Author : F&F Category : New Hausa Novels 2026
itace da furanni sai na'urorin dake aiki da sassarfa na fara taka stair ina kokarin isa kofar da zata sadani da waje naji kukan tsuntsa ban san daga inda ya tashi bah ya fara kewaye ɗakin tsuntsu ne mai bala'in kyau ya tafi da imani na kalar sararin samaniya sai ratsin wasu kalolin da suka kara mah zanen halittar shi kyau motsi na yasa shi tashi ya zagaye ɗakin kusan 3 times sannan ya sauka aka frame dake zaune bisa wata drower saida ya tsayu sannan ta gane parrot ne mai kyaun gaske maganar danaji yanayi ya ƙara sheda min haka saidai ban fahimtar da wane yare yake maganar balle ai maganar fahimta MALIK kawai kawai zan iya cema naji daga ganin shi rigimamme ne musamman yadda yake tsalle tsalle kuma alamu sun nuna komai yake cewa dani yake ban san na shagala da kallon sa bah ya burge ni matuƙa .
A hankali na juya na kalli kofar dana jiyu sautin buɗewar ta shi kuma tsuntsa ya tashi sama ya cigaba da zagayen sa nanny ce sai habib, Aziz sai Apip dake bayan su su duka fuskar sun kwance da murmushi banda Apip dakan sa ke duƙe ya kasa kallo na, yana cikin shigar su Pakistan dressing mashallah yai masu kyau sun amshi patar shi yayi kyau har ya gaji saida ni kam hankali na ya kasa kwanciya nasan yau juma'a ana shigar mutum ammh kallon dasuke bina da shi yasa ni bin su da irin nawa shigowar wata mata data kasance baƙuwar fuska a gare ni na bita da kallo tana tunkaro ni da fara'arta "mashallah, tabarakkallah, Alhamdulillah, insha'Allah zaki zamo haske mai kwaranye duhu" baya naja kaɗan na kalli nan tana share hawaye da bayan hannun ta, sannan na kalli Apip fuskar shi tayi ja sosai gab yake da fashewa da kuka "Apip ko zaka faɗa min mike faruwa ne" idan kujerar da ya jingina jiki ta motsa toh shima ya tanka min "APIP" na kira sunan shi da karfi magana ta ba ƙaramin tsoratar dashi tai bah daga yanayin yadda ya zabura na shaida hakan ba shi kaɗai bah duk wanda ke falour saida ya kalle harta tsuntsun da Aziz ya kama da kyal saida ya fire yai sama "ki wantar da hankalin eta ba abin tashin hankali bane........"
"Assalamu alaikum" murya mai cike da dattaku da kamewa ita ta hanani bama matar amsa na bi mutumin da kallo ma'abocin ƙasubar da cikar kamala mutum ne mai cikar zati da annura Muslunci ya ƙawata fuskar shi a kallo guda da nai masa na fahimci malami ne ko limami daga yanayin shigar shi zaka sheda hakan "HAMDA MAS'UD WAGINI" ya kama suna na kan shi tsaye murya ba gargada shi yasa ni kallon shi a razane yana min nuni wai in natsu cike da dattakun sa ashe bani kaɗai yasa cikin halin ɗimuwa bah harda nanny da matar da bansan ko wacece bah tun shigowar sa fuskar nanny ta canza, akwai Magana sosai a baki na ammh kwarjinin sa ya hanani amayar dasu kawai na fashe da kuka ko na samu sauƙi abinda ke cin zuciya ta "kanwar" Apip ya faɗa yana tunakaro ni shima kuka yake sosai sai dai ban san dalilin nashi bah kusa dashi na matsa nima shi kaɗai nasani shi kaɗai nake sa ran zan iya samu makafa a wurin shi da irin tafasar da tsokokin jiki na ke min "Apip don Allah kafaɗa min mike faruwa miyasa hankali ya kasa kwanciya. "ƙwanwar aure suka ɗaura maki yanzu haka daga cen muke ku....." A take ji na da ganin su ka ɗauke na wucen gani ban samu damar jin karshen maganar tashi ba ras³ sau uku kirji na ya buga wannan wane kalar hauka da jahilce ne taya ta ina aka taɓa ɗaura aure akan aure kuma lokaci guda anya mutanen nan basu sabauce bah kallon su nake da idanuna ammh bana jin abin da suke cewa harta ƙarin bayanin da Apip ke min ban tsinci komai bah shike nan shirin da nake akan mahaifina ya tarwatse komai ya lalace saboda aurin fin ƙarfin Nan da aka min ba haka nai fata bah nasa rai sosai akan auren haɗin da Arɗo ne ya jagorance shi shikenan komai ya tashi aiki kallon mutanen dake falour nake kowa na ƙoƙarin tofa albarkacin bakin sa wajen kwantar min da hankali da gudun gaske na kwasa na koma ɗakin da yake matsayin nawa jin ƙafafu na na niyar zubar dani muryoyin su ƙara dagula min lissafi suke Apip bai bani space bah ya take min baya yana kira na da muryar shi ta ƙarshe.................
[16/12, 10:01 pm] Teemah MS 🥰💖: CINNAKA 🐜🐜🐜
BAI SAN NA
GIDAH BAH
SAI YA CIZAH
STORY
&
WRITTEN BY
F&F
(PERFECT PAIRS 🌺)
59..........
Ajiyar zuciya mutumin ya sauke yana bubbuga sandar ban girma dake rike a hannun haggun sa a ƙas a alamar takaici nanny ya kalla data gama haɗe rai kamar wadda akai mah bushara da mutuwa murmushi yai irin nasu na masu ilimi yana shirin magana nanny ta ɗaha mashi hannu Fuska a tunkushe ta fara magana "Na taka matakin nasara a karo na biyu akan zaɓin matar MALIK nice wadda na zartar dashi har yaushe ne zaka cigaba da kutse a cikin lamurran mu zuwa yanzu yaci ace ka saduda ka bar wahalar da kan ka akan alaƙatar data riga ta tsinke a tsakanin su akwai tazarar biliyoyin shekaru ka sani MALIK yayi nisan da baya jin kira"
Faffaɗan murmushi dattijon yai mai cike da dattaku daya ƙawata da ilhamar ilimin sa saida ya daidaita tsayuwar ta riƙaƙƙun malamai sannan yace "hmmmm!!! Ba komai zan kira tunanin ki dashi ba sai yaudarar kai mai mahanga irin taki kamar misalin wanda ya shuka ƙwai ne a cikin ƙasa da fatan wata rana zai fito ya ginu kamar sauran itace har ya fitar da 'ya'ya kwatankwacin abinda ke cikin ƙasa wannan shi ake kira da jiran tsammani ko nace aikin banza kina mance cewa ita zuciya a kullum cikin canji taake abu da ta so yau wataƙil shine abun kyamar ta gobe zaki sha mamaki aka wayi gari masoyi ya zama maƙiyi haka zalika maƙiyi ya juye ya zama masoyi kibar yaudarar zuciyar da ɓata lokacin ki domin MALIK ba yaro bane sannan kuma ba kanwar lasa bane ya wuce tunanin duk yadda kike hasashe bazan ɓata lokaci wajen maki bayanin waye shi sai dai ke ki bada labari sannan batun maganar zaɓin matar shi mu jira lokaci shi zai tabbatar mana da zaɓin kine ko zaɓin Allah har ila yau ina ƙara tunatar dake ba'a canza wa tuwo suna......"
Yana kai nan ya juya ya nufi hanyar fita fuskar shi shimfida da kayataccen murmushi, nanny har saida ya ɓace mah ganin ta Sannan ta ɗauke kai ta rumtse idanun ta da ƙarfi takun saƙa da mutumin nan akwai haɗari kullum cikin duhu yake sa akan wannan sarƙaƙiyar tarasa gane kuramen baƙin sa ammah koma minene dole ta motsa kar ta tsaya kallon ruwa kwaɗo yai mata ƙafa" kukan tsuntsun ya katse mata tunani ta bishi da kallon sai shawagin sa yake da iya gudun sa yana kiran sunan mai shi MALIK duk ya takura kanshi (alamar yana kewar sa) duban ta ta maida kan habib dake amsa waya mai mahimmanci daga yadda ya natsu shida Aziz da ke kusa dashi ta fahimci MALIK ne abinda suke cewar ne bazata iya juyo bah daga bisani taga sun nufi wata ƙofar data kasance a cikin folour ba kowane zai san da ita ba sai su da suka san kan gidan da alamar gaggawa tattare dasu ajiyar zuciya ta safke tana wani tunani harta isa ga ƙafar fita ta fice idanun ta na kallon ƙofar ɗaki na..
"Hamda don Allah ki tsaya ki saurare ni ki tsaya nai maki bayani duk ba yadda kike tunani bane akwai abunda nake so ki fahimta akwai wani abu da ya daɗe yana ci min rai yau na samo mafita akan shi ki natsu ki bani aron hankalin ki "Apip mi kuma ya rage kafaɗa min bayan ka taimaka wajen rusa min rayuwa da hankalin ka da tunanin ka zaka yarda a ɗaura auren nan nayi tunanin ko wane abun cutar daya dumfaro rayuwar kafin ya cimmin zaka ci galaba akan shi ko minene sai inda karfin ka ya ƙare ammh a yau na fahimci nayi kuskure Apip ina alƙawarin daka ɗaukar mah ya AJMAL kenan ka cika na faɗa maka bana son auren nan bana so! Bana so!! Duk wata fitila da nake tunanin haska gobe na da ita ta toshe taya kake tunnain zan iya fidda Abba na daga kurkunun ƙaddarar cen bayan ina garƙame anan ba abinda zance. Mah APIP sai godiya good for you daka biye masu".
Hawayen fuskar shi ya share ya matsa daga kofar ta datse ya fara taku cikin ɗakin yana koƙarin magana a tsiyace na dira ɗayan side ɗin n agado kamar naga mugun abu a halin dake cikin bana buƙatar wata takura ina son kasance ni kaɗai na tattauna da zuciya ta "HAMDA...... Maganar sa ta tsinke sakamakon hannu na dana daga masa "Apip ka fita ka kyale ni wallahi ban son ganin ka "pls 🙏 ki ....... "Nace ka fice 😡😡" cikin tsananin daka tsawa na katse mashi hanzari data rikita duk wani kuzari nashi ni kaina saida ya bani tausayi yadda yasa hannu bibbiyu ya rufe kunnuwan sa idanun shi su rine sunyu masifar jaah ga uban gumi da yake fitarwa jijiyoyin kansa sun fito raɗo raɗo anan take jini ya faɗa bibbigo masa baki da hanci da kunne tabbacin ciwon sa ne ya taso gadan gadan kamar fitar bullet haka ya bar ɗakin da gudun masifa ina jin lokacin da yafashe da marayan kukan daya karya zuciya ta na sandare a inda nake tsaye ban san mah miye abin yi bah gaba ɗaya kwalwata ta toshe zuciya ta ta daina aiki na manta bai son ko faɗa bare tsawa musamman ga wanda yake so baƙin cikin auren nan ya rufe min ido har na manta da raunin APIP da ciwon sa juwar data kwashe ni na zube bisa gadon ta hanani bin bayan sa da gaske nima ban lafiya ina buƙatar mai kula dani ga sahihiyar yunwa data gama cinye en ciki na tunda nazo AFTABUDDEEN ban ci wani abinci mai nauyi bah sai ruwa da kayan marmari komai nasu tsarguwa nake dashi......
NAMIR 🌺🌺🌺
Wannan ai zancen banza ne mikai bayan tafiya ta na sakar maka ragamar kula da komai ammh ka nemi tarwatsa komai sai in ni na samu tangarɗa ka dunga dangata ta da bama NAMIR dama kasan girman asarar da wannan wautar taka zata haifar mana "banda wani zaɓi ne Excellency mi kake tunanin zan iya akan hatsabibin yaron nan kasan ya wuce tunanin duk manazarta ya sha gaban su hatsabibin gaske ne ka bar tunanin muke juya lissafi shi lisssafi ya kwance min a jiya dana ganshi a fadar shugaban kasa a matsayin baƙo na musamman ban san mi NAMIR ya taka bah mi yake nufi damu bah wallahi kamar akan ƙaya nake haka aka gama zaman nan abun ya ɗaure min kai sosai shiyasa nai maka kiran gaggawa muma tufkar hanci NAMIR ya wuce duk inda tunanin ka zai kai.
A slow Excellency ya zauna yana shafa sajen sa daya fara ajiye furfura sai dai ba sosai bah duk duniyar nan ba wanda ya tsana irin uwaiz Alhassan bayan wasu mutanen dasu nasu wurin ya wuce misali yana kawo mashi cikas sosai a harkokin rayuwar sa ya dakushe masa walwa gashi yanzu abubuwa sai kwance masa suke saboda NAMIR shi yanzu babban tashin hankalin sa dukiyarsa daya mallaka mashi ita ya rasa gane manufar shi ya canza salon tafiyar tun kan azo wannan gaɓar ya gama fahimtar hatsabibancin NAMIR baya ɗaukar wargi in baiyi niyar abu bah ba wanda ya isa tilasta tashi koda yake cika bakin shi ya raine shi tsakanin sa dashi ya saki kuɗi ne yai masa aiki ya biya sa ammh bai
san faɗi tashen sa bah balle akaiga sanin wurin kwanan sa da mutanen da yake cuɗanya da so ko sanin tushen sa bai damu da sanin hakan bah tunda yana samun biyan buƙata dalilin shigowar sa wannan tawwagar silar uwar gayyar wannan kungiyar Leena ita ta tsince sa a lokacin yana cikin halin neman taimako ta bashi mafaka sannan suka ɗaura shi akan turbar data zama makamar aikin su da lasisin zama ɗan kungiya har yanzu da Excellency ke wannan tunanin bai taɓa bin kanunun labarai bah akan shi daɗin aiki dashi ya mantar dashi mahimmancin bi diddiqi.
Leena dake a wani ɓangare na ɗakin tana duba wasu takardu ta gyara zaman ƙasaitar ta tana sanye cikin classic suit data maida sutura golding colour ta ciki white ta kama ta sosai ta yadda ta bayyanar da zubin halittar ta kallo kawai abin tsoro ne da tashin hankali ga wani wulaƙantaccen Aski data ɗaura mah kanta babu wata alama dake nuna ita ɗin mace ce sai Muryar ta data kasa canza da zubin kamannun ta riƙaƙƙiyar en jagaliya ce shaharar er daba da yanayin rayuwa yasa ta zabar ma kanta wannan hanyar suna ɓuya a bayan wasu suna baza nasu Mulkin dabancin matar nan iya kane ta saita kibiyar sharrin ta akan abu sai ta ɗaiɗaita shi sannan zata bar zuciyar ta ta huta, shiyasa tunda ta rasa dama akan Apip ta rasa sukunin ta ta kowa ne hali neman shi take a raye ko a mace dalilin wayar da sukai da Excellency yasa ta shirya wannan zaman a en kwana kin nan abubuwa taɓarɓare masu su silar mutane 3 NAMIR, HAMDA, APIP dole mah suma tufkar hanci.
Kallon shi tai a karo na biyu tana shafa wuyan ta daya sha zanen tatu lokacin guda ta amshi abinda madam ke muƙo mata dake a matayin pa nata "ƙhamis just come down mana" leena ta faɗa tana zuƙar sigari "taya Leena! Taya!! Kin san mafarin takun saƙar nan babu buƙatar jan maganar nan da nisa rasa wannan damar kamar rushewar ginin da muka ɓata lokuttan rayuwar mu nuna aikin shi ne gwagwarmayar da muka sha nisan ta mai tazara ne babu wanda zai shiga tsakani na da cikar muradi na na barshi ya shaƙi iska mai daɗi a duniyar nan" a matuƙar azalzale ya ƙarasa maganar kamar zai kai bugu zuciyar sa na daɗa kumbura nauyi kaɗan zata ƙara ɗauka taa tarwatse a mamakin su maimakon Leena ta fusata kamar yadda ta saba sai ta saki lalataccen murmushi irin na gogaggun en barikin nan "tunda nace ka kwantar da hankalin ka bai kamata kasa mah ranka damuwa bah sanin kanka ne in akwai wadda akafi tauye mah haƙƙi a tafiyar nan bayana yake ammh inna tuna Aski yazo gaban goshi yafi zafi sai in sake sabunta ɗamara ta tsarin na nan ba abinda ya canza Excellency, NAMIR ƙaramin alhaki ne da nake hango ƙarantar sa kwatankwacin ƙwayar gero a cikin ruwan maliya yadda geron nan bazai tasiri a cikin ruwan bah haka zalika sha'anin shi bs zai gilgiza dashen mu bah matakan da muka biyo muka zo wannan matsayin da muke yanzu ba ba wani mahaluki da isa taka irin sa bayan all what happened akwai tazara mai yawan gaske a tsakanin mu"
Ajiyar zuciya ya safke a karon farko yasan ya kawo kuka gidan mutuwa in tace zata yi toh tabbas tama aikatan ne baida shakku akan ta maganar taya ji ta cigaba dayi yasa shi sake kallon ta "khamis saidai wani hanzari bah gudu bah "mike nan..."
Shigowar wanda basu zata ko tsammani ba yasa su hucking suna kallon shi basu zaton zai bari suƙara 4 eyes dashi wasan ɓuya zasu fara ammh da yake gawurtaccen ɗan rainin hankali ne ashe yana cikin gidan babu wanda yasan ta ina ya shigo kuma a wane lokaci alamu sun nuna ya jima don daga upstairs yake safkowa yana sanye cikin wayayyun suit shima dark blue da suka amshi ƙirar jikin sa ajibota ɗan gayu akwai iya sarrafa wanka irin sune ke sa kyau yai kyau ko bashi da kyau dukda bai da wannan shahararran kyau kamar yadda ake zuzuta tautarun hikayoyi a zubin halittar da Allah yai mashi shi ke ɗauke hankalin mai duban shi ga ko wane wanka na hawa da kirar halittar sa gizazon sa shine adon sa yayin da kamewar sa da dakiyar sa suka zamar masa kwarjini mutane da dama na shayin sa, idanun sa akwai glass kamar ko yaushe wanda mutane da dama ke tunanin medicated ne saboda yawan amfani dashi shiyasa da yawan su basu taɓa cin karo daa kwayar ido sa bah saidai shatin zanen sa the glass is unique.
Cikin takun sa na sa kai da neman magana ya tunkaro su irin wanda ke ƙara masu tsanar sa da ruru wutar kiyayyar sa don alamun rainin ne karara saida ya tako tsakiyar falour ya tsaya farkon kujeru ta yadda zasu ganshi ya gansu face to face Yana kaɗa key ɗin mota dake sagale a yatsan sa manuniya hannun damar sa na haggun wayoyin sa ne 2 ya riƙe. Mamaki ya ci ye su daga zaune watau yaron nan bala'ine shi ɗin mai laifi ne a gare su ammh har yake da karfin halin fuskantar su haka kai tsaye baya fargabar tsotsan da zai iya faɗawa kan shi.
"Hy guys" da yatsu biyu yai masu wayayyiyar sallamar sa data kara kumbura zuciyar su ta kawo wuya motsi kaɗan zai kara su amayar da ita yaron nan ya raina masu yawo a haife zasu iya haihuwar sa har gara sp daya fisu kananun shekaru shi ke bai tolerating iskancin sa daya yi yake take shi birki yanzun mah shine ya fara magana "A lallai yaro yaro ne bai san wuta bah sai ya taka