Chapter 27 Reading CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx Arewa Novels

CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx

Author :  F&F Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   27 / 64

78K to 81K   out of 190.4K words

da dalilin zuwan shi "ka kira shine" a fusace ya aiman ya kalle shi kamar zai kai mai bugu "komai ni zanyi kai minene aikin ka a matsayin ka na babban yayan mu wannan fah aikin ka ne nake yi ga wayar kai zaka kira shi" ya faɗa yana dangwarar mai da wayar bisa cinya ya murguɗa baki tare da ɗauke kai. Faffaɗana murmushi yai yanzu baida lokacin sa yasan yanzu yace wani abu tijara ce yaringa yinta daga nan har lokacin da Allah zai sanyaya shi shiyasa bai biye mashi bah ya lura neman masifa yake number da yaga anyi saving da hammad ya danna mah kira aiko cikin Sa'a ta fara ringing.

HAMMAD dake tsaye gaban cloth set ɗin shi da zafi nama yake en dube dube ya gama haukata ɗakin tsaf yai wankan ƙananan kaya gefe guda trolling ne daya gama haɗa kayan tabbacin tafiya zaiyi at any moment dai dai yazo kwasar wayoyin nashi kira ya shigo wayar datai ringing yasa bai wani ja aji bah ya duba duk wanda yai saving number shi a cikin wayar mutum ne mai mahimmanci a wurin shi ganin sunan dayai mah miran saving na wayo yasa shiga shock yana ƙare ma sunan kallo kamar zai iya hango taswirar photon ta  a cikin sunan wannan ne karo na farko a rayuwar shi da miran ta taɓa kiran shi har ta tsinke bai dawo daga duniyar mamaki bah ya Aiman bai karaya bah ya sake kira kamar mai tsoron wani abu haka ya ɗaga kiran yakai wayar kunne maganar 5minute sukai ya janye wayar daga kunne ya koma gefen gado ya zauna yana son gazgata abinda kunnuwan shi suka jiye mashi bai samu isashen lokacin tantance yanayin da yake ciki bah wayar shi tai ƙara alamar shigowar message address ɗin inda zasu haɗu ne ya Aiman ya turo mashi ya daɗe yana kallon message ɗin har saida wayar ta gaji ta mutu don kanta kafin ya ɗauki key ya fito folour a nan ya tarar da tawwagar dandazon abokan shi da suke kwana a tare (da yake gidan maza ne ) wata inkiya yai masu da hannu suko sukai mai alamar jinjina suka 4 eyes da wani saurayi dake cen nesa dasu kaɗan a tare suka sakar ma juna murmushi Sannan ya fuce .

Mintuna 30 sukai shi gidan ya Aiman, acen ɓangaren bayan ya Aiman ya tura message ɗin ya kalli ya Aryan da yaƙi taunuwa ya ƙi haɗuwa  cikin tsokana yace "sai kuma mi ranka ya dade kamar bazai kula shi bah yace "jiran zuwan shi "gaskiya yau ka zafafa ɗan uwa bari na kawo mah abinda zai sanyaya ka" bai jira cewar shi ba yamiƙe ya fuce.

Da bala'in sauri big aunty dake laɓe bayan labule tana sauraron su tai azamar barin wurin ta nufi kichen ba shiri saboda yafi kusa da ita ta san dole ya Aiman ya biyo ta kichen daman nan yayo ɗaukar cup, hakan yasa ta ƙirƙirar sanwa marar dalili ko shawarar abin da zata dafa bata gama bah taji muryar shi kamar daga sama "lafiyar ki kuwa" cikin kama kai ta juyo tana en kame kame shidai ya Aiman kallon ta yake yana son fahimtar wani abu ganin fah allura na niyar tono galma yasa big aunty mazewa tace fruit nake haɗa ma baƙon mu  bai kula ta bah ya ida shiga kichen ɗin yana wani taɓe baki saida ya ɗauki cup ɗin yai mata kallon data kasa bashi ma'ana da babbar murya ya sake maimaita "fruit da albasa"  sai lokacin ta kula albasa fah take yankawa kafin tai wani yunƙuri ya fuce ta saki wawiyar ajiyar zuciya ta safke harda su duƙewa tai zaman dirhen a kichen a hankali murmushi ya fara bayyana a fuskarta har takai ga ƙyalƙyacewa da dariya kai kace sabon kamu a hauka "wai da gaske wannan mayyar yarinyar nan aure zatai kuma shine Aiman bai taɓa faɗa min bah ammh baƙin hali bai bah komin baƙin cikin ka baka isa rusa min shiri bah yanzu zan tai mataki na biyu tunda wannan aikin yaci" kamar an tsikare ta haka ta miƙe "kar wani abun ya faru bata nan da a bata lavari gwara ta ba wani.   Bata daddara bah ta koma inda take masu leƙe dai dai lokacin ya Aiman ya shigo da hammad big Aunty har dasu ƙara zungura kai sai dai duk da haka bata samu damar ganin face nashi bah.

Ya gabatar mai da kayan abinci da shi da kan shi ya shirya su in dai don ta matar shi ne sidai suji kunya iya ruwa kawai hammad ya iya sha ba tare da ɓata lokaci bah ya Aiman ya mashi bayanin komai bai ɓoye masa ba h sai abun da ba'a rasa bah shiru wurin ya ɗauka na wasu daƙiƙu again ya Aiman ne ya ƙara magana saboda ya Aryan ramawa yai ya share su "HAMMAD wannan ba magana bace ta dole magana ce ta ra'ayin kai burin mu miran ta faɗa hannun wanda zai ƙaunace ta ya riƙe mana ita amana  har yanzu kana sonta " in a very slow motion hammad ya ɗago ya kalle su jijiyoyin kan shi sun mugun tashi idanun shi sun yi red completely fuskar shi ta canza lokaci guda kamar mai shirin shiɗewa shin shauƙi ne ko mamaki Allah ne masani yama kasa magana murmushi ya Aiman yai ya samu amsar tambayar shi tundaga body language "Alhamdulillah minene shirin ka kallon shi yakuma yi yana sakin sanyayyan murmushi da ba kowa ke fahimtar hakan bah sani mai ɗauko maku rahoto 😁😁 cike da girmamawa yace "na gode sosai da wannan karramawar Allah ya bani ikon riƙewa ammh daso samu ne kar asa bikin lokaci mai tsayi saboda tsaro (badon tsoro bah na ida mah kar wani ya kasa ka)  "karka damu muma baza mu saka shi da nisa bah 2 weeks masu zuwa muke son komai ya kammal" da murmushi all over his face yake wannan maganar.

Ya Aryan da tun ɗazu baice komai bah yana dai sauraron su  ya yunƙura tare da miƙewa  tsaye lokaci guda yana cewa "tunda kun gama daidaitawa saika turo magabatan ka gidan mu gobe su tattauna bai jira amsar su bah ya fice zuciyar shi na suya yana son ƙanwar shi bai so sha'anin auren ta yazo a haka bah gagarumin shagali yai niyar shiryawa da mijin da take matuƙar ƙauna shi kan shi ya samu natsuwa dashi ammh hammad ɗin nan sama sama bai wani kwanta mashi bah irin sosan nan.

       Tuƙi yake yana tariyo tattaunawar da sukai da yayyan miran yarinyar da ya daɗe yana fatan mallaka zuwa wannan lokacin mah ya fidda rai sai gashi Allah yayi nashi ikon yana ganin abun kamar a mafalki wayar shi ya ɗauka ya nemo photon miran daya daɗe yana mata bata sani bah ya shagala da kallon ta sai kace ya manta tuƙi yake yi bai san lokacin da yai cilla wayar bah ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya da tasa ya kusan cin karo da icce Allah ya taƙaita wahala yaci birki daman da yake titin bah yawaitar mutane idanun shi sun ƙara jaah sosai a cikin wannan yanayin ya koma gida.

(Hammad yaya dae mi kake nufi masu karatu ku tayani judging).  

Ya Aiman bayan tafiyar su falour ya dawo ya cigaba da aikin shi da ya soma ya Aryan ya tashe shi big aunty na zaune gefen shi gulma na cinta ammh bata ga fuskar amayar da ita bah kasa jurewa tai saida tace "munyi wayada hajja tace tare za'a haɗa auren miran da Aryan haka ne"

Ɗan kallon ta yai kaɗan ta saman  glasses dake idanun shi sai kuma ya janye idanun shi ya basar da ita kamar bai ji ta bah a fakaice ta antaya mai harara duk da haka batai zuciya bah  saida ta kuma cewa magana fah nake my dear "uhmmmm" ya fitar da sauti ba tare da yako motsa bah "kuma shine baka faɗa min bah mu fara shirye-shirye waye mijin da zata aura ? Ko shine dalilin dayasa Aryan yazo a fusace ? Wannan karon gaba ɗayan shi ya ɗago yana kallon ta har glasses ɗin sai da ya cire ya banko mata harara kamar daga sama taji yana cewa "wanda kika laɓe kika ji bai ishe ki bah sai kin ƙara bugun ciki na wallahi ki kiyaye ni kar ki fusata ni ki kama min ƙeyar ki kafin na rage mata tsawo ki fita harkar ahlina ki tsaya iya matsayin ki miye haɗin ki da auren miran miye ne zai ƙare ki in kin san mijin da zata aura koda sanin ki ko babu ko dake ko babu ba abinda zai hana miran aure tun ba yau bah na lura kamar kishi kikeyi da ita wallahi in baki fita harka ta bah ranki zaiyi mummunan ɓaci ki canza hali stupid girl mtswww " ya maida glasses ɗin shi ya cigaba da aikin shi, cikin ƙunƙuni big aunty ta murguɗa baki "aammh Yanzu mun zama ɗaya daga cikin ku inda mutunci ai nima er uwar kuce" cikin daka tsawa yace "bahijjah bar wurin nan kafin na safke maki kai ki bace min da gani kona saɓa maki kamanni" ai ba shiri ta tashi tana dire dire ita ala dole ya ɓata mata rai indai kaga suna faɗa kan miran ne ita kaɗai ke haɗa su fada.     

Da isar ta ɗaki kan gado ta faɗa tasha kuka mai isar ta "wallahi Aiman zan baka mamaki zan gwada maka gudunmawar dazan bayar a wurin auren mayyar ƙanwar nan taku da take neman handame komai tai bake bake  tai babakere ta hana komai motsi ni kaina ta hanani rawar gaban hantsi gidan mijin da gidan mu

(Gidan su ya Aiman take nufi fa kuji min wannan matar marar guri irin wannan kakkaɓar rikici zan kira shi ko cigiyar sharri lallai kina tare da baƙar  wahala kishi da kanwar miji da alama kin zare)

In mah mijin bai man bah bazaki aure shi bah kai kuma zaka same ni ne zakai masu bayani dalla dalla dani kake zancen haka ta cigaba da sabbatu tana kwale kayan jikin ta komai tana tilli dashi son ranta.

🌺

Zazzabi ne yaci ƙarfin miran yasata barcin dole zuwan maah 4 tana barci momy na sashen hajja data tutse ta gaba wai Dubai zata tura ta zaɓo ma miran rantsatstsun kayan ɗaki irin waɗan da babbar yarinya mai class kawai ke iya mallakar su duk sun gama shiri yadda tafiyar zata kasance ita ma maah abun yaci ta tayi waya da su aunty sugrah sun tabbatar mata gobe zasu ɗauko hanya twins da maah kawai suka samu damar sallama takaici hajja yasa basu da momy bah saboda tana sashen ta sai dai a waya sukai sallama ita da paah da sauren yayyan su sunso ganawa da miran ammh tana barci wuraren mangarib ta tashi shima kiran hairan ne ya tashe ta cikin magagin barci ta ɗaga wayar da sallama muryar ta na bayyanar da halin jinyar da take ciki  "A subhanallah ranki ya daɗe baki da lafiya ne "kar ka damu hairan mi ya faru "ɗazu da safe na amsa kiran shugaban human rights she accepted our request zatai fira dake 30 ga watan nan  anyi min afuwa ranki ya daɗe na aran maki baki na ci albasa na bata ok "ba komai hairan ko nice abinda zanyi kenan ranar yaushe ya kama "talata  "aikin ka na kyau hairan ku shirya komai yadda ya kamata na ɗan ɗauki hutun aiki kwana 2 saboda banji daɗin jiki na  "ba damuwa ranki ya daɗe Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana bara in gwada kira hammad"  daga haka ta katse kiran wayar.

Zazzaɓin ya safka sai uban gumi da take yi a hankali ta fara tariyo  abunda ya faru awannin 6 da suka wuce ya Aryan kawai take jiran jin ta bakin shi  tasan ba zai yarda da auren fin ƙarfi da ake shirin aza mata ta ƙarfi da yaji zai tsaya mata duk abin da ya yanke zata haƙura tabi tana tsaka da tunanin nan hamda ta faɗo mata a rai tunda sukai chat kwanakin baya basu sake gaisawa bah tuna alƙawarin da taimin yasa ta ɗaukar waya ta kira ni sati biyu nan ke gare ta duk wata a gender ta cikin su take san kammala su musamman waɗanda suka danganci aikin ta .

HAMDA 🌺🌺🌺

Lokacin na sallame sallar ina addu'a kiran ya shigo har ya tsinke ban ko kalli wayar ba sai da na kammala da har zan fita kiran da inna ke min wani ya kuma shigowa ganin sunan mommy's girl yasa ni ɗaukar wayar ba wani jan aji lokaci guda ina kallon Apip da ya wani ɗage min labule yana en zazzage zazzage ni ban ma san mi yake cewa bah sai tijara yake ban kula shi bah na amsa mata sallama muka gaisa a mutunce kamar daman mun san juna  "hamda kinji ni shiru wallahi uzururruka ne  sukai min yawa " ba komai a daman irin ku saida uzurin "toh ya maganar mu har yanzu tana nan "murmushi ne ya kufce min da ban san dalilin yin shi bah na ɗauke kaina daga kallon Apip dake ta antayo min harara sannan nace "Ehh tana nan "ok mu bari next week wanna satin I'm busy "ok ba damuwa Allah ya kaimu "inna fidda rana zan ƙara tuntubar ki' kafin na bata amsa fit Apip ya fizge wayar "time over" yace yana kashe wayar "wai don Allah Apip miye haka kasan da wa nake waya "ba damuwa ta bace sanin wannan abinda ya dame ni kije gidan su juhud ki amsovmin p cap ban san gulmar da yasa kika ɗauke ta bah har kika baro min kaya na  "haba gidan su juhud ɗin nan baƙon ka ne kaje ka amso mana aiki zan taya inna  "ni na kaita kin san dai gidan nan ba wurin zuwa na bane just je tashi ki tafi gobe ita zan saka" siririn tsaki naja ina cire hijabi sannan na kalle shi tare da antaya mai harara  "wai miyasa abu baya wucewa wurin ka Apip koda su ko babu su Allah ya ƙaddara a ƙofar gidan za'a tsinci gawar ya AJMAL miye na ruƙo" kafin ya gama daidaita tsayuwarshi  fit na fuce na faɗa ɗakin inna da yafi kusa suna magana da wata maƙwafciyar mu data shigo "lafiya" suka ce suna tsare ni da ido kafin na samu damar basu amsa Apip ya shigo yana huttai  "mi ya faru" inna tace cikin katse mashi hanzari  kafin yai magana nace "inna gidan su juhud zai aike ni da tsakar daren nan (kuji wai tsakar dare a lallai hamda ƙarfin hali kike) na amso mashi p cap nace ya bari sai gobe wai shi a'a "haba Apip ka bari sai gobe mana tunda ba amfani zakai da ita bah yanzu itama matar tasa baki suka cigaba da ba Apip baki ni dai gwalo nai masa na shige ƙuryar inna ai kasa magana yai nasan ba don babu ita bah kawai yana da abinda yafi wannan mahimmanci ya fuce.

MIRAN 🌺🌺🌺

Wayar tabi da kallo bayan Apip ya kashe mamaki ƙarara a fuskar ta ta ƙara maimaita time over tai shiru na tsawon lokaci har saida kanta ya fara sarawa shigowar maah shi ya ɗauke mata hankali tana tambayar ta jiki ta amsa da sauƙi nasiha tai mata sosai akan hakuri da biyayya kafin ta bata umarnin sallah.

Bara mu leƙa ɓangaren Excellency muga su kuma ina suka kwana...............................

[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜

                BAI SAN NAH

                             NA GIDAH BAH

                                     SAI YA CIZAH

STORY

     &

WRITTEN BY

    F&F

  (PERFECT PAIRS 🌺)

    33.....................

        ZAUNE suke a katafaren gidan da suka kaɓe don irin wannan zaman na sirrin su daga gani wannan na musamman ne tun daga yanayin shigar su zaka shaida hakan, su biyar ne Excellency, SP, DSP, madam (mamar Afrah), sai driver mota ta biyu (wanda ke bin bayan ta farko nasan dai baku manta NAMIR ba) wanda suke kira da jay shima ɗaya ne daga cikin manyan yaran Excellency ne ammh yafi bada ƙarfi a ɓangaren SP saɓanin NAMIR dayake ɓangaren Excellency wuri yayi shiru jay na narrating masu abinda ya faru a filin shaƙatawa daman saboda hakan SP ya tura shi daman cen bai yarda da Namir bah bayan ya kai aya ya ɗaura da cewa "ranka ya dade tun ranar naso sanar dakai halin da ake ciki sai na samu labarin kayi tafiya lallai ku ƙara bin cikar Namir ba haka kawai yake zaune bah" a fusace sp ya karɓi zancen da cewa "ai yanzu ka dawo cikin natsuwar ka ranka ya daɗe tun yaushe nake mah hannun ka mai sanda akan yaron nan na faɗa maka mu rabu da kwallon mangwaro mu huta da ƙuda  na ga take taken shi manyan kuɗi yake hari ji wata babbar dama da ya samu ta kawar da shegen  yaron nan ammh yai watsi da ita in bazai iya bah ya faɗa sai muyi assigning wani" Excellency dai baice komai bai sai iska da yakai ma naushi yana murzar da mai huce daga bakin shi alamar disappointed tsanar da yake ma guru iyaka ce bai da burin da yace ace yau babu shi a doron duniya ammh wannan sakaran da yaba matsayi  matsayin bawan shi yai watsi da damar DSP ya amshi zancen da cewa "jay kasan mutumin da ya kawo mashi motar ina nufin cikin yaran mu ne " a'a ranka ya daɗe duk bin ciken da ya kamata nayi nayi ban taɓa ganin shi bah new face ne kuma mah kamar ba ɗan nan yankin bane he look different  "good aikin ka na kyau ka cigaba da sa mana

27 / 64