Author : F&F Category : New Hausa Novels 2026
mana rashin maganar ta bashi ne damuwa bah no mattet how karda wani yasamu wannan information ɗin komin kankantar sa in bazata faɗi mana bah a rufe mata baki abinda nake so ya kasance ɓengaren mu take don yanzu ita kadai ce tarkon mu maƙiya da ita zasu cigaba da amfani ku kasance cikin shiri akoda yaushe "
Cikin gamsuwa da bayanin nashi suka fara kaɗa kai kamar ƙadangaru sannan ina son abinci ko min WACECE ITA raina na bani akwai abinda ta taka ina son bayani in details" kark ka wani ji ka wani damu Excellency kabar komai hannu na zan cika aiki" " banda shakku akan ka sp na baka go a head yanzu lokacin barci na yayi sai mun ƙara Zama ɓat fuskar shi ta ɓace a jikin system ɗin.
Dogon lumfashi SP yaja yana tunanin wane shiri Excellency keyi akan yarinyar yasan ko minene abun ba Alkhairi bane abun bazaiyi kyau bah .
HAMDA 🌺🌺🌺
Hamda mu haɗe a gida kawai sauri nake yanzu juyowa nai na kalli Apip daya sa kai yana cigaba da tafiya " wai da gaske Apip bazaka shiga bah ka gaida mammah "idan na dawo na shiga yanzu akwai inda zani yai maganar cike da ɓadda sawu bawai don zai shigan bah ya fadi hakan kawai, hanyar zillewa yake nema . Na kasa fahimtar irin takaici da kuncin da mutanen gidan da yake ji gawar ya AJMAL da aka tsinta a kofar gida tasa duk suka sire mai shiyasa tunda suka ɗauko hanya yake neman hanyar kawar min da hankali na ƙi bashi dama sai yanzu ganin bah kula ni zai yi yasa na shiga gidan da sallama
Mammah na samu tana kuciniyar kunna wutar murhu yayin da juhud ke gyaran shinkafa babpi ( mahaifinsu juhud ) zaune bisa tudinkar ɗakin shi yana ɗinka linzamin doki suna firar su cike da shaƙuwar su a guje juhud ta taso ta rungume ni cikin tsanani soyayyar da take min babpi ina wuni na gaishe shi ina raba jikin mu da fara'ar shi ya amsa "a'a hamda ya jikin naki harkin fara fitane "jiki ya warware babpi "toh Allah ya kyauta gaba "ameen ya Allah babpi cikin jin daɗi na amsa addu'ar sannan na ƙarasa inda mammah ke zaune tana sakar min murmushi "mammah ina wuni "lfy klau diyar albarka ya jikin naki har kin shigo da kanki mu bamu shiga bah "ba komai mammah jiki da sauki sosai ya warware "mashallh Allah ya kyauta gaba "Amin "hamda ya jikin ki nayi kukan rashin ki baki na taɓe ina kokarin amsar mammah in taya ta aiki " a'a ɗiyar nan barshi kinga har yanzu jikin ki ba kwari juhud ku shiga daga ciki "toh mammah tai maganar tana kama hannu na muka shiga ɗakin juhud da baida yawan tarkace katifarta ce dake kwance a tsakiyar ɗakin sai tabarma dake gaban katifar side guda kayan sawar tane sai abinda ba'a rasa bah muna shiga saman katifar na kwanta ita kuma ta fita kawo min ruwa ba jimawa ta dawo tana cewa "wallahi yanzu muke maganar ki da mammah da damun gama girki zan shigo gidan ku "na hutashshe ki ina yunkurin zama na bata wannan amsar "juhud ina waya ta "gwara da kika tuna min duk lokacin da zan fita mantawa nake a cikin akwatin ta ta buɗe ta ciro min wayar sannan ta dawo inda tabarni tana miko min amsa nai ina kokarin kunnata kasancewar wayar akashe take "hamda baki ban labarin abinda ya faru dake bah tsawon kwanakin nan "uhmmmm juhud in ana sallah ba'a magana islamiyya fah nai wannan tambayar don in ɓatar da wancen zancen "Alhamdulillah mun kusa sauka saura 1month muyi waleema wani kalar mummunan faduwar gaba ya ziyarce ni da bansa dalilin haka bah ammh nafi danganta hakan da kalaman ya AJMAL yasa mah saukar nan buri da an motsa sai kaji yace sai kunyi safka zan maki kaza ko in kunyi sauka kaza ko lokacin saukar ku kaza Allah sarki ashe baida rabon gani hawayen dake kokarin fin ƙarfina na haɗiye murya a raunane nace "kun gama suratul nãhl kunshiga isrãfil "ehh har munyi shafi 2 "Allah ya ba ni ikon taddo ku dai dai nan messages da aka turo wayar na kashe suka fara shigo wa siririn tsaki juhud taja "saboda aljanin ki na kashe wayar na tsani en iskan messages da yake turo wa zan iya masa rashi mutunci "zaki aika na ayya cikin raina ammh a zahiri bance mata komai bah saboda takaici naya linka nata kuma kamar yadda nai tunani haka na samu na iske massages da unknown kamar kullum babu wata rana banxa ta Friday daban ganin massages dinnan hakan ya fara ne tun bayan rasuwar ya AJMAL duk friday sai naga messages da boyayyar number kona canza layi a banza ba abinda zai canza tun ina sharewa har abin ya fara damuna yanzu kam ya zaman man jiki yau kusan shekaru 2 kenan in dai Allah ya nunamin friday inshallah sai naga messages ɗin yanzu hakan ce ta kuma faruwa message 2 na gani wani lokacin raina na bani Apip ne ammh inna tuna bazai iya rike abu ɗaya har tsowon lokaci irin wannan bai faɗa min bah yooh shi dakan shi zai tona kanshi sai in saki tashar juhud na tunanin adnan ne ammh ni sam ban yarda bah bai yi nisa cikin ilimi da zai ringa kalamai masu daɗin lafuzza da sauri na tunkuɗe tunanin jin kai na ya fara nauyi kamar yadda ya saba inna fara irin wannan tunanin na maida hankali na gun juhud jin tana cewa gaskiya ƙara zamu kaishi iskanci ya isa haka yayi yawa "hmm juhud kenan komun je maganar guda ce zasu ce zasu canza min layi may be har da wayar kuma ke kin san a banza ni duk ba wannan ba ina son zuwa prison da wani kallar sauri juhud ta .........,,,..............
[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜
BAI SAN NA
GIDA BAH SAI
SAI YA CIZAH
STORY
&
WRITTEN
BY
F&F
( PERFECT PAIRS 🌺)
17.............
Da wani kalar sauri juhud ta kalle kamar wadda tayi gamo ni fuskar ta na bayyanar da tsantsar damuwa tabbas juhud yarinya ce but she have an excellent mental age tana da tunani irin na en 25yrs kuma tana da cikakken jiki in ka ganta zaka ɗauka Sa'a tace ammh na bata 4yrs shiyasa bana jin komai na faɗa mata damuwa ta wani lokacin takan fini rabawa
"Ammh hamda nasan dai baki mance abinda ya faru last year bah "juhud bazan taɓa sarewa bah cikin sauƙi dama ce Allah ya bani in har na cigaba da tuna baya haka shekaru zasu ta shuɗewa komai zai faru wanna shekarar Inshallah saina gana da MAHAIFINA koda zasu ringa yankar naman jiki na "don Allah hamda ki rufa mana asiri ya AJMAL ne kawai ke da lasisin shiga inda yake har su gana in ba tare da shi bah ba yarda za'ai su barki ki shiga " hmm juhud wacce shekarar sunce ni under age ce nayi ƙarana yanzu I'm 19 basu da wata hujja da zata hanani shiga na ɗauki Alkawarin no matter how ............
Sallama mammah ita ta katse mana fira ta shigo ajiye kayan da suka wanke sun bushe, murmushi tai mai kama da dariyar alamar dai taji tattaunawar tamu sai dai ba tace komai kayan ta ajiye a mazaunin su ta juya har takai kofa magana ta ta dakatar da ita "mammah don Allah kar ki tafi kice wani abu man, juyowa tai ta kalle ni kamar zata fita komi ta tuna ta kalli juhud cikin dattaku tace je ki duba min ruwan in sun tafasa kin wanke shinkafar ki zuba min toh tace sannan ta tashi ta fita inda juhud ta tashi nan mammah ta zauna shiru ya ziyarci ɗaki na wani lokaci kafin mammah tasa bayan hannun ta ta goge min hawayen da na kasa dakatar dasu sannan ta dafa kafaɗa ta ta soma magana cikin karfafa min gwiwa.
"Hakika mu masu rauni ne masu kararriyar zuciya ne bazan hanaki kuka bah hamda saboda suna nuna mana muna da rai in zafi yai zafi azaba takai azaba damuwa da ƙunci suka tsanan ta zaka iya faɗuwa kai kuka but never give up karki taɓa sadaƙassa wa don wanna mah alamun nasara ne kece ƙashin bayan ahlin ku mai basu garkuwa a yanzu ke kaɗai ce fatan su ki jure ki jajirce ki zaƙe damtse duk wanda kika ga yana jin daɗi a duniya ki duba bayan shi zaki sha mamaki ita kan ta jarabawa daga Ubangiji ɗaukaka ce kuma duk tsananin da mutum zai tsinci kansu bazai taɓa kamo koda kafar annabawa da suka fi kowace halitta daraja a wurin mai duka, komai hannun ki yake yanzu ke zaki tsara yadda rayuwar familyn ki zata cigaba da gudana anan gaba fata na ki zamo silar kawo sauyi kina da dakiya ni kuma zan kasan ce mai ƙarfafa maki karki taɓa sanyaya koda abinda kika tun kara zai murƙushe ki a koda yaushe kalmar da nake yawan fada maki zan kuma mai maita wa *RESPECT EVERYONE BUT FEAR NO ONE *
Ki rike wannan zaki sha mamaki nauyin da yake kan AJMAL yanzu ya dawo kan ki ki dogara da Allah da yarda shi komai zai dai dae ta"
Hawayen dake fuska ta kaf na share ina sabunta ƙwarin gwiwa ta wannan matar tayi ita ɗin duniya tace kuma role model (allon kwaikwayo) duk yadda matsaloli suka dunkile min kai da nazo wurrin ta na warke Allah ya ba ta baiwar sarrafa halshe mutum ce mai wani kalar yanayi bata taba bari inyi giving up nasani nace zan iya magance matsalolin rayuwa ta ni kaɗai yaudarar kai na nake ammh koda yaushe da kalaman ta inna tuna sai in ga kamar sun kau suna rike a matsayin jagora
Hawaye na nakuma sharewa sosai na fuskance ta "mammah ban sani bah zan iya ƙetare wannan sabon lamarin da ya dannomin kai wasu kalar hatsabiban mutane ne Allah ya haɗa ni dasu da suke neman haɗa tarko dani yanzu fah ba iya mutanen rugar mu idon su ke akai na ƙasa ce baki ɗaya mammah raina na bani abubuwa da dama tabbas mutanen AFTABUDDEEN akwai abunda suka taka suka barni da rai "ki koma ki bin cika mana" da sauri na kalle ta "taya mammah "hmmm hamda ina so kisa a ranki cewa labarin bai zo karshe bah akwai fita ta gaba ki sani duk wani abu da kika ga Allah yayi shi a duniya to akwai dalili kina ɗauke da wani babban nauyi da zai iya kawo sauyi ko akasin haka ya danganta da irin jajircewar ki da yadda abun yai tasiri a zuciar ki ammh tabbas wasan bai ƙare bah wannan shine mafari akwai wani ɓoyayyan al'amarin da Allah ya bar ma kan sa sani.
Shiru mammah ta kuma yi bayan na gama bata labarin kwana ki 10 danai a AFTABUDDEEN tana jinjina kan ta alamar akwai abunda take hasasowa
"Domin kauda kakwanto ki koma kiyu bincike na haƙiƙa" abinda ta ce kenan ta tashi ta fice babpi na kwala mata kira kaina a tunkushe in koma AFTABUDDEEN kamar yaya mi mammah take nufi da yanzu ne mafari wasan bai ƙare bah haka fah waɗanda suka mai doni yake faɗa min lokaci guda gaba na fadi duk tambayoyin nan bani da mai amsa min su kawai nabi hanyar da mammah ta bi da kallo kamar zanga majigin ta.
Dai dae nan juhud ta shigo ni kuma na yunkura na mike "badai tafiya zaki bah "daman waya nazo amsa kuma inji a ina kuke islamiya "toh don Allah ki tsaya kici abinci "a'a juhud saida Apip ya cika min ciki sannan na fito "yana ina ina ta so in tambaye ki "tare muke dashi nasan yana bakin ruwa "ɗan ruwa kenan Apip nason wasan ruwa "uhmmmm kawai nace na fita juhud ta biyo baya nq zatai min rakiya banga mammah bah a tsakar gida tana ɗakin babpi hakan yasa kai tsaye muka yi waje mun ɗanyi nisa da tafiya juhud tace "hamda saura 4 weeks mu shiga sabuwar shekara a"ina lissafi juhud kuma kinsan 31 december kawai ake barin maziyarta su ziyarci en uwan su dake prison (kurkuku) "kin gama tsara yadda zaki fuskanci wannan lamari "juhud nasan wannan lamarin bana wasa bane yana da bukatar natsuwa ammh in kin lura sadaukarwa zanma family na sau ɗaya na taba jin muryar shi tunda nake ban taba ganin shi bah sai a photo shima tun ina ƙarama ya AJMAL ya nuna min yanzu bama zan iya tuna fuskar bah tunda aka sace waya muka rasa photu nan duka wannan ita ƙadaice dama ta ba lallai ne Allah ya ƙara bami irin ta bah ya bani aron aron rai wallahi juhud ina mugun takaicin uba na na raye a wannan duniyar ammh nake rayuwa a matsayin marainiya .
Hamda nasan ki da sa abu a rai mu bi komai a sannu washe garin ranar za muyi waleemae safka 1 ga wata kenan kuma kin san mi hakan ke nufi "karki damu juhud ɗaya bazai hana faruwar ɗaya bah yanzu muje wurin Apip nasan in bakiran naje yi bah zai iya kwana bakin ruwa ne
Haka muna tattauna matsalolin rayuwar mu har muka isa babban kogi mai guda na na rugar mu wanda har yau masu hasashe basu hango ƙarshen saba kuma ɗaya daga cikin ni'imar da Allah yaima ƙasar mu wadatar ruwa masu ɗan karen daɗi gaske shiyasa muke da kyakkyawan yanayi a ƙasar mun iske mutane jefi jefi zagaye da ruwan wasu na shan iska suka zo wasu kuwa wasan ruwa suke ammh iyakar su gefen ruwan don duk haukansu babu wanda ya taɓa kuskuren shiga ruwan koda gigin wasa kuwa in ma mutum ya shiga saidai uwar shi ta haifi wani cen nesa damu kaɗan na hangi Apip duke gaban ruwa ya saka hannun shi na dama cikin ruwa tare da tsura masu na mujiya "yawwa hamda gayacen cewar juhud tana murmushi daga inda nake tsaye na fara kwala mashi kira ammh ina kamar baya cikin duniya irin tamu still juhud na cigaba da kiran shi muna gab da isa inda yake wasu samari suka sha gaaban mu a ɗatace juhud ta ɗago zatai magana ya nuna mata wuƙa ni kuma idanu na zaro ina karanto addu'o'i da duk suka zo baki na ganin yadda matasan dake bayan Apip suka danna kanshi cikin ruwan da murya ta taƙarshe na kira sunan shi tare da ƙoƙarin raɓawa ta gefen wanda yake gaba na zan wuce naji an riƙe min hannu ta baya an kuma shan gaba na cike da ɓacin rai na juyo zanyi magana sai dai wanda na gani ya sani saurin maida idanu na na rufe ina neman tsari da ga Ubangijin talikai "fuskar ya AJMAL da ta saba min gizau da sauri na ƙara buɗe idanuna akaro na biyu tsananin ɓacin rai na ƙara mamaye zuciya ta ya maye gurbin fargabata ina aika ma mulook mummunan kallo shikau ya watse min jajayen haƙoran shi da suka dafe saboda tsabar ƙazanta "baby yanzu dai daga ni sai ke ba AJMAL ba Apip dake tare maki faɗan "kalli" yai maganar yana nunamin yaran shi da suka ɗaga Apip sama suka jinjina tare da wullashi cikin ruwan jikake tinjim!!! Shikau kamar saƙago ya wani sandare ruwan suka yi sama wani marayan kuka ya kufce min Apipppppppppppppp !!!! Lumfashi na har barazanar barin gangar jiki na yake ban san lokacin dana dartsa mah mulook cizo na isa gaban ruwan da zuwa yanzu sun cigaba da gudana kamar ba yanzu aka jefa mutum bah gaban ruwan na zube ina kiran Apip! Apip wata kuturwar dariyar mulook ya feshe da ita shi da yaran shi da duk yawan ci sune a gaɓar ruwan hankali na ya tashi ganin ruwan sun koma normal sai iska mai ƙarfi ya kaɗasu sannan su tafi da ƙarfi lokaci guda na daina jin dariyar su sakamakon shahararren marin da juhud ta watsa ma shafaffar fuskara mulook "kai wani kalar daƙiƙi, dabba, sakarai, bagidaje, banza, gantalalle ne don tace bata son ka shine zaka huce kan dangin ta wallahi ban raba ɗayan biyu da sa hannun ka a mutuwar ya AJMAL zaiyi magana ta ƙara kwasa mai wani mari shi kau kamar wani banza haka yake binta da kallo har taa iso ina da nake ta durkusa da alama dai mulook mutuwar tsaye yai yana dafe da kunci sa yana cigaba da binta da kallo kalaman ta na maimaita amo cikin kunnen shi duk da dabanci da yake kuri dashi .
Ganin ba sarki sai Allah kuma Apip dake kwance cikin ruwa ba alamar yana jin kiran da nake mai balle in sa ran zai motsa har ya fito yasa na mike cikin ficewar hayyaci na nufi hanyar shiga cikin gari neman agaji sai dai taku 6 zuwa 9 nayi from no where kamar daga daga sama naga dirar adnan gaba na yana rangaji (autan inna ramma ) kamar wanda yasha ya bugu muryar shi na fita da kakari
"Hamm.......da.....kkki..........gudu........mah........kirrrrr...........ccccccci........zaaaaa.,..su.......haɗa.......maki
Kafin ys ida naga gaba ɗayan shi yayo kaina da sauri na matsa gefe yayin da shi kuma ya kife ƙasa sai kyarma da yake yayin da lumfashin shi ke fuzga alamar fitar rai lokaci guda komai ya tsaya mashi cak .
Yalwantaccen murmushi mulook yai yana shafa sajen shi daya fara futowa "cika aiki knn" ya faɗa a fili lokaci guda ya daddage ya buga wata kururuwa karar amon yasa har jejujjukan dake kusa damu saida sukai amsa kuwa harta