Author : Jeedderh Lawals Category : New Hausa Novels 2026
itama".
Sai tayi kus, tana gunguni can kasan makoshinta.
Yace "shikenan babu wani mai magana a cikinku kuma?".
Jin munyi shiru yasa ya gyada kai, ya rufe mana taro da addu'a.
Ya mike tsaye yana kallonmu mu duka, yana cewa, "don haka sai ku fara shiri. Ki tashi ki koma sashen ki, ke kuma zo in maida ki gidanki".
Ya fara tafiya, Ameerah ta tashi ta take mishi baya. Nima tashi nayi sadaf-sadaf na bi bayansu, muka bar Raheemah har yanzu a zaune a inda take babu alamun zata motsa.
Muna fita suka wuce wajen gareji, ni kuma na nufi sashena.
Janan bata nan lokacin dana koma dakin. Har na shiga bandaki na watsa ruwa, na fito na shirya cikin kayan barci, ban ji motsinta ba.
Na dauki waya na kirata tare da tambayar inda take, tace "makwanci mana".
Nace "ban gane ba, nayi zaton tare zamu kwana dake?".
Tace "rufa min asiri mana, in koma wajen Ummah na a yadda nake. Kinga, yanzu naji dawowar angonki, ki dauki jikinki ki tafi kije ki taro shi sai da safe".
Ta kashe wayar ba tare data bari nace wani abu. Na bi wayar da kallo, kafin na ajiyeta a gefen gado.
Shiru ina zaune ni kadai, ban ma san zaman me nake yi ba, daga karshe dai na fita na kaso wutar falo da kayan kallo, na koma na lalubi gefen gado na kwanta tare da kashe wutar dakin. Addu'ar kwanciya barci nayi na shafa a jikina, na lumshe idanuna.
#F.W.A
*☆⋆36⋆☆*
Ina rufe idanuna, naji an turo kofar dakin an sake kunna wutar dana kashe yanzu. Na bude idanuna da suka fara yin nauyi saboda gajiya da barci, na saukesu a bakin kofa.
Yaya Bilal yayi tsaye a bakin kofar hannunshi harde a kirji, da alama har ya dawo daga maida Anty Ameerah din. Kayan jikinshi ne na dazu har yanzu bai cire su ba, casual outpit ne, shigar da ban saba gani a jikinshi ba. Yawanci daga suits sai manyan kaya, riga da wando na shadda, watarana ma ko hula baya dorawa.
Muka tsaya muna kallon-kallo ni dashi, kafin ya maida kofar dakin ya rufe. Kai tsaye bandakina ya wuce, ina nan a kwance a inda ya barni, ina jin motsin ruwa dai. Ba'a jima ba, ya fito daga bandakin yana gyara links din hannun rigar shi. Na bi shi da kallo.
Sai daya kawo tsakiyar dakin sannan ya kalleni, "kin yi sallar isha'i?".
Wani kwarjinin shi ya cika min idanu, na kasa daga idanuna gabadaya in kalli tsakiyar nashi idanun. Kai na gyada mishi a hankali.
Ya sake cewa "kina da alwala har yanzu?".
Na sake girgiza mishi kai, alamun a'ah.
Ya tsaya yana kallona ba tare da yace komi ba, kusan tsayin minti daya, har sai dana kai ga dan dago kaina na kalleshi. Wani irin abu a tattare dashi dana kasa fahimtar koma menene, bugun zuciyata naji ya dauka da sauri da kuma karfi.
A hankali ya juya zuwa wajen da muke yin sallah, da alama dama an tanadi wurin ne saboda sallah.
Yace "ki tashi kiyo alwalar ko? Muyi sallah".
Ni wannan sabon attitude daya kirkiro na kasa fahimtar shi, kodayake ai dama can ba wani sanin shi nayi ba sosai, zata iya yiwuwa halin shi kenan. Na daga kafada tare da saukowa daga kan gadon. Kayan barcin dana saka a jikina dogon wando ne da riga karama top, wadda bata kama jikina ba. Na shiga bandakin na daura alwala kamar yadda ya umarceni.
Lokacin dana fito daga bandakin, har ya shimfida abin sallah. Na bude wardrobe na ciro doguwar hijabi na saka. Na karasa wajen da yake.
Ya tada sallah, na bi bayanshi. Raka'ah hudu muka yi dogaye, muka dora da shafa'i da wutiri.
Bayan mun gama, ya juyo ya dafa kaina, yayi addu'o'in da annabi S.A.W ya umarcemu da mu yi a lokacin da muka yi sabon aure. Neman alkhairan juna, da kuma neman tsari daga sharrin juna.
Bayan nan juyawa yayi, yaci gaba da janyo wasu addu'o'in, ni kuma na zauna muk'u a bayanshi, ban ma san kalar addu'ar da nake yi a cikin raina ba har ya gama. Ya tashi tsaye tare da linke abin sallar, nima na mike na nade wanda nayi amfani dashi na ajiye a inda muke ajiyewa.
Nayi tsaye anan kaina a kasa, ban san abinda yakamata inyi ba daga nan, it felt very awkward. Subhanallah! Haka kowace mace take ji idan aka barta da mijinta su kadai a dakinta, ko kuwa ni kadai ce nake jin haka?.
Shi kuwa gogan da alama ko a jikinshi, kamar baya jin komi, idan ma yana ji ba karamin kokari yayi ba wajen murje shi.
Yace "kin ci abinci? Kina jin yunwa?".
Ai ko ina jin yunwa bana tunanin wani abu zai iya shiga cikin cikina bayan numfashi, yadda nake jin shi dinnan yayi knotting da nerves, fargaba da rashin sanin abin yi. Na sake girgiza mishi kai. Ina tunanin dai na zama kurma yanzu, ko kuwa?.
Bai sake cewa komi ba, ya juya ya bar dakin. Na sauke numfashin da ban san na rike ba. Na jima a tsaye sosai, kafin na cire hijabin jikina na linke na maida inda take, na sake komawa na kwanta. Sai dai wannan karon ban kashe wutar dakin ba tunda bani da tabbacin zai dawo ko ba zai dawo ba.
Zuwa can, sai gashi ya sake dawowa. Wannan karon ya canza kayan jikinshi zuwa jallabiya fara kal, hannunshi kuma dauke da leda babba. Ya ajiye a tsakiyar dakin ya sake fita, can ya dawo da plates da kofuna guda biyu, ya janyo karamin carpet dake jingine acan gefe ya shimfida ya zauna.
Ya fara fitar da kayan ciki, tatacciyar madarar hollandia da gasasshiyar k'afaffiyar kaza. Kamshinta ya hade dakin gabadaya, cikina ya fara juyawa saboda yunwa, amma na kasa motsawa. Ina kallo yayi amfani da wuka karama ya yanka kazar ya zuba a cikin plate, ya kuma tsiyaya madarar a cikin kofunan biyu.
Sai daya gama, ya dago kanshi ya kalleni. Nayi sauri na kauda kaina daga kallonshi da nake yi.
Yace "ba zaki ci bane?".
Nayi shiru ina kallonshi kamar ba zan ce komi ba. Bai sake ce min uffan ba, yayi bismillah ya fara cin abin shi.
Da naga uwar bari, sai na silalo daga kan gadon a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a jiki, na lallaba na zauna a gefenshi.
Ina kallon murmushin daya saki a hankali, na turo baki gaba. Ya turo min plate din kusa dani da kofi daya. Kaina a kasa na fara ci bayan nayi bismillah.
Shirun da duk muka yi ni dashi, babu mai motsin kirki a cikinmu shi ya cika min ciki, sai kuwa taraddadi daya kara cika min ciki.
Na kara tsiyayar madarar dake ajiye a gefenmu bayan na shanye wadda ya zuba mana. Ina kallonshi yana cin namanshi hankalinshi kwance, har ya gama. Lokacin nima na shanye madarar dana tsiyaya.
Ya zari tissue ya goge hannunshi, tare da kokarin fara hada kan kayan. Da sauri na riga shi fara daukar kayan, nace "uhm, ka bari zan hada".
Bai ce komi ba, ya dai sakar min kayan, ya tashi ya nufi hanyar bathroom dina. Na bishi da kallo cikin sanyin jiki, haka kawai naji ina tausayawa kaina. Haka tawa rayuwar auren zata kasance kenan?.
Na dauki kayan dai gabadaya na fita zuwa kicin dasu. Na wanke plates da kofunan, sauran kazar da bamu kai ga cinyewa ba, na nade a foil paper na saka cikin fridge. Sannan na koma dakin.
Wayyo faduwar gaba! Zuciyata tayi wani irin bugawa lokacin dana ganshi kwance dai-daya akan gadona, ya dago daga kan wayarshi ya kalleni da alama cikin mamaki ganin yadda naja tunga na tsaya kyam, kamar wata wadda taga wani abin tsoro. Sai dai bai ce komi ba. Ni wannan silent treatment da yake bani ya fara bani tsoro kuma maimakon haushi.
A hankali ya kauda kanshi ya maida kan wayarshi kamar ma bai ganni ba. Ni kuwa naci gaba da kafewa a tsaye a wajen. A kalla nafi minti goma a wajen har sai da naji kafafuna sun kage. Har ya gama latsa wayarshi, ya kashe hasken tare da ajiye wayar a kan bedside drawer.
Ya kalleni yace "idan kin gama, ki kashe wutar dakin". Daga haka ya juya min baya.
Na kara wasu mintunan a tsaye ina kallon bayanshi, kafin daga karshe na yanke shawarar wannan tsayuwar da nake yi anan babu abinda zata kare ni dashi, ga barci da gajiya da suka dabaibaye ni. Idan kuma ba so nake yi inyi barci a tsaye ba, ina bukatar wajen da zan kwantar da hakarkarina.
Na lallaba na kashe wutar dakin, a hankali, cikin sanda na taka zuwa kan gadon kamar mai tsoron a kamata, na kwanta a gefen gadon nima na juya mishi baya. Na sake yin addu'ar kwanciya barci tare da lumshe idanuna. Sai dai wannan karon babu alamun yin barci a cikin idanuna, zuciyata cike take da tsoron abinda zai je ya dawo. Ban san lokacin da barci ya kwashe ni ba. Cikin dare na farka na jini kwance luf akan kirjin Yaya, ban san ko ni ce na gangara wajen da yake ba ko kuma shine ya gangaro inda nake ba, ban kuma damu da in janye jikina ba. Sai ma kara lafewa da nayi, saboda a lokacin ji nayi kamar duk duniya babu abinda ya kai kirjin Yaya Bilal dadin kwanciya sai dumi.
Lokacin dana tashi, ni kadai ce kwance a tsakiyar gadon. Sai kuwa tarin fululluka a gefena da ban san yadda aka yi suka zo wajen ba.
Dan hasken da dakin yayi da kuma motsi da naji a bandaki ya tabbatar min da cewa Yaya yana can. Na juya na kalli agogo, karfe biyar babu mintuna goma, asubahi ta riga tayi kenan. Daidai lokacin da naji karan bude kofar bandaki ana fitowa, nayi sauri na koma na kwanta kamar mai barci.
Ina kallon Yaya yazo ya tsaya a gefen inda nake yana kallona ta idanuna dana dan lumshe.
Ya jima a tsaye yana kallona, har dai naji kallon ya isa haka nan, na danyi motsi. Da sauri naga ya ja da baya, na bude idanuna a hankali na sauke su a kanshi.
Ya wani yi kici-kicin da fuska har yaso ya bani dariya, kamar ba shine ya gama kare min kallo ba yanzun nan.
Yace "lokacin sallah yayi". Na gyada mishi kai tare da tashi zaune, shi kuma ya juya ya fita daga dakin.
Bayan ya maida kofar ya rufe, na sauka daga kan gadon ina yin mika, strangely feeling good and relaxed. Kamar wadda ta samu dadadden barcin data jima bata yi ba. Na shiga bandaki na dauro alwala na fito na tayar da sallah.
Ina nan a zaune har gari ya gama yin haske, Yaya Bilal bai dawo dakin ba. Wani barcin na sake komawa. Sai karfe tara na safe na tashi.
Wanka na fara yi, cikin kayana na fiddo wasu riga da wando na Pakistan na sanya. Na bade jikina tun daga kafa har kaina da turare. Show glass babba guda aka cika min da kayan kamshi iri-iri yan asali irin na mutanen Bare-bari, dama su ba baya ba. Kamshi mai dadi da sanyayar da zuciya. Na dauki gyalen na nada a kaina, na fita falo. Lokacin karfe goma na safe. Babu kowa a falon, kamar yadda naji babu hayaniya a cikin gidan.
Tunda na tashi cikina yake kiran yunwa, na duba kicin da dinning table ko Janan ta shigo da abinci lokacin da nake yin barci, naga wayam. Ina shirin juyawa in koma daki in dauko wayata in kirata, kofar dakin Yaya ta bude.
Ya fito, da alama shima wankan yayi. Ya sanya wandon jeans navy blue da farar rigar top wadda ta dan kama kirjinshi. Sai bada kamshi yake yi. Ya zauna akan kujera yana lalubar remote ya kunna talabijin.
Na duka har kasa na gaida shi, ya amsa yana wani fuskewa. Na girgiza kai a hankali, wannan basarwa ta Yaya Bilal na kasa gane kanta balle dalilinta.
Yace "miko min abinci".
Nayi shiru ina muzurai, ya kalleni cikin mamaki. "Abinci nace!".
Yadda yayi maganar cikin rashin alamun wasa, yasa naji jikina ya dauki rawa cike da tsoro, nace "ai.. uhm... Da naga ana kawowa kwana biyu sai banyi ba".
Ya dago ya kalleni sosai, "to ita wadda take yi girkin, tare aka kawo ku da ita ne ko kuma zata kare ne wajen girka miki abinci? Banda ma rashin tunani, a kawo ki gidan aurenki, ki zauna kina jiran wata ta dafa abinci ta kawo miki? Lalaci kenan ko kuma duk cikin rashin so ne!?".
Na daga kai da sauri, kuma cikin kaduwa na kalleshi. Shima kallona yake yi, fuskarshi babu alamun nadamar abinda ya fada. Sai a lokacin na fahimci dalilin hade fuskar da yake tayi. Naji wata kwalla ta cika min idanu, a hankali nayi kasa da nawa kan.
Na daga baki da kyar, nace "kayi hakuri... Bari in dafa maka yanzu". Na tashi cikin sanyin jiki, na shiga kicin.
Tsayawa nayi a tsakiyar kicin din ina share hawayen da suka fara zarya a fuskata, wace irin rayuwar aure ce haka muke yi ni da mijin aurena?. Sai dana dan nutsu, sannan na fara dube-dube ina neman abinda yakamata in dafa mishi mai sauki.
Da yake kicin din shake yake da kayan abinci kala-kala, sai na shiga store na dauko ledar cous-cous. Na bude fridge da yake shake da vegetables da abubuwan gwangwani, na ciro abubuwan da nake bukata. Fridges din guda biyu ne, daya na kayan miya, nama da sauransu, dayan kuma na ruwa da soft drinks.
Cikin sauri nayi vegetable sauce, na dafa cous-cous din, tare da hadawa da ruwan shayi.
Na zuba mishi komi, na dora akan tray na fita na kai mishi. Yana nan zaune a inda yake, na hada komi a gabanshi, na koma gefe na zauna.
Kasa ya sauko, ya dauki cokali zai fara ci, sai ya dakata ya kalli inda nake.
Yace "ba zaki ci ba ne ke?".
A hankali na girgiza mishi kai.
Yace "me kika ci?".
Ban ce komi ba, na sake girgiza mishi kai.
Yace "to matso maza ki sa hannu ki ci, bana son zama da yunwa".
Na matsa a hankali kusa dani, na dauki wani cokalin nima na ci. Wannan karon ma har muka gama babu wanda yayi magana a cikinmu, ya tashi ya kwashi wayoyin hannunshi daya ajiye a kan center table, yace min ya fita.
"Allah ya tsare", kadai na iya ce mishi. Yasa kai ya fita.
Bayan fitarshi na maida kayan kicin nazo na zauna ina kallo cikin rashin dadin rai. A haka Janan ta shigo ta sameni. Zuwanta ne ma ya dan sanya na saki jikina, muka shiga hira da ita. A bakinta ne naji ashe Yaya da kanshi ya cewa Anty Sarah kada ta kara turo mana da girki nan. Nayi kwafa a cikin raina, amma ban ce komi ba.
*
Yau ma ana yin sallar isha'i ta tsere sashen Anty Sarah. Ashe a can ta kwana jiya ma, wai Raheemah rufe mata kofa tayi. Na jinjina girman al'amarin, nace 'Allah ya kyauta', tace ameen.
Yau tun kafin in kwanta Yaya ya dawo. Na kai mishi abincin dana girka mishi, ya ci ya tashi ya tafi dakinshi, ni kuma na dauke kayan. Na koma daki nayi shirin barci, na kwanta.
Ina jin lokacin daya shigo dakin har ya kashe wuta, yazo ya hayo kan gadon ya kwanta shima, ban motsa ba.
Lokacin da naji ya matso zuwa tsakiya gadon, hannunshi yana ratsawa ta kan ruwan cikina, kanshi kwance akan kafadata, ji nayi kamar an tsayar da duk wani gudun jini a jikina. Nayi sak, hatta da numfashina sai daya tsaya cak.
Cikin wata irin murya, kamar ba ta Yaya Bilal din dana sani ba, yace "amarya ta!".
Naji wasu irin emotions a cikin raina kala-kala, iri-iri, har na rasa da wanne zan ji. Idanuna suka ciko da hawayen dana rasa dalilin su, murya a cushe, kamar zan fashe da kuka, nace "amaryar da ake fushi da ita?".
Ya sake janyo ni cikin jikinshi sosai kamar zai balla ni biyu, yace "to Na'ilah ya kike so inyi ne kam? Kiri-kiri fa haka kika fito kika nuna duk duniya baki da makiyi kamata, kika ki aurena, saboda tsabar rashin so ma har suma kika yi fa da kika ji labarin an daura miki aure dani ba wani ba. To ya kike son inyi? In dinga binki sawu da kafa, duk da rashin son da kika nuna min? Anya Na'ilah, anya baki so kanki da yawa ba kuwa?".
Na hadiye wani yawu daya tarar min a baki, nace "wa yace maka na tsane ka?".
Yace "ko baki fada ba Na'ilah, yadda kika badawa idanunki toka kika ki aurena kadai ya isa ya tabbatarwa da mutum cewa baki so na. Ba wannan ba, tunda abinda ya faru ya riga ya faru, me zai hana ba zamu bar abinda ya faru a bayanmu ba, mu fuskanci gaba? Mu fara rayuwar aurenmu ta hakika? Don in fada miki, aurena dake babu saki. Idan ma zaki hakura ne, ki hakura. Ba ki tunanin jan aji da yawo da hankalin ya isa haka?".
Na turo baki kamar yana ganina, "wa yace maka jan aji nake yi?".
Ya kara matsoni jikinshi, kanshi yana kara nutsewa a cikin gashin kaina, yana kara shakar daddadan kamshin da yake yi.
Muryarshi bata fita sosai saboda yadda ya gashin kaina ya rufe mishi baki da fuska, yace "nace miki rashin so, kin ce ba haka ba, shima jan ajin kin ce ba haka ba. To menene? Tsabar so ce, uhmm??!".
Na daga baki da niyar bashi amsa, hannunshi da yake kan ruwan cikina ya fara zana circles, jikina ya dauki rawa kamar ana kada min mazari, na rasa muryar maida mishi martani.
A hankali naji ya juyo dani, hannunshi daya yana shafa gefen fuskata zuwa bayan wuyana, kafin ya hade bakinmu waje guda. Na lumshe idanuna a hankali, savouring the moment.
Zuciyata tayi nauyi, tunanina yayi nisa, babu abinda nake ji kuma nake fahimta a lokacin sai Yaya Bilal kadai da abubuwan da yake min, da kuma abubuwan da suke haddasa min a