AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   26 / 52

75K to 78K   out of 155.4K words

murmushi na yake, ba ita bace ta farko ba, ba kuma ba yau aka fara tarana da magana makamanciyar wannan ba, duk dai akan Dr. Na Abba. Cikin sati biyun da suka wuce, a kalla mutane fiye da shida, ciki har da Doctors da matrons, sunyi min magana ko ince sun buga min gargadi game da tarayya ta da Dr. Na Abba. Sai dai wani abu da basu sani ba shine, ni dai ba son shi nake yi ba. Ban kuma taba considering din maganar shi ba a cikin raina koda wasa. Saboda haka ni a ganina bata yawun bakinsu ne kawai suke yi, da kuma bata lokaci. Sai dai ban taba fada musu hakan ba, illa iyaka kawai duk abinda suka ce in tsaya in saurara, idan suka gama in musu godiya a wuce wurin.

Yanzu ma abinda na yiwa Aisha kenan, na mata godiya tare da tabbatar mata da cewa zan kiyaye kamar yadda ta bukata. Tace tayi farinciki da fahimtarta da nayi muka yi sallama da ita lokacin da muka shiga hostel, na haye sama ita kuma ta wuce sama dakinta.

Na saka key na bude dakin, kasancewar yau juma'ah, Esther ta tafi weekend, nasan cewa ni kadai zan dinga kwana a dakin daga yau har zuwa ranar sunday.
Na cire kayan jikina na rataye a jikin kusar da muke rataye kayanmu, na saka riga da wando cotton, na barci. Ba sallah nake yi ba, saboda haka lafiyar katifa kawai na bi na kwanta. Na janyo wayata na kunna, na hau chatting, bugs games, kallo, jin wakoki, har kokarin yin reviewing din project work dina dana kammala nayi, amma babu abinda ya dauke hankalina daga kan abu dayan nan da nake ta gujewa; Bilal Al-Qaseem.

Na rasa abinda zan yi akan mutumin nan, Allah ya gani, nayi iyakar kokarina, amma a banza. Gabadaya duk wata idea da tunanin yadda zan yakice duk wasu feelings da nake ji game dashi, na rasa. Duk wata hanya da zan bi, na bi. Amma a banza.
Kullum ta Allah ji nake kamar kara min so, bege, da kaunarshi a cikin raina ake yi. Na rasa kalar wannan masifar.
Wadannan yan lokutan, lokuta ne masu tsananin wahala da ban taba fuskantar irinsu a cikin rayuwata ba. Saboda haka ne na rasa yadda zan tunkari wannan al'amari.
Yaya Bilal ya zamo wata gagarumar wuta da take ci ganga-ganga a cikin raina, amma na rasa kalar ruwan da zai kashe min wannan wuta. Na kuma rasa yadda zanyi, saboda a kullum wannan wuta kara ruruwa take yi a cikin raina, tana kuma kona ni fiye da tunanina. Tana azabtar dani.

Yau dai kwanaki kusan goma sha uku rabon da inyi waya da Yaya Bilal. Tun washegarin ranar da yazo ya turke ni, ya kira ni. Lokacin muna cikin yin wayar, I snapped. Ban san lokacin dana mishi tsawa ba. Yana magana ne akan da gaske yana son aurena tsakaninshi da Allah, ya dage akan ba zai hada mu waje daya dasu ba, zai min nawa gidan daban. Ban san abinda ya shiga kaina ba a lokacin, su kansu kalmomin dana furta ban san na fade su ba sai bayan da suka fita daga bakina, nace "Wai ana dole ne? Ko kuwa ance maka ban san ciwon kaina ba? Dole ne? Ka kyaleni don Allah, nace maka bana son ka!!".
Nayi shiru ina sauke ajiyar numfashi kamar wata kumurcin macijiya.

Yaya Bilal shiru yayi a lokacin, kusan mintuna biyu tsakanin ni da shi babu wanda yayi magana. Sai sautin saukar numfashinmu dake tashi kawai. Daga baya ma sai ya kashe wayar shi, bai ce komi ba.
Daga wannan rana bai sake kirana ba, ban sake ganinshi ba.

Daga farko cewa nayi tafi nono fari tas. Sai dai me! Ba'a cinye kwararan kwanaki biyu ba, jikina yayi sanyi da jin yanayin shirun da yayi. Ban san me yasa na damu ba. Haka zan saka wayata a gaba ina kallo sau tari, ina contemplating din in kira shi ko kuma in kyale shi. Komi da yake faruwa a lokacin sabo ne a gareni, wanda ban taba experiencing dinshi ba a tsawon rayuwata. Ko rabuwar mu da Umar, ban ji kwatankwacin abinda nake ji a halin yanzu ba. Duba kuma da tsawon lokutan da muka dauka tare da shi, da kuma wanda muka dauka da Yaya Bilal, abin mamaki ne.

A kwanaki na hudu sai gani kunshe akan katifata cikin dare ina shakar kuka na fitar hankali. Kamar wadda aka sanarwa da wani babban jigo nata ya bar duniya. A lokacin kukan shine kadai abinda nake gani mafita ce mai kyau. Bayan nan barci ya kwasheni, wanda washegari na tashi da ciwon kai mai zafi da kumburarriyar fuska. Tun daga wannan ranar har yau ban daina yin wannan ciwon kan ba.

Janan, dama duk wani wanda ya sanni, ya san irin natural cheery behavior dina, yasan cewa wadannan yan kwanakin ba lafiya ta lau ba. Duk wanda muka hadu dashi sai ya tambayeni, lafiya?. Tun ina murmushi ina basar da maganar, har na gaji, idan ma an tambayeni sai dai kawai in kalli mutum blankly ko kuma kawai in basar in ki amsa tambayar, yaudarar kaina kawai nake yi, ba lafiyata lau ba. Ta yaya ma zan zauna lafiya bayan na ki ba zuciyata abinda take muradi?.

Yau Janan ta gayyaceni zuwa Kaduna mu yi weekend a can, sai dai kai tsaye nace mata ba zan je ba. Tunanina daya, idan fa naje muka hadu da Yaya Bilal acan? Me zan yi, ko kuma me zan ce mishi? Ita kanta Ummah ban san da wani ido zan kalleta ba idan naje, don haka duk da ina son zuwa, haka nan nace mata taje ni ina da abubuwan yi. To itama bata matsa ba, tace to, muka yi sallama ta tafi.

Itama na kula tun maganar nan da muka yi da ita ranar da Yaya Bilal zai zo, bata kara tado min zancen ba. Amma kuma gabadaya sai nake ganinta kamar ba Janan dita ba, kamar ta canza. Duk da bata fito kai tsaye ta nuna min wata canjin fuska ba ko wani abu, amma she just seems very distant.

Shi yasa nake jin kamar an dauko duk wani nauyi da damuwa ta duniya an dora min. Duk duniya, Janan ita kadai ce abokiyar shawarata. Kafin in nemi Kulsum ko Yaya Mudatthir ko Fatsu da suke manyan abokan shawarata, da wata shawara, Janan nake fara nema. Mu zamu kashe mu binne a tsakaninmu babu wanda ya sani balle yaji labari, sai idan tayi wari ne a mafiya lokuta suke ji.
Yanzu kuwa da babu ita, sai naji kamar komi ya hargitse min.

Nasan babu ta yadda za ayi in nemeta da shawara game da dan uwanta, bayan duk wasu abubuwa da maganganun da nayi game dashi. Nasan ranar na bata haushi ba karami ba, amma kuma ai gaskiyata na fada mata ba wani abu ba. A tunanina zata fahimceni, nayi zaton zata fahimci inda na saka gaba. Sai dai abinda na manta shine, dan uwa, dan uwa ne. Yaya Bilal dan uwan Janan ne, hakan yana nufin cewa ko a halin runtsi da wuya, zata iya zabar Yaya Bilal da gudu ta barni. Balle wa zai juri yaji kalmar rashin so zuwa ga Yayanshi da yake matukar so da girmamawa na fita daga bakin abokinshi? Babu.
Shi yasa na fahimceta, ban kuma ji haushinta ba. Shi yasa nima ban kara tada mata maganar ba, kunya ma ba zata barni ba. To wai ma ince mata me? 'Ni fa tunanin Yayanki ya ki barin zuciyata, kuma lokaci na karshe da muka yi waya dashi na zabga mishi rashin mutuncin da bai cancanta ba, shi yasa bai sake bibiyar rayuwata ba har yanzu, me kike tunanin yakamata inyi yanzu!', yeah, da alamu na fara rasa alkiblata ma ni yanzu.

Tun wannan kwanciyar da nayi, ban motsa ba. Sai da Janan ta kira ni, lokacin har duhun dare ya fara shigowa sannan na motsa. Wuyana ya amsa da ciwo saboda kwanciyar da nayi a gefe daya na tsawon lokaci ba tare da na motsa ba, haka nan ina yamutsa fuska na dauki wayar muka gaisa. Ta sanar dani isarta gida kenan, na mata sannu da zuwa tare da sakon ta gaida su Ummah.

Muna cikin maganar na jiyo sautin muryar Yaya a can background din wayar, kamar ma dariya yake yi lokacin. Naji kamar anyi freezing din komi da kowa a lokacin banda ni dashi, muryar Janan ta dauke kamar bata wajen, babu abinda nake ji a cikin kunnena a lokacin sai sautin tattausar dariyar Yaya Bilal da take tashi a lokacin ina jinta kamar busar sarewa saboda yadda take tashi very deep, very soothing.

Ban san dalilin da yasa naji kwalla mai zafi ta ciko min idanu ba, amma zata iya yiwuwa saboda tsananin dadi da salamar da naji sun sauka a cikin zuciayata ne a lokacin, ban taba tunanin zan ji dadin jin muryar wata halitta a doron kasa bayan dogon lokaci da muka dauka ba tare da mun hadu ko mun ji muryar juna kamar yadda naji dadin jin muryar Yaya Bilal yanzu ba, ban taba ba.

Allah ne ya bani ikon dawowa cikin hayyacina kafin Janan ta fahimci wani abu, ko kuwa ta fahimtar kyaleni kawai tayi? Koma dai menene ban damu ba a lokacin, damuwata daya a lokacin inyi gaggawar katse kiran wannan kafin jin muryar Yaya ta sanya ni yin abinda ban shirya yi ba, ni da nake gudunshi tun karfina, in kare da making fool out of myself.
Don haka nayi gaggawar yin sallama da Janan, tana tambayar lafiya? Ina lalubo dalilin da nasan ko dan jariri haihuwar yau ba zai yi convincing ba na jefa mata, na kuma kashe wayar ba tare dana jira abinda zata ce ba.

Lokacin dana koma kan katifa na kwanta, idanu a lumshe, hannu daya dafe da gefen kaina da yake bugawa, zuciyata da wani irin nauyi kamar an dauki wani gungumemen dutse an aza mata, babu abinda yake cikin raina sai tunanin azabar bata isa ba haka ba? Anya, ba zan nemawa zuciyata sanyi ba??!.







~Am really, very, very sorry. Please ku yi maneji da wannan, in shaa Allah gobe zaku samu dogon feji.













*☆⋆27⋆☆*





Ranar Lahdi a cikin makaranta na yini. Tun wajen karfe goma sha daya na safe na tafi wajen Aylah, tsohuwar room mate dina wadda muka zauna da ita last year. A wajenta na yini, muka sha hirar yaushe gamo da ita. Da yammaci kuma na tafi wanke kaina saloon din cikin makaranta.
Tashin hankalin dana shiga cikin yan kwanakin nan, ba muhimman al'amura kadai na banzatar ba, har ma da kananan irin wanke kai da yanke farce na manta. Ban ankara ba sai da naji kaina yana masifar tashi, sannan.

Da yake akwai wata mata dana saba zuwa wajenta tun ma muna cikin makaranta, nasan duk da cewa yau Lahdi ce tana nan saboda musulma ce ita. Don haka kai tsaye na wuce shagonta. Abinda naci karo dashi ne a gabana daga shiga cikin shagon, ban shiryawa ba.

Adi, Raheemah da Salamah a zaune akan kujerun jira da aka tanada a shagon, yayin da ake wa Adi karin gashin kanti a kanta. Muka tsaya muka danyi kallon-kallo dasu, kafin muka kauda kanmu mu duka, babu wanda ya nuna alamun yasan wani. Na dai musu sannu, nima kuma na samu waje can gefensu na zauna.
Rabon da in gansu su dukansu, tun azumin farko da naje gidansu, gashi yanzu har muna tunkarar watan Zhul-Hijja nan da yan kwanaki.

Ina nan zaune ina wasa da wayata kawai, ina sauraren hirar da suke tayi da yake mu kadai ne a cikin shagon. Tsantsar gulma ce suke yi, wadda nafi kyautata zaton akan Haleemo ce, babu kunya balle tsoron Allah. Wani karin abin haushin shine, Raheemah tana fita domin ta dauki kiran da aka yi mata a waya, suka ajiye hirar Haleemo gefe suka dasa tata. Na girgiza kaina cike da takaicin halayya irin tasu, ku a tsakaninku kuna a matsayin yan uwa babu aminci da amana, ina ga wadanda ba yan uwansu ba kuma?.
Kafin kace me, naji na kosa da zama wajen, da ba don na riga na shigo wajen ba da wallahi baya zanyi.

Allah ya taimaka ba'a jima ba wata daga cikin yan aikin wajen tazo ta kama kaina. Ta tambayeni retouching zanyi ko kuma wankewa kawai? Nace mata wankewa, don ni koda wasa ban taba sanyawa kaina relaxer ba. Yanayin natural santsi da laushin shi yafi yi min.
Na cire gyalena na ajiye a gefe, muka koma can gefe inda ta wanke min shi tas, muka koma tayi drying. Tana gama gyarawa, na sallameta na kara gaba na barsu acan.

Ina fita na sake cin karo da Haleemo, wani mutum daga ganinshi babba ne ya sauketa a mota, itama dai kallon-kallon muka yi, na tabe mata baki na wucewa ta.
Sai da nayi sallar magriba anan sannan na koma cikin asibiti.


*


Washegari da safe bayan duk mum gama ayyukan da suka kamata muyi a cikin ward, su dressing, bada magungunan yara majinyata da sauransu dai, duk muna zaune a nurses station. A yanzu wani yaro da ake yiwa blood transfusion muke monitoring dinshi duk bayan mintuna sha biyar, don haka muke zaune kusa da wajen.

Wasu matrons ne su biyu daga can gefenmu, suna ta zuba hirarsu. Da alama daya daga cikinsu ce aka yiwa aure, yanzu haka tana kan yin hutun amarcinta ne.

Sister Mairo ce take cewa "... Ai ina gaya miki, daga zuwanta sai ga mata a kicin washegari tana girka abinci, ba fa nata ita kadai ba, wai har uwargidan da 'ya'yanta saboda uwargidan ta tashi da ciwon ciki. Nace to a haka za'a ci amarcin ne? Me zata ji, me zata karas? Allah na tuba duk wanda bai ji dadin kwanakin nan bakwai na aure ba, ai bai ji dadin amarci ba!".

Daya sister din da ban san sunanta ba ta kwashe da dariya, tace "maganinta kenan ai. Nan muka zo, wace irin nasiha ce ba'a mata ba akan Alhaji Mati? Amma ita ta nace ta kekashe kasa, wai mutum mai mata ko wanda ya taba yin aure is more responsible, waye da waye, gashi nan ai tun ba'a je ko'ina ba, zata zama yar bauta. Ai ni wallahi inaa, Allah ya tsare ni wallahi. Ko a lokacin da Abban su Humairah yake ihun mata biyu zai aura ban ko daga ido na kalleshi ba balle in wani daga jijiyar wuyana, abu daya na sani koma mata nawa dai zai aura, anan zasu zo su sameni dai. Sai na gama tsintar abinda zan tsinta, na gama morewa mijina yadda naso sannan in bar mata sauran. No biggie!". Suka sake sakin dariya.

Ina kallon yadda Janan take watso min wani irin kallo daga can kasan idanuna. Ban san abinda take sakawa ba a cikin ranta, bana kuma fatan in sani. Don haka nayi shiru, kunnuwana duka biyun akan hirarrakin da su sister Mairo suke yi, wanda yawancin hirar akan ire-iren abubuwan da suke yawo ne a cikin raina.
Har dai lokacin da zamu sake duba yaron nan yayi, muka dauki abubuwan da zamu bukata ni da Janan muka je muka duba shi tare da rubuta cigaban da aka samu game dashi, muka fito.

Muna fitowa, muka ci karo da Dr. Na Abba, ya ja ya dakata yana kallonmu cikin murmushi, "hey, 'yanmata!".

Ni da Janan muka maida mishi martanin murmushin tare da gaida shi ya amsa. Janan ta dan yi gaba kadan, ni kuma na dan dakata haka nan muka gaisa. Bamu ja hirar da tsayi ba, saboda yace yana da patients amma yayi min alkawarin sake zagayowa zuwa anjima, nace mishi babu damuwa. Ya wuce, ni kuma na daga kafa na karasa wajen Janan muka cigaba da tafiya zuwa wajen da muke zaune.
Zuwa lokacin da muka koma, su Sister Mairo sun canza hirar da suke yi zuwa ta sana'o'in hannu.

Muna sake komawa wajen yaron a karo na hudu, muka tarar an gama mishi transfusion din. Saboda haka bayan munyi handling din bayanan yaron wajen likitan daya duba shi, ni da Janan muka wuce masallaci domin raka Janan tayi sallar azuhur.

Bayan tayi sallar, muna kan hanyar dawowa, Janan ta kalleni, tace "na yi zaton zaki sayi wani abu ki ci tunda ba azumi kike yi ba yau?".
Tunda muka fito waje sai lokacin tayi min magana. Na girgiza mata kai a sanyaye, nace "bana jin yunwa!".

Daidai lokacin mun je wani dogon corridor, Janan taja ta tsaya tana fuskanta ta. Tace "kada ki ce min rashin son auren Yaya da kike yi, yana da nasaba da maganganun da su sister Mairo suka dinga yi dazu?". Na zuba mata idanu kawai ina kallonta.

Tace "Na'ilah, haba don Allah! Wa yace miki rayuwa zata tafi a haka ne? Da dai nayi shiru in ga iyaka gudun ruwanki ne, amma da alamun baki da niyar tsayawa a matsaya daya, don haka na gaji da kallonki haka nan. Duk kin bi kin kwarzabi kanki Na'ilah, kin hana kan ki sukuni, kin hana kanki kwanciyar hankali, haka ake yi dama? Wai a kanki ne mai mata ya fara neman auren budurwa ne? Shi Yaya Bilal din ba mutum bane? Mutum ne shi, guda dayan shi sukutum. Amma ke kin hana kanki kwanciyar hankali, kin hana na kusa dake samun nasu kwanciyar hankalin saboda wani dalili naki mara fa'ida!". Tayi shiru tana ajiye numfashi. Har yanzu ban ce mata komi ba, ban ma yi yunkurin tanka mata ba.

Tayi kwafa, "to naji. Ina ce kin ce baki son Yayan? Kin ce ya kyale ki? Ba ya kyale ki din ba? To kuma menene na sanya kanki cikin damuwa? So kike yi ya dinga bin ki duk inda zaki je, kina wulakanta shi Na'ilah? Meye haka kike yi wai?".

Nan ma na sake yin shiru, haka kawai naji kwalla ta ciko min idanu, na sadda kaina kasa ina sauraronta tana zuba bayanai. Ni kaina a halin da ake ciki yanzu, ban san me nake tunani ba, ban kuma san me nake so ba. Ina

26 / 52