AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   6 / 52

15K to 18K   out of 155.4K words

bakwai na safe ban ga motsin kowa a tsakiyar gidan ba. Matan sun riga da sun san dama ni nike ayyukan gidan, shi yasa daga ranar da nazo, har in bar gidan babu wadda take ayyukan gida. Duk da har yanzu Ramata bata sakar min ragamar ayyukanta ba, ranar girkinta ita take yin girkinta gabadaya, wanke-wanke da shara ne dai take bari na dasu. Hakan bai dameni ba.

Yanzun ma ina kan zuzzubawa yara taliyar dana dafa musu a cikin kulolim makaranta, sai gata ta fito daga dakin Baba. Kicin din ta shigo, na gaidata ta amsa. Tukunyar ruwan zafi ta bude, ta zuba daidai wanda zata hadawa Baba shayi ta fita daga kicin din.
Daya bayan daya yaran suka fara fitowa, na dauki kofi ina zuba zuzzuba musu. kowannensu yazo, sai ya duka ya gaida ni, ni kuma sai in mika mishi kofin shayi da biredi ya amsa ya tafi.
Maryam da take tsaye a gefena tun dazu, tayi murmushi lokacin dana mikawa Auwal nashi kofin shayin bayan na shafa kanshi.
Tace "shi yasa nake son ki zo gida wallahi, yaran nan sun fi behaving. Yanzu da ni ce da har yanzu ina nan ina ta faman su zo su amshi abincin, amma su ki".
Nayi dariya, "kin san yara sai da lallashi da lalama. Yadda nasan halinki na zafin kai dama, ta ina yara zasu dinga binki sau da kafa?".
Duk muka yi dariya ni da ita. Itama na zuba mata nata ta tafi ta karya.
Ban fita daga kicin din ba sai da duk suka tafi, sannan nima na zuba nawa nan tafi daki na karya.

Bayan na gama gyara kicin, wanda nasan idan ban gyara ba haka zan dawo in same shi. Musamman ma tunda yau da safe Ramata ta fita daga girki. Haka kuma Anty Alawiyya zata shiga tayi nata girkin ta barshi kaca-kaca. Na girgiza kai cike da takaicin halayen wannan matan.
Dana gama da kicin daki na koma shima na gyara shi. Kai tsaye wanka na fada, na sanya riga da zani na atamfa, dinkin single da fitted riga. Sallama na wa mutanen gidan na shiga cikin unguwa. Daya baya daya na bi gidajen makota muna gaisawa, daga karshe na dire a gidan su Kulsum, a raina ina ayyana sai da yamma sannan zan je nata gidan, in yaso bayan magriba sai in dawo.

Ina yin sallama a tsakar gida, na ja nayi turus ganin yar halas din a tsakiyar gida tana wa yarinyarta yar shekara uku, Muneerah wanka.
Tana ganina tayi murmushi, "saukar yaushe?".
Nayi dariya ina zama a gefenta, "jiya da yamma wallahi. Me kike yiwa mutane a gida haka tunda safiyar Allah Ta'ala? Inna ina kwana?". Na gaida Inna data fito daga cikin madafi. Inna ta amsa tana min sannu da zuwa.

Na kalli Kulsum, "ko dai awon ciki kika zo ne?".
Ta dan harareni, "wani irin awon ciki kuma ana zaman lafiya? Mu a gidannan ma muka kwana in fada miki!".
Jikina yayi sanyi da jin abinda tace, nace "kamar ya? Ban gane ba, wani abu ya faru ne?".
Inna tace "menene ma bai faru ba yar nan? Ai tafi wata daya a gida yanzu".
Naji zancen kamar wani saukar guduma a kaina, nace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!".

Inna ta girgiza kai kawai, "ai ke dai abin ba'a cewa komi Na'ilah. Sai dai abinda Allah ya kaddara dama babu makawa sai ya faru, sai hakuri kawai".

Na fara cira idanu tsakanin Inna da Kulsum, Babu wanda ya sake yin magana a cikinmu har ta gama yiwa Muneerah wankan, ta tsaneta cikin zani. Muna zaune ta shiryata cikin kayanta, ta tura ta zuwa wajen Inna. Kallo kawai nake binta dashi.
Tun can nasan cewa dama suna ta faman samun sabani da mijinta Mukhtar. Ko waccan zuwan da nayi dama, sai da suka sha dabi har sai da Iyaye suka shiga cikin maganar. Sai dai wannan karon, jikina yana bani cewa wannan yafi karfin fadan da suka saba yi.

Tana gama hada kan kayan, na ja ta zuwa dakin da yake nata da. Tarin akwatunan dana gani da kuma kayan kwalliyar daki yasa naji jikina ya kara yin sanyi. Na zaunar da ita a gefen gado nima na zauna, tun kafin in daga baki ma in tambayeta ta riga ni, tace "rabuwa muka yi da Abban Muneerah!".

Na zare ido kamar zasu fado kasa, na kara yin wani salatin dai na sanar da Ubangiji. Ta girgiza kai, "Abban Muneerah ya rikice. Zama yaki ci yaki cinyewa. Ki duba lokacin da aka yi aurenmu, yazo ya hana ni karatu kiri-kiri, haka muka hakura ni dasu Baba. Yazo ya dinga gallaza min a zamanmu, wasu abubuwan ma kawai shiru nake yi. Tun ina kawo kara gida ana mishi fada, har aka daina. Abinci wannan haka ya dinga gagarata a gidanshi, ke kin san yawancin abubuwan dake faruwa. Sana'a na fara yi da kudina, amma haka zai zo ya cinye kudin kuma ya hana ni. Kwanan nan aka ba Inna kudin adashi, ta hada kan kudinnan ta sai min keken dinki, wallahi ko sati uku keken bai rufa ba ya dauke shi yaje ya sayar. Wai kudin toshi ya kai da kudin...". Kuka ya kwace mata anan.
Na dafata ina lallashinta har tayi shiru.

"Ashe wata ce ya hango a wajen aikinsu. Bai ma gaya min yana nemanta ba, sai a gari naji labari. Wata makociyata ta jiyo labarin take gaya min. Dana tuhume shi, kai tsaye ya amsa babu musu. Na tambayeshi dalili, sai cewa yayi saboda tana da ilimi, kuma ta fi ni hankali da natsuwa. Nace laifin waye to da bani da ilimin? Sai ya hau cewa ni ce sakara ai. Daga wannan rana gabadaya sai ya kara rikicewa, wallahi bamu kara samun zaman lafiya ba. A gabana zai kira ta a waya, su raba dare suna hira, tun ina kuka har na hakura na daina. Iyayenmu duk sun shiga cikin maganar, Kawu Bala da yaje akan maganar baki ji zagin kare dangin daya mishi ba, yace ina ruwanshi tunda ni matar shi ce? Bashi da ikon da zai hana shi yin abinda yaga dama. Ke magana taki ci taki cinyewa fa. Ranar nan kawai ina zaune da dare, sai gashi ya shigo gidan. Yace min an sanya aurenshi watanni biyu masu zuwa, nace mishi to Allah ya sanya alkhairi, yace ameen. Washegari wai sai ya sameni yace shi tafa bashi da wajen da zai saka amarya idan tazo, nace 'to Abban Mufeedah, ya kake so ayi kenan?', bai ce komi ba dai ya tafi. Haka muke ta zama dai, hatta yan uwanshi sai da suka fara shigowa suna zagina. Wai ni matsiyaciya ce, ban iya komi ba sai ci. Ita kuma wadda yake neman auren tana ta musu hidima. Abubuwa fa duk suka rikice. Yanzu kawai ranar nan ina zaune, sai gashi yazo da takarda ya miko min, wai ya sake ni saki biyu. Nace 'me na maka?', sai ya hau zage-zage da daga jijiyar wuya, wai shi dama can ya gaji da zama dani, yana ta hakuri da nine dama, kuma hakurinshi ya kai makura, in fita in bar mishi gidanshi kawai. Nace to shikenan, shine na tattara kayana na dawo gida abina!".

Cike da jimami nace "to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Kuma babu wanda ya same shi game da maganar akan haka?".
Tace "ace mishi me Na'ilah? Last week aka daura mishi aure, har cikin gidannan yayi sallama ya kawowa Malam katin gayyata".
Na zare idanu, "ikon Allah! Wannan ai cin fuska ne!".
Tayi dan murmushi cike da takaici, "cin fuska kuma wani iri ne ban gani ba a wajen Mukhtar? Ai sai dai in karas kawai. Kuma yaje na barshi da Allah!".

Nayi saurin girgiza kai, "a'ah, kada ki ce haka mana. Ko babu komi mahaifin diyar ki ne, kuma akwai sauran igiyar aure a tsakaninku, idan Allah ya nufa sai ki ga kun komawa aurenku!".
Tace "da wa? Allah ya tsareni wallahi. Kinsan cewa sauran Kayankayan dakina da ba'a dauka ba, ya sayar dasu?".
Nace "me yake damun wannan mutumin ne haka?".
Tayi kwafa, "tijara mana! Su Malam zasu yi magana, nace su barshi. Wallahi na yafe mishi duniya da lahira, Tunda dai na samu aka rabu lafiya, to ni na godewa Allah".

Na janyo ta jikina na rungume cike da nuna lallashi, nace "to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareku ku duka".
Tace "Ameen. Ni yanzu haka so nake in gama iddata, makaranta zan koma in cigaba da karatu na".
Nace "haka ne, Allah ya sanya albarka to. Allah kuma yasa hakan shine daidai".
Tace "Ameen. Ina Janan?".
Daga nan muka canza akalar hirar zuwa ta Janan. Sai ma dana kirata muka sha hira da ita. Ita kanta taji haushin abinda Mukhtar din yayi, ta ma so ta fi ni jin zafin abin. Sai data gama kumfar baki sannan kuma muka hau hira.

A gidan na yini, muna daki muna ta maida bayanai, irin zaman da suka yi da tsohon mijinta, da yadda danginshi suka juya mata baya lokaci daya. Wasu abubuwan ma dai gwanin ban takaici. Tunda kwata-kwata wasu abubuwan kawai sai dai fa yayi su ya kawo wani excuse da bai hau ba ya dora. Kawai abin dai dama kamar yana neman hanyar fita ne, shi yasa.

Da lokacin yin abinci yayi na shiga gida na dafa, na koma muka dora daga inda muka tsaya.

Da yamma na raka Maryam islamiyarsu, na samu malamanta muka yi magana dasu. Korafinsu daya, rashin maida hankali da take yi. A sati bai fi taje makaranta sau biyu ba, idan tayi da yawa sau uku. Na musu alkawarin idan Allah ya yarda za'a mata magana, nan suka ce idan ma ta maida hankali zata iya bin yan ajin nasu, dama as a warning ne yasa aka yi mata hakan, ko zata hankalta. Nan dai na musu godiya tare da biyan kudin watanta da bata biya ba, tace Baba ya bata amma cinyewa nayi. Anan na barta ni kuma na koma gida.


Kwana na shida a gida, komi yana tafiya yadda yakamata. Yawanci a gidan su Kulsum nake yini. Da safe idan na gama yin komi nawa zan shiga can. In taya ta aikin awara da dankali da take yi na saidawa da rana. In muka gama kuma mu hau aikin zobo shima da take yi ana kaiwa shaguna suna sai da mata. Haka dai nake juya rayuwar tawa.



Na shigo gidan kenan da yamma, daidai kofar dakin Aliyu dake kusa da kofar gida naji motsi da hayaniya. Sautin kida yana ta tashi daga dakin nashi. Na girgiza kai, ban san me yake damun yaron ba, haka zai tara yaran unguwa sa'anninshi su yi ta hayaniya a daki. Basa komi sai jin kida da wake-wake. Bana tunanin yaje makaranta ma yau.
Har na wuce ta kofar dakin, sai kuma na koma sakamakom hayaki da naga yana fita daga jikin labule da aka sakaye dakin dashi. Daga farko nayi tunanin ko girki ne yake yi a dakin, tunda wasu lokutan yana shiga cikin gidan ya kwashi garwashi yace zai dafa ruwan shayi.
Sai dai abinda na gani ne yasa na yaye labulen dakin sosai.
Shisha ce a tsakiyar dakin, sun sakata a tsakiya shi da abokanshi su uku suna zuka.

Nace "Aliyu!! Meye haka kuke yi?".
Duk suka dago a tsorace suna kallona, sai dai idanun Aliyun kyar suke a kaina, babu ko dar a cikinsu.
Na harari abokan nashi da suka yi cirko-cirko a zaune, nace "ku tashi ku fita". Babu musu suka mike sumi-sumi suka fita daga dakin.
Na maida kallona ga Aliyun, nace "kai yanzu abinda kake yi dama a cikin dakin kenan kai da abokanka? Shi yasa kullum kuke shiga ku rufo daki a rasa abinda kuke yi?".

Ya mike tsaye yana wani muzurai, "to meye hadin mutum dani? Naga cewa dai rayuwata ce bata uban wani ba! Meye hadinki dani?".

Nace "ko banza naci darajar kasancewa yayarka Aliyu. Wannan sam ba dabi'ar data dace bace, ka rasa a inda ma zaka sha shisha sai a gidan mahaifinka?".
Caraf! Sai Ramata ta cafe maganar, "kinga kada ki sake cewa d'a na yana shaye-shaye. Gwanda ma shi an san abinda yake yi, kuma a gabanmu yake. Ke waya san wace tsiyar kike yi a can?".

Na kalleta idanuna har juyawa suke yi saboda yadda maganganunta suka dake ni, nace "ke kan ki kinsan cewa nafi karfin yin wannan rayuwar da kike ambatowa, kuma karya kike yi kice saboda bana gaban iyayena zanyi rayuwar da bata dace ba!".

Ai sai shima Aliyun ya hayyako min, "kada ki kuskura ki zagar min uwa fa!. Ba gaskiya ta fada ba? Ke har kina da bakin kirana dan shaye-shaye??".
Nace "Aliyu ka kiyaye ni, kada bakinka ya sake kuskuren ci min mutunci!".
Sai ya kara matsowa daf dani, "idan naki fa? Nace idan naki fa? Kashi zaki bani? Ke din banza! Ke har kin isa ki zauna kina gaya min kabli da ba'adi? Wallahi idan baki kiyaye ni ba sai in kwantar dake anan wajen!!".
Ramata tace "yayi daidai da na. Yanzu na tabbatar da cewa nice na haife ka! Ka cika da!!".

Inna data jiyo hayaniya da wata Assibi makociyar mu suka shigo, itace ta tari bakin Ramata din, tace "haba ke kuwa! Da girmanki zaki biyewa yara har ki goya mishi baya. Yanzu ko Na'ilah bata girmi Aliyu ba, ai tana da damar idan yayi abinda bai yi daidai ba ta kwabar mishi!".

Sai ta harari Innar, tace "yo meye a cikin shishar? Uban wa yace miki kayan shaye-shaye ne ita?".
Inna ta kama baki cike da mamakin zagin data yi. Assibi tace "amma kuma ai daga nan yara suke ganin hanyar shaye-shayen ko?".

Sai Ramata ta kara kumbura, ta karkace daurin dankwali ta kawo shi goshi ta kafe. "ni fa dama ina sane da duk munafurcin da kuke min a cikin unguwar wannan musamman ma ke!", ta nuna Inna. "Na'ilah tana zuwa gidanku kuna zagina da gulmata. To wallahi ta Allah ba taku ba! Kuma ni da 'ya'yana nan gani nan bari. Idan ma wani kulli ake musu don su lalace to wallahi sai dai dan wani ya lalace don ni naci dubu sai ceto! Kuma bari uban Na'ilar ya dawo, sai ya gaya min in uban wani ne ya haifar min diyana ko ni!!". Ta kama hannun Aliyu suka shige dakinta ta barmu anan a tsaye.
Assibi tace "to kuwa Allah ya kyauta miki gaskiya lamarinki sai du'a'i!".
Tuni mutane har sun fara shigowa gidan jin hayaniya. Inna da Assibi ne suka kore su, bayan sun tafi suka lullube ni suna bani hakuri. Ban iya magana ba, na zame na shige daki.

Ina shiga daki jikina ya shiga rawa, na zame gefe katifa na zauna. Ban iya rigima ba ko kadan. Sam bani son rigima. Barni da tsiwa dai da mita, da kuma rashin barin ko ta kwana. Abin ya min ciwo kwarai da gaske, kanina wanda na bashi shekarun da suka fi yatsun hannu, zai tsaga tsakiyar idanuna yaci mutuncina a gaban uwarshi. Kuma nasan cewa ya zage ni a bulis, nasan cewa ko na gayawa Baba babu abinda zai yi akai.

Abubuwa irin wadannan ba yau ne suka fara faruwa ba, kuma kowane lokaci haka abin yake, ya zageni, kuma bani da bakin ramawa ko na kai korafi, sai dai in shige daki in shaki kuka. To na gama kukan. Nayi alkawarin in dai akan Aliyu da uwarshi ne, to na daina kuka.

Wayata na janyo, banyi tunanin komi ba na dannawa Ya Mudatthir kira. Ina jin sautin muryarshi, naji na fashe da kuka. Take naji ya rikice, ya fara tambayata lafiya? Me ya faru? Duk yadda naso in daina kukan kasawa nayi, sai da nayi mai isa ta, sannan na fara zayyane mishi dukkan abinda ya faru tun daga farko har karshe. Nasan wasu abubuwan kawai yaji su ne ba don ya fahimta ba, saboda yadda muryata dama jikina suke rawa.

Bai katse ni ba har na gama mishi bayanin, sai dana gama sannan ya fara jefo min tambayoyi. "ita babar tashi me tace ne?".
Nace "itama fada ta hau yi, tana cewa wai nace mishi dan shaye-shaye, kuma ni wallahi ban ce mishi haka ba. Kawai magana ce na mishi!".
Yace "na sani Na'ilah, nasan ba zaki ce mishi haka ba. Zan kira Baban anjima, yana nan aka yi?"
Nace "a'ah, baya gida".
Yace "to shikenan. Kina son zuwa nan ne?".
Da sauri na hau daga kai kamar yana ganina, nace "ehh!". Yayi yar dariya, "to shikenan, zan turo miki kudin mota. Idan zaki iya tahowa gobe, sai ki taho. Idan kuma baki samu dama ba, sai ki bari sai jibi".
Nace "to Yaya, nagode. Allah ya kara girma".
Muka yi bankwana dashi na kashe wayar.

Sau tari ina fata dama ace ni ce na samu damar da Yaya ya samu. Yana gaban danginmu lullube dasu hankalinshi kwance. Tun lokacin daya gama sakandire, Yobe ya koma yayi degree dinshi acan. Da Allah ya taimake shi ya samu aiki yana gama makaranta, sai ya zaune acan abinshi. Ni kam tsakanina dasu sai dai zuwa hutu, ko kuma idan wani daga cikinsu yazo, ko kuma wata sabga ta biki wanda Baba bai cika bari na naje ba.

Duk da hakan akwai shakuwa da kusanci a tsakaninmu dashi sosai. Yana so na kuma yana tattalina.

Ina gama sallar isha'i na hau hada kan kayana waje guda. Maryam da take kwance tana kallo ta kalleni, "wai garin zaki bari ne kike hada kaya?".
Nayi dan murmushi, "wallahi kuwa".

Ta tashi zaune, "ba dai akan rikicin dazu bane ba ko?". Tunda aka yi abin ma ni babu wanda ya tuntube ni da zancen, sai naji abin ya dawo min sabo.
Na girgiza kai, "ko kadan. Dama ina son zuwa".
Tace "to shikenan. Ki dai kara hakuri don Allah. Mama ta daure mishi gindi da yawa wallahi, ni kaina rashin kunya yake min, bani da yadda zanyi dashi kuma".
Kai kawai na iya daga mata don bana ma son maganar tayi tsawo.

Washegari tunda safe nayi wanka na shirya tsaf, na fito da akwatuna na ajiye a kofar daki nayi sallama a kofar dakin Baba. Sai da aka amsa min sannan na shiga.
Yana zaune a kan kujera yana duba jarida, na durkusa a gefenshi na gaida shi ya amsa. Nace "Baba zan tafi Gashua!".

Nayi zaton ma zai yi magana

6 / 52