AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   47 / 52

138K to 141K   out of 155.4K words

*☆⋆48⋆☆*




A gida muka sauka, da yake tare da Balarabe muke, Yaya ya tsaya suka gaisa da Baba, anan ma suka sha ruwa tare da Baban da Balarabe, sannan suka wuce masauki.
Tarba mai kyau muka samu wadda ban yi zatonta ba, ba daga Baban ba, ba daga matan nashi ba, ba daga yaran ba, kowa ya nuna farincikinshi da ganinmu har abin ya bani mamaki.

Sai bayan tafiyar Yaya sannan na fahimci cewa da wani abu a kasa. Tunda muka je, Aliyu da Ramata suna daki, tun lekowar da suka yi suka mana sannu da zuwa suka koma daki, basu kara lekowa ba.
Yanayin yadda na ganta ya tsorata ni, tayi wata irin rama, sai girman shekarunta ya kara fitowa.
Bayan mun kebe a dakin Maryam inda nan na saba sauka, na tambayata abinda yake faruwa da masu gidan. Abinda ta fada min ya girgiza ni.
Wai Aliyu aka kama yana saida ganyen Iblis. Jiya yan sanda suka zo unguwar aka kama gungun yan unguwar da suke shaye-shaye, ga namakinsu sai aka hada dashi. Har wajen karfe ukun dare suna police office din wai, da kyar aka bada shi.
Na kama baki ina jinjina kai kamar zanyi ihu, "garin yaya haka?", na tambayeta, "ban sani ba", itace amsar data bani.

Muna nan a dakin nata muna maida magana, Awwal ya leko yace in je dakin Baba yana kirana. Na dauki hijabita na saka na tafi. Shi kadai na samu a dakin nashi. Na zauna a kasan kujera, muka sake gaisawa dashi a nutse ba kamar ta dazu ba da aka yi ta a tsaitsaye.

Kafin ya daga baki ya sake magana, sai ga Alawiyya da Ramata sun shigo dakin kusan a lokaci guda, duk suka samu waje suka zauna. Na kurawa matar da tunda na mallaki hankalin kaina ta hana ni shakar numfashi mai dadi a rayuwata. Akwai wani lokaci a can baya, da ko sautin muryarta naji tana tashi, sai naji faduwar gaba ta ziyarceni. Akwai wani lokaci da zan mata kallo daya, inji babu abinda nake so da kaunar sake gani kamar in daga idanuna in ga gawarta shimfide a kasan.

Sai dai a yanzu da nake sake dubanta sai naji babu wannan tsoron, babu wannan tsanar, sai tsananin tausayinta daya lullube ni. Hakan kuma baya rasa nasaba da yadda naga ta makure a gefe kamar bera a gaban mage, kanta a kasa yake tunda ta shiga dakin, bata yi gigin daga ido ta kalli kowa ba.
Ba'a jima ba, sai ga Aliyu ya shigo shima, ya nemi waje can kusa da Ramata shima ya makure.

Sai da kowa ya nutsu sannan Baba yayi gyaran murya. Hakan yasa duk muka maida hankulanmu gare shi.
Ya fara da cewa "Ke Na'ilah ke da baki gida, ke kadai ce anan da baki san abinda yake faruwa ba...", nan ya zayyane min duk abinda Maryam ta sanar dani.
Baba ya cigaba da cewa, "saboda haka na yanke shawara, ba zan cigaba da zama da tantirin yaro kamar Aliyu a gidan nan ba. Ba zai lalace ba, kuma daga baya yazo ya lalata min yara, ba zai yiwu ba. Don haka nace mishi ya fita ya bar min gida na tun a jiyan. Ban fada maka kada ka kuskura in dawo gidannan in gan ka ba?".

Aliyun bai ce komi ba sai kara lafewa da yayi a jikin Mamanshi yana shesshekara kuka, yayin da Ramata din take share hawaye itama.

Alawiyya ta wurwusa ta matsa kusa da Baba, tace "Alhaji kayi hakuri da wannan magana da zanyi, amma matakin daka yanke kwata-kwata bai dace ba, ina ga da dai ka sake shawara".

Baba yace "shawarar me zan sake? Zubda kimata da mutuncina yaron nan ya riga yayi, yanzu duk cikin unguwar nan kowa zancen yake yi. To zai zauna yayi min a gida kuma? Ba zan iya ba, ya tarkata nashi-i-nashi ya bar min gida kawai".

Sai lokacin na samu kwarin gwiwar yin magana, nace "Baba kamar yadda Anty tace, wannan fa ba shawara bace. Zancen zubewar girma da sauransu, duk bata taso ba, tunda abinda dai ya faru ya riga ya gama faruwa, kuma ba'a dawo da hannun agogo baya. Abinda ya faru ya riga ya faru, sai dai a tari na gaba kawai. Amma korar Aliyu daga gidannan ba mafita bace, Allah ya gani. Baka tunanin idan ka kore shi din, maimakon ya saduda, sai hakan ya kara sanya shi yabi wata hanyar daban kuma? Duk kuma dai abinda zai yi nan gaba kana da alhaki akai, kuma duk inda zai je ya dawo dai, nan da shekaru goma ko dari, dole ya dawo gareka saboda danka ne, tsatsonka ne. Shi hannunka ai baya rubewa ka yanke ka zubar".

Baba yace "sai dai in hannun baya damuna. Amma tuni zan yar da dan banza in huta. Tun yaushe Aliyu yake bata min rai? Makaranta baya zuwa daga ta boko har ta islamiyar, bai san komi ba sai daukar magana a cikin unguwa. Yau ya zagi wancan, gobe ya bugi dan wancan, shi kadai ranshi yabi ya addabi mutane ina dalili?".

Nace "hakuri dai za ayi, shima ba zai kara ba".

Baba ko in ce iyaye da dama, suna da wani hali na sangarta yaransu, to the extent that sangartawar zata wuce misali. Yara zasu lalace, su daina ganin kan kowa da gashi, wani abin dariya ko tausayi shine yadda hatta da iyayen nasu ma zaki ga basa jin maganar su. Sai labari ya sha banban, yaro yaje ya dauko magana, sai kuma anan iyaye suzo su ce basu san wannan ba. Su zo su kori yaran. To me kenan aka yi? Ihu bayan hari kenan. Maimakon tunda da sanya hannunka hakan ta faru, ka tsayawa yaronka ya koma gagara-badau, lokacin da yayi tashen tsageranci da rashin da'a ka tsaye mishi, maimakon idan sun dauko maganar da tafi karfinsu su sake tsaye musu, a'ah, sai suce sun janye hannunsu daga garesu.
Sun manta lokutan da suka tsaye musu suka dinga yin abinda suka yi din, har suke ganin babu wani ko wata wadda ta isa sai su.
Don bana manta lokuta da dama da mutanen unguwa zasu kai karar Aliyu wajen Baba, akan wani abu da zai musu, muma mun sha kaiwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, amma bai taba daga baki yace mishi don me? Ko kul ba.
To yanzu idan iyaye basu dauki responsibility din laifukan 'ya'yansu ba, wanda idan aka yi duba tun tali-tali suna da kamasho a ciki, wa zai dauka?

Bayan doguwar muhawara da jeka-ka-dawo, da kyar muka samu ni da Anty Alawiyya Baba ya sassauto. Duk wannan abu da ake yi, Ramata da Aliyu na gefe in banda sharar hawaye babu abinda suke yi.
Daga karshe dai yace ya hakura, akan sharadin idan makamancin haka ta sake faruwa lallai zai kore shi. Ni dana kasance zabiya, ni nace naji na amince. Nan ya sake hada mu yayi mana nasiha mai shiga jiki, yace ya sallamemu.

Ina tashi, Ramata ta kamo hannuna. Kuka take sosai kamar wadda aka yiwa mutane, godiya take jera mana kamar harshenta zai fado kasa, "nagode, nagode, Na'ilah! Yau da ba don ke ba ban san yadda zanyi ba, Allah yayi miki albarka, nagode!!".
Ni kam na ma rasa abinda zan ce mata, jiki a sanyaye na dinga binta da kallo har sai da tayi radin kanta ta sake ni, sannan na juya na fita daga dakin.

Kai tsaye dakin Aliyu na wuce, na same shi a gefen katifarshi a zaune. Zama nayi dirshan a tsakiyar dakin, magana muka yi mai tsayi ni dashi game da abinda ya faru. Ba karamin mamaki na ci ba lokacin daya fada min wai kudi yake bukata shi yasa ya fara saida tabar saboda yaga abinda yaran unguwar sa'anninshi suke yi kenan, kuma suke samun kudi.
Nace "kai kuwa me ka nema ka rasa haka?".
Yace "to Baba baya bamu kudi, yanzu ko Mama baya bata. Kudin makarantarmu kusan term biyu bai biya ba, sai da aka koro mu. Kuma Mama bata da lafiya, in taje asibiti aka bata magunguna, Baba baya sai mata. Ya zamu yi?".

Wannan a halin Baba kam ba abin mamaki bane, haka yake. Duk wadda baya dasawa da ita a cikin matanshi, to ba ita kadai ba, har 'ya'yanta ma sai sunji a jikinsu. Na gani a kaina, hakan kuma ta faru akan ido na. Ina ga ina bukatar mu sake zama na musamman da Baba. Yana bukatar wani ya fahimtar dashi irin wannan rashin adalcin nashi, ba abu bane mai kyau. Sai dai dana sake tunanawa, sai naga ba hurumina bane hakan. Watakila Yaya dai zai iya shiga cikin maganar tunda duk cikinmu, baya jin maganar kowa kamar tashi.

Nan na zaunar da Aliyu, na fahimtar dashi cewa hakan fa ba mafita bace, sai jefa kanshi daya kusa yi a cikin halin k'ak'a-ni-kayi. Na tunatar dashi muhimmancin hakuri, da cewa ita rayuwar duniya ba lallai bane sai ka mallaki abinda kake so ba. Tunda ba duka kake samun komi ba, kuma idan kace kai sai ka mallaki komi to kai zaka kwana ciki kuwa. Na jima sosai a dakin nashi kafin na tashi na koma dakin Maryam.
Ina zuwa na tadda Kulsum, nan muka hau hirar yaushe gamo. Tana nan har an sanya musu ranar aure da wani lakcaran su. Sai da za'a rufe gida sannan ta mana sallama ta tafi.
Bayan munyi shirin kwanciya, na dauki waya na kira Yaya Mudatthir na zayyane mishi duk abinda ya faru. Yace Baban ya mishi waya a jiyan, amma bai sanar dashi hukuncin daya yanke ba. Mun jima muna tattaunawa dashi, daga karshe muka yi sallama dashi akan cewa cikin satin zai zo. Bayan mun kashe wayar, Yaya na kira muka raba dare muna hira. Muna gamawa ko barcin minti talatin banyi ba, na tashi sallar tahajjud.

Da asuba muka tashi ni da Maryam muka dafa abincin sahur. Bayan munyi sahur, Mazan sun tafi masallaci, mu kuma muka yi tamu sallar a daki. Na dauki Al-Kur'ani mai girma na fara karantawa.

Gari ya fara yin haske lokacin da Ramata ta fado dakin kamar an jefota, ni da Maryam duk muka bita da kallo cike da mamaki. Ta tsaya a bakin kofa muna kallon-kallo da ita. Maryam ce ta tambayeta, "Mama lafiya?".

"Na'ilah kiyi hakuri!". Itace kalmar data fara fita daga bakinta. Tsabar mamakin jin kalmar yasa na saki baki hangangan ina kallonta kamar wata sabuwar halitta.

Bata damu da kallon da nake jifanta dashi ba, ta fara cewa "nasan cewa bani da hurumin baki hakuri akan duk wasu abubuwa dana miki, nasan na aikata abubuwa da dama na rashin kirki a gareku, amma wallahi na aikata hakan ne cikin tsananin jahilci wanda kishi ya haddasa min. Amma yanzu na gane, na kuma dawo cikin hayyacina, don Allah ku yafe min abubuwan dana aikata muku".

Har lokacin bakina a bude, bansan abinda yakamata in ce mata. Strangely, sai naji wata fahimta ta shige ni. Wani fannin na raina ya fahimci abinda tayi din. Ban sani ko hakan yana da nasaba da halin da nake ciki a yanzu bane. Zama tsananin mata irin Ameerah da Raheemah, zai sanyaka ka fahimci abubuwa da dama kamar halin da muke ciki yanzu da Ramata dai.

Akwai lokuta da dama, da tsabar kishi, son zuciya da zugar shaidan suka sha taso ni a gaba da wasu irin shawarwari da muggan sake-sake. Wadanda tsabar tsananin tsoron Allah da abinda zan tarar idan nayi abinda Ramatan tayi ne kawai yake dakatar dani, don haka ne na dage da rokon Allah akan ya yaye min irin wadannan abubuwa. Allah kuwa maji rokon bawanshi ne, a hankali naji duk wadannan sake-saken na daina yin su.

Nasan Ramata tabi zugar shaidan ne da son zuciya. Son zama da tauraruwar da haskenta bashi da wani tasiri balle hasken azo a gani.. Sai dai son zuciya irin nata ya janyo mana yin rayuwar kunci da wulakanci a lokacin daya kamata ace munyi mabanbanciyar rayuwa.
Sai dai idan na sake duba hakan da wani ido na daban, son zuciya irin nata ne ya tseratar dani daga aikata mugun halin data aikata mana ga sauran abokanan zama na. Allah ya sani, ina da damar yin hakan, ina da fadar yin hakan, sai dai tunanin cutar da wani ta hanyar data cutar damu yakI ya zauna min, na kasa yin hakan. Idan na tuna zafin da naji, idan na tuna tsananin kunar da naji, idan na tuno darare da dama da nayi su cikin kuka da bakinciki da takaicin abinda matar nan tayi a gareni, sai inji ba zan taba iya aikata hakan ga kowa ba. Ba zan taba iya so wani yaji rabi-rabin abinda naji ba.

Sai dai ban hakuri daga bakin Ramata, abu ne da ban taba zaton zanji daga gareta ba, ban kuma shiryawa hakan ba.

Don haka naci gaba da kallonta kawai, har ta gama fadin abinda zata fada, ta juya ta fita daga dakin. Shiru ya biyo baya daga nan, ni da Maryam muka hau yin kallon-kallo, kafin na maida kallona ga kur'anin da nake karantawa.

Zuwa lokacin dana gama, gari ya gama wayewa, yara sun tashi suna ta shigowa gaisuwar safe. Sai lokacin na bude gwangwanin alewar eclairs dana kawo musu, bayan sun gama karba sun fita, sannan fa na koma barci. Ban tashi ba sai wajen karfe sha biyu na rana, shima wayar Yaya ce ta tada ni. Bayan mun gaisa dashi, na tashi na fita tsakar gida.

Babu kowa duk suna daki. Nan na fada bandaki nayi wanka. Sai anjima da yamma zamu tashi, hakan ya bani damar gudanar da duk wasu shirye-shiryena a nutse.

*

Kafin mu tafi na kira Aliyu dakina, na bashi kudi nace washegari ya raka Mamansu asibiti a dubata sosai. In yaso koma menene daga baya, zan kirasu inji.
Har bakin motarmu suka raka mu, Ramata har da kukanta tana ta godiya. Aliyu ya bude min bayan motar na shiga, ya maida ya rufe. Har lokacin kalma daya bata sake hada mu da Ramata ba, saboda ban san abinda yakamata in ce mata ba.
Yanzu da nake kallonta, ita da dan nata da a da, babu abin wulakantawa a wajensu kamar ni, abu daya ne yake min yawo a ka, 'lallai abinda ya baka tsoro, wata rana sai ya baka tausayi!'.

Muna first class ni da Yaya. Bayan jirgi ya gama lodi, aka fara sanarwar tashin jirgi. Kaina yana kan kafadar Yaya, hannuna na dama cikin nashi yana shafawa a hankali. Hankalinshi yana kan jaridar Vanguard yana karantawa.

Na lumshe idanuna a hankali kafin na bude su, ina kallon gajimare da muke ta ratsawa ta cikin tagar dake kusa dani. Na sauke wata doguwar ajiyar zuciya. Dana duba baya, shekara daya data wuce, ban taba zaton cewa yanzu war haka zan kasance akan kafadar mijina, Yaya Bilal, muna tsallaka Nigeria zuwa yin ibada a kasar Makkah ba. Idan na tuna gwagwarmayar da muka sha, da yadda abubuwa suka juye, har zuwa yadda aurenmu ya kasance, sai naji ina girgiza kaina kawai, hikimar Allah da ikonsa suna da ban al'ajabi.
Can kasar zuciyata, na kasa yakice wata murya da take mintsini na, 'shin ban ga aya ba?!'.

Yaya ya shafo kumatuna da bayan hannunshi, hakan yasa na bude idanun da ban san na rufe ba, na sauke su a kanshi. I can't help myself, duk lokacin da zan kalle shi, sai naji tali-talin yawon abubuwa a cikin cikina, tunanin how I've come to be this lucky yaki barina.

Yace "tunanin me kike yi ne haka, kin barni ina fama da takarda?".
Babu tunanin komi nace "kai!". Sau tari bana tauna maganganu irin haka kafin in furta su, Yaya Bilal has that effect on me.

Shi kanshi bai yi zaton amsar da zan bashi ba kenan, ya daga girarshi cikin mamaki, yana wani irin murmushi, "haba? Akan me?".

Na kara gyara kwanciyata a jikinshi, nace "ta yadda aka yi ka fara so na mana. Tell me, love at first sight ce, ko kuma sai a hankali?".

Yaya yayi shiru yana kallona kamar mai tunani, amma kuma har yanzu murmushi yake yi. Yace "kin tuna ranar farko da muka hadu dake?".

Nace "sosai ma. Ranar da kazo ka daukemu ni da Janan ka kaimu Kaduna, lokacin bikinka da Ameerah idan ban manta ba".
Ya girgiza kai, na kalleshi in confusion, "no? Ba lokacin bane?".

Ya jinginar da kanshi akan seat din, hakan ya kara bani damar sake makale mishi.
Yace "zaki iya mantawa, amma ni ba zan taba mantawa ba. How could I?". Yadda yayi maganar ne, yasa na daga kai na kalleshi. Idanunshi na kaina, cike suke da longing da ban taba katarin gani a cikin idanunshi ba.

"Akwai wata rana, da ban san dalili ba, kawai tsintar kaina nayi a cikin mota na tafi Funtua. Ban sani ba, tunanin Yaya Sa'a ne a cikin raina ko kuwa Janan? Na kasa mantawa. Sai dai duk wadannan tunanikan sun bi iska lokacin da nayi tozali da kyakkyawar halittar dana kusa bugewa da motata lokacin dana dora idanuna a kanta a karo na farko. Ban san cewa a take a lokacin tayi awon gaba da zuciyata ba sai da nayi nisa, nisan da ba zan taba iya dawowa daga inda na tafi ba har abada".

Kallonshi kawai nake yi cike da alamun tambaya don ban fahimci inda maganganunshi suka sa gaba ba.
Ya kalleni yana murmushi sosai, da alamu ba karamin dadada mishi rai abinda ya tuno yake yi ba, yace "kin tuna watarana da kuka shiga staff quarters ke da Janan siyan wani abu, meye ma sunan?".

Na zare idanu na kalleshi, mamaki kamar zai kashe ni, ta yaya ma aka yi na manta ranar?.
Watarana muka taba shiga cikin staff quarters, makotan gidan su Anty Sa'a a lokacin suna saida iloka, muka je saye. Ga takaicinmu muka samu babu, akan hanyarmu ta fitowa, muka ci karo da wani kare. Nan muka yi cak muna kallon-kallo dashi, yana shirin juyawa ya kara gaba, kawai Janan da dama tunda muka ganshi, ta fara rawar jiki, sai kawai ta dafe keya ta ranta ana kare. Shikuwa kare yace da wa Allah ya hada mu idan ba daku ba! Nan muka kafa tsere.

Tabbas, wannan rana itace ranar farko da muka fara haduwa

47 / 52