AZATONA COMPLET HAUSA NOVELS BY Jeedderh Lawals.txt

Author :  Jeedderh Lawals Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   51 / 52

150K to 153K   out of 155.4K words

kure, yasa nayi sauce din kwai kawai na dafa shayi, na kai kan dinning da biredi na ajiye. Har yanzu Yaya bai fito ba, watakila barci ne ya kwashe shi. Nayi kwafa da nayi tunanin haka, watau shi har lokacin yin barci ya samu? Ya mishi kyau.
*
Tunda naje asibiti na kasa tabuka komi, tun safe har lokacin tashinmu yayi. Yan kananun ayyuka kamar su dressing da sauransu, sai sauran abokan aikina ne suka dinga yin su. Sunyi tambayar duniya, ce musu ciwon kai nake yi kawai na dinga yin. Haka nan na koma gida dai ranar.
Kasa daurewa nayi, na kira Sailu a waya ina kuka tun karfina da jan majina, mata ta rikice ta hau tambayata abinda yake faruwa. Na zayyane mata abinda kenan, ban boye mata komi ba.
Ina gamawa taja tsaki, na daga baki hangangam cikin mamaki ina saurarenta, tace "to sai me? Ni Wallahi nayi zaton wani mummunan abu ne ya faru, har kin bani tsoro".

Na share hawayen fuskata nace "haba Sailuba, yanzu wannan ba mummunan abu bane?".

Tace "mummuna a ina? Yo wai ita kishiyar karshen rayuwarki ce ko me? Yadda kike yi dinnan sai wani yayi tunanin baki taba zama da kishiyar bane, ke da kika zauna da mata har biyu, kika kuma zauna lafiya balle daya?".

Nace "to ita dayar kinsan halinta ne? Ko kuwa kinsan da abinda zata shigo? Su biyun kin san kalar gwagwarmayar da muka sha dasu? Wata fa har sanadin rayuwata ta kusa yi, dayar kuma taso laka min sharrin kisan kai. Haka kawai ina zaman-zamana azo a sanya ni a uku!".

Sailu ta dan saki dariya, "haba dai, kada ki zama raguwa mana. To wai ma, zaki hana shi yin auren nan ne? In fada miki gaskiya, gwanda tun kuna shaidar juna ki hakura, wallahi ki bashi amincewarki. Allah kadai yasan abinda yake cikin auren nan, kuma duk wasu bore-borenki da tashe-tashen hankulanki, babu fa abinda zai hana. Sai dai idan Allah bai nufa ba, ko kuma idan shi din bai ga damar yi bane kawai. Wannan zamani ma Allah na tuba, wa yake wani tayar da hankalinshi akan wata kishiya? Kin san Allah? Ki daina gani yanzu yana wani bin kanki yana lallashinki, na dan lokaci ne. Tun kafin ya daina biye miki, ki bada kai bori ya hau, don ba zaki ji dadi ba wallahi".

Na daga baki nace, "amma...".
Tace "amma me? Ni fa in nice ke ko? Wallahi babu wani tada hankalina da zanyi, akan me? Miji ne, nasan yana min son da babu wata 'ya mace da zata iya kamo kafata. Idan kuma kika iya rawar ki da takunki, wallahi ko ta shigo babu wani abu da zai sauya. Don haka don Allah ki kwantar da hankalinki Na'ilah, nasan cewa baki son kishiya, amma ina tabbatar miki da cewa ba duka fa aka taru aka zama daya ba. Duk wadda kika ga tayi wani da ba daidai ba, dama can halinta ne. Ke yanzu da ya aureki, kin taba tunanin daidai da rana daya akan kiyi yadda zaki yi ki kori kishiyoyinki?".

Na girgiza kai a hankali, kafin na tuna cewa bata gani na, na daga baki da kyar nace "a'ah", maganganunta sun sanya min rawar jiki, sun kuma jefa ni cikin tunani.

Tace "to kin gani? Halayenki masu kyau ne, haka kuma niyarki tsarkakkiya ce. Zata iya yiwuwa itama wadda zai aura din, maybe, itama niyarta daya da taki. Ba zaki taba sani ba. Kada ki damu, kinji?".

Na kai hannuwa ina share hawayen fuskata with determination, nace "haka ne, nagode Sailu".

Tace "ni ce da godiya Na'ilah, naji dadi da kika fara nema na. Baki nemi wadda zata jefa tunanin da zai jirkitar dake ba. Sai anjima". Muka kashe wayar.

Na koma na kwanta tare da ajiye wayar a gefena, maganganun da muka tattauna da ita suna kara min tariya a cikin kaina.



Karfe kusan bakwai Yaya ya dawo daga wajen aiki. Ina kan abin sallah ina lazumi lokacin daya leko dakina, bai ce komi ba ya wuce inda Muhaaseen take kwance yana mata yan wasanni. Ban ce mishi komi ba har ya gama, ya juyo yana kallona with wariness.
Wani abu yazo ya cake ni a kirji, har yaushe ne mijina ya fara kallona da wannan sigar? Har yaushe ya fara kallona a tsorace, kamar wanda yake tsoron yana daga baki ruwan alkaba'i ne zai fita daga cikin bakina? Ko kuma yana tsoron in yanke mishi kai ne? Oho!. Kodayake, wannan ba shine karonshi na farko ba, waya san abinda tsofin matan shi suka mishi lokacin daya tashi yin aurena?.
Wata dariya ta nemi ta kubce min a lokacin, the irony! Wani lokaci can daya wuce, nima fa shirin shigowa gidan nake yi, ba tare da tunanin abinda matanshi suke dandana ba ta dalilin haka. Sai gashi yanzu nima ina dandanarshi. Allah kenan. Kodayake, auren da aka yi bada son raina ba, ina ma hankalina ya kai ga tunanin halin da matanshi suke ciki?.

Yace "madam, barka da war haka".
Murya a sanyaye nace "sannu da zuwa, ya aiki?".
Yadda ya kalleni cike da mamaki yasa nima na kalleshi cike da mamakin, ko bai yi zaton zan amsa mishi bane? Yace "uhmm, lafiya lau. Ya asibitin?".
Na gyada mishi kai.

Muka yi shiru daga ni har shi, kafin yace "Baby, don Allah ki fara saurarata kiji abinda zan ce". Yayi shiru yana kallona yaga ta yadda zan karbi zancen, ban nuna komi ba, sai idanu dana zuba mishi alamun ina saurarenshi.
Yace "Hajara, diyar Alhaji Musbahu ce, abokin baban nan nawa da naje dubawa a Zaria kwanaki. Cewa yayi kawai ya bani ita, zai aura min ita, ni kuma ban san ta yadda zan yi in ce mishi bana son diyarshi ko kuma ba zan iya aurenta ba. Yayi mana halacci matuka a lokacin da muka bukaci taimako. Don Allah kiyi hakuri, amma idan har ba zaki iya ba, wallahi zan iya cewa na fasa".

A raina nace 'kamar gaske!'.
Na kauda kaina gefe ina jin kwalla na ciko min idanu, nace "ni har na isa in hana ka kara aure? Wacece ni?".

Ban san cewa ya tashi daga inda yake ba, sai da naji ya kamo tafin hannuna, yace "saboda kin isa baby, kin kuma kai matsayin da zaki hana ni din in hanu".
Wata yar siririyar kwalla ta zubo min a kan kumatu ya kai yatsa ya dauketa. Sai na fashe da kuka na fada jikinshi, cikin kukan nake cewa "nasan cewa fada kawai kake yi, amma ba zaka fasa ba!".

Yana shafa bayana a hankali, cike da alamun lallashi yake cewa "try me baby, da gaske nake".
Sai dana lafa da kukan, sannan yaci gaba da cewa, "zata zo ta ganki, idan kika ji bata kwanta miki a rai ba, to sai dai suyi hakuri".
Na dan jefa mishi harara, "ni bana wani son ganinta!".
Yayi murmushi a sanyaye, "I'm sorry baby, I love you!".
Ban ce mishi komi ba, don a lokacin wani sashe na zuciyata rada min yake, 'ya daina sonki yanzu!'.


**


Ranar Lahdi da rana, ina falo ina duba wasu manyan textbooks akan midwifery, duk da karatu dana gama hakan bai hana ni cigaba da neman ilimi ta textbooks ba, idan ma Allah ya bani dama so nake in cigaba da masters dina. Kofa naji ana knocking. Cikin mamakin wanda zai zo a daidai wannan lokaci na tashi na nufi kofar. Yaya ya fita dazu da safe, kan cewa zai je wani waje ya dawo, nasan ma bashi bane tunda da shine da ba zai tsaya yin knocking ba.

Wasu matasan yan mata biyu naci karo dasu, ba laifi dukansu kyawawa ne. Dayar zata yi sa'ata, fara ce ba can ba, doguwa mai dan jiki, yayin da dayar kuma daga ganinta kasan kanwar dayar ce, yanayin kamanninsu da surarsu kusan daya ce, kawai dai karamar tafi babbar kiba da fari.
Nayi yar fara'a duk da cewa ban san su ba, na musu iso zuwa ciki. Sai da suka zauna akan kujera, sannan naje na dauko lemu da ruwa na kawo musu.
Na zauna muka gaisa dasu, nace "ko kuna neman wani gida ne?".

Karamar ce tayi saurin cewa "a'ah, Yaya Bilal ne ya kawo mu nan!".

Na karkata kai ina kallonsu cikin mamaki, me zai hadinsu da Bilal? Na gyada kai a hankali nace "Allah sarki!".

Karamar ta sake cewa "ni sunana Zainab, wannan kuma Hajara". Ta nuna babbar.
Sai lokacin na kula da yadda babbar take ta sunke kai tunda suka shigo. Wow!! Sai lokacin na fahimci komi. Ita ce Hajarar dama? What a nerve she has! Da har ta iya kwaso kafafu tazo min gida.

Kafin in iya daga baki in ce wani abu, Yaya ya shigo cikin falon. Ya zauna a gefena, Allah ne ya iya bani ikon samun dauriya, na cije ban dankara mishi harara ba.
Yace "Madam, ga Hajara na kawo miki".
Na gyada kai ina dan murmushin yake, "aikuwa na ga Hajara"...


Shi ya zama jagorar hirar tamu, ga mamakina cikin dan lokaci kankani muka saki jiki daga ni har su. Ko lokacin da lokacin sallah yayi, tafiya yayi ya barmu. Na kaisu dakina suka yi sallah, muka koma falo. Dana shiga kicin haka suka biyo ni, duk da magiyar dana musu akan su koma falo suyi kallo ko wani abu, fir suka ki. Duk wannan abin da ake yi, Muhaaseen na bayan Hajara a goye.
Kafin Yaya ya dawo mun gama girki. Muka zauna mu duka muka ci ana ta hira.

Anan na fahimci cewa dukansu a Abuja suka tashi, shima Babansu matanshi biyu, in fact, Zainab step sister din Hajarar ce. Ita Zainab tana Abuja uni tana karantar mass com, tana aji daya. Ita kuma Hajara wannan shekarar ta gama degree dinta akan architecture a jami'ar Tafawa 'Balewa, Bauchi.
A abinda na karanta a cikin dan lokacin, shine suna da wani irin sanyin hali da hangen nesa, haka iliminsu ya tabo ta kowane fanni.

Zuwa lokacin da yamma tayi, suka mana sallama akan zasu tafi, sai naji kamar kada su tafi. Allah ya gani, naji dadin zuwansu sosai. Suma daga ganin yadda suka mike din zasu tafi, hakan take. Shima sai da direban da aka turo ya daukesu yazo, sannan suka tashi.

Na shiga daki cikin drawers dina da nake ajiyar abubuwa saboda bakin ba zata, na ciro musu turaruka masu kamshi, chocolates, kayan kwalliya, cike da leda na fito. Muka musu rakiya har gaban motarsu ni da Yaya. Sai da zasu shiga sannan Yaya ya karbi Muhasseen a hannun Hajara, na kula Allah ya hada jininsu sosai.

Na mikawa Zainab ledar hannuna, da taki karba, na harareta cikin wasa, "ko dai kin raina ne?".
Ta zaro ido da sauri, a lokaci guda kuma ta sanya hannu ta karba, "haba dai Anty! Mungode sosai, Allah ya amfana!". Wani halin nasu mai burgewa kenan, akwai godiya. Daidai da abinci wannan dana zuba mana, sai da suka biyo mu da godiya da addu'a.
Nace "babu komi wallahi, ku gaida su Mama Sai mun zo ziyara".
Hajara tace "sai mun ganku!". Daga haka direban yaja mota suka fita daga cikin farfajiyar gidan.

Yaya ya sakalo hannunshi daya akan kafadata, dayan kuma yana rike da Muhaaseen. Yace "ya?".

Na daga kai na kalleshi ina dan murmushi, "uhmm, ba laifi. She doesn't look that bad!".
Yaya yayi murmushi a hankali, ya shafo hancinshi da nawa, "haka ne?".
Na gyada kai ina murmushi. Da gaske ne kuma, haka kawai naji hankalina ya kwanta da ita sosai. Kai duk da cewa tun kafin zuwansu dama na saddakar, amma hankalina bai kwanta ba.
Yanzu kuwa dana ganta, sai naji hankalina ya kwanta da ita sosai, shima auren hankalina ya kwanta dashi.

Watakila maybe, just maybe, ba zata yi halin Ramata, Ameerah ko Raheemah ba. Kila ita za ayi zaman mutunci da ita!.








K'arshe!


'THE GREATEST HAPPINESS OF LIFE IS THE CONVICTION THAT WE ARE LOVED; LOVED FOR OURSELVES, OR RATHER, LOVED IN SPITE OF OULSELVES!'.
VICTOR HUGO






*☆⋆Epilogue⋆☆*





Bayan Shekaru Biyar...


"Ni abinda yake daure min kai shine, babu fa abinda na mishi, kawai daga sama kamar saukar aradu naji maganar, ya sakar min ita aka kamar tashin bomb!".
Janan take fada cikin tsananin kunar zuci.
Ni kuwa me zanyi in ba shekewa da dariya ba? Na dinga kya-kyatata kamar ba zan daina ba. Tana gefena tana jefo min bama-baman harara ita kuma. Sai da nayi ta isheni, na gyara zamana ina kwashe kwallar data zubo min.

Tayi kwafa, "baki da kirki wallahi Na'ilah. Saboda ke kina da kishiya, shi yasa kike sheka min dariyar mugunta nima don za'a min?".

Na daga kafada, "tunda na dandana, kowa ma ya dandana mana. Ke dalla ki kwantar da hankalinki, ki daina wani daga hankalinki akan abinda bai taka kara ya karya ba. Ita fa kishiyar nan, wallahi gane mata ne mutane basu yi ba saboda kawai sun riga sun fadawa kansu ba abokiyar zama bace, amma da gaske abokiyar zama ce. Ke ni yanzu wallahi Abban Maama ko ta uku da hudu yace zai karo, zamana zan gyara kawai ince Allah ya shigo dasu gidan lafiya. Ga fili ga mai doki, to ma wai, a kaina zasu zauna ne? Wasu ayyukan ma zasu rage min karewa. Ko ba komi, kin samu rarar kwanakin girki, kin samu abokiyar tayin ayyuka da hira, kin samu yar tayin raino da hidimar gida, sannan at least, wulakancin namiji ba sai kare a kanki ke kadai ba, ya dinga rabawa biyu yana bata rabi itama".

Janan ta kame baki, tace "Innalillahi! Na'ilah, kece kuwa ko dai wata ce mai kama dake?".
Nayi murmushi nace, "shafa ki ji!".

Ta jinijina kai, "Allah kenan! Kuma rayuwa kenan, babu abinda ta bari. Idan wani yace min akwai rana da zata zo ki tausar da wani akan zama da kishiya, wallahi ba zan taba yarda ba".

Na gyada kai a hankali, ko ni kaina ina mamakin kaina.

A shekaru biyar ko shida da suka wuce, idan wani ya fada min cewa zan zauna in fadi wani alkhairi game da zama da kishiya, hakika da idan muka fara fada dashi babu wanda zai iya raba mu dashi sai Allah.
Ban taba zaton akwai lokacin da zai zo, in so kishiya ba, in kuma kaunace ta, ban taba ba.

Duk a zato na, kishiyar bala'i, masifa ce, wadda zata kawo maka rashin zaman lafiya da kowa naka, wadda zata kawo maka bakin jini ta sanya maka cuta a cikin jiki da zuciyarka. Ashe duk rashin fahimta ce ta kawo hakan.
A zato na, bata nufar kowa da alkhairi sai sharri. Nayi zaton tana shigowa tunanin fitar dani daga cikin gidan aurena zata fara yi, sai naga banbanci.
Tabbas Anty Sailu tayi gaskiya, da tace ba duka aka taru aka zama daya ba. Duniyar Allah mai fadi ce, ba'a rasa mutanen kirki a cikinta. Kamar yadda ba'a rasa abokan zama na gari a cikinta.

Ina ga ni nayi dace ne sosai, Allah ya hada ni da wadda ban taba zaton zan hadu da ita ba.
Koma dai menene, ta dalilinta sai gashi ina kallon abokiyar zama da wani ido daban, in a different way, in a different light.
Ta saka ni fahimtar cewa, tsanar kishiya dana taso ina yi, saboda banyi dacen haduwa da mai halin kirki bane, wadda take kaunar zaman lafiya da zaman aminci da amana.
Ramata dama can halinta mara kyau ne, irin mutanen nan ne da dama can tun asali basa son wani daban ya rabe su ko wani nasu, sun fi son komi ya kasance nasu ne su kadai, basa son cigaban kowa sai nasu. Saboda haka ne suke yin duk abinda suka ga zasu iya, don su ga cewa sun kawar da duk wani abu da zai yi threatening dinsu da cigaban su. Saboda haka ne su son kishiya ko diyanta, baya cikin lissafinsu, me yasa zaka so abinda kasan cewa ya fika matsayi a inda kake so kaga cewa kafi kowa matsayi?.
Haka Raheemah, haka ma Ameerah.

Na fahimci cewa su irin wadannan mutanen, son zuciya da son kai ya musu yawa. Shi yasa basa tunanin komi, kuma basa tunanin kowa sai kansu.
Ita kuma duniyar yanzu, cike take da mutane masu son kai da son zuciya, yan kalilan ne masu son farincikin wasu da cigaban wasu.

Duk ban fahimci hakan ba sai a dalilin zaman da nayi da abokiyar zama na, Hajara. Yanzu zan iya fada da alfaharina, cewa ita ba kishiya ta bace, 'yar uwa ce. Ta dalilinta idanu na suka washe sosai, har nake iya dauko uzurirrika akan dalilin da yasa wadanda na zauna dasu a baya suka dinga yin abubuwan da suka yi din, sai naji na dan fahimce su. Duk da cewa naga rashin wayonsu, tausayinsu yafi rinjayata.
Dama sun bi ta wata hanyar da ba wannan ba.
Dama basu biyewa rudin duniya, shawarar abokan banza, da bakar zuciyarsu ba.
Dama sun bi ta hanyar data dace, dama sun sowa wasu daban irin rayuwar da suke sowa kansu.
Watakila da yanzu muna tare dasu cikin aminci kamar yadda muke zaune da Hajara.

Kwanaki naji cewa Ameerah ta samu tayi aure da kyar, bayan manema kusan shida na fitowa suna guduwa saboda zancen dalilin da yasa ta bar gidanta na farko da suke ji. Sai daya zama kamar ma kyautar da ita ma iyayen suka yi. Gidan mata uku aka kaita, itace cikon ta hudu. Ga tarin 'ya'ya. Hakan yasa ni zama wani tunani, duk wata kauna da iyayenki zasu nuna miki a matsayinki na 'ya mace, ta dan lokaci ce. Dole dai gidan aure nan ne gidanki na har abada. To ko meye amfanin shiga cikin rayuwar auren 'ya'ya

51 / 52