Author : Jeedderh Lawals Category : New Hausa Novels 2026
son Yaya Bilal ya cigaba da kirana, ya cigaba da kulawa da ni, ina son in kasance dashi. Sai dai a duk lokacin da tunanin zama da kishiyoyi musamman irin su Ameerah da Raheemah ya fado min cikin raina, sai inji duk wani abu da nake ji game dashi ya bi iska.
Darare da dama da na sha zama, ina kokarin lallashin kaina, sai dai I just can't bring myself to do that! Na kasa! A duk lokacin dana tuna da irin ukuba, tashin hankali, damuwa da rikicin da muka shiga ciki, ko kuma wanda muke ciki har yanzu a gidanmu, wanda kishiyoyi ne suka yi sanadin haka sai inji zuciyata ta dugunzuma, inji hankalina ya tashi.
Jin shirun da nayi, yasa ta dafa kafadata, tare da tallabo kaina da hannunta daya. Bani da zabi sai na daga idanuna da suka cika da kwalla na sauke a kanta.
Ta girgiza kanta, tace "wallahi mamaki kike bani Na'ilah. You are just beating yourself akan abu mai sauki. Sai me don Yaya Bilal yana da mata? Ke yanzu ba abin alfahari bane a gareki, mutum kamar Yaya Bilal ya so ki, ya sadaukar da muhimman bigire nashi a kanki? Ba yabon kai ba, Yaya Bilal kyakkyawan mutum ne, mafarkin kowace diya mace. Amma ke ga damar samunshi a ruwan sanyi kin samu, kin zauna kina jan aji da kawo wasu dalilai naki da basu da makama ko kadan. Gaya min, matan shi ne, rashin haihuwar da baya yi ne, ko kuma shi a karan kanshi ne?? Idan mata ne, yace miki ba a waje daya zai hada ki dasu ba. Idan kuma haihuwa ce, ina mai tabbatar miki da cewa Yaya Bilal lafiyarsa lau, Allah ne bai kawo mishi haihuwa ba har yanzu. Idan kuma shi dinne, menene aibun Yaya Bilal saboda Allah? Ni dai nasan Yayana mutum ne mai nagarta, sai dai idan anki Allah ne za'a ce bai yi ba!".
Tunda ta fara maganar nake girgiza mata kai, amma banyi yunkurin katseta ba sai data dire aya. Nace "ban taba tunanin kin Yaya saboda rashin haihuwa ba, ita haihuwa nasan ta Allah ce, duk kuma kokarin mutum, idan Allah bai mishi baiwar haihuwar ba, babu abinda zai iya yi game da hakan sai dai hakuri kawai. Don haka ban taba yin wannan tunanin ba. Sai dai kamar yadda kika ce, yes matan Yaya, sannan shi a karan kanshi ba tsaran aurena bane. Meye hadin biri da gada idan ba rigima ba? Daidai ruwa daidai tsaki, sai kiga an zauna lafiya. In gaya miki gaskiya Yaya Bilal ya fi karfina.
Ba son kai ba, aure nake so inyi mai cike da kwanciyar hankali Janan, ba zan baro masifar kishiya ba, sannan kuma in fada cikin wata wadda ma tafi waccan, kuma ina sane. Idan nayi haka ban yiwa kaina adalci ba. Na fa san komi Janan, ba yau aka auren soyayya ba a gaban idanunmu ba, amma tun kafin aje ko'ina kiga labari ya sha banban. Wannan wadanda ba zaune suke da kishiya bama fa kenan, ina ga wadanda zasu zauna da kishiya? Allah ya gani, so nake in shimfida rayuwar aure mai ma'ana, daga ni sai mijina sai 'ya'yan da zamu haifa. Wannan itace rayuwar dana dinga hangowa kaina Janan, bana kuma tunanin zan iya kauda kai, ina ji ina gani, in kai kaina cikin kabari na!".
Ina dire maganar ta tare ni, "to wa yace miki ba zaki iya irin rayuwar da kike hangowa ba da Yaya Bilal? Kin gwada ne kin gani?".
Nayi dan murmushi cike da kunar zuciya, nace "Janan kenan! Ke baki san kaidi irin na kishiya ba, baki san komi game da sharri da kissa da kisisina irin ta kishiya ba, bana kuma tunanin zaki taba sani. Don haka ki kama bakinki kawai ki ja, ni naga abinda na gani da idanun nan nawa, abinda na gani kuma ba abu bane mai kyau, don haka tarihi fa ba zai maimaita kansa a kaina ba Janan! To dame ma zan ji ne? Da miji zan ji, ko kuwa tashin hankalin kishiya? Barni dai inji da abu daya, hankalina zai fi kwanciya!".
Janan kallona take yi kamar wata sabuwar halitta, nasan yadda na hakikance ne abin yake bata mamaki. Bazan damu ba though, ance wai riga-kafi yafi magani, kuma hanyar lafiya a bita da shekara. Gwanda dai in tsaya kyam akan ra'ayina, idan zuciyata ta fara rawa akan wannan maganar, me zai faru kenan? Na san it's only a matter of time, da zan manta da wani Yaya Bilal. Balle duka mai ya rage mana a Zaria? Yan watanni ne kawai. Idan na samu na lallabi zuciyata, na lallaba na bar Zaria, nasan ikon Allah ne kawai zai sake dawo da ni cikinta. Kenan idan na tafi, ta ina zan ga Yaya balle har wani tunanin zama dashi da masifaffun matanshi ya darsu a cikin raina? Abinda nake bukatar inyi kawai shine in daure, in kuma yi kokarin mantawa dashi.
Sai dai fadar, tafi aikatawar dadin fada.
Janan ta girgiza kanta cikin rashin sanin abin cewa, tace "gaskiya kinyi nisa da yawa, Allah ya ganar dake".
Nima na girgiza mata kaina, nace "ba zaki taba ganewa ba Janan, ba zaki gane ba!".
Bata ce komi ba, ta cigaba da tafiya. Nima na bi bayanta.
Tun daga wannan yar sa'insa da muka yi, babu wanda ya sake tado maganar har lokacin tashinmu yayi. Kai babu ma wata doguwar magana data sake hada mu da ita, naga kamar ma wani haushi na take ji. Ni ma da yake raina a dagule yake, ban wani damu ba. Lokacin tashi yana yi, na bar ward din. Ranar ko sallama bamu yi ba.
Ina komawa daki na dora indomie, ba wata yunwa nake ji ba, amma tunda ranar garin yau ta waye babu komi a cikin cikina sai biskit din pure bliss da hot chocolate. Ina gama dafawa na dora ruwan shayi, na dauki lemun tsami na matse a cikin shayin na juye a cikin mug. Dana gama na daukesu zuwa gefen katifata na ajiye, ni kuma na zauna. Laptop dina na dauka na kunna kallon wani American film, 'Another Cinderella Story' na fara kallo ina kuma cin indomin. Kallo kawai nake yi, amma bana wani fahimtar kallon. Har na gama na kauda kayan, na dawo na cigaba da kallon. Ina nan zaune Esther ta dawo, na mata sannu da zuwa, na maida hankalina kacokam ga film din da nake kallo don bani da kuzarin zama yin hira da ita. To da yake ma ba zama ya kawo ta ba, kayan jikinta kawai ta canza ta sake fita.
Ina cikin yin kallon barci ya kwashe ni.
*☆⋆28⋆☆*
Ban jima da fara barcin ba amma, kiran daya shigo cikin wayata ya katse min shi.
Na zabura na tashi zaune tare da lalubar wayata, duk da kalar ringtone din, hakan bai hana ni kara duba sunan mai kiran ba domin in tabbatar da cewa da gaske ne ba mafarki ba.
Ban san dalilin da yasa na kasa goge lambar Yaya Bilal daga cikin wayata ba, kai ko suna har yanzu ban iya canza mishi ba. Har yau 'Muhammadu na' ne a jiki, shine kuma yake tsalle yana karawa akan screen din wayata.
Duk da tsananin rawar da hannuna yake yi, da yadda zuciyata take bugawa, da yadda nasan bani da abinda zan ce mishi, hakan bai hana ni dagawa ba.
Hatta da muryata rawa take yi lokacin da naji muryarshi tana ratsawa ta cikin dodon kunnena, na amsa cikin sanyin jiki da murya. Yaushe rabon da inji wannan muryar? Ji nake kamar na shekara da shekaru.
Yaya Bilal yace "hmmm, Na'ilah kenan, manyan kasa. Kin gama fushin ne?".
Nace "fushi kuma, fushin me zan yi?".
Yace "nima ban sani ba Na'ilah, kawai dai nasan kina yin fushi. Amma duk ba wannan ba, kina ganin zamu iya magana yanzu? Are you ready for that?". Nayi shiru ina sauraronshi, ina tunanin ya dauki shirun da nayi a matsayin go ahead, don haka ya fara magana.
Yace "ba kya ganin it's high time, mu ajiye duk wasu abubuwan da suka faru a baya a bayanmu mu fuskanci gaba? Bai kamata ace muna ta tsalle-tsalle a waje daya ba kamar kananan yara, please let's do this like the matured people we are!".
Tabdijam! Naji wani kululu ya makale min a makoshi, cikin nuna alamun bacin rai nace "kana nufin kace min ni yarinya ce ko kuma ina dabi'a irin ta yara?".
Yace "ban ce ko daya daga ciki ba, illa iyaka ina so in nuna miki cewa wannan kauce-kauce da kike yi babu abinda zai haddasa mana sai bata lokacinmu da yake yi kawai. Na'ilah, mu fa ba kananan yara bane, bai kamata ace mun dauki magana daya muna ta nanata ba, bayan muna da yadda zamu fuskanci matsalar mu kuma magance ta. Saboda haka yanzu ki fada min, meye matsalar ki game dani? Kin san ina son ki ko?".
Amsar dana bashi ta fito daga cikin bakina tun ma kafin in tauna ta, kai ban ma san na fade ta ba sai dana ji tana ringing a cikin kunnuwana, da kuma shirun daya biyo bayan na furta ta, da alamun shi kanshi bai yi tsammaninta ba; "nima ina sonka!".
Kusan sakanni biyar da fadin hakan, kafin naji yayi gyaran murya, ni kam sai aka barni da kyafta idanu, yace "good. To menene matsalar? Na riga na fada miki idan ta matana ne baki da matsala da su, gidan ki daban zan ware miki, ba lallai sai kun hadu dasu ba. Wannan ganin damar ki ne, idan kin so haduwa dasu sai ki hadu dasu, idan baki so ba, sai kiyi yadda kike so. Bayan wannan kuma sai me? Ban takura ki ba Na'ilah, zan jira ki gama karatunki kafin a tado maganar auren, bayan nan zan bar ki kiyi aikinki, ba zan hana ki ba. Sai me kike bukata kuma?".
Shi a tunaninshi rashin hada mu gida daya kamar wani solution ne, sai dai a nawa tunanin, wannan ba komi bane. Ya hada mu gida daya ko bai hana ba, duk dai yana da mata ne dai, kuma zamu yi sharing dinshi dasu. Na daga baki nace "bani da wata matsala Yaya, kayi hakuri. Nima ba wai ina jindadin wasa da hankalinka da nake yi bane, amma the fact that zan zauna da kishiya daya ma bana so balle kuma har biyu, kayi hakuri don Allah".
Yace "shi kuma son da muke yiwa juna fa? Kin kasa daukar matsaya daya Na'ilah ki zauna a kanta, daga yau kice wannan, sai gobe ki ce wannan. Kina ganin ina da lokacin zama bin kanki ne? I can't leave my work da duk wasu harkokina, ina chasing dinki Na'ilah! I just can't. Don haka idan zaki zauna ki yanke shawarar da zata fisshemu, gwanda ma tun wuri ki yanke. Haba! Na gaji! Na gaji wallahi!! Wai baki da zuciyar tausayi ne? Ko ke baki san kaddara ba ne? Kada ki manta da cewa Annabinmu ma da muke yin koyi da koyarwa shi bai zauna da mata daya ba. Ke a ganinki rashin zama da kishiya zai hana ki rayuwar farinciki a gidan aurenki bane ko me? Kina ina mata da dama suke baro gidan auren nasu babu kishiya ba kome, gasu nan birjik suna yawo akan titi muna ganinsu, amma kuma masu kishiyar suna zaune a nasu gidan salin-alin suna zaman lafiya? Kin kishiya da kike yi kamar izgilanci ne kike yiwa Allah, tunda kin karanta, kin kuma san cewa ba haramun bane a musulunci. Ita kishiyar hauka ce?!".
Yadda ya hakikance yana fada yasa naji nima raina ya dauko baci, a tunanina idan ba'a lallasheni ba, bai kamata ace za ayi min ihu ba. Nace "da kake maganar kaddara da kuma izgilanci, shi Allah ai baya dorawa rai abinda ba zai iya dauka ba sai dai bawa ya dorawa kanshi. Saboda haka ina ji ina gani ba zan kai kaina wajen wahala ba. Tunda nace ka kyaleni, bana so, ba sai ka kyale ni din ba? Ana dole ne?!!".
Yace "haka kika ce ko? To ba laifi. Dama ina bin kanki ne kawai saboda kada kice anyi miki rashin adalci ko wani abu, amma tunda ke kunnenki na kashi ne, kuma idanuwanki a rufe suke, ba kya fahimtar komi, to zan biyo miki ta hanyar da baki so. Idan ke kin iya yiwa zuciyarki rashin adalci ne, ni ba zan cuci kaina ba akan wani dalili can naki! Ina ce ba mahaifinki ne da bakinshi yace ba zaki aureni saboda ina da mata ba ko? Kuma ba Allahn daya halicce ki bane? To ki kashe kunnenki da kyau, ki saurareni kiji, maganar neman aurenki yanzu na fara ta, ba kuma zan tsaya ba sai inda karfina ya kare. Zan kuma yi duk abinda zan yi in ga cewa kin shiga gidan da kike matukar ki, don Allah ki kashe kanki ranar da aka kaiki gidana a matsayin matar aure, sai in ga karshen tsana!".
Nace "Wallahi ba zai yiwu ba, ba kuma zan yarda ba. Ni dama nasan ba sona kake yi ba kamar yadda kake ikirari, in Allah ya yarda sai Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu. Mugun kudirinka ba zai cika a kaina ba!".
Yace "zamu gani Na'ilah!". Daga haka ya kashe wayar.
Naji kamar in fasa ihu, jikina har rawa yake yi tsabar bacin rai. Lallai Yaya Bilal has got some nerves! Har yana da bakin da zai daga yace wai zai aureni ba da izinina ba? Har yana da wannan ikon a kaina?! To ai idan yasan wata bai san wata ba. Zan ga da abinda yake takama dashi kuwa!.
Na share hawayen da suka zubo min, na kara daukar wayata da nayi jifa da ita, na shiga cikin contacts dina. Ina ganin sunan wanda nake bukatar gani, na danna kiran ba tare da bata lokaci ba. Tayi kara daya, biyu, ana uku aka dauka.
.Cike da cheeriness da alamun tsokana da baka taba raba muryarshi da ita, yace "hello, Nas. Ya kike?".
Na dauki ajiyar numfashi na sauke a hankali, na dan kakaro murmushi duk da nasan cewa ba ganina yake yi ba, nace "hello Doctor, maganar ganin iyayena da kayi ranar nan, ka shirya yi yanzu?".
Yace "of course Na'ilah! Dama ni ai jiranki kawai nake yi. Yaushe ake bukatar gani na ne?".
Nace "idan ma a gobe ka shirya, zaka iya zuwa ka gansu".
Yace "Masha Allah, that's good. How about in zo anjima sai mu sake tattaunawa akan yadda za ayi?".
Na dan jinjina kai sama, "yeah, hakan ma yayi. Sai ka zo kenan?". Yace "in shaa Allah. Gani nan zuwa".
Nace "sai kazo!". Na ajiye kan wayar.
*
Kwana uku bayan haka, Janan ta shigo asibiti tun da safe ranar alhamis. Abin ya bani mamaki. A bakin hostel muka ci karo da ita, ni zan fita ita kuma zata shiga. Na kalleta cike da mamaki, nace "lafiya kuwa? Mai ya shigo dake nan da wuri ne?".
Bata tsaya amsawa ko yi min bayani ba, taja hannuna muka koma daga ciki, can gefe, tace "abinda kika yi kina ganin shine daidai a wajenki?".
Nace "me nayi?".
Tace "Yaya Mudatthir ya kira ni dazu tun da sassafe".
Sai lokacin na fahimci dalilin shigowarta din da kuma tambayoyinta. Nima bamu jima da yin wayar dashi ba.
A yadda muka yi da Dr. Na Abba lokacin da yazo ranar litinin, mun tsaya akan cewa zai je Gashua ya samu su Malam su akan maganar mu. A washegari talata na kira su Fatsu na sanar dasu bakin da zasu yi, zai je ne kawai suyi magana, a san dashi, sannan a tsaida ranar da yakamata magabatanshi su je. Su Malam suka yi farinciki matuka, har Fatsu tana cewa har ta cire rai da zaton zata ga wannan rana, ni dai kawai uhmm nace mata.
A daren ranar jiya bayan Dr. ya kira ni ya sanar dani cewa sun dauki hanyar Kano daga Gashua, Yaya ya kira ni. Tambayata kawai ya hau yi akan wai na tabbatar da cewa wanda na turo mishi na amince dashi? Nace ta yaya zan tura wanda naji ban aminta dashi ba wajen iyayena?. Yaya yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, kafin yace "amma kuma Baba yace wani yaje wajenshi a jiya din, shima duk akan maganar ki ne!".
Naji an fara min wani luguden daka a kirji, ashe dai Yaya Bilal da gaske yake ba da wasa ba. Amma a zahiri sai na dake, nace "ni fa bansan ko wanene ba, don ni babu wani wanda muka yi magana dashi akan zai zo bayan Dr. Na Abba".
Yaya yace "to ai shikenan".
Daga nan muka dan yi hira, na tambayeshi jikin Sailu da har yanzu tana asibiti. Yace dukansu lafiya lau. Sannan muka yi sallama.
To yau kuma da safe sai ya sake kirana, yana tambayar wai dama wanda yaje wajen Baba Yayan Janan ne? Nace "ni fa Yaya na fada maka ban san kowanene ba".
Yace "kada ki raina min wayo mana Na'ilah. Ni nasan yadda kika sako karatun nan naki a gaba, maganar aure yanzu bata cikin kanki. Tunda naji dama wai kin turo wani gida kai tsaye, nasan da wata a kasa. Don haka ki fada min abinda yake faruwa".
Nace "to ni Yaya sai dai kuma in karya kake so in maka, amma babu abinda yake faruwa. Kawai na samu wanda hankalina ya kwanta dashi ne, dama can don dai ban samu wanda ya shiryawa auren bane".
Yace "ina wannan yaron da kuke tare dashi kuma fa, sojan nan?". Nace "ni tun yaushe da muka rabu dashi?".
Yaya Mudatthir yace "shikenan Na'ilah, ni dai ina shawartarki da ki bi koma menene a hankali!". Bai jira abinda zan ce mishi ba ya kashe wayar.
Na bi wayar da kallo cikin yamutsa fuska, me yasa ne yake wani magana yana bani a linke? Sai ban saka maganar a kaina ba, naci gaba da shiryawa ta.
To kuma gashi ina fita naci karo da Janan, itama tana bani tata linkakkiyar maganar.
Nace mata "eh, ina ganin shine mafi a'ala a wajena Janan. Ina ganin kuma hankalina zai fi kwanciya a hakan".
Tace "ki dai bi a hankali, kada kije ganin neman gira ki rasa idanu. Ki gujewa garwashi ki fada cikin wuta!".
Na dan jefa