Chapter 37 Reading CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx Arewa Novels

CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx

Author :  F&F Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   37 / 64

108K to 111K   out of 190.4K words

samu er natsuwa  "hmm hamda wannan kasada ce kike shirin yi da rayuwar kisan ko wanene kike shirin ƙalubalan ta  wannan  kai tsaye rayuwar ki ce kike wasa da ita a saman gadar da ambaliyar ruwa ta ya dagargazata baki da masaniya yadda ƙarshen wasan zai kaya "

"Na sani miran ammh dole ce wannan kasadar in bah ta hakan bah bazan samu cikar buri na bah kisan rayuwar gaba ɗayan ta kamar cacaca ce iya kasadar ka gwargwadon nasarar ka na shirya mah wannan faɗan ina son in jefi tsuntsaye 3 da wannan damar na farko hankaltar da manyan ƙasar nan da aka maida jahilan ƙarfi da yaji na biyu ceton  Apip da Abba na Sannan tsallakar da mutane daga faɗawa haɗari na sani cakwalkwalin wanna hanyar dabaibayin sa yawa ne da shi ammh ko minene na shirya akan Apip da Abba na tare da haka nai imani Allah yana tare dani a kwafta kawai miran".

Murmushi tai min da alamar jinjina akan ƙarfin hali na rayuwar ta tana son mace mai self confidence da zata iya tsaya ma kan ta. Cikin son sanyaya min rai tace "Ni kuma ki ɗauka wata garkuwa ce da Allah ya aiko maki a wannan yanayin naki zan tsaya maki wannan faɗan sadaukar wane zan saki video da nai maki ammh ta wata fuskar daban ta yadda saƙon naki zafi tasiri zuwa dare inna gama editing  muga mi zai faru zuwa safe yanzu sauri nake akwai hidimomi sosai a gaba na,

murmushi nai da ya maye gurbin ɓacin raina nace "haka fa gobe ne ɗaurin auren ki fa" murmushin yaƙe tai min daya jefa ni tunani tana yunƙurin miƙewa sai dai ban ida tantance manufar murmushin taba naga juwa ta kwashe ta tai baya zata zube da sauri na taro ta  dukan mu kan carpet muka samar ma kan mu gurbi  "miran lafiya kike kuwa mike damun ki haka" ba amsa sai lumfashi da take fitar wa sama sama zuwa shuɗewar wasu mintuna inai mata fiffita na ga tana yunƙurin miƙewa  a galabaice "baki da lafiya ne" na kuma nanata tambaya ta  "da dai sauƙi hamda taimaka min in tashi" tai maganar da koƙarin ƙaƙaro murmushin ƙarfi hali. Lokacin da muka miƙe daidai hairan na shigowa da ladabi ya ɗan rinsina "ranki ya daɗe na samu ya ɗaga wayar da kyal bayan an tashi masallaci zai shigo. "Ka faɗa mashi na fasa yasha zaman shi ni yanzu gida zan wuce".  Jim kaɗan hairan yayi yana kallon miran dake magana a zafafe ganin fuskar ta ba yanayin mata musu yasa ya bita da toj ya fice Ni kaina saida na tsare ta da idanu.

Tare muka fito da ita duk da ina lura da yanayin ta komai cikin ƙarfin hali take yin sa kuma taƙi bani fuskar tambayar abinda ke damun ta saida ta matsa suka sauke ni a mashigar rugar mu kamar waccen ranar a hanya kowa da abinda ke daƙaiƙayar zuciyr shi da damuwar shi shi yasa mukai zaman shiru ba mai wani magana har muka rabu.

Ba gida na wuce bah direct gidan su juhud na fara shiga nayi sa'ar samun mammah ita kaɗai nan nake faɗa mata duk abinda na shirya don bazan ɓoye mata na ɗauki matar kamar matattarar siriri na dake na ji nan nafi ko ina aminta da wanzuwar shi  wannan karon faɗa ta rufe ni da shi bata bani goyon baya ba wai wauta ta tayi yawa banda ƙarfin da za'a kai ƙarshen wasan nan dani ta umarce ni dana kira miran na  faɗa mata ta dakatar da komai har sai mun sake shiri mai lasisi na dai bita da toh da bata haƙuri ammh bawai don zan kira bah in dai ba Apip suka saki bah bazan saurari kowa bah a yadda nake jina yanzu yaron da ko misƙala zarratin bai san wahala bah Apip irin mutanen nan ne da yafi dacewa a kira su da en madara koya ya samu chanjin weather sai fatar shi ta nuna ga ciwo yana fama dashi iya daɗewar shi a hannun su iya yadda ciwon zai ci jikin shi kuma wannan haɗiri ne ga Lafiyar shi rashii samun haɗin kan mammah yasa ban. Wani jima a gidan bah na nufi gida duk da ban so shigar sa saboda kewar Apip dake hanani sukuni  kum nasan halin da zan iske inna da Ardo zai ƙara min damuwa  kamar wadda ƙwai ya fashe mawa a cikin haka n shiga gidan ban san ina zan saka kaina naji sanyi bn son ganin waɗannan mutanen a damuwa saida nakai zuciya nesa sannan na shiga gidan da sallama ta  cen ƙasa maƙoshi abinda na tarar a cikin gidan ya sani tsayawa daga baki ƙofa na kasa ida shiga saɓanin abinda nai tunani na tarar na tarar da abinda yai bala'in gigita tunani har ƙaramar haddar dake kaina saida ta taɓu ya kuma sake shigar dani a wani sabon babi.

Abinda na tarar shine..........,......................

  

[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜

             BAI SAN NAH

                    GIDAH BAH

                          SAI YA CIZAH

STORY

     &

WRITTEN BY

    F&F

  (PERFECT PAIRS 🌺)

   

   43................

Abinda na tarar shine zaune na same su tsakar gida sunyi jigum jigum tsananin alhini bayyane yake a fuskar su yoo sun kasa zaɓa tsakanin murna da kuka wanene mafi da cewa a wannan yanayin da suke ciki sai dai damuwar ɓatan Apip ya dakushe farin cikin su  tabbas inna ta tabbatar da ba wata ƙura a ƙasa ba abinda zai hana Arɗo haɗa liyafar cin abinci a gidan sa sai ikon Allah tun daga yadda suke bina da kallo bayan shigowa ta yasa na ƙara shan jinin jiki na hankali na ya kuma tashi kusa da inna na rakuɓe ina bin uwayen tillin kayan da ban san Asalin su bah kaya ne na ban girma  da bajin ta da kuma karrama wa a kallo guda na shaida daga gidan sarauta suka fito a ido da ka kalla no need of more explanation silar halin da nake ciki na rashin natsuwa ya hana mani damar ɗauko maku rahoto  na dai lura da kayan abinci da sutura.

   Kallon da suke min yana kuma ɗaga min hankali kuma sun ƙi cewa komai ga fuskar su ba walwala yasa na kasa jurewa sai da nace "Don Allah kuyi haƙuri ku faɗa min mike faruwa  wani abun ne ya samu Apip ko ƙarata aka kawo maku don Allah kumin magana".

Maimakon su bani amsa sai suka sakar min murmushi a tare da ya kuma jefa ni ruɗani  ganin da gaske fa hankalin nawa ya tashi yasa Arɗo faɗaɗa murmushin shi a ƙoƙarin shi nason kwantar min da hankali sannan ya soma magana "ki kwantar da hankalin ki hamda ba abinda kika yi kuma inshallah ba abinda zai faru sai Alkhairi inai maki fatan Alkhairi da sabuwar rayuwar da zaki shiga Allah yai maki Albarka" ni dai kallon shi nake yadda yake suɓurɓuɗo min Albarka with smile all over his face  ganin ban fahimci inda kalaman nashi suka dosa bah yasa yafara man bayani

"Bayan na bar wurin taron chief imam ya bada umarnin ya nemo mashi iyayen yarinyar nan shine fah shine fah aka ringa wannan ƙus ƙus ɗin daga karshe har saƙon ya isa kunnen Arɗo sai bayan da aka safko juma'a suka samu damar tattaunawa  a kilisar maimarta ba inda yake keɓancewa don tattauna family issues matuƙar mamaki Mutanen masarautar sunyi mamaki girman matsayi da Arɗo yake da shi a gurin maimarta saboda ba kowa yake samun damar da ya bama Arɗo mafi yawan lokuta wakilta wasu yake musamman akan maganar da mafi yawan manyan sarautar sun san dalilin zaman kuma a keɓantaccir kilisar maimarta shikan shi Arɗo yasha jinin jikin shi ya tsora yadda Chief imam ke mu'mulantar sa kamar ya san shi bayan abubuwan da suka gudana na al'adun masarautar chief imam ya bukaci sanin cikakken tarihi na dana yaya na da labarin sa ya karya masu zuciya. Abinda bakin Arɗo zai iya lalubowa kawai ya bashi don bazai yiyuwa ya faɗa mashi komai bah a irin wannan taƙaitaccen lokacin, jin shirun chief imam yayi yawa bayan yakai aya yasa Arɗo satar kallon shi harda waɗanda zaman ya shafa tabbas duk wanda yasan waye chief imam ya hangi fuskar shi a wannan lokacin zai ci karo da canjin yanayi. Sai dai maganar da yai yasa duk mai rai a wurin saida ya kalle shi da tsantsar mamaki babu wanda yai zaton hakan shi kan shi Arɗo saida wutar kan shi ta ɗauke.

A sanin da sukai mah chief imam mutum ne mai tausayi da mutunta ƙimar ɗan adam sun ɗauka tallafin daya saba bayar wane zai bayar mah a yanzu ammh sai yazo masu da babar kalam "AURE"  yana neman ma yaron shi UMAR  aure na  kuma wai Umar  gaskiya mai martaba ya matuƙar basu mamaki duk da Arɗo maganar ta zo mashi a bazata baiyi ƙasa a gwiwa bah ya bada aure na kai tsaye ba tare da wani dogon  tunani bah ka wai abokin sa yake hangowa da girman amanar daya damƙa mashi"

   Shirun da yai yasa na sake kallon shi sai kuma naji ya cigaba da cewa "Da yau za'a ɗaura auren na nemi alfarmar a barshi sai sati mai zuwa in mun sake shiryawa  kuma kema kina da haƙƙin ki sani waɗannan kayan" yai maganar yana nuna min uban tilin kayan nan da zamu iya raba shekara muna amfani dasu basu ƙare bah  "kayan sa ranar ki ne hamda, Alhmdllh ina matuƙar godiya ga Allah da nuna min wannan ranar na kusa sauke  nauyin da mahaifin ki ya ɗaura min na tarbiyyar ki har kika kai matakin aure"

Sai kuma yai shiru sakamakon 4 eyes da sukai da inna dake ta sakin murmushi tana shafa baya na ni kam tuni na daina fahimtar zantukan Arɗo tunda yai maganar  AURE na daina fahimtar zantukan nashi maganar mahaifina kawai ke amsa kuwa a raina

"MIJI KI SHINE ZAI NUNA MIN HANYAR DA ZAN FITAR DA MAHAIFI NA DAGA WANNAN HALI"

   "UMAR" na sake maimaita sunan ƙasan zuciya ta tun kafin na ganshi nake jinsa a kaina tabbas duk abinda zai kaini ga cikar buri na komai ƙanƙantar bana wasa da shi  "hamda kinyi shiru tunanin mi kike  karki sa a ranki don ina son ki aure na sauke AMANAR mahaifin ki zai sa nai maki auren dole ki faɗi gaskiyar abinda ke ranki ni mai fahimtar kine" murmushin yake nai masa haka nan naji bugun zuciya ta na da ɗa linkuwa ko don Abba na zan amince da auren nan na yarda na sadaukar da farin ciki na  yanayi na duk ya canza bansan ta yadda a kai  baki na ya furta kalaman amincewa bah sai da naji  sai da naji Arɗo na zabga hamdala da ƙara sundumo min Albarka ni ban san yadda suka kare bah don ɗaki na koma.

   Kamar ko wace juma'a unknown ya turo min saƙo taya murna akan wannan ranar da dogon gargaɗi da banda natsuwar  karanta shi yadda ya dace bare har ai maganar fahimta saboda saƙo na biyu da yai masifar ɗaure kai na ya jefa ni duniyar tunani yadda akai naji  maganar aure na bakin shi da ina da tabbacin bayan su Arɗo da masarauta har yanzu maganar bata kaiga fita bah  kaina ciwo yake min sosai ga tunani na ƙara ta'azzara yanayin nawa na damfarar da wayar a ƙasa ba tare dana mayar da reply ba kamar yadda na saba na tafi duniyar tunani  wallahi zuciya tai min nauyi sosan gaske na kai matakin da bazata iya ɗauka bah kamar yadda mammah ta daɗe tana faɗa min abubuwa sun min yawa  ammh inna tuna Allah baya ɗaura mah bawa abinda bazai iya ɗauka bah sai naji na ƙara samun kwarin gwiwa but for know i need shoulder to cry, Apip shine babbar matsalar da tafi addabar ruhina wallahi wani abu ya same shi bazan yafe mah kaina bah ammh ina ƙoƙarin tausar zuciya ta wajen hanata wani yunƙuri zan hakura har sai miran ta saki video a yanzu  na ajiye batun Abba na har sai na haɗu da wanda suka kira da UMAR zanga wace gudunmuwa zai bama rayuwa ta kamar yadda Abba na yace  ( wai nace ba  hamda kina da tabbacin shine kalaman Abba sukai inkiya akan shi da zanyi wata Magana ammh dai nayi shiru).

  Har marece ina ɗaki zazzaɓi ya rufe ni sosai saboda nauyin da zuciya ta tai  duk da halin da nake ciki bai sa saduda ba a lokacin na tuna da number wayar ɗawisu da yace ya saka min hauka hauka nake  so ai ma case ɗin Apip saboda haka na danna mashi kira  bayan mun gaisa yake faɗa min halin da ake ciki kamar yadda Adda tace jami'an tsaro zasu zo su ɗawisu sunje  sai dai basu samu wata hujja bah dake nuna yaje ɗin  bah kenan messages dana ke mai bashi ke maido replay bah "ehh hamda wani salon ɓadda kama ne don kar ai wani yunƙurin har san da abubuwa zasu cakwale mana  na ƙara bincike tun daga prison cikin sauƙi ya samu dukkan bayanai da yake akan idon mai gadin komai ya faru waccen rana tsoro fya fargaba ya hana yai min bayani  saboda barazanar da sukai mai in ya bari maganar shi ta fito jinin  dangin sa fansar tona masu asiri ne shiyasa yai shiru da siyasa irin ta en sanda ɗawisu ya matsi bayanai daga gare shi "wai wata baƙar mota ce tata fi dashi bayan sun shaƙa mai abu da ya fito yana neman wani wannan bayani ya matuƙar daga hankalin mu ya ƙara narkar da zazzaɓi na"

  Dole ɗawisu ya zo gidan mu ya kwantar mah da inna da Arɗo hankali da tabbatar masu da izinin Allah zai bayyanar dashi  nan kusa bayan Addu'ar samun nasara da nabi su da ita ban kuma cewa komai bah na rakuɓe jikin bangi kaina da zuciya ta ciwo suke min sosai abubuwan sun min yawa na rasa ta ina zan fara har barci ya kwashe ni ban samu hanya ɗaya bah ta warwarar matsalolin

  MIRAN 🌺🌺🌺

   Zuciyar ta a dagule haka ta isa gida ta rasa mike mata daɗi mike damun hammad tun ranar da ya tabbatar ta amshi soyayar shi  yake ta wulaƙanci bai kiran ta bai ɗaga wa in takira bai kuna biyowa yanzu mata tana tunanin kamar blocking nata yai bai kuma taɓa zuwa gidan su bah da sunan zance ta wai mi hakan ke nufi ne yaƙi bata koda ƙofa ɗaya taji damuwar wai a hakan zasu aure ba wata sahihiyar fahimta a tsakanin su gaskiya da sakal dole mah a sake zama hawayen fuskar ta share ta fito daga motar gidan su makil yake da mutane abin tausayi wai sunan murnar taya ta biki suke bil haƙƙi hidima suke akan wannan aure da ta ɗauka dashi da babu duk ɗaya ne bata da yadda zatai Ammh da bah hakan bah.

  Yawan jama'a yasa ta wucewa sashen yayyan ta cen ne kaɗai take tunanin ke da sauƙi mutane ga kanta dake mata ciwo sosai sam bata buƙatar hayaniya a irin wannan lokacin a kulle ta same shi saida tai amfani da keys ta buɗe a tsaftace komai yake kamar yadda tasan mamallakin muhallin yake sarkin tsafta (ya Aryan) batai mamakin jin ɗakin tsit bah yanzu 2:10pm basu isa dawowa masallaci bah itama haramar sallah tai a bedroom ɗin ya Aryan tai duk duminiyar ta harta gama ta dawo falour basu dawo bah bata mah da tabbacin shigowar su yanzu abine mai wuya musamman ya Aiman muskili  Sarki kunya ita a yadda mah take kallo tsoron mutane yake bai cika shiga cikin su bah sosai har gara ya Aryan da zaren ya babbanta da yadin kwata kwata halin su ya bambanta yana shiga mutane sosai ammh wani lokacin kanwar jaah ce.

Ganin har 3:00 ta gota yasa ta fidda ran shigowar su  ta miƙa hannu ta ɗauki system ɗinta da ta ajiye akan kujera ta fara rage aikin hamda a yau take son ta gama komai  gobe tasan bata da lokaci, kusan 10 minute kenan da ɗaukar system ɗin ta zuba mah screen ɗin wayar ido ta kasa taɓuka komai photon ta da yayyan ta duka da yake matsayin wallpaper ta tsura mah idanu damuwa na neman mah zuciyar ta illa da sauri ta ture system ɗin gefe sakamakon cikin ta da yai bala'in hautsina mata kamar ta cire shi ta ajiye gefe haka take ji hawayen data kasa tsayar dasu ta share ammh hakan bai hana wasu zuba ba in ta tuna gobe ne ɗauri auren ta jikin ta mutuwa yake musamman da wanda ake shirin haɗa ta dashi, tsabar ƙin da take mah auren ba wata alama da zaka kalla ka shaida amarya ce to be sai gyaran da Aunty sugra ta tilas ta matayi dashi kawai ta tsira.

      A haka gwarazan yayyan ta 2 suka shigo suka same ta (ko ban faɗa baj kisan su) ya Aiman ne gaba sai ya Aryan na biye da shi a baya ya tsaya danna waya suna maganar akan humaid da junaid ko zasu zone ko sun zo ohoo!!! ban fahimci kan zancen nasu bah sakamakon ya Aiman daya taƙaita shi silar tozali da lil sis ɗinsu dake yunƙurin miƙewa tana cigaba da zubar hawaye don wani kuka mah ta ƙiƙira sabo marar dalili ya Aryan takalmi yake cirewa idon shi akan ta har ta iso inda ya Aiman ke tsaye ta fashe ta sake fashewa da kukan da ta daɗe tana tanajin sa don irin wannan ranar ta faɗa jikin sa da iya ƙarfin ta riƙeta ya Aiman yai sosai ganin tana niyar zubar dasu ya fara shafa bayan ta da sigar kulawa da lallashi kafin ya raba jikin su ya

37 / 64