AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   31 / 52

90K to 93K   out of 155.4K words

angon nawa ta waya inji yadda ake ciki, waya bata shiga. Tun da yau tayi ban samu wayar shi ba, nayi tunanin ko network ne ya hana tunda a jiya da rana da muka yi wayar mu ta karshe dashi, yace yau da sassafe zasu taho da abokan shi.
Na sake kokarin tuntubar babban amininshi, Salisu inji ko me yake faruwa, wayar shi ta karaci kara har sau biyu bai daga ba. Daga karshe na maida wayar cikin jaka.

Haka kawai naji wani kuzari ya shige ni, na mike na fito tsakar gida, muka cigaba da harkar mu ni da 'yanmata na.

Kafin yammar tayi, gabadayanmu mun canza kayan jikinmu. Ni da Janan muka saka yadin da Ummahnsu ta dinka mana, su kuma sauran yanmata suka sanya ankon da muka yi.
Duk kokarin su shirya suke yi, saboda saurin kada anguna su zo damar hoto ta wuce su. Angunan da har yanzu banji wani yace yaji daga garesu ba. Har yanzu muna gidan Inna ne.

Bayan gotawar karfe hudu da mintuna kadan, muka jiyo sautin guda daga cikin gidanmu. Naji kafafuna sun yi wani irin lakwas, na fara kokarin zamewa kasa da sauri na jingina da bango.

Duk da haka, sai da naji wasu irin black spots suna kokarin dabaibaye idanuna lokacin da wata zabiya, irin marokan nan, ta fado gidan tana rangada guda.

"Ina amarya, amarsu ta ango! A zo a bani tukuicin wannan daddadan sako da zan isar, nima kakata ta yanke saka. Wa ya sani ko daga kanki sana'ar roko ta barni? Allah ya yarda, alkawarin Allah ya tabbata, aure ya dauru....!!".





✌✌✌😉😎











*☆⋆33⋆☆*





Marokiya bata kula da halin hargitsi da amarya ta shiga bane da alama. Sai data gama jan kirarinta, ta kara gaba. Duk cikinsu bana tunanin wani ya kula da halin da nake ciki ma gabadaya.

Tana fita, wani marokin ya leko shi har da yar karamar gangar shi a hannu, ya tsaya daga soro yana zuba nashi kirarin.
"Ina amarya, tazo ita kuma ta bani kujerar makkah. Ranar farinciki da murna ga masoya, Allah ya nufa, alkawarin Allah ya cika, aure ya dauru tsakanin Muhammadu Bilal da Malama Na'ilah!! Allah ya bamu ikon dawowa badi war haka mu sake shafa wata fatihar ta 'ya'yanku! Eh, a gayawa amarya, maroki dan na Halimeme na jiran nashi kason, ango Bilalu ya burge shi da sababbin kudi babu ko kari, farare tas bugun Abuja!....".

Ai lokacin amarya Na'ilah babu ita. Tunda ya furta kalmar sunan Bilal, naji duk wata dauriya ta rike kafafuna su tsaya a tsaye ta bar jikina, karshe dai sai dana kai ga silalewa kasa.
Abu na karshe dana gani, shine confused fuskokin mutanen da suka yo kaina a rikice, suna kwala min kira, duhu ya mamaye ni gabadaya...!


*


Ban tuna komi ba lokacin dana tashi. Mutane hudu ne a kaina lokacin dana farfado daga suman da nake kyautata tunanin nayi. Janan da Anty Halima kadai na iya ganewa, sauran biyun tare suka zo da Anty Haliman daga Gashua, ban gane su ba.

Na tashi zaune, Janan tayi saurin tara filo a bayana yadda zan ji dadin jingina duk da protests dina na cewa kada ta damu.
Dakin da muke ciki daga gani babu tantama asibiti ne, ko kuma karamin clinic.
Janan ta bude gorar ruwan faro ta tsiyaya a cikin kofi ta miko min, na amsa na kafa kai na sha tare da mika mata, ta amsa ta ajiye.

Na dafe kaina da yake sarawa tunda na tashi, ina kallonsu.
"Me ya faru ne?". Na tambaya cikin sarkewar murya, wincing lokacin da naji kaina ya kara sarawa kamar ana buga ganga.

Janan tace "Wanda zaki aura ne ya faru!", duk yadda taso ta nuna tsana da venom a cikin muryarta, fuskarta dauke take da murmushi mai tsananin taushi.

Sai lokacin komi ya fara dawo min cikin kai daki-daki.

Na fara girgiza kai a hankali, kafin na fara da karfi ina ja da baya har sai da bayana ya hade da allon gadon. Na dora hannuwa biyu kai, ihu naso kurmawa, amma babu abinda ya iya fita daga bakina. Daga karshe dai na samu sautin, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku na lalace!!".
Kafin naji na barke da wani irin kuka.

Anty Halima ta matso ta rungumeni jikinta ta fara shafa gadon bayana cikin alamun lallashi. Tace "ke 'yar nan, ki kiyayi kanki ke kuwa, menene na shiga uku? Allah ya dube ki, ya baki miji na nunawa sa'a. Kowa yasan dama hakan da mamaki, ka auri wanda baka shiryawa ba, amma bai kamata kalma ta shiga cikin uku ta fita daga bakinki ba. Ki godewa Allah, Allah kadai yasan irin hikimar da take cikin wannan juyin lamari daya faru".
Amma kuma kukan naci gaba dayi, har ma na yanzu yafi na dazu sauti.

Tun tana lallashi, har ta gaji, ta koma gefe ta zubawa sarautar Allah ido, tana kuma mitar ai sai inje inyi tayi, a kaina farau?, amma ban kulata ba.
Sai da nayi ya ishe ni, kuka share-share har da majina, 'sai kace wadda aka aiko mata da sakon mutuwar uba, ba aure ba!' a cewar Anty Halima bayan taga yadda fuskata ta baci da hawaye.

Janan tana gefe, kallona take daya bayan daya, babu alamun damuwa ko digo daya akan fuskarta sai ma amusement rather. Hakan ya kara tunzura ni.
Ta zari tissue ta miko min, na warta na share hawayen fuskata da majina, nayi jifa da tissue din can gefe guda.

Janan ta kasa danne dariyarta, tace "a'ah, baiwar Allah. Ba fa shi ya kar zomon ba, haka muma da kike wani huhhura mana hanci. Don haka idan ma zaki ware ne yarinya, ki warware".

Na harareta tare da sake wartar wani tissue din na goge idanuna da suka cika da hawaye.
Nace "wane warwarewa kuma? Ai wallahi zuwa zasu yi su warware aurennan yadda suka kulla shi, don wallahi ba za ayi wannan kwamacalar dani ba! Idan kuma ba haka ba sai dai in bar musu garin wallahi!".

Su duka suka yi shagara da baki suna kallona, kafin Anty Halima ta daga baki da niyar fara magana, "wannan wace maganar banza ce kike yi? Ke...".

Maganar ta katse sakamakon kofar dakin da aka turo aka shigo, duk muka kalli kofar. Faduwar gaban data ziyarceni a lokacin da muka hada ido da ba kowa ba illa Yaya Bilal Allah kadai yasan irinta. Nayi saurin kauda kaina na kalli Yaya Mudatthir, daga ganin yanayin fuskarshi kasan cewa sun gama jin abinda na gama fada yanzu. Sai dai ban ji ko dar ba a cikin raina, hasalima can cikin raina cewa nayi gwanda da maganar ta shiga kunnen wanda aka yi dominta.
Fuskar Yaya babu yabo babu fallasa, ya cewa su Yaya Halima "Anty ko zaku dan bamu waje?".

Babu musu suka fita suka bar dakin, suka barmu mu kadai. Yayan ya kalleni fuska cike da warning tsantsa, kafin ya shima ya juya ya fita, har da maida kofar dakin ya rufe. Na harari kofar kamar ita ta min laifin.

A hankali ya tako cikin taku dai-daya, yazo ya tsaya min aka kamar wani tsohon soja, ya zuba min ido. Ni kuwa naci gaba da kallon kofar da Yaya Mudatthir ya bi stubbornly.

Ganin an dauki lokuta masu yawa ba tare dana sake ko jin motsin shi ba, yasa na daga idanu a hankali na kalli inda yake. Yana tsaye a wajen har lokacin, ko yanayin tsayuwarshi bai canza ba, idanunshi manya tubarkallah dasu kamar na Janan, a kaina. Na turo baki tare da sake dauke kaina.

Ina jin sautin murmushin daya saki, ya ja farar kujera dake can karshen dakin, ya ajiyeta a gefena ya zauna.
Murya can kasa, kamar mai rada yace "ya jikin?".

Nan ma ban ce komi ba, na kurawa mayafin da aka lullube gadon da nake kai idanu.

Ya sauke ajiyar zuciya, "ko ki amsa, ko kada ki amsa, hakan babu abinda zai sa, kuma babu abinda zai hana Na'ilah. Abinda ya faru dai ya riga ya faru...".

Nayi saurin katse shi, "bai riga ya faru ba, ni wallahi ban yarda ba, aurennan sai an zo an raba shi, dama tun farko ai sai dana ce ba zan aure ka ba!".

Yayi wani kicin-kicin da rai, "wannan kuma sai ki samu wanda ya daura auren kiyi mishi bayani, sai ya warware. Tunda nima ina zaman zamana sai kiran waya kawai naji ance za'a karbi wakilcin aurena, in kawo sadaki. Kin kuwa ga nima daga sama na tsinci maganar kamar ke dinnan".

Nace "to haka ake aure, babu tambayar wadda zata yi zaman auren?".

Ya daga kafada sama, "kamar yadda nace ne, zuwa zaki yi ki tambayi wadanda suka daura auren. Amma a shawarce, zan baki shawarar ki ma sauke wani girman kai, jiji da kai da jan ajin da kike yi, kamar yadda nace, abinda ya faru dai ya riga ya faru sai dai kuma a tari na gaba. Yakamata ki san irin kalaman da zasu fito daga bakinki, saboda da da yanzu ba daya bane, idan kinyi da na kyaleki, ina mai tabbatar miki da cewa yanzu fa ba zan kyaleki ba saboda a karkashin Ikona kike, saboda haka ki kula".

Kawai sai na sa kuka, yayi zaune a gefe yana kallona bashi da niyar furta ci kanki, nayi na gama na share hawayena, nace "to dama haka ake auren ne, tun kafin aje ko'ina ka fara cin zalina da gindaya min sharadi".

Yace "watch it Na'ilah! Yadda fa baki shiryawa auren nan ba, haka fa nima. To meye ma amfanin auren idan babu doka da sharudda? Abinda nake so ki sani shine, lokacin lallashi da bin kai ya kare tsakanina dake, tunda ke kafiyar kai tasa baki fahimtar komi sai an biyo miki ta bayan gida, let's bring it on then. Ta kowace hanya kika bullo, nasan ta yadda zan taro ki.

Ke yanzu hakan bai isheki ishara ba? Ki hakura ki saddakar, ki mika wuya ga hikima irin ta Allah ba? Ni din dai da kika dinga gudu Na'ilah, kina ihu da sanarwar ba zaki aure ni ba, ni din dai kika buge da aure bayan kin gama kewaye-kewayenki. Dama kin hakura tun farko, kin kauda wannan girman kan da kike ji dashi, da yanzu muna cikin farinciki gabadayanmu. Amma yanzu wa gari ya waya? Saboda tsabar son kai da taurin rai irin naki, kinga abinda kika janyo mana ai. Yaushe rabon da kici abinci ya cika miki ciki? Yaushe rabon da kiyi barci mai dadi? Yaushe rabon da ki samu sanyin zuciya da sukuni a cikin ranki? Yaushe rabon da ki samu wadataccen kwanciyar hankali? Ki duba kiga yadda kika bi kika rame, kika kare kamar kudin guzuri? Ni da kika dinga gudun ma dai sai da nazo na fiki kwanciyar hankali da jindadin rayuwa. Hakan bai isheki ishara ba Na'ilah? Me kuma kike bukatar gani da zai tabbatar miki da cewa ba'a taba tsallake abinda Allah ya riga ya tsara maka? Duk zullewarka, zaka yi ne ka gama. At the end of the day dai, sai ka komawa wannan kaddarar taka!".

Nayi shiru ina sauraron yadda yake maganar a zafafe, daga ji babu tambaya a matukar fusace yake, dani ko kuma wani.
Naci gaba da shesshekata har da jan majina, yace "ni yanzu haka Zaria zan wuce abina, zan je in fara shirin inda za'a sauke ki. Don haka kina da sati daya, daga yanzu zuwa rana irin ta yau, ki gama yanke shawarar yadda zaki yi, aure tsakaninmu dai ya dauru, babu kuma wani mahaluki da zai sanya ni datse shi, don haka you might as well take heart, shawarata a gareki kenan".

Ya mike yana gyara link din hannun rigar shi, "duk abinda kike bukata, zaki iya kiran wayata, ko kuma ki fadawa Janan, zata fada min. Sai anjima!".
Yasa kafa ya fita daga fadin haka, babu ko waiwaye.

I was too shock, ko hannu na kasa motsawa balle gangar jikina. Baki a dage, ido a bude akan kofa, haka su Janan suka shigo cikin dakin suka sameni. Wato ni za'a nunawa attitude? Lallai kuwa.

Janan ta fara tarkata mana kayan da aka baza a dan lokacin, likita ya shigo ya kafa min dokar cin abinci da samun barci isasshe. Ni dai jinshi nake yi, ya gama dogayen bayananshi, ya sallame mu muka kara gaba.

Da yake clinic din anan cikin unguwarmu yake, a kafa muka karasa gida.

Zuwa lokacin kowa yaji labarin yadda daurin aurena yazo da canjin yanayi, kuma canjin ango. Nan da nan mutanen da suka yi saura suka rufa a kaina da kalmomin 'sannu, ya jiki? Ashe abinda ya faru kenan? Sai ayi ta hakuri, Allah ya nufa shine mijin', wasu kuma har su kara da 'ai dama naji ance kun yi soyayya dashi, abin ya kwana gidan sauki ma', da dai sauransu.

Muka samu muka yakice su da kyar muka shige can kuryar dakin Anty Alawiyya, Allah yasa babu mutane sosai.
Na zauna a gefen gado, Maryam ta tafi nemo min abinda zan ci in sha magungunan da aka bani, Janan kuma ta zauna a gefena.

Nace mata "me ya faru da Dr. Ne?". Babu wanda naji ya sake tado zancenshi, ga yanayin yadda suke nunawa kuma, basu da alamun yi mun bayanin abinda ya faru.

Ta tabe baki, "hmm, mutuminki ba sai suka shanya yan daurin auren ba? Tun ana jira har aka gaji, babu wani dangin ango da aka gani a wajen daurin aure. Yaya Jameel ne da yazo daurin aure ya kira wani abokinshi yaje har can gidan su angon ya tambayo ko lafiya? Zancen da nake miki, ashe bawan Allah ya kwana ya huce a kasar London, ya bar sakon a gaya miki yana miki fatan alkhairi, amma idan kinga zaki iya jiranshi nan da shekaru biyun, to babu damuwa. Amma a halin yanzu ba zai iya daukar hidindimu masu yawa ba, liability yace. Shine su kuma cikin wadanda ya barwa sakon, daga abokai har yan'uwa, aka rasa wanda zai iya tako kafarshi yazo yayi bayani a mutunce kamar yadda aka faro a mutunce. To ana shirin sallamar mutane ne a basu hakuri, Yaya Jameel yace ba za'a yi haka ba, tunda an san da manemi a gida, ai kawai yazo ya biya sadaki, shine fa aka daga daurin auren zuwa yamma yadda Yaya Bilal yazo ya samu daurin auren".

Na jijjiga kai cikin sanyin jiki, wato har zabata aka yi akan abin duniya, aka kuma kirani liability? Allah kenan. Shi kuma Yaya Jameel, apparently shine makasudin jefa ni cikin ha'ula'in da nake ciki yanzu kenan?.
Janan ta dafa kafadata, "meye na wani abin damuwa anan? Ai in gaya miki ki kwantar da hankalinki Hajiyata, ki je ku kwashi soyayyarku wallahi. Shima Yayan fa ba karamin dace yayi ba, naji ance kusan mutane hudu suka nemi aurenki a take a lokacin".

Na ciza lebe kawai ban ce mata komi ba. A haka Maryam ta dawo ita da Kulsum, da kwanon abinci a hannunta. Haka nan saboda damun da suke yi min, na tuttura abincin ba don ina so ba. Kafin in gama an kira sallar magriba, duk muka yi harama suka yi.


*


Zuwa washegari gidan ya baje da yan biki, sai yan daidaiku da zasu tafi washegari. Shima Yaya Mudatthir a ranar ya juya. Janan tana makale a gefena, bana lekawa ko nan da kofar gida sai na sha fada da mita kamar itace mijin gabadaya.

Sai da safe dana je gaida Baba, sannan yayi min bayanin halin da ake ciki. A raina nace 'ihu bayan hari kenan'. Ya nanata min nan da sati daya za'a tafi dani, in shirya, nace mishi to.

Anty Halima taci gaba da zama damu, wani sabon gyara suka fara min ita da Anty Alawiyya babu kakkautawa. Anty Alawiyya ta kan ce, "zama cikin mata biyu musamman hamshakai yadda naji ana bada labarin matan mijin nan naki sai an dage Na'ilah. Don haka ki dage, ki kama kanki, ki taimaki kanki kafin ki zama saniyar ware".
Abinda bata sani ba shine, maganganun nan nata babu abinda suke kara min sai tashin hankali da taraddadi.

Wasu lokutan kuma haka zata zaunar dani tayi ta min nasihohi da maganganu, salo iri-iri na kissa da kisisina har mamaki take bani wani lokacin. Sai dai bana bin abinda take fada ko daya, kawai jinta nake yi. Mijin da ba'a so, gidan da ba'a so, meye na koyan makaman zama dasu? A ganina fa kenan.

Cikin dan wannan lokacin ban sake ji daga angon nawa ba, babu kira, babu text, babu komi. Wani lokacin ina ji zasu dinga yin waya da Janan, ya tambayeta ya nake, ko kuma akwai wata matsala ne? Haka zasu yi wayar su gama ya kashe, babu ko sakon gaisuwa.

Hakan ba karamin kona min rai yake yi ba, a ganina tun ma kafin aje ko'ina ya fara wulakanta ni, ina ga yaga na shiga gidanshi? Nima sai na shaka fiye da yadda yakamata, nayi watsi da al'amuranshi. Tashin hankalin da nake ciki ma baya barina tunanin wulakancin da yake yi min.

Kwanakin sai suka dinga wucewa kamar a cikin kiftawar ido da bismillah, kafin in ankare, lokacin barina gida yayi.
















*☆⋆34⋆☆*





Kafin zagayowar ranar tarewata, sai dana zama kamar wata matar Malam. Kullum ina fama da carbi da doguwar hijabi a jiki ina ja, cikin dare zan tashi tun daga farkon dare har karshen shi, washegari in tashi da azumi a bakina, addu'a daya ce nake yi ina maimaitawa; 'gidan Yaya Bilal, Allah ka tsareni da shiga wannan gida, Allah kamar yadda ka raba gabas da yamma, Allah ka raba ni da shiga wannan gida'.

Sai dai a kwana na biyar, dole na gama saddakarwa, na fara addu'ar neman ceto da taimako saboda babu alamu ta ko'ina mai nuna cewa zuwana gidan Yaya Bilal zai fasu. Ranakun kullum kara matsowa suke yi, hakan kuma yake kara saka ni cikin tsananin damuwa. Watakila dai karshen farin cikina ne yazo.

Tunda aka daura auren, na fara wasu irin mafarkai masu ban tsoro. Sai inyi mafarkin wata mata, fuskarta a rufe da

31 / 52