AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   42 / 52

123K to 126K   out of 155.4K words

gaba, "kuma shine baka fada min zaka zo ba?".

Ya janyo ni cikin jikinshi yana yar dariya, "kada fa kice zaki fara yi min rigima yanzu. Ganin mun gama muhimman abubuwan da suka kaimu, yasa na baro sauran a baya na taho. Na kasa jira har sai gobe kafin in ganki. Ya baby na, baya takura ki dai ko?". Na girgiza mishi kai.
Yace "yau baki leka asibiti bane? Naga kamar morning kike yi wannan satin ko?".

Nayi hamma tare da kara komawa cikin jikinshi na langwabe, shi kuwa ya kara rike ni, nace "sister Hanifa taga ina ta layi saboda barci, shine tace in taho gida kawai zata kula min da nawa aikin".

Ya shafa sumar kaina, "ta kyauta gaskiya, ki tuna min idan muka hadu da ita nan gaba in mata godiya sosai. Wai ina Ameerah ta shiga ne, ko barci take yi? Naji dama tana cewa kwana biyun nan ta cika yin barci".

Nayi shiru ina muzurai don ban san me ya kamata in ce mishi ba, bana so yaji mutuwar sarki a bakina. Ganin yadda nayi shiru ina kallonshi, yasa ya fara dube-dube kamar wanda yake neman wani abu.
"me ya faru ne? Ko bata jin dadi ne?".

Naga dai duk wani boye-boyena babu abinda zai sa ko ya hana, Ameerah dai bata gidan, Yaya kuma gashi nan a gidan, idan ma nace zan kareta zata iya karewa in kwana a ciki, tunda babu ranar dawowarta.

Nace "bata fada maka ranar da zata dawo bane?", Allah ya gani, banyi don in hada su ba, don dai babu yadda za ayi in kaucewa hakan shi yasa.

Yace "ban gane bata fada min ba, ina ta tafi, kuma yaushe?".
Na dago na kalleshi, haka kawai naji tausayinshi ya ratsa ni. Ban ga amfani, ko dalilin da zai sa haka kawai mata ta bar gidan aurenta ba tare da ta nemi izini daga mijin aurenta ba, akan wane dalili? Kodayake, rashin tsoron Allah yayi karanci a zukatan mutane a yanzu. Rayuwar auren an maidata kamar wata wasan yara, matan aure basa girmama mazajen aurensu. Gani suke yi kamar yan kananun abubuwa kamar tambayar miji zuwa anguwa wani kankanin abu ne. Bayan babbar magana ce, kuma babbar matsala wadda idan muka yi da wasa, zata iya kaimu wuta. Balle kuma, fita unguwa har ki kwana ki wuni a wani waje can daban? Shi mijinki yana can ya bude baki da hanci, yana tunanin ya baro ki a gida a zaune, cikin tsarewar bangon gidan aurenki, ba tare da yasan abinda yake faruwa ba. Ko tunanin yanayin rashin tsaro da wannan duniyar tamu take ciki bata yi, idan ace wata matsala ta samu, misali hatsari ko kidnapping Allah ya kiyaye, me zata ce mishi; me kuma zata cewa Allah?.

Nace "ai kamar tun ranar da ka tafi itama ta tafi, bata dawo ba har yanzu".

Rubutaccen mamaki ya zanu a fuskar Yaya, ba karami ba kuwa. Bai ce komi ba sai kai da ya girgiza, yace "ok!". Sai dai daga jin yadda yayi maganar kasan cewa ranshi yayi matukar baci.
Nima ban samu na iya cewa komi ba saboda bani da abin cewar, sai kawai na kara kwanciya a jikinshi. Muka cigaba da kallonmu ni dashi, babu wanda yake iya magana a cikinmu, sai sannu da yake yawan jefo min a duk lokacin da na motsa.

Sai da aka kira sallar La'asar sannan muka tashi, kafin ya fita ya umarceni da in sama mishi abinda zai ci kafin ya dawo. Bayan nayi sallah, na shiga kicin na dafa mishi abinci mai kyau, daya dawo muka ci tare. Shi ya dauko laptop dinshi ya fara aika bayanai akan ayyukan da yaje yi a Niamey, ni kuma na zauna a gefenshi.
Anan ne Maryam ta kira ni daga gida, mun jima muna hira da ita, har su Anty Alawiyya da su Kulsum sai da muka gaisa dasu. Tunda labarin cikin nan ya same su, kusan kullum sai munyi waya dasu, ko su ko Janan. Ummah ma da Yaya kusan kullum muke yin waya dasu, kullum maganarsu daya, yadda zan kula da kaina da dan cikina, abinda ya kamata in ci da wanda bai kamata in ci ba, kulawar da muke samu daga wajensu ni da abinda ke cikin cikina ma kadai ta isheni, balle kuma ta wajen uban gayya, Baban baby na.

Karfe shida ta dan gota na yamma, lokacin da muka ji an shigo cikin falon. Lokacin mun koma kasan carpet din falon, har yanzu Yaya yana fama da rubutu a laptop dinshi, ni kuma nayi matashin kai da cinyarshi. Ayaba ce a gefena ina barewa ina ci, shima idan na ci na kan kai wata bakinshi ya ci.

Ameerah ta shigo da waya sarkale a kunnenta tana amsa kira, hannunta mai rike da wayar rataye da jaka, dayan kuma yana jan karamin trolley.
"... Yanzun nan na shigo gida fa ko daki ban karasa ba. Idan na huta zan kirak...", ta kasa karasa maganar da zata yi sakamakon ganin Yaya zaune ya zuba mata idanunshi.

Bata san lokacin da wayar hannunta ta zame daga hannun nata ta fadi a tsakiyar dakin ba, tayi sak kamar wadda aka kafe da wani abu a wajen.
Da kyar sautin "baby....!!", ya fita daga bakinta. Daga ganinta kasan cewa ta rikice, ta kuma tsorata da ganin Yayan a gida.

Yaya yayi zaune very calm and collected, yana kallonta yadda kasan ranshi ba a bace yake ba. Ganin babu wanda yayi yunkurin ce mata kala, yasa ta durkusa ta dauki wayarta data fadi, ta tashi tsaye tana kallonmu fuska dauke da wadataccen murmushi kamar ba ita bace aka kure tayi satar hanya ba. Tace "baby... Banyi zaton cewa yau zaka dawo ba ai, ya hanya? Yaushe ka da...??".

Yaya yayi saurin katseta ta hanyar cewa, "daga ina kike?".

Ko kadan bata girgiza da tambayar daya jefo mata ba, tace "kasan cousin dina Mubeenah ko? Kanwar Mommy. To ita ce tazo ganin gida daga Switzerland, na fada maka ai ko?".

Yaya ya hade fuska iya hadewa, ban taba ganin zallan bacin ranshi irin na yau ba, ko lokacin da muke cikin je-ka-dawo kafin mu shirya kuwa.
Yace "zan kuma iya tuna abinda na fada miki a lokacin, ban yarda ki taka kafa ki bar nan gidan ba, ko ba haka na fada miki ba?".

Ta wani marairaice fuska kamar karamar yarinya, "amma Baby... Sai dana fada maka fa daddy ne yace inje mu gaisa da ita saboda mun jima bamu hadu ba. Kuma ma, kai da baka gidan, menene a ciki?".

Ran Yaya ya baci iyaka baci, ya tashi tsaye cike da matsanancin bacin rai, jikinshi har wata rawa yake yi, "akan meye zaki tsallake dokar dana kafa miki kamar wani sa'an wasanki, ko kuma wanda baki dauki maganar shi da mutunci ba, kodayake, dama yaushe kika taba girmama wani abu dana fada miki? Wai saboda Allah, ke nake aure ne ko kuma iyalan gidanku gabadaya?? Kwata-kwata an maida min rayuwar aure wasa, ni da matata, amma ban isa in zauna in gindaya mata sharadi ba tare da an san yadda aka yi, aka yi watsi da lamarin ba? Shin ni din ba mijinki bane? Idan ma baki sani bane, ki san cewa yanzu duk wata hidima da dawainiya da komi naki ya tashi daga hannun iyayenki, ya dawo hannuna. Baki da wani hurumin bin maganar mahaifinki ki tsallake tawa. Amma gabadayanku kun rufe idanunku, kuna abusing kalmar aure, saboda kun dauketa a ba a bakin komi bane ko me? Kin dauka rayuwar auren, abar wasa ce? Rashin sani ne yasa haka ko kuma rashin sanin yakamata??!".

Ameerah bata iya cewa komi ba saboda yadda taga ran nashi ya baci fiye da tunaninta.

Yaya yaci gaba da cewa, "na gaji da yadda kuke take min rayuwar aure haka nan. Ban isa dake ba, ban isa da komi naki ba. Saboda haka daga yau a gidannan, zaki zaba, umarnina ko kuma na mahaifinki? Idan har kin ce ba zaki bi umarnina ba, to tun kafin tafiya tayi nisa, ki koma inda kika fito. Idan kuma kin shirya yin zaman rayuwar aure kamar yadda yakamata, to daga yau sai yau, ban yarda ki taka kofar gida ba tare da kin nemi izinina ba Ameerah idan kuwa har hakan ta sake faruwa, duk abinda ya biyo baya, ki zargi kanki!. Zabi ya rage naki!".
Ya hada kan kayanshi ya wuce daki a fusace.

A hankali ta duka ta janyo akwatinta ta shigo cikin falon sosai, na mata sannu da zuwa, bata amsa ba, sai ma la'adar harara da nasha. Taja akwatinta ta wuce dakinta kamar tashin duniya, na bita da kallo cikin tabe baki. Meye laifina anan, ni da bani na kar zomon ba? Na sake tabe wani bakin.

Yaya bai fito ba sai da aka kira sallar magriba.
Kiri-kiri yaki cin abincin data dafa ranar, a gabanta ya kira wata hadaddiyar restaurant 'cloirassantz' daya saba yi mana odar abubuwan tande-tande, yayi placing order aka kawo mishi abinci, ya zauna yaci kayanshi ya wuce daki abinshi.

Washegari ina daki ina shirin fita ya leko dakin, na gaida shi. Yace min idan na dawo inyi girki, in kuma cigaba da yi har sai shi da kanshi yace min in ajiye. Ban iya cewa komi ba sai 'to', na kula hukuntata yake so yayi tun karfinshi.
Ban sanya bakina cikin fadansu ba, ko tambayarshi dalilinshi na damka min girki gabadaya ban yi ba.

Kwana biyu suna ta fadansu, fadan masoya hutu, ban san ta yadda ta samu ta shawo kanshi ba, naga dai sun koma sun dinke kamar tif da taya, nan ma ban ce komi ba, na damka mata girki taci gaba da yi.
Ya karbe motar hannunta yace ta maidata gida, ya kuma hanata yawan fita gatsar, dokoki sosai ya kafa mata, duk tace taji ta amince.
A haka Raheemah ta dawo muka cigaba da bugawa dai. Ta kawo mana souvenirs na bikin, ga hoton Haleemo nan da Umar ya sha uniform dinsu na sojoji radam a jikin komi, memo ne, jaka ce, calender ce, kai tarkace dai. Lokacin data bani, dariya nayi tare da musu fatan alkhairi na kai daki na ajiye. Ko tayi tsammanin haushi zan ji ko kishi??.



*


Cikin jikina yana ta tasawa cikin koshin lafiya, yanzu yana cikin satikan shi na goma sha daya.
Har yanzu muna cigaba da gwabzawa da matan Yaya, duk da cewa yanzu da Ameerah muke yi. Raheemah sam yanzu ba na ta tata, fada ne, bana biye mata.
Wata tsirfa data dauko ma sabuwa, haka zaka ganta a dakin Yaya ranar girkina tun da safe, ta kuma ci kwalliya ba ta wasa ba. Har magana sai da na yiwa Yaya akan haka, nace ya daina biye mata suna yin haka, suna shiga hakkin mai yin girki.
Amma maimakon yace wani abu, sai yayi dariya, wai "menene abin shiga hakki anan Baby? Mu da babu abinda muke yi sai hira kawai? Idan kika tafi yin girki, kadaici yana damuna, kinga tana taya ni dauke kadaicin".
Da naga dai bashi da niyar daukar mataki, sai na gyada kai nace "to babu laifi".

Da ranar girkinta ta zagayo, sai naci kwalliyata ta gani ta fada da safe, English wears mini skirt da wata vest, na gyara gashin kaina ranar ko hula ban saka ba, na yiwa dakin Yaya tsinke. Na samu gefen gado nayi daya kan daya, har tazo ta sameni anan, abin ya bata mamaki, amma bata yi magana ba.
Da dare ma da ya dawo haka ta faru, naje na musu zaune har dare ya tsala yadda ta saba yi min.
Zuwa karfe goma ta wani tashi tana mika, cibiyarta tana nunawa ta cikin half vest din data saka, tana wani fari da idanu da rangwada, tace "baby, muje mu kwanta ko?".

Yaya da yake shan dariyar hirar da nake mishi akan kiriniyar dasu Auwal suka sha lokacin da suna yara, ya kalleta yace "kiyi gaba, gani nan".
Ta turo baki cikin jin haushi, amma bata ce komi ba, ta shige uwar daka.
Muka kuwa cigaba da hirarmu, har sai da ta sake lekowa ta mishi magana, wai ai ita ta kasa yin barci saboda baya kusa da ita, lokacin karfe sha daya ta kusa.

Ina dariyar mugunta a ciki, nace "Yaya kaje ka kwanta mana, kasan fa gobe akwai aiki".
Yace "ke fa?".
Na girgiza kai, "bana jin barci, kaje ka kwanta abinka, idan na gama barcina zan je in kwanta. Sai da safe...", na dan juya ina kallon Ameerah da take tsaye a jikin kofa har lokacin, nace "sai da safe Anty Ameerah!".
Ta hadiye wani yawu da nafi kyautata zaton na takaici ne da bakin ciki tace "Allah ya tashe mu lafiya", ta juya cikin dakin. Yaya ya bani peck a kumatu tare da dukawa ya shafa cikina, sannan ya min sai da safe ya bi bayan matarshi. Na bishi da kallo ina murmushin mugunta. Matarshi tayi tsamnanin taci bulus ne? Ashe kuwa tana da sauran aiki a gabanta, domin kuwa ba'a buga irin wannan wasan da ni.

Washegari ma abinda ya faru kenan, hakan kuma yaci gaba da faruwa na wani dan lokaci.


Ranar Alhamis girki a hannuna yake. Tun da na dawo daga wajen aiki, nake shirya abincin dare. Dambun shinkafa nayi, mai kyau, na yanka hanta, carrots, kabeji, da sauran tarkacen veggies a ciki. Nayi sauce itama da na wadatata da su nama da kifi. Nayi lemun kankana da lemun zaki wanda na dan diga lemun tsami da zuma a ciki.
Lokacin dana gama girkin, yamma tayi. Don haka na bar miyar akan wuta domin ta karasa yi, na tafi dakina inyi wanka.
Ina cikin yin wankan naji dawowar Yaya daga wajen aiki, jin ina yin wanka yasa ya wuce dakinshi.

Daga bandakin na dauro alwala saboda lokacin sallah yayi. Na koma duba miyar, na ga har yanzu da sauran ruwa a cikinta, abin ya bani mamaki kwarai. Zan iya rantsewa akan cewa ruwan da na bari dazu bai kai haka yawa ba. Amma sai ban kawo komi a cikin raina ba, na kara rage wutar na koma daki domin inyi sallah.

Ina kan abin sallar, Yaya ya dawo daga masallaci, daga ganinshi kai tsaye dakina ya shigo. Na dago ina kallonshi cikin murmushi, "baby abinci... Abinci baby...". Ya fada a dan gaggauce, ya juya ya fita.
Na tashi tsaye ina dan murmushi, wato yau da yunwa ya dawo kenan. Na cire hijabin jikina na tafi kicin da niyar zuba mishi abincin.

Miyar dazu, ta koma kamar miyar tanade, ruwa tsululu kamar lokacin na fara dafa ta. Ban san lokacin da naji kwalla ta cika min idanu ba, na maida murfin tukunyar na rufe tare da kashe gas din. Na jingina da counter din kicin ina tunanin abu mai sauki da zan dafawa Yaya wanda ba zai dauki lokaci ba, sai dai duk abinda nayi tunani, sai in ga sam ba zai yiwu ba. Gabadaya duk wata idea ta dauke min, daga karshe dai na yanke shawarar kai mishi dambun a haka, tunda akwai komi a ciki, har maggi da mai sai dana saka a ciki, dama miyar don dai garnishing ne kawai.

Na ciccibi kayan na tafi falon Yaya dasu.

Tunda na fara zuba mishi yake kallona yana murmushi kwanannan abinda yake min kenan, idan na mishi magana yace ai cikin jikina ya canza ni ne shi yasa. Na tura mishi plate din gabanshi tare da tsiyaya mishi lemun a cikin kofi.

Ya ja plate din gabanshi, "yau kuma a haka zamu ci dambun?". Ya tambaya cikin alamun tsokana.
Na dan yi murmushi cike da fargaba, "uhmm, wani lokacin komi yana bukatar canji ai".
Yace "haka ne baby na". Yayi bismillah tare da kai cokalin farko bakinshi, take yanayin fuskarshi ya canza, da kyar ya hadiya. Naji gabana ya fadi cikin fargaba, nace "me ya faru?". Ban jira ya amsa ba na dauki cokali na kai bakina, yaji ya fara ziyartata kafin wani masifaffen gishiri mai rikita kwalwa ya biyo baya. Da sauri na kai lemun dana zuba mishi cikin bakina da niyar kora abincin dashi, domin ba zan iya hadiya shi ba. Nan kuma wani matsanancin tsamin lemun tsami daya min bismillah.

Ban san na tara kwalla a cikin idanuna ba, sai dana ji tana bin kumatuna. Da sauri Yaya ya kai hannu yana dauke min kwallar, yace "menene abin kuka kuma? Kada ki damu kanki, girki ai ya gaji haka. Bari yanzu in aika a sayo mana wani abincin".
Ban ce mishi komi ba, naci gaba da share kwallata. Yanzu duk wahalar wannan da naci ta tashi a banza kenan? Babu abin ban haushi da takaici ga matar aure, ace mijinta bai ci abincinta ba ya tafi neman na waje yaci.
Cikin kwallar da nake yi, nace "a'ah, bari in shiga in yi wani abu mai sauki".
Yace "inaa, ba zaki wahalar min da baby ba. Baki ji ance miki ba'a son ki cika yin aikin wahala ba? Maza daina kukan, kada ki sanya min baby kuka".
Duk yadda yaso inyi shiru, abin gagara yayi. Har aka kira sallah ya koma masallaci, raina a jagule yake.

Daya dawo sai gashi da ledar take away, har daki ya kaiwa kowa nata. Daya kawo min nawa ko kallonshi banyi ba saboda masifar bacin rai. Allah ya isa kadai nake ja ina karawa a cikin raina.
Muna zaune yana cin nashi abincin, nawa kuma yana gefe, sai ga Raheemah ta shigo falon. Ta kallemu ta tabe baki, "uhhum! Su yan gaban goshi masu juna biyu manya, wato yanzu abincin ma an daina yi sai dai a tafi a siyo na waje? Kwarai kuwa, Allah muma ya azurtamu da namu cikin dai!".

Kwata-kwata yau bana cikin jin zama in saurari korafe-korafen data saba, don haka na mike na wuce dakina, ban san yadda suka kare da ita ba. Sai wajen karfe goma sannan naje na kwashe kayan da muka bari. Ranar haka na kwanta zuciya a cunkushe.

Cikin dare fa barci ya gagareni, yunwa kamar zata kashe ni. Allah yasa na sanya abincin da Yaya ya kawo min cikin microwave, na zame jikina daga na Yaya a hankali na fita daga dakin. Kusan karfe biyu da rabi na dare lokacin. Shiru gidan, baka jin motsin komi.
Na shiga kicin, maimakon in kunna wuta, sai nayi amfani

42 / 52