AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   50 / 52

147K to 150K   out of 155.4K words

Ta ja tsaki kafin ta kwashe da dariya.

Ni kuwa da nake ta binta da kallo cike da mamaki, na sake ware idanu ina kallonta. Dama naji Janan tace wai ance tun bayan rabuwarsu da Yaya, kamar kwalwarta ta tabu haka take, ban tabbatar ba sai yanzu. Ta kalli Muhaaseen da tunda muka shiga gidan ta makalkaleni, haka take duk lokacin data ganta a gaban mutanen da bata sani ba.

Ta zare ido, "laa, wannan ce diyar da kika haifa? Amma fa kyakkyawa ce!". Ta kai hannu kamar zata dauketa, yarinyar tayi saurin kara makalewa a jikina, ni kuwa na sanya hannu na kara riketa tsam a jikina, a can kasan raina ina cewa Tubarkallah. Duniyar yanzu baka san bakin mutane ba.

Ganin na riga na gama yin abinda ya kawo ni, ga wani irin wari da yake tashi a cikin falon da yake kokarin tasar min da zuciya, yasa na mike tsaye ina cewa "bari mu tafi, sai anjima".

Tace "da wuri haka?".
Na kalleta cikin rashin abin cewa, idan na tsaya mai hakan zai kareta dashi?

Tace "to shigo ki duba jikin Salame mana".
Bata jira nace komi ba ta tunkari wata kofa, cikin sanyin da jikina yayi na bi bayanta.

Ina shiga dakin nayi baya da sauri, wannan warin da nake ji a falo sama-sama ya bugo ni full force. Sai lokacin na fahimci daga inda warin yake fitowa. Daga inda nake na hango Salamen kwance acan kuryar dakin kamar kayan wanki akan shimfida, rabin jikinta lullube da mayafi inda aka sakaya private parts dinta.
Naji wani irin tsoron Allah ya kamani a lokacin, lallai shi dai mutum ba a bakin komi yake ba a wajen Allah.
Kamar yau ne fa, suka tareni suna min dibar albarka a cikin gidan aurena, akan mijin da nake aure. Yanzu dana duba baya, lallai ba karamin lokaci bane ya wuce, amma kuma a cikin kaina sai nake ganin kamar yau hakan ta faru.

Da kyar na iya karasawa kusa da ita, da alama ma barci take yi. Itama gefenta kwanuka ne birjik a ajiye, wasu ma daga ganinsu ba karamin lokaci suka dauka anan ba.
Nace "har an sallameku daga asibiti ne?".

Tace "ina fa! Koro mu suka yi saboda babu kudin gado dana magunguna. Ni kuwa nace aikin banza kenan, muka maidota gida. Ai yanzu maganin gargajiya ma ake mata. Shima kwana biyu dai an daina bata ma".

Na gyada kai a hankali, ina so in kara watso mata wata tambayar, amma bakina ya kasa budewa, don haka na dinke bakin nawa kawai na mike tsaye. Ina ji Raheemah ta biyo bayana tana wasu surukai dana kasa fahimtar abinda take cewa, na dai tsinci sunan Salamen da kuma zagin da take dankarawa.

Na kara rike Muhaaseen sosai ina kokarin sanya takalmina, wani zagi data saki ne yasa na daga kai na kalleta cikin mamaki. Tace "kan ubar nan!! Wannan shegen hadadden takalmin fa? Zai yi dubu nawa? Kai, wallahi dama ki bani shi in dinga kwalliya dashi abina".

Ni yanzu tsoro ma take bani kuma, yadda tayi tsaye a kaina tana watso min hakoranta da tsabar rashin wanki yasa suka yi wani yalo-yalo, gani nake kamar a kowane lokaci zata iya kawo min mazga. A karo na farko na fara tambayar kaina tsautsayin daya kawo ni nan. Musamman idan na tuna ta yadda ma aka yi Yaya ya barni na zo gaisuwar nan.

Ban ce mata komi ba, na tunkari kofar fita da sauri, ta biyo bayana. Muna gab da kofar gidan hayaniyar yara ta kusantomu, ihu kawai kake ji da kururuwa.
Haleemo da itama babu banbanci tsakaninta da Raheemah, duk da ita suturar jikinta da yar dama-dama akan ta Raheemah, ta fado gidan hannu rike da fararen manyan plastic bokitai da sauran shinkafa da tarin kabeji a ciki. Tsinin dake cikinta zaka fara gani kana dora idanu a kanta.

Waka da shewar da yaran suke yi ta kara yawa,
_'Yar iska taki zaman aure, daga talla sai yawon iskanci!_
_'yar iska tayi cikin shege...!_

Ita kuma tana korarsu da kayan hannunta tana dankara musu zagi da tsinuwa, har dai Allah ya bata sa'a ta shigo gidan ta maida kyauren ta rufe da sauri tare da daukar wani gingimemen dutse ta jingina da jikin kofar.

Tana juyowa ta kallemu tayi turus! Ta kalli Raheemah tace "wannan fa wacece?".

Raheemah din ta watsa mata harara da sauri, "to uwar yan tsegumi, ina ruwanki da bakuwata?".

Ta tabe baki, "jibeta sakara kawai, banza mai tabin kwakwalwa, to sai me don kinyi bakuwa? Daga gani ma kuskuren gida tayi ba wajenki tazo ba don daga gani bata yi kama da irinki ba".
Raheemah ta tunzura da abinda tace "na dai gode Allah, duk da tabin kwalwar tawa dai ban je nayi cikin shege ba!".

Ta daga baki kamar zata yi magana, sai kuma ta fasa, tayi cikin gidan tana "oho miki dai, mahaukaciya".

Ba shiri na kama dutsen nan na janye da sauri na fita daga gidan, Raheemah ta sha gabana tana wasu yan soshe-soshe.
"To Hajiya Na'ilah, na gode ko? Yaushe zaki sake dawowa? Gashi kin zo ko ruwan sanyi ba'a baki ba. Nasan ba zaki iya shan ruwan randa ba, ni kuwa bani da ko sule balle ko na fiya wata ne a sayo miki".

Ganin take-taken bata da alamar rabuwa dani don wasa da kuma abinda take hinting, yasa na zage jakata na ciro kudin da ko kirga su banyi ba, na mika mata. Ta warta kamar wadda take tsoron zan kwace ta jefa su cikin rigarta. Sai data tabbatar ta boye kudin sannan ta juyo ta hau zuba min godiya, tana lissafo abubuwan da zata sayo taci dasu ta hana 'yan uwan. Ban kara cewa komi ba na juya da sauri, ina ji kamar ma in sheka da gudu. Jindadina daya, da bata sake biyo ni ba.

Na bude wajen direba a motata Benz, ruwan ash mai haske sosai daya zama kamar white-gold, wadda na saya da kudina da albashina duk da dai sai da Yaya ya min ciko, lol.
Na maida kofar na rufe, na kwantar da Muhaaseen a seat dinta dake bayan motar. Sannan na sauke wani dogon numfashi da ban san na rike ba.
Sai dana nutsu, sannan na tashi motar tare da ja na fita daga cikin unguwar a hankali.


*


Na kwankwasa kofar dakin Yaya sannan na tura kofar na shiga.
Yana zaune a tsakiyar dakin akan carpet, Muhaaseen na kwance akan cinyarshi tana yan wasanninta na yara. Laptop dinshi da tarin takardu da jaridu shimfide a gefenshi suna jiran ya karkata hankalinshi garesu. Hankalinshi baya kan su though, kai gabadaya ma baya cikin dakin. Idanunshi na kan Muhaaseen, kamar wanda yake kula da duk wani motsi da tayi, sai dai daga gani kawai idanunshi ne suke kallonta, amma gabadaya hankalinshi baya ma cikin dakin. Tuni yayi nisa a cikin duniyar tunani.

A nutse na ajiye farantin dana shiga dashi a kusa dashi. Karamar kettle ce dana zuba shayi a ciki, sai fresh grapes da berries a cikin wani bowl.
A hankali na kai hannu na dauke Muhaaseen daga jikinshi. Yayi firgigit! Ya zabura yana kallona a dan rikice.
Na kalleshi cike da alamun tambaya, kusan kwananmu takwas da dawowa daga Zaria, amma na kasa gane kanshi. Duk lokacin da zaka ganshi, a zaune yake ko yayi tagumi, ko kuma yayi zurfi cikin tunani. Haka a yawancin lokuta zan tashi cikin dare in ganshi zaune a tsakiyar gado cikin zuzzurfan tunani, sai dai duk lokacin da zan tambayeshi abinda yake faruwa sai dai ya girgiza kai kawai. Ko yace ya gaji ne, ko aiki ne ya mishi yawa, ko kuma wani abu dai. Wanda daga ni har shi mun san cewa ba haka bane.
Amma gabadaya yan kwanakin nan naga abubuwan nashi sun fara yin yawa, na kula har wasu dark spots sun fara fito mishi a kasan idanunshi alamun akwai abin da yake matukar damunshi.

Ban ce mishi komi ba, na tura mishi plate din dana shigo dashi. Cikin sanyin jiki ya janyo laptop dinshi ya fara aiki, na kula da yadda hannunshi yake dan yin rawa slightly. Nan ma na kauda kaina. Na dauki inabin tare da kaishi saitin bakinshi. Ya dago kai ya kalleni yayi dan murmushi tare da daga bakinshi ya karbi inabin, sai daya hada da yatsata ya dan ciza.
Da sauri na janye yatsar tare da sakin dan kara a hankali, hakan yasa Muhaaseen dake kan cinyata ta zabura. Nayi saurin fara lallashinta ina hararar shi ta kasan ido, yayi kamar bai san abinda yake faruwa ba, sai dan siririn murmushin daya saki na tsokana.

Ina gama lallaba Muhaaseen tayi barci, na kwantar da ita a cikin crib dinta dake gefen gadon da muke kwanciya. Na sake komawa gefen Yaya na zauna, yana aikinshi ni kuma ina cin abubuwan da na ajiye ina kuma bashi, har muka gama su. Sannan na dauke kayan na kai kicin. Sai dana tsaya na kashe duk wasu abubuwan wuta sannan na wuce dakina, nayi shirin da zanyi na kwanciya sannan na koma dakin Yaya.
Har yanzu yana zaune inda yake, sai dai ba aiki yake yi ba, al'adarshi ta tunani yake. Raina gabadaya naji ya dagule.

Na zauna a gefenshi tare da nade kafafuna sosai ina fuskantarshi, cikin sanyin murya nace "Abban Maama, wani abu yana faruwa ne?".

Yayi saurin girgiza kai yana kokarin mazewa kamar yadda ya saba, "me kika gani?".

Nace "meye ma ban gani ba? Wani abu ya faru ne a Zaria? Tun muna can fa na kula da canzawar da kayi, ina kuma ta tambayarka amma sai dai kace min babu komi. A tunanina ni din abokiyar shawararka ce, kamar yadda kake abokin shawarata?".

Da sauri ya hau gyada kai kamar wani karamin yaro, "haka ne baby, na sani. Just... Ban ma san ta inda zan dauko zancen bane".
Jin haka yasa na kara matsawa kusa dashi sosai, "to menene? Ka fada min, kaji? Idan ma wani abu ne da yafi karfinka zamu iya hada karfi da karfe, idan ma yafi karfinmu dai duk babu abinda zai gagara, kaji? Menene?".

Yayi shiru yana kallona cikin tunani. Kai ya girgiza kawai, "I'm sorry baby, maybe next time, amma ba yanzu ba".
Nayi kasa-kasa da ido, "Yaya...!"
Sai dai ban kai ga karasa fadar abinda nayi niyar fada ba, naga ya tashi da sauri kamar wanda aka mintsina yayi hanyar bayi. Na bishi da kallo cike da tsananin mamaki, a hankali wani abu mai kama da takaici ya tsaya min a makoshi. A ganina ina laifin wanda ya damu da damuwarka? Akalla kullum zan tambayi Yaya abinda yake damunshi, yafi sau a kirga. A tunanina, ko bai fada don muyi maganin abin ba, ai zai fada ko don raba damuwarka da wani kamar ka cirewa ranka rabin damuwar ne.
Nayi kwafa a hankali tare da mikewa tsaye ina karkade kayan jikina. Ko kofar bayin daya shiga ban kara kallo ba, na wuce wajen da Muhaaseen take kwance na tofe ta da addu'o'i. Na haye kan gado tare da shafe nawa jikin nima da addu'ar kwanciya barci.

Ban ma san lokacin da Yayan ya fito daga bandakin ba saboda lokacin barci ya fara daukata. Daga can dai naji lokacin daya hayo kan gadon ya kwanta tare da laluboni jikinshi, nayi banza na share shi. Kodayake, shariyar ta dan lokaci ce, babu shiri na manta da dan guntun fushin da nake yi na kara kwantar da kaina akan faffadan kirjin mijina.

Cikin tsakiyar dare na farka, tunda na laluba gefena naji babu kowa nasan cewa Yaya sana'ar yake yi. Na mike zaune da kyar tare da daukar bargo na rufe saman ruwan cikina dashi, saboda sanyin da yake dan bugowa a lokacin.
Kamar yadda nayi zato, zaune yake a gefen gadon, ya zira kafafunshi ta kasa, kanshi a kasa, ban sani ba duk cikin tunanin ne, ko kuwa barci yake yi a haka?.

A hankali na kai hannu na dafa samar kafadarshi, daga yadda jikinshi yayi tensing, nasan cewa idanunshi biyu.
Nace "Abban Maama...".

Kaico! Masana iya magana dama sukan ce wai rashin sani yafi dare duhu, kuma dana sani k'eya ce.
Da ace nasan kalmomin da zasu fito daga bakinshi, da ban farka ba, da ban yi tunanin yi mishi magana ba a tun farkon fari, dana sani da naci gaba da kwanciyata koda kuwa na kasa komawa barci. Ban shiryawa jin abinda ya fito daga bakinshi ba.

"Na'ilah, aure zan yi!".

Kalma mafi muni data taba shiga cikin dodon kunnena a cikin tarihin rayuwata kenan. Naji duk wasu ayyukan dake wakana a cikin kwalwata sun dakata da aiki, kai ni a karan kaina sai naji ni kamar wata sassaken sak'ago, ko wata statue. Na kasa numfashi, na kasa motsa komi a jikina, na kasa tuna komi a cikin raina. Wadannan kalmomi hudu daya furta, su kadai nake fahimta, su kadai kuma suke min yawo a cikin kaina.

Ban san lokacin daya juyo ya fuskanceni ba, sai da naji hannunshi da a da, idan ya taba ni dasu na kanji duk wata gajiya da wahala dake tattare dani ta gudu daga jikina a take, amma yau ya banbanta. Sai naji kamar ya dauko duk wata gajiyar duniya ya dora min ne, babu shiri na fara kokarin zame nawa hannun daya kama, amma bai bari hakan ta faru ba.

"Na'ilah, baby, ki saurareni don Allah, wallahi ba wai don bana sonki bane zanyi wannan auren, I love you more than anything in this world, bani da zabi ne, don Allah ki saurareni, kinji?".

Na daga idanuna da na kasa tsayar dasu waje daya. Daga jin zafin da suke min, nasan cewa cike suke da hawaye, sun kuma canza kala. Cikin muryar da ni kaina sai dana yi mamakin jin ta fita daga bakina, nace "me kace?".

Ya kara damke tafin hannuna cikin nashi, "please baby, ki bari in fara miki bayani kafin...".
"aure kace?", na katseshi ta hanyar jefe mishi wannan tambayar, ba tare da tunanin maganganun da yake fada ba.

A hankali, kamar wanda yake tsoron wani abu, ya daga kai sama.

Ban san lokacin dana kwace hannuna ba, na dira daga kan gadon cikin wani irin sauri da rawar jiki da ban taba zaton akwai irinsu a duniya ba.
Yaya yayi kokarin sake kamo ni, amma ina! Gabadaya duk wani sauran tunani daya rage a jikina yayi kaura. Ture shi na sake yi. Daya matsa da kiran sunana da kokarin kamo ni, sai kawai na kasa da gudu. Na fada dakina na maida kofar da sauri na kulle da makulli na hada da sakata.

Tsaye a tsakiyar daki, hannuwa biyu da suke ta rawa rike da wayata ina lalube cikin jerin contacts dina, amma na kasa ganin komi saboda hawaye da suka cika min idanu har sun fara zuba, balle inyi tunanin wanda zan kira a cikin tsalelen daren wannan.
A gefe guda kuma Yaya yana daga waje yana buga min kofar dakin tare da magiya akan in bude muyi magana.
Daga karshe dai silalewa tsakiyar dakin nayi da hannuwana biyu aka.

An fara kiraye-kirayen sallah a wasu masallatan lokacin da Yaya ya dakata da bugun kofar da yake yi, ina jin karar sawayenshi lokacin da yake barin kofar dakin. Na bi kofar dakin da harara kamar shine tsaye a wajen.
Ba'a jima ba sai gashi ya dawo da Muhaaseen, karan kukanta da naji ne yasa na dan dawo cikin duniyar, daga fari da kamar ba zan tashi ba, naga dai babu laifinta a ciki. Na mike tsaye ina layi da jan kafa na bude kofar dakin, nayi tsaye kyam tare da mika mishi hannu, naki matsawa gefe balle ya samu damar shigowa.
Yana miko min ita na karbeta tare da kokarin maida kofar in rufe, yayi saurin sanya kafarshi daya ya tare ni, "baby please...".
Ban jira ya karasa ba na katse shi da nawa warning din, "don't!".

Babu musu ya janye kafarshi, na maida kofar na rufe garam, da ba don Allah yasa ya matsa da wuri ba da babu abinda zai hana in buga kofar nan a fuskarshi. Too bad, abinda naso ya faru kenan, babu abinda nake tunani a lokacin sai gwara in saba mishi kamanni in gani ko wadda zai aura din zata cigaba da son shi a hakan. Juyawa nayi zuwa cikin dakin na zauna a gefen gado.

Tunani na farko daya fara zuwar min shine asubahi ta farko in kama hanya in bar mishi gidan, in yaso sai ya dauko wadda yake so din ya ajiye a gidan nashi, daga baya dai naga cewa wannan gurguwar shawara ce, idan ma na tashi ina zan tafi? Gida dai nasan ko na sha giyar wake, Baba ba zai barni in zauna ba, in ma ce mishi me? Gashua kuwa... Bana ma sako ta cikin lissafi. Nasan ko numfashi ba zan gama ajiyewa ba zan ganni na dawo Abuja.

Tunda nayi sallar asubahi, na koma na kwanta. Duk da dan banzan barcin daya cika min ido, amma na kasa komawa barci. Ta yaya ma zan iya barci a cikin wannan halin?. Hawaye ne masu dan karen zafi da daci suke min zarya a kumatu. Rabin filon da nayi matashin kai dashi ya jike da lemar hawayena.

Wani sashe na can kasan zuciyata kuwa yana fada min I'm just being a hypocrite.
Bai taba fada ba, amma can wani bangare na tunani na yana fada min cewa ba zan taba zama ni kadai a cikin gidan Yaya ba, na sani. Shi yasa na kasa zama comfortable, na kasa sakin jiki balle har in saba da zama ni daya din, amma me yasa duk da hakan, zafin da nake ji a yanzu ya wuce misali?.

Har gari yayi haske, rana ta fito, ban motsa daga inda nake ba, ganin barcin ba zai yiwu ba yanzu yasa na tashi. Sai dana fara shirya Muhaaseen data tashi sannan nima na shirya cikin uniform dina.
Na nadeta cikin shawul mai taushi, na dauki abubuwan da zan bukata na bude kofar dakin na fita.
A falo na kwantar da ita tare da sauran kayan hannuna na shiga kicin. Duk da bana jin yunwa, amma kuma I can't find it in me to starve my husband, ba ma zan ji dadi ba idan ban mishi girkin ba. Don haka na kunna gas. Ganin cewa lokaci ya riga ya

50 / 52