Author : F&F Category : New Hausa Novels 2026
mata da illar auren wuri da ake masu.
Tana fuskantar ƙalubale kala kala akan wannan aikin nata ammh ta dame ta shanye don samun cikar buri ta. Yanzu haka waccen satin suka aje agenda r fitar ammh case ɗin guru yasa suka ɗaga dole zuwa wannan satin da ya kama 4 ga wata.
A mutunce suka gaisa da mutanen da a tarar (kamar yadda nace miran sam bata da girman kai sai dai idan kaine baka fahimce ta bah ko ka shiga gonar ta ).
Murmushi mai sauti tai lokacin da suka fara tafiya tana jin tsantsar soyayyar mahaifin ta da take ma so marar iyaka ganin guard ɗinshi na bin bayan su tasan shine ya turo su har saida hammad ya kalle ta aiko sukai 4eyes ta danna mashi hararar wasa tana maida idanun ta ka hanya shi dai murmushi kawai yayi yana maida hankalin shi kan driving da yake yi.
Har suka fara ratsa ƙauyukan basu ƙara kula juna bah, sun shiga gari a kalla 3 a yinin ranar ana farko suka tarar da mummunan tashi hankali kusan an tattare en matan garin da du du du ba zasu wuce shekaru 10----12 wai za'a kaisu cikin birni aikatau iyayen su baza su iya riƙe su bah sun zaman masu reability wasu tun suna shekaru 8 akai masu aure wasu sun haihu a jigace, wasu sun kamu da cutar yoyan fitsari, wasu kam wannan shine silar ajalin su sunga abin mamaki a ƙauyen jahilci tsantsa ke cin su duk ya rakwakkwaɓar dasu miran ta nemi alfarmar a barsu nan zata cigaba da kula dasu ammh sam iyayen su suka ƙiya suka shafa ma idon su toka, sai dai ita ce ta taho dasu.
A ƙauye na 2 sunsha kuka kamar ran su zai fita mazauna cikin ta Allah ya wadata su da rama gasunan kamar skeleton yunwa duk ta ciye tsokar ta bar m@su ƙashi da fata sakamakon rashin noma da suke sosai ga socioeconomic status saboda ruwan TANVIR da ke amai duk shekara yana ɓata masu amfanin gona saboda rashin maguda nan ruwa abin gwanin ban tausai
Ana 3 taƙadiran mutane suka tarara da zukatansu suka gama bushewa da kafirci kusan mutane ƙauyen duk suna kama da juna sunsha baƙaƙen maganganu haka suka fito rai ɓace shiyasa miran tace gida zata ba don sun gama vah yaran da suka samu damar ceto a gidan marayu na jakada inda anan take aje ire iren su tana in ganta rayuwar su wasu har sun fara aiki asibitin ta miran cikakkiyar likintan mata ce (gynecology knn) .
Midwifery student wannan page ɗin naku ne 🥰
Aikin jarida hobbing tane bashi ta jaranta bah kusan duniyar nan tamu ta yanzu kuɗi ke magana in kana dasu zaka iya taka kowa mah Paah shi ya gina mata gidan T.v na jakada.
A gajiye ta dawo gida yanzu ma hammad ne ya maido ta ana kiraye kirayen sallar mangariba har ƙafar gida ya ajiye ta kallon ta yaiyi lokacin da take ƙoƙarin fita ya riƙe handbag ɗin ta hakan yasa ta juyo tai mashi kallon tsakiyar ido a tsiyace yadda idanun shi sukai jawur da farar fuskar shi yasa tai saurin kawar da kai don wani tashi taji zuciyar ta na mata a dake tace "hammad ka sakar min jakata miye haka "miran ki taimake ni nima , ki tallafi maraici na wai mi nai maki arayuwa da kika kasa fahimtar irin son dana ke maki nayi hakurin shekaru 3 yanzu har abin yana neman zaman man cuta, lower lips ɗinta ta cije kamar mai shirin huda su ta ƙara cewa a ɗan tsawace "bansan irin haka hammad ka sakar mun jika ta ko nabar maka ita kuma nayi alƙawarin bazan kuma shigowa motar ka bah da sauri ya sakar mata jikar ya mai da kanshi jikin site idanun shi na ƙara rinewa zata kulle mashi motar ta kuma tsinkayo muryar shi yana cewa "MIRAN" dole ta juyo ta kalle shi saboda abune mai wuya kaji ya kira sunana ta haka gatsau kai tsaye "magana zamuyi" ya faɗa cikin tsare ta da idanunsa kai ta runsunar saboda batsao ya fahimci halin da take ciki "kayi hakuri" kawai ta iya faɗa ta fara tafiya tana jin shi yana cewa "bazan tafi bah ina nan har sai kin kula ni "bata bi takan shi bah ta shige gida.
A kujerun da ke compound ta yada zango saboda kukan dake bala'in cinta har wata juwa juwa take gani zuciyar ta na suya zuwa yanzu ta gama amincewa zuciyar ta ta kamu da matsananciyar soyayyar hammad ta kuma gasgata soyayyar shi bata ƙarya bace kuka ta ci sosai saboda yadd zuciar ta tai nauyi har ta kaiga hawayen basu fitowa sai kukan zucci dalili da kukan da take akai akai.
A haka ya Aryan da junaid da suka fito tafiya masallaci suka tarar da ita, sauran damshin ruwan alwala dake hannun ya Aryan ya shafa mata a fuska a xabure t@ ɗago ta kalli yayyan nata ajiyar zuciya ta safke mai sauti zatai magana ya Aryan ya ɗaura mata yatsan shi manuniya akan lips ɗin ta yana kaɗa mata kai junaid ya katse mashi hanzari da cewa bro mun makara fah wannan yarinyar rigima ce kawai ke cinta hararar shi ya Aryan yai sannan ya kalli miran "lil sis ki shiga ciki inna dawo masallaci zamuyi magana yai ida maganar yana raɓawa ta gefen ta zai huce har yai gaba sai kuma ya jiyo yana kallo miran dake yunƙurin miƙewa "am miran kar ki shiga sashen maah koh na Paah ki wuce part ɗin momy .
Ba wani fahimtar shi take bah sosai zuwa wannan lokacin ta dai bishi da toh tana gyaɗa mashi kai ta ida miƙewa tsaye jiru na ɗibar ta abu 3 ke da mun ta yunwa, da period pain, sai zuciyar ta dake suya da kayal ta kai kanta sashen iyayen ta kasancewar na maah ne farko yasa cen ta nufa domin a halin da take ciki yanzu bata iya jin zata iya isa har sashen momy cikin galabaitar ciwo ta tura ƙofar ta shiga bakin ta ɗauke da sallama tana tangaɗi saida tazo tsakiyar folourn zuciyar ta tai wani kalar azababban tsinkewa jin murya da ko a mafalki ta jita saita firgita "sannan da zuwa gantalalliya gantalin ne sai yanzu maraba dai" cak ta tsaya kamar mutumbutumi da aka aje don tarihi kafin ta juyo a hankali tana kallon mutanen faolour one by one.
HAMDA 🌺🌺🌺
BABBAR MAGANA WAI ƊAN SANDA YAGA GAWAR SOJA 😳😳
Abu fah kamar wasa wasa ba hamda ba dalilin ta , ba ɓurɓushin jami'an da suka tafi da ita, abun tun ba'a ɗaukar shi serious har yana neman girman shekarun dattawan ƙasar mu, har yau da ake maganar kwana uku da ɓata na ba'a san inda en jarida suka samu labari bah sun fara sakin labarai na ƙarya da gaskiya an fara yamiɗiɗi wai AFTABUDDEEN suka ƙara ram dani. Uhmmm!!! Watau ina kana raye a duniya kasha kallo mutane rugar mu sai dai nace Allah ya ƙara masu lafiya da nisan kwana bana fatan mutuwar su yanzu basu gama shan kallo bah, Adnan dai ya mutu tun a washe gari aka sada shi da gidan shi na gaskiya anyi zaman makoki, Allah sarki jauro ya sha kuka ya gode Allah har ramar dole yayi inna ramma saida aka kulle don hauka ta ringa zuba masu tuburan.
Bayanin da likita yai masu yasa sun sassauta zargin da suke min cewa guba aka ringa ɗirka mashi tsawon kwanaki uku ita ta dagargaje en hanjin sa har ya zamo silar mutuwar shi, ni kuma a lokacin ina asibiti kunga bah hujjar zargi, ammh likita ya ƙara d@ cewa harda ciwon zuciya yana cin sa a tsaitsaye toh fah nan ne mata suka cigaba da zuga inna ramma ai sona shi ya kashe shi babu wata guba da yasha duk tatsuniya ce kwana 10 da nai a AFTABUDDEEN ai asiri naje nai mashi sabodaa, tunda na tafi bashi da lafiya kuma arɗo shi ya shirya ya kuma gabatar don ya ɗauki fansar akan tauye haƙƙin shi da sukai,. Kuji mutanen nan en albarka en cigiyar sharri yooh in vah cigiyar sharri ba da kakkaɓar rikici da jahilci dake ɗawainiya da su yai masu ɗaurin goro ya hansu walwala taya zasu kafa hujj@ da wannan zancen marar kan gado (nace b@h Allah ya kara maku ilhama irin wannan shiri da tsari haka). Sufa anasu ɓangaren wannan shine dai dai kuma ita ce gaskiya sannan sun kafe sun tsare sun danne akan ta, harda su jauro manyan gari tsab sun gama shirya akan in akai sadakar 7 lokacin mutane sun rage zasu tarkata mu su kore mu daga cikin garin su sun gaji wallahi sai mun bar masu gari muddin jami'an tsaron basu ɗauki matakin gyara bah ana cikin wannan hargagin aka nemi mulook sama ko ƙasa bashi bah dalilin shi tun jiya ake neman shi har zuwa yau da nake cika kwana 4.
A ɓangaren gidan mu "ya salam" faɗin tashin hankalin da Arɗo yake ciki ɓata lokaci ne a wannan karon saida hawan jini yaci galaba akan shi kamar yadda yake mashi barazana abu goma da ashirin sun haɗu sun tarar mai a kai. Ga jikin APIP da yai bala'in rikicewa yai fayau abun gwani ban tausayi duk wani magani da Arzu ke tunanin zai sassauta ciwon nashi yayi amfani dashi Amma kamar kara ingiza ciwon yake ga soki burutsun en rugar mu ɓangare guda kuma gani abun gwanin ban tausayi
da ban dariya da takaici a ɗayan ɓangaren.
Yayinda da iyaye na ke cikin wannan yanayin na tashin hankali ni kam sam ba haka bane a ɓengare na bah kwanciyar hankali na samu wadda rabon da inji kalar ta tun kafin mutuwar ya AJMAL duk da wani ɓangaren na zuciya ta ba'a kwance yake bah saboda halin dana baro Apip da kewar su Adda sannan da fargabar dalilin zamana anan. Zan iya ce maku ban san nayi kwana 4 bah a inda nake daular da nake ciki bata bani damar
ganin rana balle in san dare yayi sai inna duba agogo kuma gashi ina off bani sallah, bani da matsalar komai ina samun duk wata kula wa da nake buƙatar har fatata ta nuna. Abunda na sani jami'an tsaro ne suka killace ni anan wai akwai masu farautar rayuwa ta wai a cewar su su wasu rukunin jami'ai ne na musamman case ɗina a hannun su yake duniya abun kallo baya ƙare wa ni dai naji ne kawai don ya zama dole ammh bawai don na yarda bah duk da wani yanki na zuciya ta na faɗa min AFTABUDDEEN duk suka tsara wannan koma minene hakan baya damu na saboda nasa a raina ba abinda zasu iyayi min domin na kai ƙarar su inda baza su iya kuɓutawa bah (kotun sama).
Damuwa ta guda wane hali su Arɗo suke ciki a yanzu, musamman Apip yaya jikin shi yake hankali na ya ƙi kwanciya da halin dana baro su ciki.
Kamar yadda suka saba shihowa kawomin abinci ko in wani uxuri ya kawo su yanzu mah haka suka shigo sai dai wannan karon jami'ai 3 ne suka shigo lokacin ina zaune falour dana maida wurin rayuwa ta tun da na zo gidan ban taɓa shiga ko ina bah sai toilet, ina kallo, cikin bada umarni ɗaya daga cikin su yace "biyo mu" yana faɗin haka ya juya zuwa ƙofar shigowa biyun suka tsaya suna tsare ni da idanu bani da zaɓin da ya wuce bin umarnin su don haka na mike ɗaya a cikin su ya jera dani yayin da ɗayan ya tsaya daga bayan mu ya zamana sun sani tsakiya tafiya mai ɗan tsayi mukayi har muka zo......................,,
[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜
BAI SAN NA
GIDAN BAH
SAI YA CIZAH
STORY
&
WRITTEN BY
F&F
(PERFECT PAIRS 🌺🌺🌺)
22..................
Tafiya mai tsayi mukai har sai da muka zo wani wuri da na gama tabbatar da garden ne tun kafin mu isa ni'imtaccen sanyi da wani daddaɗan ƙamshi su kai mana welcome jami'ai na ta sintiri ta kowa ce kusurwa ni dai nawa ido sai binsu ne duk inda suka sa ƙafa kamar raƙumi da akala, Turus ne ina kallon su bayan mun shiga ainahin ƙofar da zata sada mu da asalin garden ɗin mutane 2 ne ke zaune a jerun kujerun da aka tanada don zaman nasan ɗaya ɗayan dene bana ce bah sai wasu jami'ai dake kai da komowa, murmushi ya sakar min gane mamakin ganin shi nake lokaci guda yana ɗaga min hannu alamar in ƙaraso ba musu na fara tafiya ina tunani inda na san shi "na tuna shine wanda suka zo gidan mu nema kanun labarai AFTABUDDEEN (sp a takaice ) abinda ya ba ni tsoro duk taku ɗaya da zanyi ina yin shine dai dai da ƙaruwar gudun buguwar zuciya ta, tunda na shigo gidan hakan bai riske ni bah saida na shigo wurin (garden) umarni sp ya bada kowa ya fita ya rage su biyun dai nan dake zaune, sai nesa damu kaɗana na hango wani a zaune shima sai dai ya bamu baya hakan ya hanani damar ganin fuskar shi ya miƙe ƙafar shi guda a saman kujerar da yake kai yana sarrafa system dake gaban shi.
Idanu na na ɗauke ina ƙara kallon SP da ya cigaba da safgar gaban shi zuciya ta wani kalar tsalle take kamar zata faso ƙirji na ta fito nake ji ammh na dage na cigaba da zaman jiran tsammani bayan shuɗewar wasu mintuna da bazasu gaza 5 bah ina zaman shiru sp ya kalle ni da murmushin shi mai tarin manufah yace ki ƙara hakuri yanzu zamu sallame ki bai ida rufe bakin shi bah na jiyo sautin takun tafiya cike da kamala da natsuwa hakan yasa SP duk suka mike banda ni da wancen dake nesa da mu.
Zuciya ta daina aiki tai yayin danai tozali da wanda suke kira da Excellency gwiwoyi na sunyi sanyi yayin da jinin jiki na ya tsinke na kafe shi da idanu don koh kaɗan bai man kwarjini bah idanu na har yaji yaji suke tsabagen kallo, tabbas wannan ko ba'a faɗa min bah na sanshi "ƘHAMIS MUHAMMAD AL-QASIM" ne dake takarar kujerar shugaban kasa da za'ayi watanni kaɗan masu zuwa zasu gwabza da adalin shugaban muu da ƙasar kasran ke ji da alfahari dashi wanda da ana ƙara mulki bayan shekara 8 tabbas babu ko shakka yama ci wannan zaɓen ammh wa'adin shi ya cika dole ya safka ba ƙaramar kitimurmura da ƙura ta tashi kan wannan lamarin da har yanzu bata zo ƙarshe bah HIS EXCELLENCY UWAIZ AL-HASSAN wannan bawan Allah mutum kirki ne tsakanin mu dashi sai dai godiya da sam Barka duk wanda ya. Kwana ya tashi a ƙasar kasran yana alfahari da shi, kar in cika ku da surutu ku dai kar ku gaji muje zuwa.
Har ya zauna ban sani bah saboda mamaki ya gama kashe ni a zaunen da nake, ƙarar desk da naji dake gaba na ita tasa na kalli system da wayoyin shi da ya ajiye a sama suka haifar da ƙarar sannan na kalle shi fuskar shi ɗauke da murmushin da shi kaɗai yasan ma'anar kayan sa sp ya fara magana cike da girmamawa ga Excellency (wanda sukai vedio call dashi a system).mun cika alkawari ga HAMDA Mas'ud wagini nan a gaban ka, idanun shi ya ɗake daga kan SP mai magana ya sake kallo na murmushin shi na ƙara faɗaɗa yace cikin sanyayyar muryar shi "ki saki jikin ki ki bamu haɗin kan da muke bukata bamu da niyar cutar dake ya faɗi hakan ne ganin yadda naso fita hayyaci na lokaci guda "babu abinda zamu yi maki muddin kika bamu haɗin kai buƙatar garemu SP ne mai wannan maganar. Ni nawa ido da kuma kunne ina sauransu jikina tsimar tsoro kawai yake yi don haka nan hankali na ya kasa kwanciya da waɗannan mutanen ammh na daure nayi ta maza na aro jarumta na yafa ma kaina na dake,
Sp ya cigaba da cewa "maganar baya ce ta ƙara tara mu anan wannan itace damar ki ta ƙarshe hamda ki buɗe baki ki mana bayani fah gaskiyar abinda kika gani da abinda ya faru dake a ƙabilar AFTABUDDEEN sannan suwa suka cece ki . A wannan karon mah kasa magana nai abu kamar almara ammh wannan karon na fi danganta yanayin da tsoro kuma ban san ta ina zan fara koro masu bayani bah babu wani abu special dana gani da har zai zama abun laburtawa (ni a nawa ganin kenan) hakan yasa nai shiru ina ambaton sunan Allah cikin zuciya ta kamar dai waccen ranar.
Maimaita min tambayar sp ya kuma yi da yaci ace mun shiga sabon babi don na daɗe da haddar wannan kamar wancen karon banyi respond bah ganin haka yasa ogan nasu ɗaga mai hannu alamar yayi shiru cikin son cimma manufar su ogan nasu yace " hamda ki natsu mu ba masu cutar dake bane da akwai wannan manufar a ran mu da tuni mun cimma mata mun bi ta kan ki tuni kin san muda wannan power ki bamu haɗin kai shine buƙatar mu in kikai mana haka nai maki Alƙawarin zamowa silar warakar matsalolin ki na san ki fiye da ke ɗin nan a karo na ƙarshe zan sake baki dama ta ƙarshe zan sake tambayar ki miya faru dake a ƙabilar AFTABUDDEEN