murmusa.
Yace "da gaske fa! Da har munyi fushi ai, daga baya dai na hakura. Allah yasa ranar asabar din zamu je daurin auren wani abokinmu, tunda shi nashi da safe ne ba kamar naku na rana ba, in Allah ya yarda zamu yi kokari mu leka".
Na gyada kai a hankali, nace "Allah ya yarda". Ban tsaya jiran jin wani yace wani abu ba, na daga kafa na fita daga cikin falon da sauri Janan tana bina a baya.
Muna fita, Allah ya taimakeni naga dan adaidaita sahu, na tsayar dashi da sauri na haye. Ko tsayawa muyi sallamar kirki ni da Janan banyi ba, dan adaidaitan yaja muka tafi.
A cikin adaidaitan, na saka fuskata cikin hannuwana, ina kokarin slowing down irin gudun da zuciyata take yi. Nayi tunanin na manta da Yaya Bilal a cikin raina. Nayi zaton na binne shi a cikin raina gabadaya. Ashe I was wrong. Innalillahi, na shiga uku. A haka zanyi auren?.
Cikin wannan tashin hankalin na sauka garin Gashua washegari. Ganin su Fatsu da kuma yan biyun Sailu da suka yi wayo bul-bul abinsu, shi ya sanya gabadaya na manta da ganin Yaya Bilal da abinda hakan ya haddasa min a cikin raina.
Tunda na sauka ban huta ba, Fatsu bata bari ko rintsawa inyi cikin sauki. Ina sauka, masu gyaran jiki suka tare ni da kayansu na tsuguno da turaruka. Washegari kuma aka yi su dilka da halawa. Kwana biyun nan da nayi, ba karamin gyara na sha ba. Ni a karan kaina sai da naji canji a jikina ba na wasa ba.
Ko a ranar da zan tafi, tare muka tafi da wata mai gyaran jikin, zata cigaba da gyaran data fara har zuwa ranar da za'a kaini gidana. Daga Maiduguri tazo, diyar wata aminiyar Fatsu ce wadda suke mutunci da ita sosai.
*
Tun ana saura kwana uku biki gida ta fara cika da yan'uwa na nesa. Mutanen Gashua da yawansu sun zo, sauran kuma sun tsaya a gida da yake suma can kalar nasu bikin zasu yi.
Janan ana saura kwana biyu fara biki tazo, muka hadu dasu Kulsum da sauran abokanmu muka cigaba da planning harkar bikinmu.
Da yake akwai dakuna biyu manya spare a cikin gidan, nan aka gyarawa yan biki. Duk da haka, ranar da aka fara harkokin bikin, sai da wasu bakin suka dangana da dakin Anty Alawiyya da namu dakin. Su Hajiya Ramata kam kane-kane tayi, babu wanda yayi gigin tunkarar dakinta ma saboda yadda ta cune fuska.
Ranar bikin ma haka ta yini tana ta shiga da fita tana zubda habaici, sai dai duk cikinmu babu wanda ya tanka mata. Muka cigaba da gudanar da bikinmu.
Wani abin mamaki shine, har ranar da muka yi walima, babu wanda muka gani ya leko daga cikin dangin anguna. Shi dama ango sai ranar daurin aure muka yi dashi zai zo, kwana uku ne kadai aka dauka ana shagulgulan bikin Koda na mishi korafi, cewa yayi kada in damu, zasu zo ne. Har ranar daurin aure shiru.
Maganar tafiya ma bai sake tada min ita ba, kuma a yadda muke tunani, an daura aure ranar asabar, jirginsu zai tashi ranar Lahdi da yamma. Dana taba tambayarshi yadda za ayi, naga yana neman manna min hauka, wai me yasa na cika wutar ciki ne da gajen hakuri? Na ga an daura auren ne ya dauki kafa ya barni ne? In zuba idanu mana in ga abinda zai faru. Na bashi hakuri a lokacin, na kuma kawo idanun na zuba mishi kawai.
Ranar assabar, ranar da za'a daura aure. Karfe goma sha biyu na safiyar ranar za'a daura auren a babban masallacin juma'ah dake nan cikin unguwarmu. Da safen muna can gidansu Kulsum saboda yadda gidanmu ya cika da jama'a babu masaka tsinke.
Na lume akan katifar Inna a can uwar daka, duk da uwar kwalliyar da nasha, da kuma zufar da ake yi, hakan bai hana ni fita ko nan da falo ba. Tunda garin yau ya waye, ko in ce tun a daren jiya ma, nake jin wata irin faduwar gaba akai-akai. Zuwa yanzu gabadaya jikina yayi sanyi lakwas kamar an watsa min ruwan sanyi a jiki.
Idanuna kur akan agogon bangon dake cikin dakin makale a jikin bango. Duk wucewar dakika daya, da karuwar faduwar gabana take wucewa. Har lokacin da hannuwan agogon suka hau kan sha biyu, suna nuna karfe sha biyu ce daidai a wannan lokacin. Jikina ya hau rawa yana kadawa, shikenan, na zama danyar nama.
Karfe goma sha biyu da rabi, na jiyo muryar Malam a tsakar gida da sauran muryoyi. Ban san abinda yake faruwa ba, ban kuma yi yunkurin tashi inji mai yake faruwa din ba, na cigaba da zamana. Sai da Inna ta shigo dakin ta ganni, tace "kina nan ashe? Ai an daga auren zuwa karfe hudu na yamma".
Daga farko ajiyar zuciya naji ta ziyarce ni, kafin na kalleta a rikice, "me yasa?".
Tace "wallahi nima Malam bai fada min ba, kawai dai yace sun ce an daga".
Ina ji da yawa suna fata da addu'ar Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, a zuciyata nace ameen.
Idan haka ne, kenan yana nufin sai gobe sannan za'a tafi Zaria da ni. Tsarin dama shine idan aka daura auren yanzu, zuwa bayan azzuhur kuma sai yan kai amarya su dauki hanya. Nayi kokarin tuntubar