Chapter 19 Reading CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx Arewa Novels

CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx

Author :  F&F Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   19 / 64

54K to 57K   out of 190.4K words

ajiye bisa side drower ta haye kan gado ta janyo blanket tana rufe rabin jikin ta hakan ya hanani damar ɗauko maku rahoto 😛😛.

Ƙanƙara ta ɗaura akan marar ta (yin hakan na rage raɗaɗin ciwo yayi jinin al'ada) zuwa shuɗewar wasu daƙiƙu ta fara safke ajiyar zuciya sai jikin ta dake kyarma tabbacin zazzaɓi ke neman rufe ta harda shida ke cinta a tsaitsaye.

Ya Rahman hakika kowane bawa da irin ƙaddarar da yadda Allah ya tsara mata ƙaddara miran kan period (al'ada) ta faɗa itace matsala mafi girma a rayuwar ta sunan abun taji sai zuciyar ta ta motsa ita kaɗai tasan halin da take shiga in tana cikin wannan yanayin (nata ba irin nasu bane) shiyasa ranakun ƙarshen wata zuwa farko sune ranaku mafi hatsari a rayuwar ta yana birkita mata lissafi taya ma zata fara kuskuren auren wani ɗa namiji tana cikin wannan gagarumar matsala da waɗannan kalamai zatai amfani dasu wurin mashi bayani ya fahimce ta ba tare da anje inda bata so bah kukan da ya zamo mata jiki ta fashe dashi jikin ta na bata abubuwa da dama zuwan hajja ba Alkhairi bane yau tayi kukan rashin er uwa , er uwa duniya ce rashin ta baiyi bah ko yayane zata rage maka wani abu ta tsaya mah ta baka shawara ta kasa tattauna matsalar ta da kowa ( saboda miran irin mutanen nan ce masu masifaffan zurfin ciki na bala'i da basu bari ko iyayen su su san damuwar su ) a nata haukan zata cigaba da nema ma kanta magani har Allah yasa a dace tunda itama likitace (hmmmm 😏) wannan dalilin yasa take blocking kowane namiji a rayuwar ta ammh hammad na neman goge mata tarihi ya fara fasa ƙirjin ta.

Wannan daren tasah kuka ta gode Allah kamar ranta zai fita a haka ta samu barci ya kwashe ta mai cike da munanan mafalkai wanda yasata tashi a razane harda xufa dake tsatstsafo mata ta na bin jikin ta wanda ko kaɗan baya cikin lissafin rayuwar ta shi ta haɗu dashi a cikin duniyar mafarkin ta GURU a nan inda suka gasa ma juna magana ta tattare babin rayuwar shi ta watsar a cikin dustben ɗin office nata ta cigaba da safgar gaban ta mafalkin yai masifar tsaya mata a rai ta ɗauki lokaci mai tsayi kwance har saida aka gama salla asuba sannan ta yunƙura ta tashi dafe da kanta dake sara mata wani kalar faɗuwa gabanta yayi tai saurin janye blanket ɗin tans bin jikin ta da inda ta kwanta da kallo tasa hannu ta don ta tabbatar da gaske damshi ne batai mamaki bah in dai tana cikin wannan yanayin Hakan na riskar ta bata farga bah kuka take saida taji hancin ta ya toshe bata iya shaƙar lumfashi sai ta baki saboda hancin ta daya toshe tana kuka sosai ta shiga toilet ta tsarkake jikin ta wanke kayan data cire a cikin toilet ɗin sannan ta fita ta yaye blanket da bedsheet tabi wata ƙofa dake kusa da ta toilet da zata sadata da wani space wanda aka tanada don washing machine ta saka su a ciki still kuka take bayan ta fito ta shiraya cikin ƙananan kaya marar sa nauyi sannan ta shimfida preymat ta tada sallah

(Tof fah masu karatu ku ta yani ido 😳 mai al'ada da Sallah towai mike faruwa da miran ɗinne mi kuke tunani 🤔🤔🤔 nasan wannan tambayar na nan na maku ƙaiƙayi cikin rai da zanyi wata magana bari dai inyi shiru🤫🤫 ku cigaba da bina sannu a hankali da kanku zaku kamo bakin zaren).

      A folour kuwa hankalin ya Aryan ya tashi haiƙam tun jiya yake son magana da ƙanwar shi momy ta hana shi zuwa, wai ko yaje bazata kula shi bah taje da kanta taƙi buɗe mata maah duk kawaicin ta taje itama kamar momy bata buɗe mata bah paah kuma aikin dare ya kama shi shiyasa bai san tuwan da suka tuƙa bah da yake paah  ambassador ne.

   🤍 ASALIN SU MIRAN🤍

        Cikakken sunan paah shine ABUTTURAB JALALAIN (ALIYU) Asalin su  mutanen ƙasar Egypt ne aiki ne silar zuwan su ƙasar kasran kakan su tsoho mai ran ƙarfe Abraham kalid  Ambassador ne na ƙasar kasran tun kafin yai aure yake zaune a ƙasar bai san kowa bah a cikin ta rana tsaka a kai mai canjin wurin aiki  dole ya tattaro ya dawo  ya dawo a lokacin yana da aboki  da yake kira jeen  sojane shi kaɗai ya sani a lokacin don haka yana dira ƙasar shi ya fara kira kasancewar jeen mutumin kirki ne na gaban kwatance shi ya safke shi a gidanshi kasancewar gida 2 ne a haɗe a wata estate dake cen ƙarshen gari wadda in ba sojojin bah bamai ƙarfin halin zaman cikin ta   sai dai lokacin jeen yanada mata kuma da alamun sabon aure ne Abraham yayi mamakin zaman su anan a yanayin yadda ya fahimci zaman su kamar suna gudun wani abu koda ya tamabaye shi sai yace yanayin aikin sune a haka dole saida taka tsantsan har cikin zuciya sa Abraham ya gamsu da bayanin shi suka cigaba da zama a haka natsawon lokaci har Allah ya haɗa Abraham da hajja ameeyna suka fara soyayya tun suna yinta a ɓoye har abun ya fito fili hajja anan tsakiyar gari gidansu yake kaddara ce kawai ta haɗa su kamar yadda ko wane masoya ke haɗuwa har alaƙarsu ta kankama koda  Abraham ya koma ƙasar su ya faɗa ma iyayen shi ƙura taso tashi bayan ɗan  harmutsin daya gudana a tsakani daga ƙarshe akai auren silar auren yasa shi ƙara sakewa da mutanen sabon wurin da yasamu kan shi  don dole ya koyi zaman cikin ta Allah kuma yasa mah hannun shi albarka duka abinda ya taɓa sai ya zama kuɗi bayan aikin da yake jeen da kanshi ya bashi jari ganin tarin baiwar dake tattare  dashi ya fara business na kayan sakawa ɗinkaku daga ƙasar kasran zuwa Egypt harda wanna dalilin ƙasashen 2 suka da kyakkyawar alaƙa a tsakanin su ta kasuwanci da har yanzu anayin shi ba abinda ya canza sai cigaban  da ake ta samu kafin kace mi sunan shi ya fara amsa kuwa a cikin ƙasar a tsakanin wannan buɗin daya samu yasiye estate da suke ciki ya gina tambatsetsen gida na zo a gani sannu a hankali silar zaman shi har wurin ya dawo cikin gari mutane nata gine gine duk yadda yaso jeen ya shiga cikin harkar kasuwancin sa ya ƙiya yace aikin da yake ya wadace shi su zauna a haka ba yadda ya iya dole ya hakura. Ammh abin ya tsaya mashi a rai yana nazartar abokin nashi wanda ya lura kamar a ƙaya yake zaune tun lokacin da ya fara samun ɗaukaka hankalin shi ba a kwance yake.

A cikin gida suna zaune lafiya da matar shi da abokin shi da ya maida  tamkar ɗan uwa sun ɗauki tsawon shekaru basu haihu da matar shi bah hakan bai damun shi saboda aikin shi da yasa gaba  sai ma ita musamman in ta buɗe ido taga tagwayen jeen kyawawa na fitar hankali da suka fara takawa hankalin ta na tashi sai taji inama inama  matar jeen mah mutunniyar kirki ce kwata kwata bata da hayani sau da yawa Hajja takan taƙile ta da faɗa (don Hajja tun lokacin ƙuruciya masifaffar mace ce ) ammh bata kula ta takan ce ita abokiyar zama ta ɗauke ta ba kishiya bah haka dai ruyuwa ta cigaba da gudana har shekaru ritayer suka kusanto Abraham gadan gadan knn ya kusa komawa mahaifar sa har zuwa waɗannan shekarun shiru kake ji a ɓengaren hajja ba wani bayani zuwa wannan lokacin ta fidda ran zata haihuwa yaran jeen sukai shekaru 15 kamannin su yanzu sun babban ta ba kamar lokacin suna yara.( Ba identical twins bane )

Ranar wata talata Abraham ya samu kiran gaggawa daga ƙasar su aka buƙaci zuwan shi mahaifiyar shi ba lafiya ba lafiya  dole ya yanki biza ba shiri wannan tafiyar tare da hajja ya shirya yin ta saboda haka tun a daren jiya suka shiga sukai sallama da jeen da matar shi  sun daɗe suna fira har wajejen 12 basu an kara bah saida jeen ya tsawatar kowa ya kama makwancisa sannan sukai ma juna saida safe harda ɗaya daga cikin yaran jeen usainin hassan ɗin ya daɗe da yin barci shima naci ne ya hanashi wai yana roƙon iyayen su barshi yabi uncle rigamar shi ita ja su tsawon lokacin suka maida abin wasa.  Sai a washe gari suka tabbatar usaini har cikin zuciyar shi yake maganar don kuka yasa masu sosai akan shi fa sai an tafi dashi badon ran iyayen shi sun so bah suka barshi shima don suna jin nauyin abokin nashi sati guda zasuyi don haka kayan sati ya haɗa da murnar shi shidai ɗan uwan nashi na gefe yana ta binshi da ido alamu dai sun nuna shima bai so tafiyar bah usaini bai kula shi bah don karma yasa mashi rauni yaji ya fasa.

    Dukansu suka shirya  masu rakiya har airport mamaki yaso kashe su ganin harda maman en 2 aka zo rakiyar matar da tun zaman su basu taɓa ganin ta fita bah duk shekarun nan sai lalura mai tsanani itama fitar dare suke ammh yau sai gata waje. yadda suke ban kwana inka  gani sai kace daga ranar bazasu ƙara ganin juna bah twins da kuka suka rabu kamar waɗanda zasu ƙiyama sunaji sun gani jirgins ya cilla a gajimare saida jirgin su ya ɓace sannan sukai haramar dawo gida.

    Bayan sati 1................................😔😔

         

[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜

               BAI SAN NAH

                        GIDAH BAH

                                 SAI YA CIZAH

STORY

         &

    WRITTEN BY

         F&F

      (PERFECT PAIRS 🌺)

24...............

     

  Sun sauka lafiya sun samu jikin mahaifiyar sa ya tsananta family su mah ba wani yawa ne da subah yayan shi ne sai ƙanwar su mace shiyasa sukai gamayya duk abinda zai faru da mahaifiyar su ya kasance suna atare a kusa da ita daman mahaifin su ya rasu tun da jimawa a halin da suka kai ta asibiti basu tunanin zata tashi bah ammh Allah cikin ikon sa sai gashi ta warware har suka fara shirye-shiryen dawowa lokacin da sati ya cika kamar yadda sukai da iyayen Husain da yaji daɗi garin kamar kar ya barshi, daman nan suke zaune, a cikin kwakin 7 shaƙuwa ta kuma tsananta sosai tsakanin Abraham da husain in ka gansu ba zaka taɓa cewa ba ɗan shi bane  in ma tattauna tai zafi wani na iya cewa suna kama saboda dukan su farar fata ne.

Makarantar husain yasa dole suka tattaro suka dawo ƙasar su ta haihuwa husain na zalƙin bama ɗan uwan shi labarin da yayo masu guzira basu kira su bah lokacin isar su a cewar su bazata zasu masu jiya da sukai waya da jeen yace sai sun ƙara kwana 3  tunda suka doso unguwar suka ga  canji unguwar tai mugun shiru Kamar maƙabarta don har ƙara wata maƙabartar kaji kukan tsintsaye hankalin su bai ƙara tashi bah saida suka shigo babban gate da zai sada su da ainahin harabar gidan anan ne suka shaida akwai gagarumar matsalar da ta auku  gawawwaki bodyguard da basu da da natsuwar ƙilga adadin su cikin mashahurin tashin hankali suka ringa tsallake su har suka samu damar shiga cikin gidan kaca kaca suka same shi ai husain bai wani tsaye dogon jinkiri ba ya faɗi ƙasa ba rai  yadda suka samu gidan abune me matsanancin wuya waɗanda ke cikin sa rayu hakan hakan Abraham ya samu da yai ta maza ya ƙara sa har bedroom ɗin su yanayin yadda akai masu kisan wulaƙanci shi yasa shi yanke jiki shima, likitoci basu barsu  suka farfaɗo bah sai da ƙura ta lafa musamman husain da yaso zautuwa (danma baiga gawawwaki bah).

    

    Abraham ba'a barshi ya ƙara ganin gawar bah har sai da aka kai su gidan su na gaskiya abinda bai sani bah harda Hassan ko ban da shi shidai bai ga gawar shi a gidan bah kuma jami'an tsaro sunƙi mashi gamsashshen bayani, duk iya binciken en  sanda basu iya gano komai akan yadda al'amarin ya faru bah taya? Suwaye? dalilin faruwar hakan? Babu mai wata idea zuwa shuɗewar wasu watanni aka bar maganar yayinda jikin husain ke ƙara ta'azzara hauka yake tuburan daya tabbatar an kashe masa kowa nashi Ganin da gaske illa zaima kanshi likita ya bada shawarar ai mashi allurar mantau ta wasu shekaru don lafiya sa ya manta Rayuwar shi ta baya na ƙididdigaggen lokaci by the time zata sake shi ya dawo ckin mental health nashi Abraham ya yarda ne da wannan shawarar kwai don bai san kowa ba a dangin jeen labari bai taɓa kowa su ya bashi tarihin rayuwar shi shima bai taɓa nema bah ammh a wannan gaɓar yayi nadamar hakan.

Dole ragamar kula da husain  ya dawo hannu Abraham ya zame masu ɗan da basu samu bah tun bayan aure hajja tafi kowa farin ciki musamman da ta fahimci bai iya tuna rayuwar shi ta baya kwata kwata don gudun matsala hajjah ta matsa ya aje aiki subar ƙasar baki ɗaya bai musa bata bah ya ajiye su suka koma ƙasar Egypy baki ɗaya da zama suka ci-gaba da rainon husain kamar ɗan da suka haifa husain shine mahaifin su miran Abutturab shine a salin sunan da iyayen shi suka samai (Aliyu knn) don kauce mah kowace matsala hajja ta kashe sunan husain ta maida mashi Aliyu Abraham ne kawai ke kiran shi da Abutturab Amma ta ƙarƙashin ƙasa yana bincike akan ainahin abinda ya faru da neman dangin Abutturab.

    Bayan shuɗewar wasu shekaru ƙura ta lafa kamar basu taɓa rayuwa ba a ƙasar kasran bah Aliyu ya zama cikakken saurayi grandfah (Abraham) yai tsayin daka Aliyu ya gaji aikin shi duk da hajja na nuna bata so saboda sam zuciyar taƙi kwanciya ai hankalin ta bai kuma tashi bah saida taji wai shima ƙasar kasran zashi ya Rahman masifa ta ringa surfa masu ta inda take shiga bata sannan take fita bah grandfah ya toshe ido da kunne kamar baisan kiɗin da take bah a wurin samun cikar manufar shi ba wanda ya isa ya dakatar dashi dole Aliyu sai ya rayu a ƙasar sa ta haihuwa ko mizai faru shikaɗai yasan abinda ya shirya. Aliyu tun baiso har grandfah ya tusa mashi son aiki ta ƙarfin tsiya gudun kar hajja ta kawo masu matsala duk shirye-shiryen da akai basu sako hajja sai ranar tafiya ƙura ta tashi sosai har Aliyu ya tafi bata lafa bah.

Kasancewar an samu cigaba saɓanin baya government dakan taba shi wurin zama da kula da duk wani buƙatu na rayuwa hankalin sa kwance yake aiki grandfah ya cika burin shi na farko saura na gaba shine aure ya fahimci sam aure bai gaban shi aikin shi kawai yasa gaba shima cikin hikima ya tusa mashi wannan ra'ayi har hankalin shi ya fara kaiwa kan wata yarinya da ya taɓa rage mah hanya yana yawan ganin ta zata islamiyya a hankali ya fara bibiyar ta har yai nasarar sace zuciyar saidai ƙalubale na farko da suka fara fuskanta bazawara ce ta taɓa aure sai dai ba yara hajja ta   rufe ido ta haɗe sama da ƙasa bazai aure ta ba rkici ne akai mai yawan gaske shidai grandfah tunda ya fahimci suna so juna yai alƙawarin aura mashi ita haka akai wannan bikin badon ranta yaso bah don anfi ƙarfin tane kawai ba kowa bace face maah (lailah).

Soyayyar da basu samu damar yinta a waje bah sun sha ta a cikin gida shekara guda da auren su Allah ya albarkace su da samun ɗa na miji kyakkyawan gaske ranar suna yaci suna aiman babu wanda yakai hajja farin ciki lokacin ne ta fara sakewa da maah shekarar ya Aiman 2 ta ƙara haifo shantalelen ɗa namiji ya Aryan a lokacin ne grandfah ya sakar ma Paah duka ragamar kasuwancin sa da yake a ƙasar kasran yai taking over .

Hajja taso ta tada ƙura a wannan haihuwar akan ita fah mace taso a haifa (kuji banni da matar nan sai kace suke bah kan su ) grandfah ya take mata birki bada mah ita akai suna bah ya tattara ta suk koma Egypy tasa kuka ta gode Allah  ta hakura da Alkawarin ta ƙara haihuwar na miji sai ya ƙara aure sai gashi cikin ikon Allah ba wai mazan ta cigaba da haifa bah haihuwar ce gaba ɗaya Allah ya ɗauke mata gaba ɗaya tsawon shekaru ai sai ƙofar sabon wulaƙanci ta buɗu ba'a taƙale ta bah tayi ina ga an taɓo ta gudun kar grandfah ya kawo mata cikasa ta tattaro tai bakeke gidan ɗa ta hakimci grandfah saida ta safka yake jin lavari baice da ita komai bah ya zuba ido harda hajja ta bugi ƙasa tace sai ya ƙara aure baice da ita komai bah sai eyes wai bazata yiyu aita haifo mata yara maza bah ai suma mata rahma ne tana son ta gansu cikin zuri'ar ta ita ta haɗa auren momy da paah momy ɗiyar ƙawar tace ko nace aminiyar ta  ta karfi da yaji Paah ba don yaso bah ya amince da auren shi a tsarin shi mace ɗaya ta ishe shi kuma 'ya'ya bai damu mace ko na miji bah maah dai bata ce komai bah har Paah yaso nuna damuwa shi ita ta kwantar dashi.

     Bayan aure sa da momy zaman lafiya suke na ban mamaki dukan su bamai

19 / 64