AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   35 / 52

102K to 105K   out of 155.4K words

jinin jikina.

Zuwa can naji komi ya tsaya cak, kamar da can babu abinda yake faruwa. Na bude idanuna a hankali, na daga kaina da niyar ganin abinda yake faruwa.

Sai dai abinda naci karo dashi ne ya bani mamaki, ta wani bangaren kuma yaso ya sanya ni kyalkyalewa da dariya.

Yaya Bilal barcinshi yake shaka tsakaninshi da Allah akan kirjina, har da jan minshari!.









#F.W.A




*☆⋆37⋆☆*





Da asubah Yaya Bilal ya tashe ni, ban ma san lokacin da barci ya dauke ni ba jiya. Ya fita masallaci, ni kuma na dauro alwala nayi sallah ta.
Yau bai tsaya a waje ba, gari yana fara yin haske ya dawo cikin dakin. Ina zaune ina lazumi ya shigo, ya koma kan gado ya nade, ni kuma naci gaba da lazumi na. Ina gamawa kuma kicin na shiga, na hada breakfast mai kyau, na gyara ko'ina ya fito fes, sannan na koma daki. Har yanzu Yaya barci yake yi.

Na shiga bandaki da niyar yin wanka, kafin in fito Yaya ya bar dakin. Bayan na fito, na shafa mai, yar hoda da man lebe, na janyo wata doguwar rigar buba ta atamfa na sanya. Na bade jikina da turare kamar ko yaushe na fita falo.

Har yanzu Yayan bai fito ba, don haka na zauna akan daya daga cikin kujerun falon ina jiran ya fito. Kafin ya fito dinne na kira Maryam wadda naga missed call din da tayi min jiya da dare yau da safe, muna cikin hira da ita kofar dakin Yaya ya bude, na juya na kalleshi lokacin daya leko daga ciki.
Yace "kawo min abinci na nan Na'ilah".

Muka yi sallama da Maryam, na dauki kayan na wuce dakinshi. Yana tsaye a gaban mirror yana fesa turare a jiki na shiga, ya ajiye kwalbar turaren, ya matso ya karbi kayan hannuna ya ajiyesu a can gefe. Na koma kicin na dauko babbar ledar cin abinci nazo na shimfida, sannan na zauna na hau zuba abincin.

Ya gama abinda yake yi, yazo ya zauna, na tura mishi abubuwan dana zuba gabanshi. Sai daya zauna sosai sannan na gaida shi, ya amsa min fuska da walwala da fara'a, hakan ya sanyaya min zuciya kwarai.

Ina kokarin zuba nawa abincin, ya katseni, "dauki cokali ki sa mu ci wannan, idan mun cinye sai a kara. Ko ba zaki ci dani bane?".

Nayi saurin girgiza kaina, "ni ban ce ba", na dauki cokalin nasa na fara ci, Yaya yayi dan murmushi.
Shiru tunda muka fara cin abincin, babu wanda yayi magana.
Zuwa can yace "an riga an gama komi, a can Abuja zaki yi internship dinki. Ina fata babu matsala?".

Da sauri na girgiza mishi kai, nace "a'ah, babu. Nagode".
Yace "meye na godiya kuma? Kunshin hannunki yayi kyau matuka". Ya canza akalar hirar tamu.

Na dan saci kallon hannuna na hagu dake kan cinyata. Ni kaina da kunshin yake hannuna yana burgeni sosai, don ya tsaru ne.
Ban tantance ba naji ya kamo hannun nawa cikin nashi, na kalleshi a dan kunyace, amma shi ko a jikinshi. Ya cigaba da cin abincinshi a nutse, kamar babu abinda ya faru.
A hankali nayi kokari na zame hannuna daga nashi, sai dai ina maida shi inda yake da, naji ya sake janyo shi. Wannan karon kyam ya rike idanuna cikin nashi kamar wanda yake challenging dina akan in sake janye hannun, sai nayi kasa da nawa idanun, na kuma kyale shi. A haka muka gama cin abincin.
Nayi tsam na tashi, na fara hada kan kayan na kai kicin. Na tsaya na wanke su ma ajiyesu a inda yakamata, sannan na koma falo. Na dauki remote na kunna tv ina kallo har Yaya ya fito cikin shirin fita.

Ya tsaya a gefena yana daura agogon hannunshi, "zan fita, nasan sai zuwa dare zan dawo yau don haka kada kiyi abincin rana dani. Babu wata damuwa dai ko?".
Na girgiza mishi kai.

Ya sanya hannu ya dago habata yadda muke kallon juna ta cikin ido, kallon tsakiyar idanunshi ba abu bane mai sauki, ji zaka yi kamar an sanya sarkoki an daure duk wasu gabban ka masu motsi, yayin da a gefe guda kuma zaka ji kamar an dauko wani dutse ne an aza maka aka, ka kasa motsi.

Yace "wai kin koyi rashin magana ne yanzu ko kuma rowar muryarki kika fara ne? Kodayake, har da laifina ma. Saboda ba'a sayi bakin ki bane ba ko?".
Nayi saurin girgiza mishi kaina ina dan murmushi, ya sake girgiza kanshi, "uh uh?!".
Nace "a'ah, ba haka bane".

Sai lokacin ya sakeni, yace "to ko ke fa? Ki dinga hana ni jin muryarki, baki san muryarki tana da dadin saurare bane?".
Ni na rasa ta ina Yaya Bilal ya zama frank and blunt ba, ko kuwa dama can haka yake?. Ina shirin bashi amsa wayata dake gefena ta shiga yin kara, kafin in kai hannu in dauka, Yaya ya riga ni. Ya kalli sunan mai kira, ya kalleni girar sama data kasa a hade.

"Waye kuma wani Hamza cm?", ya tambaya cikin hade fuska.
Nace "classmate dina ne", tunda aka daura min aure nake samun kiran waya daga yan ajinmu da muka gama makaranta dasu suna taya ni murnar yin aure.
Bai ce komi ba ya kashe karan wayar, ya saka ta cikin aljihun rigar shi. Yace "bari in fita".

Na mike na mishi rakiya har bakin kofa, nace "Allah ya tsare, a dawo lafiya".

Yace "ameen baby na, sai na dawo".
Ya wuce, ni kuma na maida kofar na rufe ina murmushi kamar wata kuntacciya. Damn, why does it feel so good to be his baby again?!.

Bayan ya tafi, gidan na rufe na tafi sashen Anty Sarah. Janan da Mimah na falo suna karin safe lokacin dana shiga, Anty Sarah kuma da alama tana daki.
Muka gaisa dasu, Janan ta min tayin abinci nace na koshi, na nemi waje na zauna ina kallo har suka gama. Nan Janan ta dawo wajena muna hira da ita, har Anty Sarah ta fito daga dakin Yaya Jameel, Yaya Jameel din yana bayanta hannunshi dauke da Rabi'ah.

Muka gaida su, suka amsa, Yaya Jameel din yana ta tsokanata har dai ya fita. Anty Sarah ta zauna muka cigaba da hirarmu.
Sai da azahar sannan muka koma bangarena ni da Janan. Bayan na dafa mana abinci mai sauki, muka ci. Janan ta tafi karbo min dinkin data kai mana, ni kuma naci gaba da zama anan har ta dawo.

Dinkunan sunyi kyau matuka, tace "sauran sai dai ko zuwa ranar juma'ah ne ko asabar aje a amso miki, na yiwa Is'hak magana zai je ya amso miki".

Na gyada mata kai cikin daukewar hankali lokacin dana daga wata riga, na hangame baki da hanci cikin mamaki, nace "meye haka nake gani wannan Jan? Wannan show me din ai yayi yawa".

Tace "ke ja can! Wani irin yawa kuma? Ba mijinki zaki yiwa kwalliya dasu ba?".

Ban kulata ba na tashi na hau gwada kayan. Na cire wata doguwar riga da tsabar tsagar da aka yiwa hannuwanta, baka banbanceta da vest sai idan kaga dogayen lebatun da aka mata, na ja tsaki, nace "gaskiya baki kyauta min ba Janan, wannan ai bata min kaya kawai kika sa aka yi ba wani abu ba".

Janan tayi murmushi, tace "kada ki damu matar Yaya, zaki gode min ne nan gaba".

Haka dai na hada kayan naje na shirya su cikin wardrobe, sai dai bani da niyar sanya su a cikin raina koda kadan. Kawai na riga na gama rayawa raina asarar kaya da kudin dinki Janan tayi.

Na koma falo muka cigaba da hirarmu ni da ita, har yamma tayi, Is'hak da zai kaita gida ya mana sallama da yake yau zata koma gida. Na rakata har bakin motar muka yi sallama da ita cike da kewa da kauna.
Anan muka hadu da Mimah itama tazo mata sallama, naja hannunta muka koma sashena, na kunno mata cartoons tana kallo, ni kuma na shiga kicin na fara hada dinner.

Da dare sai ga Yaya Bilal ya dawo da sabuwar waya kar a kwalinta, da sabin sims guda biyu.
Nace "ita fa waccan wayar tawa?".

Bai ko kalleni ba, yana ta tura abincin dana girka mishi, yace "nayi kyauta da ita!".

Na turo baki gaba kamar zanyi kuka, nace "amma fa akwai lambobin mutane da dama da zan rasa, kuma za ayi ta kirana ba'a samuna!".

Yace "manufar hakan kenan ai dama, ba zai yiwu in zauna in rabbe hannu a kirji ba ina kallo wasu gardawan kawai na kira min mata ba. Ban yarda ki ba kowa lambar wayarki ba sai wanda ya dace, kina ji na?".

Duk da na jinjina wannan karfin iko da mallaka, hakan bai hana ni amsa shi ba, nace "to, nagode, Allah ya kara budi".

Ko baiyi tunanin zan amince cikin sauki ba ne? Ya kalleni cikin mamaki, kafin yayi murmushi yace "yauwa baby na, ko ke fa?". Muka cigaba da cin abincinmu.

Bayan mun gama, ya wuce dakinshi zai watsa ruwa a cewarshi, ni kuma na koma dakina nima. Nayi brush, na fito na sanya kayan barci, nayi shafa'i da wutiri, sannan na kwanta.
Ban jima da kwanciyar ba sai gashi ya turo kofar dakin ya shigo. Ya kashe wutar dakin tare da hayowa kan gadon da nake, ya janyo ni cikin jikinshi.
Gabana dukan uku-uku yake yi, musamman lokacin da naji ya fara aika min nauyayan sakonni a cikin sassan jikina. Sai da tafiya tayi nisa, ni a kaina na fara fita daga hayyacina, naji tausassan sautin minshari yana tashi a kusa dani. Sai dai wannan karon, ban samu kaina da darawa kamar jiya ba, daga kai nayi ina kallonshi cike da mamakin abinda yake faruwa. Wani abu a tattare da wannan lamari just seems off.


*


Wasa-wasa abin dariya fa yake neman juyewa ya zama abin kuka. Kullum haka abin yake kasancewa, wani abin mamaki ma shi Yayan kamar bai san hakan tana faruwa ba. Saboda washegari normal zamu tashi ni dashi, babu wata alama ta ya tuna abinda ya faru a daren daya gabata a tattare dashi. Damuwa ta fara lullubeni, tunani ya fara addabata, tabbas akwai wata a kasa. Sai dai kafin in tono abinda yake a kasan, har ranar Lahdi ta zagayo, ranar dana fita girki, ranar da zamu koma Abuja kuma.

Ranar tun da safe na gama hada duk wasu kaya da zan tafi dasu. Duk wadanda yakamata mu yi sallama dasu, mun riga mun yi.
Karfe hudu Yaya ya leko yace min in fito zamu tafi, tun dazun aka fitar da kayan dana riga na shirya. Su kuma kayan dakin na samu manyan ledoji na lullubesu saboda kura.

Na fito tare da kulle kofata, na saka makullin cikin jakata.
Na leka sashen Anty Sarah na sanar da ita zamu wuce, ta saba Rabi'ah a kafadarta muka fito ni da ita.
Yaya Bilal da Yaya Jameel suna tsaye a gaban motar suna tattaunawa, muka tsaya anan gefensu muna jiran Raheemah ta fito. Sai yau kannen nata suka hada kan kayansu suka tafi. Da safe naga ana ta fita da kaya da tarkace, kusan zaryarsu biyu. Wani saurayin Salame ne yake ta zaryar kai kayan da dawowa ya lodi wasu. Na fito daga sashen Anty Sarah da safen, naci karo dasu sun fito kowacce na jan akwati kamar zasu je ci rani. Suna ta kwashewa mai motar albarkar saboda ya tsaida su suna ta jiran shi, suka daka min harara lokacin da suka ganni, ni kuwa na daga kafada na wuce abina.

Sai da muka kusa yin mintuna biyar muna jiranta a wajen, har sai da Yaya ya kai ga kiranta ya tunatar da ita muna jiranta fa, amma babu ita babu alamunta.
Yaya ya shaka, ya bude min gaba tare da umartata akan in shiga mu tafi, Yaya Jameel yace "kai kuwa ayi haka? Ku dan kara jiranta mana".

Yaya yace "yo ai ko aikina kenan zaman jira, yaci ace an zo an sallameni. A kanta zan kare ne?".
Yana tashin motar, sai gata ta fito tana takunta dagwas-dagwas kamar bata shanya mutane suna jiranta ba. Tazo ta gefen inda nake a zaune, ta bude kofar tayi wani kerere, ita bata juya ba, ita kuma bata ce komi ba, sai muzurai.

Yaya ya kalleta cikin kullewa, "idan ba zaki tafi bane, ki maida mana murfin motar mu mu wuce".

Bata ce komi ba, ta maida murfin motar da karfi ta rufe kamar zata balla shi. Ta bude baya ta shiga tana harare-harare da muzurai.

Su Yaya Jameel suka mana addu'ar Allah ya tsare, Yaya Bilal ya tashi motar muka fita daga gidan.
Daga farko nayi tunanin ko zamu biya ta gidan Anty Ameerah ne mu daukota, amma sai naga Yaya ya dauki hanyar fita daga Zaria straight.
A raina na raya tunda ita din shafaffiya ce da mai, yar gaban goshi, tana da motar hawa ta kanta, kila da kanta ta tafi.

Tafiya muke cikin madaidaicin gudu, bayan sautin radio da take ta aikin yi, baka jin motsin komi a cikin motar.
Yaya ya fara katse mana shirun ta hanyar fara tambayata yanayin yadda tsarin internship dinmu zai kasance. Nan da nan hira ta barke a tsakaninmu. Muna cikin yin hirar, zaka ji Raheemah itama ta tsoma nata bakin a ciki. Duk da ba tamu hirar take sanyawa baki ba, tata kalar hirar daban. Na kula tun karfinta take kokarin janye hankalin Yaya daga kaina.
Daga karshe dai da abin ya ishe ni, sai na kwantar da kaina akan kujera na kyalesu suna ta hirar su kamar ina yin barci.





🙏🙏🙏




#F.W.A





*☆⋆38⋆☆*




Gidan Yaya Bilal babba ne, mai kyau na gaban kwatance. Lokacin da muka fara shiga Abuja barci ya fara daukata, haka na bude idanu ina kallon gari. Duk da cewa ba wannan ne karona na farko zuwa Abuja ba, amma kuma na jima kwarai rabona da garin. Shi yasa yanzu nake ganina kamar wata sabuwar zuwa.
Yaya yayi ta ratsa tituna da ginunnuka har muka isa wata unguwa da tun daga bakin gate naga an rubuta Maitama. Duk yawace-yawacena ban taba biyowa ta nan wajajen ba. Daga gani babu tambaya unguwa ce ta masu hannu da shuni, tun daga kan ginunnukan da kuma tsari da yanayin unguwar. Ba karamin burgeni tayi ba.
Yaya ya tsaya a kofar wani madaidaicin gida, yayi amfani da remote, gate din gidan daya kasance ruwan zuma mai cizawa, da wata irin raga-raga daga tsakiya wadda take baka damar hango tanfatsetsen ginin dake ciki, ya bude da kanshi. Yaya Bilal ya silala kan motar ta shiga ciki, muna shiga gate din gidan ya koma ya rufe.

Wajen ajiye motoci muka fara tararwa, waje na mai fadi da zai cinye motoci akalla guda biyar. Yayi parking din motar, muka fito muna karewa gidan kallo. Motoci biyu ne a garejin, rufe da tampol dinsu. Ya mana jagora zuwa gidan. Daga gefen garejin akwai karamin waje da aka yi shuke-shuken bishiyoyi da furanni da basu fara tsayi ba, da alamu sabon garden ne aka yi. Sai kuwa kofar gidan, kana shiga dogon corridor ne da zai kaika har tsakiyar wani babban falo, kana shiga corridor din zaka ci karo da wata kofa da zata sadaka da kicin.
Babban falon ya dauki saitin royal setting, daga kan kujeru, carpet, labulaye, da fenti, duk golden ne da ratsin royal blue. A cikin babban falon dinning room yake, sai kuwa kicin da kofar su daya da dinning room din, sai babban store.
Kana fita daga babban falon anan dakunan mu suke, suma dai tubarkallah manya ne, daya yana kallon daya, inda nan ne ya nunawa Raheemah daya a matsayin nata, dayan kuma a matsayin na Ameerah da bamu gani ba, kila ita sai anjima ko kuma washegari. Daga gaban nasu kadan nan nawa dakin yake, daga gefen nawa kuma akwai dakuna guda biyu, babu komi a ciki daga carpet sai katifa da labulaye, kila dakin baki ne ko kuma na yara. Daga nan ya jamu, muka bi ta gefen dakunan zuwa master bedroom, inda dakinshi yake. Shima dakine babba mai fadi sosai. Daga dakin nashi muka sake fita zuwa wani falon da bai kai wancan girma ba, shima dai saitin kujeru ne da madaidaiciyar tv, sai tagogin wajen da suka kasance manya, irin daga sama zuwa kasa dinnan na gilasai, kana hango karamin lambun daga nan. Wajen dai ya hadu kwarai, just spectacular. Da ya bude wata kofa daga nan falon, sai muka sake bayyana a babban falo.

Bayan ya gama nuna mana gida da kuma ko'ina da ko'ina dai, sai duk muka wuce dakunanmu domin yin sallah da aka fara kira.

Dakina mai fadi ne, an sanya Italian bed, closet ta jikin bango, dressing mirror da shelves na littafai. Fentin dakin light orange ne, sai daga bangon gado da aka sanya wasu irin wallpapers masu tsananin kyau. Daga can gefe akwai study table da aka shirya, da dan karamin firjin a gefe, can gefe kuma nan ne bathroom yake. An zuba duk wasu abubuwan bukata a ciki. Sauran dakunan ma duk haka suke, hatta da kayan ma duk iri daya ne, kala ce kawai ta banbanta. Na sake bin dakin da kallo ina jinjina kai cikin jinjina namijin kokarin da Yaya yayi. Daga karshe dai na shiga bandaki na dauro alwala, ina fitowa na tadda abin sallah a shimfide yana facing din alkibla, don haka na hau kai na tada kabbarar sallah. Ban tashi daga kai ba sai dana yi sallar isha'i da shafa'i da wutiri sannan.

Kayana da aka taho min dasu na samesu a tsakiyar daki, na fara daga su ina fiddo su daga cikin akwatunan. Cikina ihun yunwa yake yi tun karfinshi, tunda yau na fita daga girki nasan bani da halin cewa zan shiga kicin in dora abinda zan ci. Nayi tunanin fita domin in ga abinda aka girka, daga baya dai kawai naga bari in dakata in gani ko za'a kira ni. Na daga fridge din dakin naga babu komi a ciki sai ruwa, shima babu sanyi saboda firjin din ba a kunne yake ba. Naja tsaki na maida firjin din na rufe. Na koma

35 / 52