Author : Jeedderh Lawals Category : New Hausa Novels 2026
alamu ne suka nuna haka ba wani abu ba. Ki duba fa yadda kika wani ciko tubarkallah, kin kuma yi haske da abubuwa, idan ba ciki bane to menene?".
Na kada mata idanu, "kiwon Yayanki ne kawai!".
Ta saki ihun dariya, abinda ya janyo su Harira dake falo kenan suma suka fado, suka cigaba da shakiyancinsu. Dana gaji sai na janyo wayata, na dannawa Yaya kira na koma can gefe muka kwashi hirarmu ta masoya.
Washegari aka yi kamu anan cikin gidan. An dauko masu decoration da masu raba abinci, abokanmu da yawa sun zo, haka dangin ta dana Almu sunyi kara ba kadan ba. Gida ya dauki jama'a sosai. Har karfe goma na dare ranar muna kan kafafunmu a tsaye muna kokarin gyara gidan.
A dakin su muka yi parking, baki duk an kaisu dakunan dake cikin gidan, wasu kuma suna dakin Yaya da Ummah.
Ummah ta kawo mana damammiyar fura da kanta, da tasha nono ga sanyi sosai. Tun bayan aurenmu da Yaya, kamar an kara mata kaunata haka nake gani, tunda nazo take ta nan-nan dani, abincin da zan ci ma daga dakinta ake kawo min. Sai naji nima kimarta da mutuncinta sun karu a cikin idanuna.
Bayan munyi wanka don mu dan warware gajiya, muka sha furar data kawo mana, sannan fa kowa ya nemi makwanci. Lokacin karfe sha daya ta wuce. Naso in kira Yaya kafin in kwanta, tun da safe da muka yi waya dashi bamu kara yi ba, amma sanin suna tare da Raheemah yanzu yasa na daure zuciyata. Sai na rubuta sako mai cike da kalamun nuna kewa da kauna, na tura mishi. Cikin sakanni talatin da shigar sakon wayarshi, ya dawo min da amsa.
Nan muka kwashe kusan mintuna arba'in muna musayar kalaman soyayya, kafin muka yi sallama dashi.
Washegari aka yi mothers eve, sai ranar Anty Ameerah tazo. Anty Sarah ita tun jiya tazo, sai dai bata kwana a gidan ba, gidan Yayarta dake aure anan cikin Kaduna taje ta kwana.
Ana gama taro Anty Ameerah ta koma Zaria.
Sai ranar juma'ah Yaya yazo shi da Raheemah. Tunda suka zo bata ma zauna a gidan ba, ranar walima muka yi. Yau ma kamar jiya, ana tashi wajen karfe shida Anty Ameerah ta wuce, ita kuwa Raheemah da tunda suka zo kayanta ma a dakin Yaya ta ajiyesu, ta wuce can. Bata shiga cikinmu ba mu kawayen amarya, muma kuma bamu nemeta ba.
Washegari aka daura aure, muka kai amarya gidan aurenta dake can unguwar rimi. Gini ne na kin karawa, idan ka shiga kamar kada ka fita saboda haduwarshi.
Yanmatan sun ce babu inda zasu tafi sai anguna sun zo sun sayi baki, duk da da yamma ne aka kaita. Na gama shan dariyata nace bari inyi tagging dai nima.
Wajen karfe shida na yamma sai ga kiran wayar Yaya, na fito daga cikin hayaniyar hirar da suke yi, na amsa kiran.
"ki sameni a kofar gida", kawai yace ya kashe wayar.
Na bi wayar da kallo cikin mamaki, kafin na sake kiranshi, nace "muna fa gidan Janan yanzu haka".
Yace "ehh, nan din fa".
Cikin sanyin jiki na koma gidan. Su Anty Sarah da basu jima da zuwa ba, su ganin gida suka zo yi kafin su koma Zaria, ciki har da Anty Ameerah, suna cikin bedroom inda amarya take suna tasu kalar hirar suma.
Na matsa na radawa Janan zan tafi, tace "ina zan tafi yanzu bayan ba'a zo sayen bakin ba?" Nace mata "Yaya yake nema na, yace yana waje".
Ta zaro ido, nayi gaggawar kai mata dukan wasa a hannu kafin tayi tunanin fadin wani abu silly, nace "kada ki wani kawo min wata maganar banza anan, sallama ce kawai zamu yi saboda yau zasu koma Abuja shi da Raheemah".
Amma bata fasa ba, sai data yi commenting din dai. Na dauki jakata kawai na musu sallama akan cewa zan koma can gida, na fita.
Kamar yadda yace kuwa, yana kofar gidan. Na bude murfin motar na shiga, yayi murmushi tare da janyo ni jikinshi, mun dan jima a haka kafin ya dago ni yana kallona, yace "kai baby na, da alama ke ko kewata ma baki yi ba, ji yadda kika yi wani irin kyau kamar ba ke ba?".
Nace "a haka din?".
Yace "sosai ma!". Ya fara kokarin tada motar.
Ban tambayeshi inda zamu je ba, ya fita daga unguwar. Sai gamu a kofar wani gida a can cikin GRA. Na kalleshi cikin mamaki lokacin da naga yayi horn mai gadi ya bude mishi kofar ya shiga.
Muka fito daga cikin motar, kai tsaye ya shige falo dani. Gidan a gyare da komi a ciki, sai dai babu alamun mutane a ciki.
Nace "nan fa?".
Yana ajiye wayoyinshi akan center table yace "gidan da muke kawo baki ne idan aka yi, musamman ma lokutan biki irin haka".
Bandaki ya nuna min yace in shiga inyi alwala, shi kuma ya tafi masallaci. Sai bayan isha'i ya dawo da ledar shake da kayan marmari da take away na abinci a hannunshi.
Ganin take-takenshi, nace "wai ba yau zaku koma ba? Kuma kada ka manta fa tare da matarka kuka zo".
Yace "to sai me? Ina lissafe da yau zaki fita daga girki fa!".
Na zaro ido ina kokarin ja da baya daga rarumar daya kawo min, amma duk da haka sai daya cafko ni yana dariya, yace "come on, anjima kadan fa zan maida ki".
Nace "da gaske?".
Yana murmushi cheekily, yace "da gaske".
A takaice ban kara tunawa da wannan maganar ba sai da naga mun yi ido hudu kuru-kuru da hasken rana, washegari kenan.
Karfe tara Yaya ya shigar da motarshi gidan su Ummah, kunya kamar zan nutse a kasa, duk da dai babu wanda yasan abinda kenan.
Yana kashe motar, na fita da sauri na fada gidan. Allah ya taimakeni babu kowa a falon, da alamu baki sun wuce, na fada dakin su Harira daban. Nan ma FirdauFirdausi kadai na tarar tana gyara gado, ta kalleni cike da mamaki, "daga ina haka?", nayi banza na kyaleta.
Karfe biyu na rana, muka wuce Katsina ni da Is'hak da Yaya ya umarce shi daya kaini. Munyi sallama dasu suna ta min sannu da Ala huta gajiya. Shi Yaya sai da yamma naji yace zasu koma.
Yaran gida sun sha ihu da murnar ganina, aka min masauki a dakin Anty Alawiyya. Da yake ranar Lahdi ce, Baba yana gida.
Aka kaiwa Is'hak abinci yaci, a ranar ya koma Zaria, ranar talata zai dawo ya maida ni.
Ranar haka muka raba dare ni da kannena muna ta shan hira. Sai washegari na shiga gari gaishe-gaishe.
Kulsum ta fara zuwa makaranta abinta, wai wani lecturer ya kyalla idanu a kanta yana ta bibiyarta. Nace mata "kema ki saurare shi mana, sai kiga kun daidaita".
Ta girgiza kai, "ba yanzu ba Na'ilah, ba zan kara yin sake irin wanda nayi ba gaskiya. Ke dai kawia ki taya ni da addu'a".
Nace "to shikenan".
Wannan zuwan nawa naji dadinshi sosai, sai da naji kamar kada lokacin komawata yayi.
Ramata kanta wannan lokacin naga ta sassauto sosai, ko kuma zata iya yiwuwa rashin lafiyar da take yi ce ta sanya hakan.
Ranar talata sai da yamma sannan muka yi sallama dasu cike da kewa, muka wuce. Dole sai a Zaria muka tsaya muka kwana, washegari Laraba muka wuce Abuja. Amma sai da na tsaya a Kaduna sannan.
Na koma gida muka cigaba da gudanar da rayuwarmu. Babu abinda ya canza har yanzu, sai ma wata tsirfa. A gidan na tarar dasu Salame ranar dana koma, wai suna ta shirye-shiryen bikin Haleemo. Sai ranar assabar suka bar gidan, habaici dai har sai dana gaji da ji, amma babu wanda na taba tankawa a cikinsu.
*
Ranar Lahdi da yamma, muna babban falo a zaune, Raheemah ce take yin girki, Yaya ya fita zuwa cikin gari da wannan yammar. Don haka daga ni sai ita, duk da ita tana ta zarya ne ma tsakanin kicin da falon saboda girki da take yi.
Kawai sai karar turo kofa muka ji, mu daga kai haka, sai ganin Anty Ameerah muka yi ta fado falon, wasu matasan yanmata biyu na take mata baya, yayin da maigadi da mai ban ruwan fulawowi suke turo akwatunanta.
Raheemah data mike tsaye zata shiga kicin, tayi tsaye kyam tana kallonsu, nima na bi su da kallon.
Yaya har ya fita bai yi magana akan dawowarta ba, ko kuwa bai san da zuwan nasu bane? Oho!.
Ita kuma ko da wacce tazo?.
Suka mana sannu da gida, Raheemah ta zungura baki gaba ta shige kicin, na amsa musu a sanyaye. Muka gaisa kadaran-kadahan dasu, suka ce sunyi waya da Yaya yace su tambayeni makullin dakinta, na tashi na shiga dakinshi na dauko musu, na nuna musu dakin, suka yi godiya suka tura kai suka shiga ciki, ni kuma na koma falo cikin wani irin yanayi.
Sai da dare Yaya ya dawo. Da yake ranar Raheemah zata fita daga girki, aka yanke shawarar Ameerah zata amsa. Da haka muka aka tashi kowa ta wuce dakinta.
Har ta fita daga girkin, wani ya sake zagayowa, babu wata matsala. Zama muke kadaran-kadahan da ita, idan muka hadu a falo, ko a dakin Yaya, za'a gaisa da ita a mutunce, haka babu ruwanta da shiga harkar da babu ruwanta. Ban taba jin bakinta yayi wata mita ba, ko ya tado magana. Kai ita kwata-kwata ma baka ganinta sai ranar girkinta, sauran ranakun a daki take yini cur, idan ta fito sai dai kicin, ta kwashi kayan makulashe ta koma daki.
Sai nake ganin kamar hakan yafi akan ka wuni kana zage-zage da yada habaici. Har nake cewa kila zata fi Raheemah saukin kai.
Little did I know....
*☆⋆41⋆☆*
Ranar Juma'ah na karbi girki a hannun Ameerah. Kamar yadda na saba, idan ina aikin rana na kan yi iyaka bakin kokarina in ga na dawo da wuri domin in dora abincin dare.
Yau ma aikin dare nayi, na samu wata nurse da muka fara gaisuwar mutunci da ita, Hanifa, na roketa akan ta shigo da wuri ta rike min nawa aikin tunda ita aikin dare take yi, ta amince. Bazawara ce in her 30th. Kirkinta yasa muka fara gaisawa sama-sama da ita, har dai aka fara gaisawa ta sosai. Yanzu yawanci ita take taya ni rike aikina idan zan fita da wuri. A gurguje na mata godiya na wuce. Na riga na kira direban da yake kaini, yana waje yana jirana. Don haka ina fita muka wuce.
Sai karfe bakwai da wasu mintuna muka karasa gida.
Cikin sauri na shige daki, ina shiga na hau cire kayan jikina ina jifa dasu a tsakiyar dakin ba tare dana damu akan in linke su ba. Da yake bana yin sallah, a sukwane na fita daga dakin na fada kicin. Babu kowa a cikin falon.
Allah yasa da zan fita da rana nayi miya na ajiye. Ruwan zafi na dora akan wuta, na nufi dakin Yaya da sauri.
Wani lokacin idan ya fita sallar asuba ya kan dawo kafin ayi isha'i ya ci abinci, idan yana jin yunwa kenan. Idan kuma ya ci abinda ya rike mishi ciki a wajen aikinshi ya kan jira sai bayan isha'i.
Yanzu so nake in ga idan yana falonshi, in ga ko yana bukatar ko da snacks ne yaci kafin in sauke abincin kamar yadda nake mishi sau tari, a ranaku irin wadannan idan ban gama abinci da wuri ba.
Tun kafin in karasa falonshi nake jin sautin karar talabijin, sai kuma sautin magana kamar ana yin hira da yake tashi kadan-kadan.
Nayi sallama a kofar falon tare da turawa, kamar yadda nayi zato, Yaya yana falon a zaune akan kujera.
Sai dai zaune a kasa, daf da kafafunshi, don idan ma wani ya kuskure zai iya cewa akan kafafun nashi take a zaune.
Amma ba ma wannan bane ya dauki hankalina ba, ba kuma dariyar dana tarar suna yi ba, kwalliyar data zabga ne kamar zata je gasar sarauniyar kyawu ta duniya, sai kuwa wani zagayayyen kyakkyawan ceramic plate da yake ajiye akan cinyarta shake da waffles da aka kwarara jam daya nutella akai, ga kuma fresh berries. Abin ya bani mamaki har na kai ga dan dakatawa.
Shirun da suka yi suna kallona ne ya sanya na dawo da hankalina kansu. Na danyi murmushi kawai tare da takawa na karasa wajensu. Sannu na mata ta amsa fuskarta da sauran fara'ar dake kan fuskarta lokacin dana shigo cikin falon.
Yaya ya kalleni lokacin da nake zama a gefenshi, akan kujerar kusa dashi, cikin murmushi.
Na gaida shi ya amsa, tare da cewa "har kin dawo? Ya asibitin?".
Nace "lafiya lau, yanzun nan na shigo. Dama lekowa nayi in ga ko kana bukatar wani abu kafin in gama girki sai kuma naga...", na kakare ina karewa plate din hannun Anty Ameerah kallo. Daga ganin yadda yayi fresh, kamshi yana tashi, kasan ba'a jima da gama yin shi ba. Probably bayan Yayan ya dawo daga wajen aiki.
Maimakon ya nuna wani abu, ko ita, sai naga yayi murmushi. Yace "ai Yayar ki ta hutar dake, sai ki sanya ranki a inuwa...", ya dauki daya ya sanya a bakinshi, ya gutsira ya tauna har da hadawa da lumshe idanu, "... kuma yayi dadi sosai. Bismillah, ki taba mana".
Na girgiza kai a hankali ina kokarin danne wani abu daya taso ya tsaya min a makogaro, kwacen girki kuma da rana tsakiya kiri-kiri?.
Nace "a'ah, na gode. Bari inje in karasa girkin. Anty Ameerah nagode fa!".
Idanunta akan allon talabijin tace "babu komi Na'ilah... Yiwa kai ne!".
Ban ce komi ba na tashi na fita daga falon.
Spaghetti na dafa, nayi warming miyar da nayi. Kafin Yaya ya dawo na kai mishi abincinshi falonshi. Su kuma matan nashi na ajiye musu nasu akan dinning table.
Daki na koma, na shirya kayan dana yasar, na gyara dakin nawa sannan na koma falon Yaya ina jiran ya dawo daga masallaci.
Yana dawowa na shirya abincin, na zauna a gefenshi na zuba mana muka fara ci. Yau abincin kadan yaci, a cewarshi Yayata ta cika mishi ciki. Murmushin yake kawai nake binshi dashi, saboda maganar gaskiya abin ya bata min rai. Akan me ni da girkina, ni da mijina, kawai tazo wai ta mishi girki? Ina so inyi magana, sai dai dole haka nayi shiru saboda bana son yace ina neman tada mishi zaune tsaye a gida, ko kuma bana son zama lafiya, ban godewa abinda ta min ba. Don haka nayi ta kauda maganar ina turata can bayan raina.
Ni kaina abincin yau haka nan dai naci shi cikin dauriya kawai. Mun saba idan muna cin abinci, haka zai yi ta yabon girkin da na mishi, wasu lokutan kuma yana ta tsokanata da yan wasannin shi.
Yanzun ma a hankali naji hannunshi yana min tafiyar tsutsa a bayana ta dan slit din da aka bari a bayan rigar dana sanya. Na daga kai na kalleshi a hankali, ya daga min gira challengely, cikin nuna alamun yana jiran yaga reaction dina.
Nayi dan murmushi, ina kokarin ganin cewa ban bari abinda ya faru yau ba ya hana ni samun farincikin raina dana mijina ba.
Don haka na biye mishi. Cikin kankanin lokaci munyi gefe da kayan abincin, sai gani a saman ruwan cikinshi ina kokarin daukar alewar bounty daya boye a bayanshi.
"Baby na.... Zaki karya ni fa, kinyi nauyi da yawa.. Baby, wayyo!".
Amma kuma dariya yake yi cikin shessheka, nima dariyar nake yi lokacin da naci sa'ar dauko sweet din.
Na koma na zauna a gefenshi ina bare ledar, shima ya tashi zaune yana maida ajiyar numfashi kamar wani wanda ya kwashi wani dambe.
Ina bare ledar na kai baki na hau taunawa, ya kalleni cikin zare idanu, "ba dai cinyewa zaki yi ki hana ni ba ko baby?".
Murmushin tsokana nayi tare da saka gabadaya sweet din cikin bakina.
Yace "kam, gaskiya ban yarda ba..".
Ganin yayo kaina gadan-gadan yasa nayi dan ihun tsokana naja da baya, amma duk da haka sai daya damko ni.
Yayi amfani da karfin jikinshi yayi trapping dina a jikinshi ta yadda babu yadda za ayi in kwace, bakina yake kokarin hadawa da nashi da niyar zakulo sauran alewar data rage a bakina, lokacin da aka turo kofar falon aka shigo.. Da sauri na daga kai naga Ameerah ce. Idanuna suka sauka akan agogo, naga karfe tara ce saura. Wani haushi yazo ya cika ni, kowa yasan a cikin gidan nan idan karfe tara ta gabato a cikin gidannan, kowa ya nemi makwancinshi, sai a bar mai girki ita da mijinta. To me kuma ya kawota yanzu?.
Kallon dana bita dashi baki a dage ne ya ba Yaya damar cikashe abinda yayi niyar yi. Sai lokacin ya sake ni, ya koma gefena yana tauna alewar a bakinshi.
Ameerah ta nemi kujera ta zauna, "sannunku da hutawa". Ta furta cikin fara'a.
Muka amsa mata, ni ciki-ciki, Yaya kuma yana dan murmushi, yace "baki kwanta bane har yanzu?".
Tayi wani fari da idanu tana rangwada, "wallahi kuwa baby, ban san me yasa na kasa yin barcin da wuri ba yau, shine nace bari dai in zo in rage dare anan".
Yaya ya daga kai distractedly, hankalinshi gabadaya akan tv, ana hasko wani labari akan wata sharia da ake kwasa tsakanin wani dan uwa da dan uwanshi.
Na mike tsaye ni kuwa na nade ledar dana shimfida mana na kaita inda ake ajiyeta a cikin falon, na dawo ina hada plates da kulolin, sai lokacin na dan saci kallon inda take, ta canza kayan dazu dana barci yanzu, riga da wando na cotton masu kyau da suka bi jikinta, ta dora hular beanie da tattausan silifas mai buzuzun gashi a kafarta. Nayi kwafa tare da kwashe kayan abincin na tafi kicin.
Ina gamawa da kicin na koma dakina. Na shiga bandaki nayi wanka, brush, na dauro alwala. Duk da cewa ina period, hakan baya hana ni kwanciya da alwala a jikina idan zan kwanta.
Bayan na gama, na dauko kayan barci masu kyau da bayyana surar jiki na sanya, na shafe ilahirin jikina da turaruka masu