Author : Jeedderh Lawals Category : New Hausa Novels 2026
da hoda. Ina cikin shafar ne naji hayaniya ta fara tashi, na dan dakata, jin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa na dauki doguwar hijabi na zura na fita falo domin in ga abinda yake faruwa.
Raheemah na jingine da bangon falon, Yaya da Ameerah kuma na tsaye a tsakiyar falon sunyi cirko-cirko suna raba idanu kamar wasu zakaru.
*☆⋆47⋆☆*
Kallo daya zaka yiwa yanayin da mutanen falon suke ciki, zaka fahimci cewa babu lafiya.
Ameerah na tsaye nesa kadan da Yaya, in banda rawa, babu abinda ilahirin jikinta yake yi. A tsorace take sosai.
Shikuwa Yaya ya tsaya jimke da hannu, sai dana kare mishi kallo sosai sannan na fahimci cewa wata yar karamar farar takarda ce jimke a hannun nashi, wadda ya kama ya rukunkume har knuckles dinshi sai da suka yi fari, a gefe guda kuma jikinshi yana rawa cikin bacin rai.
Raheemah kam ta coge daurin dankwalin nan nata a tsakiyar ka kamar yadda ta saba, da alama itama hayaniyar ce ta fiddota zuwa cikin falon.
Hankalin Yaya gabadaya yana kan Ameerah, kallon da yake watsa mata kadai ya isa yasa duk girman kai da ji da kai na mutum ya saddakar masa ko da bai yi niyya ba kuwa. Ni kaina da nake gefe sai dana ji gabobin jikina sunyi sanyi. Ban taba ganin wannan side din na Yaya ba. Da alamu ma sam bai san da wanzuwarmu a falon ba, idan ma ya sani to yayi kokari wajen nuna cewa wanzuwar tamu anan bata shalle shi ba.
Ya nuna mata hannunshi da yake rike da farar takardar nan yana nuna mata, cikin wata irin murya da ta sanya ni na kara kallonshi da kyau domin in tabbatar da cewa da gaske shi dinne dai, he sounds deadly. Calm, but deadly. Kamar wani sabon mutum da ban taba gani ba, haka ya juye ya koma a lokacin.
Yace "care to explain, ko menene wannan kike kokarin zuba min a cikin abincina?". Jin abinda yace yasa na zare ido ina kallonsu, a lokaci daya kuma ina kara matsawa kusa dasu.
Ameerah ta dan ja baya da sauri, tsoron dake shimfide akan fuskarta da baka taba rabata da kwalliya, ya bayyana zane baro-baro, instead, shi ya zame mata kwalliyar yau.
Tace "don Allah kayi hakuri. Wallah na tuba, don Allah!".
Sai dai bai jira ta gama magiyar da take yi ba, ya daka wata irin gigitacciyar tsawa, "Don't you dare Ameerah! Tambayarki nayi, damn your sorrys don ba ita nake bida ba. Ki fada min, meye hadinki da shinkafar bera na tsinceta a hannunki kina kokarin sakata cikin abincin da zan ci?!".
Naji ana min wata irin kururuwa a cikin kunne, kaina yana juyawa kamar ana katantanwa dani, kafin wani irin duka a tsakiyar ka ya ziyarce ni kamar ana buga min guduma a ka. Ala dole na lalubi kujerar dake kusa dani na zauna babu shiri saboda rawar da kafafuna suka dauki yi.
Yanzu kam hawaye ne suke ta zarya akan kumatunta, daya bayan daya suna sintiri babu kakkautawa.
Yaya ya kura mata ido, "shikenan? Kaunar da kike ikirarin kina yi min kenan? Soyayyar kenan? At the end of the day kiyi sanadin raina?".
Kai ta hau girgizawa, "ba haka bane, wallah banyi da niyar cutar da kai ba, ka yarda dani. Sharrin shaidan ne!".
Yace "kada ki maida ni sakarai mana! Da idanuna na ganki kina zuba abinnan fa. Ko kuwa kina nufin ki ce sharri na miki, ko kuma idanuna ne basu gani daidai ba?"
Tayi shiru kanta a kasa, sai kai data girgiza kawai.
Yace "kina fa bata mana lokaci, ki fada min dalilin ki, ko kuwa kina so ne kice min gishiri ne wannan a hannuna?".
Ta daga baki da kyar tace "akwai antidote dinta, da kaci zan baka yadda zaka amayar da gubar da kaci. Wallahi ba zan taba yin abinda zai cutar da kai ba, na rantse da Allah!".
Sai dai ko kadan rantsuwar da take ja bata dada shi da kasa ba. Instead, sai kallonta daya tsaya yana yi. Babu mamaki tunani da lissafin gidan kula da masu tabin kwalwa mafi kusa yake so ya lalubo.
Da kyar ya iya kakaro sautin, "me yasa?", daga can kasan makoshinshi.
Bata amsa ba sai daya kara jefa mata tambayar cikin daka tsawar da tafi ta dazu gigitarwa.
Ta ja baya da sauri, "munyi zaton idan ka ci abincin zaka zargi ita ta zuba maka, sai ka sallameta!".
Na tsayin lokaci, duniyata sai ta tsaya cak. Bansan lokacin da hawaye suka fara zarya suna gangarowa kan kumatuna ba.
Wannan shine karshen kiyayya da wani mahaluki zai taba nuna maka a cikin rayuwa, shin ta tsani ganina har haka ne da abin zai kai ga laka min sharrin kisa? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!.
Yanzu da Yaya bai shigo ba akan lokaci ya sameta cikin aikata wannan aika-aika ba, mai zai faru? Da haka zan kare rayuwata da laifin attempted kisa, haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba. Da haka rayuwata zata kare, ina tsanar kaina da tuhumar ta yaya hakan ta faru? Yaya da yan'uwanshi da suka zama nawa yan uwan nima suna tsanata?
Me na yiwa wannan matar ne da zan cancanci haka daga gareta?.
Yaya bai ce komi ba sai pacing daya hau yi kamar mai fareti, cikinmu babu wanda yayi gigin yin ko motsi, sai ni da lokaci zuwa lokaci zan ja majina ko in share hawayen fuskata.
Ya dawo ya tsaya a gabanta, "what were you thinking you silly woman?", ya furta with venom a cikin muryarshi. Kafin ya juya ya cigaba da zagayen da yake.
Falon ya dauki shiru kamar babu wasu halittu da suke numfashi a ciki.
Yace "ban san ko daga ina matsalar nan take ba, amma wannan ba hujja bace. Me kike tunani, kin tsani ganinta ne har haka ko me? Hasbunallahu wa ni'imal wakil!".
Da alamu ya. kasa iya wrapping kanshi akan wannan matsalar, nima hakan take a wajena.
Yace "kwanaki munyi ta cin karo da matsalar yawan gishiri yaji, tsami, da sauransu a duk ranakun da Na'ilah tayi girki, it was so suspicious I can't help but wonder, kina da hannu a haka?".
Ta dago rinannun idanunta da suka rine suka yi jawur saboda tsabar kuka, suka yi clashing da nashi rinannun da tsananin bacin rai, shock da tu'ajjibi suka haifar mishi. "Bab...", ta daga baki zata fara magana yayi gaggawar katseta, "cut it! Tambayarki nayi don haka amsa zaki bani ehh ko a'ah?".
Tayi kasa da kanta a sanyaye, "kayi hakuri".
Ya rumtse idanunshi yana girgiza kanshi kamar yana shaking wani abu daga ciki, "cikin da kika yi b'ari fa kwanan nan?".
Nan ma wani shirun ya ziyarce shi kafin bada hakuri ya biyo baya.
Shirun daya biyo bayan nan was deafening.
Magana daya Yaya ya iya yi a wannan lokacin, "kin cuce ni Ameerah!". Wadda daga jin yadda muryarshi ta lullube da zallan bakin ciki da sararwa, daga gani babu tambaya abin data aikata ba karamin girgiza shi yayi ba. Sai dai ni kaina abin ya girgiza ni, sosai ba kadan ba, wa ma zai taba tsammanin haka daga gareta? Da iliminta, da wayonta da komi. Rashin dabara ce ko kuwa tsananin jarumta?.
Daga lokacin da Yaya ya yanke shawara, na fahimci abinda yake shirin aikatawa, niyyarshi a bayyane take, idanunshi sun rufe da takaicin abinda tayi.
"That's it Ameerah... Kije na..."
Ban san lokaci ko dalilin daya sanya ni mikewa tsaye da sauri ba ina mai ambatar sunanshi, dalilin daya sanya shi dakatawa kenan, ya tsaya yana kallona cikin nuna alamun tambaya.
Nace "Yaya, kada ka aikata abu cikin fushi kazo daga baya kana dana sani, don Allah ka fara nutsuwa tukun".
Ya kalleni, ya juya ya kara kallonta, ya daga baki kamar zai yi magana, ko kasa yin maganar ma yayi? Kawai juyawa yayi ya fita daga cikin falon da sauri.
Ameerah tayi tsaye a nan inda ya barta, kusan minti daya, kafin ta lallaba ta fada cikin dakinta. Na koma cikin kujerar dana tashi na sake zama. Ba ni na aikata abin ba, amma har yanzu ilahirin jikina rawa kawai yake yi. Ita Raheemah na tsaye a inda take, bata da niyar motsawa. Allah kadai yasan iya lokacin da muka dauka a haka, bayan rawar da jikina yake yi, wani irin sanyi jikin nawa ya dauka ta yadda ko yatsar hannuna kasa motsawa nayi.
Zuwa can sai muka ji karar bude kofa, muna daga kai sai muka ga Ameerah ta dora gyale a kafada, ta ratayo jaka a daya kafadar, makullin motarta a hannu. Babu wanda ta kalla a cikinmu bare muyi tunanin samun karin bayanin inda ta nufa, ta kara gaba. Muma babu wanda yayi gigin tararta bare ya mata magana. Tana fita Raheemah ta juya ta koma dakinta.
Na ci gaba da zama a falon ba ko motsi, ina kallon waje daya kawai; inda Ameerah take tsaye yan mintuna da suka wuce.
Shiru Yaya zai dawo yanzu, amma babu alamun shi. Ba karamin mamaki nayi ba lokacin dana daga kai na kalli agogo naga goma saura. Sai a lokacin ne nayi kokari na koma dakina ina hada hanya. Sallar isha'i na fara yi. Ko bayan na gama sallar, zama nayi akan abin sallar ina kara neman tsarin Allah daga sharrin zafin kishi, kishi wanda zai iya sanya ni aikata mummunan abu ko kwatankwacin wanda Ameerah ta kwatanta yi yau.
Wani irin kishi ne wannan? Wane irin so ne da zai sanyaka aikata abu kamar sanya guba, da sunan son yin framing din wani, kawai don ya bar maka gida? Anya mata zamu so ganin haske a cikin rayuwarmu kuwa?.
Abin bai taba zuwa kaina ba a cikin rayuwata sai yanzu. Nasan nayi kishi, na kuma san na tsani kishiya, sai dai ko da wasa, ko a cikin mafarki ban taba tunanin zan iya aikata abu irin wannan ba. Sai dai dana zauna na kara yin tunani, sai naga ai tun daga farkon fari, abinda ya sanya ni kin kishiyar kenan. Tsoron juyewa in zama abinda ba ni bace yasa, tsoron kishi ya sanya ni aikata abinda zai zo ya zame min abin nadama nake yi, ina tsoron aikata ire-iren wadannan abubuwan ne.
Na kara rokon Allah akan ya kiyaye zuciyoyinmu daga sharrin sake-saken shaidan, da bin shawarar mugayen kawaye, har ma da yan'uwa.
Sai wajen karfe sha daya sannan Yaya ya dawo gidan, lokacin gidan yayi shiru, ko karar tv baka ji a lokacin balle na mutane, har lokacin kuma ina zaune anan inda nake.
Kirana yayi a waya yace in same shi a falonshi. Na tashi na fita, yana zaune akan kujera da ledoji a gabanshi. Sai lokacin na tuna ban dauke kayan abincin ba ma. Ya miko min nawa, buyin kuma yace in mika musu, da alamu bai san Ameerah ta bar gidan ba.
Dana fada mishi Ameerah bata gidan, bai ce komi ba, kai kawai ya gyada tare da tashi ya fada dakinshi.
Na kwashi ledojin na tsaya ta kofar dakin Raheemah na buga mata kofa, ta leko na bata. Bata ce komi ba ta amsa ta maida kofar ta rufe. Sauran kuwa sai kicin na kaisu na ajiye don babu abinda zai iya shiga cikina a lokacin. Na kwashe kayan nan gabadaya na zubar da komi, har lokacin ganin komi nake yi kamar a mafarki, na kasa yarda ya faru.
Sai wajen karfe goma sha biyu nayi sallama dakin Yaya. Yana kwance akan gado, amma ba barci yake yi ba. Na zauna a gefen gadon ina kallonshi, bai yi ko motsi ba.
Zuwa can nace mishi "ba zaka ci abincin bane? Ko zan sama maka wani abu ne?".
Ya girgiza kai. Sai ban takura shi ba, na tashi na kashe wutar dakin na koma na kwanta.
Nasan yana bukatar lokaci kafin ya samu komi ya zauna mishi a kai. Ko ni kaina abin ya kasa zaunar min, balle shi, da suka kwashe lokuta masu tsayi da ita, to think that zata iya betraying dinshi ta haka, abu ne mai wahala. It must be a big blow. Daga ni har shi babu wanda ya tankawa wani, muna ta sake-sake. Ranar kam barci sai barawo.
*
Washegari karan wayar Yaya ne ya tashemu daga barcin da muka koma bayan sallar asuba. Kaina har juyawa yake yi saboda tsabar ciwo da rashin barci.
Sai da tayi kara sau kusan uku babu kakkautawa, a raina har ina mitar wane mai gajen hakuri ne wannan da bai san ya kira sau daya ya hakura ba? Karfe bakwai da rabi ma bata karasa yi ba lokacin.
Sai da kira na uku na katse, yana katsewa kuwa na hudu ya sake shigowa. Sannan Yaya ya kai hannu ya dauka.
Murya shake da barci ya fara da yin sallama, sai dai da alama mai kiran wayar bai damu da sallamar tashi ba, ya tare shi da "Me Ameerah ta maka ka turota gida tun da sassafe?". Da alama Babanta ne.
Kasancewar a kusa dani yake, ina jin maganar da ake yi a daya bangaren.
Tashi zaune yayi yana gaida shi, wannan karon ma bai amsa ba, ya kara maimaita mishi tambayar daya mishi. Tashi yayi cimak ya fita daga dakin, na bishi da kallo.
Sai can kusan bayan minti sha biyar, sannan ya dawo dakin. Ya zauna a kan sofa tare da dafe kanshi cikin hannuwanshi. Ganin haka yasa na tashi zaune a tsakiyar gadon.
"Lafiya?". Na tambayeshi a sanyaye. Yanayinshi bai yi kama da wanda yayi tattaunawar arziki da surukin nashi ba.
Ya girgiza kanshi kafin ya dago kai ya kalleni, "ban sani ba nima, kawai dai Ameerah taje musu gidan da safiyar yau, wai tunda taje take kuka bata ce komi ba. Yanzu dai Babanta yace zai zo nan ya sameni, zamu hadu anjima kadan a Will's Park".
Na dan zaro ido, kafin na gyada mishi kai.
Nasan ko na koma na kwanta ma babu wani barci da zanyi. Don haka na tashi kawai na shiga bandaki na dauraye bakina. Na tafi na dora girkin safe.
Abincin sai tsakurar shi kawai aka yi. Karfe daya Yaya ya tafi ganin mahaifin Ameerah. Bai dawo ba sai gab da magriba. Fuska babu yabo babu fallasa haka ya shigo gidan. Ameerah da take girki, ta mishi sannu da zuwa ta bishi zuwa dakinshi.
Sai da dare muna falonshi mu duka, sannan yake bamu labarin abinda ya faru.
Mahaifin Ameerah dai yaki yarda, ko kuma ince yaki daukar laifin da diyar tashi tayi. Daga karshe ma sai ya koma accusing din Yaya kan cewa dama baya kula mishi da diyarshi yadda yakamata, ya maidata ta zama koma baya a cikin dangi. Tafi-tafiya ma sai yace yana bukatar takardar sakinta kawai. Duk yadda Yaya yayi wajen ganin cewa ya fahimtar dashi, abin yaki yiwuwa. Shi a ganinshi abin bai kai ga haka ba, sai ya gangaro yace idan bai sakar mishi diyarshi ba zai iya maka shi a kotu. Sai da ya rubuta mata saki daya sannan ya warci takardar ya kara gaba.
Daga ni har Raheemah babu wanda bai jijjiga da jin haka ba. Muka jinjina maganar sosai, daga karshe nayi fatan Allah yasa hakan shi yafi alheri.
*
Kwana biyu gidan shiru, ita kanta Raheemah ta kame kanta ta kai gefe. A hankali komi yazo ya wuce, ya zama tarihi a wajenmu. Rigima bata kuma tashi ba, kamar hakan ya zamewa Raheemah abin tunatarwa da darasi. Tsakanina da ita sai kallo kawai, ba uhm ba uhm uhm. Habaice-habaice da bakaken maganganu da take yawan jifa na dashi a kullum rana ta Allah babu gajiya, muddin muka hadu sau daya ko sau goma a rana sai an jefo shi kamar wani abin arziki, yanzu ta daina kamar anyi ruwan sama an dauke.
Ko lokacin da tafiyarmu umara yayi, bayan sati biyu da tafiyar Ameerah kenan. Lokacin mun kai azumi na hudu kenan. Yaya yayi mata maganar zamu tafi ranar da aka dauki azumi na takwas, mu tsaya mu kwana a Kaduna, washegari mu wuce Katsina mu kwana. Ranar da aka kai azumi na goma zamu wuce Umra. Daga fari nayi zaton zata hau yin kalar dibar arzikin da tayi kamar da, amma ga mamakina maimakon tayi wani abu, kawai sai gyada kai da tayi ta mana fatan a dawo lafiya.
Shi kanshi Yaya sai da ya nuna alamun yayi mamaki, kafin ya girgije. Yace to tayi list din abubuwan da zata bukata kafin mu dawo. Nan ma tace babu komi.
Wannan karon kam sai da mamakinshi ya fito fili, yace "babu?".
Tace "to duka-duka ko sati daya fa ba'a yi da kawo kayan provision ba. Bamu yi wani amfanin azo a gani da kayan ba".
Yaya yace "to shikenan".
Ranar da zamu tafi, haka ya dauko naira dubu dari cif ya dire mata a gaba. Yace tayi hidimar sallah. Tuni dama tare aka kawo mana kayan sallah da kayan kamun azumi. Manyan atamfofi da leshina, ya kuma hado mana da kudin dinki. Iyayenmu suma haka ya aika musu atamfofi da shaddoji har da kudin dinki. Hatta su Malam ma sai daya aika musu.
Duk da nima sai dana aika musu, da su kayan kamun azumi. Suka yi ta mana godiya da sanya albarka kuwa.
Kamar yadda yace, Kaduna muka tsaya muka musu shan ruwa. Janan ma ranar a gidan ta sha ruwa da yake Almunta baya gari. Muka yini muna hirar yaushe gamo. Da dan yaron cikinta ma kuwa, duk da taki yarda da zancen tana ta min kwana-kwana.
Su dukansu sunyi mamakin abinda ya faru da Ameerah. Abu ne na Ala wadai, amma su dukansu babu wanda yayi mata addu'ar banza ko yayi wata maganar da bata dace ba, sun dai jinjina abin, kafin suka yi addu'ar Allah ya kara shiryata da duk sauran ire-irenta.
Da yake da kayan sallah ta na taho, washegari kafin mu wuce zuwa Katsina, muka je wajen telarta ta auna ni, muka bar kayan dinkin anan.
Muna komawa gida muka wuce Katsina.