Author : F&F Category : New Hausa Novels 2026
tunda yana ganin idon sani nasan shi nasan halin shi nasan abinda zai iya da wanda bazai iya bah ammh bazan taɓa tilasa ta maki bah kiyi abin da baki da ra'ayi akan shi ammh ina so ki fahimci girman haɗarin da rayuwar ɗan uwan ki ke ciki kuma bashi kaɗai hakan zai shafa bah harda wasu adadin mutanen da suke gudanar da rayuwar su daga gefe ciki harda ke na baki dama rayuwar kice kuma ra'ayin kine duk Shawarar da kika yanke zan girmama ta kuma zan baki cikakken iko akan ta sannan zan tsaya maki"
Siraran hawayen da nake namijin kokarin wajen ruke su a ido sukaci karfi na suka fara zane kunci na hakika na shiga tsaka mai yuwa mai matsin gaske dana yi kuskure a wannan gaɓar matsalace mai gudana da zata cutar da mutanen da bansan adadin su bah kuma ta cigaba da bibiyar su duka ɓangarorin inada hujjar dazan yi rinye a bengare ɗaya ammh wane ne zaifi zama Alkhairi a gare ni yanzu shin mahaifi na da yake cikin kunci, matsi da takura a wurin mafi kunci a duniya ko wane lokaci labari na iya canza kanshi Abba na yana tsananin bukatar taimakon gaggawa bana fatan abinda nake fargaba ya tabbata kaddara tsi hukunci ta shiga tsakanin ban taɓa saka shi a ido na bah ko Apip mutumin daya maye mani gurbin ɗan uwa yai tsayuwar tsayin daka wajen kare ni da marta bata ina matuƙar kaunar Apip bazan taɓa yin abinda zai saka shi kuka bah balle har na sadaukar da rayuwar shi muddin wani abu ya same shi bazan taɓa yafe mah kaina ba a rayuwa bah a yanzu shine kwarin gwiwa ganin shi a cikin koshin lafiya shine lasisin kwarin gwiwa ta na fuskantar matsalolin rayuwa ta, ko kuma kasa ta da zan mah babbar sadaukarwa babbar Matsalar data fi damunta a halin yanzu itace AFTABUDDEEN da Dodon su ke jagoranta dama ce Allah ya bani a halin yanzu da ba lallai ne na kuma samun ta bah kamar yadda ummi tace.
Shin mai karatu wane sashe ne yafi cancanta na maida hankali na akan sa mahaifi na da bani da tamkar sa a duniya ko Apip mutum mai rauni da yake bukatar kulawa (son shi a rai daban ne) kokon kasa ta da zan mah babbar sadaukarwa ya zanyi da auren son zuciya da aka ƙaƙabamin har abada bana jin akwai hujjar da za'a kafa minda zata sa na amince da wannan auren gefe guda kuma hasu Arɗo.
A hankali na mike na nufi kofa ba tare dana tanka masu bah na fice daga ɗakin jiki a sanyaye ba tare dana kara furta ko harafi bah Saboda banda abin cewa a wannan gaɓar suma ba wanda yai yunƙurin dakatar dani. Ta fiya nake ina tuka da warwara ban tsaya ko ina bah sai bakin ruwa inda na hango su tsaye ɗazu saidai ban samu Apip bah daman banyi tunanin tarar shi bah kuma ban damu da neman shi bah na kai zaune a ɗaya daga cikin kujerun da aka tana don shan iska ruwa na kura mah ida yadda suke cin karo da kokowa da juna kasancewar garin akwai iska ba laifi gaskiya tunda daga tsarin su, kalar su, kamshin su na kara sheda Ruwan tanvir ne a ranar na kara jinjina girman su duk da ban san nisan dake tsakanin rugar mu da AFTABUDDEEN ba wani sashe na filin na sake kura mah ido daga haka na lula Duniyar tunani....."
MALIK 🤍🤍🤍
Ikon Allah ne kaɗai yakai shi bedroom lafiya bai ci kasa bah kanshi tafasa kawai yake mashi yana zaɓarɓa ka har ya fara tunanin gab yake daya kama da wuta Saboda hajujuwar dake wana shi ba karamar a zaftar dashi take bah ammh a zahiri da zaka ganshi zaka ɗauka gajiya ce ya kwaso yake buƙatar hutu saboda fuskar shi ma'abociyar adana sirrikan zuciyar shi ta shanye komai ta alkimta mashi koda ya killace kanshi daga idon mutane bai bayyanar da raunin shi musamman yadda yai ƙasaitaccen zama a gefen gado yana dafe da tsakiyar kanshi ji yake kamar ana tsigar gashin kanshi da karfin masifa har gudun jinin sa yana ji tsabar yadda yake sai dai wannan abun ba sabon abu bane a wajen sa inda sabo yaci ace ya saba saidai ba'a sabo da ciwo lokuta da dama idan makamanci wasu abubuwa suka maimaita kansu a tarihin rayuwar shi yana tsinta kanshi a irin wannan halin koma fiye da hakan kuma abune da bai da da ikon dakatar da wanzuwar a doran kasa balle a samu shadduz xari'a (toshe mafaka) shiyasa faruwar hakan baya ɗaga hankalin shi balle ya dame shi duk da yana cutuwa zame wa yai ya kwanta ruf da ciki ba tare da ko arziki cirin takalma ya samu bah a saman lumbutsetsen gadon sa yalwataccen wayayye mai tafiya da zamani irin wanda ko baka jin barci ka haushi sai barcin ya riske ka saboda taushin a hakan mah ba komai na samu gani ba balle na ɗauko maku rahoto sam ɗakin haske bai wadace shi bah dum light mai duhu a yadda na fahimce shi ba ma'abocin son zama cikin haske bane ammh shi sam ba wannan shaukin a tattare dashi saima siririn tsaki da yake ja akai akai saboda wayar shi data ishe shi da vibration ya murgina kwanciyar sa ta koma a rigingine ya zama na yana kallon ceiling kafafun shi na kasa tsaki ya kuma jan cen kasan makoshi wanda sautin sa ya fito da zallar ƙasaita mai cike da kasala hannu ya mika ya ɗauki wayar ba tare da ya motsa bah balle duba sunan mai kiran yakai wayar kunne yasan duk mai karfin halin yi mashi irin wannan kiran isashshe ne .
MASARAUTA🌺🌺🌺
Yau kwana biyar kenan da ɗaurin aure na chief imam ya bukaci ganin Arɗo sun fara tattaunawa bayan an tashi daga leeyafa sai tafiyar gaggawa ta kama shi sai yau yau da Allah yai mashi dawo suka samu damar zama, a cikin masarauta kananun maganganu sai tashi suke saboda jita jita da ba'a san mafarinta ba sai amsa kuwa take a cikin masarautar manyan Masarauta kowa rawar kafa yake shi zai fara tarbar wadda tai tsallan kura ta ciri tutar zamowa matar UMAR wai kuma a jiya labari yazo masu wai ya ɗauki matar shi tun bayan ɗaurin aure ya fice da ita daga ƙasar baki ɗaya a inda yake karatu nan zasu zauna Kamar yadda ya alkalwan bazai saka ɗiyar mutane a haɗari bah shi da yaza ma dolen su ya aka kare bare ita bare daga majiya mai karfi labarin ya riske su bayan mutane da dama sun shaida ko ɗaurin auren bai je bah koda labarin yaje kunnen chief imam murmushi kawai yai yasan kwanan zancen bai kuma tanka ba ya zuba masu ido yai amfani da damar wajen Kawar masu da hankali karsu fahimci sace ni akai.
A ranar masu kirdado akan Umar suka kara sallama mah lamarin shi sai Allah auren nashi mah bazai bari ayi shi salin alin bah sai ya shigo da sabon salo ya kawo mah mutane shubuha duk wata al'adar masarauta ya take ta yabi ta kanta iya kulluwa masu shirin yaƙi sun kulu gashi ba damar ɗaga murya saboda chief imam yai ma tufkar hanci daman abinda suka tsara Kenan sati guda bayan ɗaurin auren zamu koma kasar da yake karatu har sai kura ta lafa ammh sai ya nuna masu basu iya komai bah sati guda kafin auren ya tsara nashi wannan duk shiri ne da tsari ne na ummeey ita ta tsara ta kuma gaba tar ta zuba masu na muji tana kallon gudun ruwan su.
Ga rashin tankawar chief imam ya kone zuciyoyin su tun daga yadda ya haɗa jarababban aure nan (acewar su don su a haka yazo masu) suka gama tabbatar da akwai wata a kasa kuma babu wani gamsashen bayani a kasa.
A zaman da sukai da Arɗo yake shaida mashi ya kwantar da hankalin shi kar ya damu damam yasan ran fiye da hakan ammh insha'Allah ya ɗauki alhakin kula dani bazai huta bah har sai ya samo inda nake zai dawo da ni cikin koshin lafiya nida ɗan uwa na ta ko wace hanya insha'Allah sosai Chief imam ya kara kwantar mashi da hankali daga karshe ya kara da cewa ya ɗauki nauyi rashin lafiyar Adda da jikin ta kullum ga yake kara rikewa yake ba sauki saidai a wutin Allah, zasu bar kasar na tsawon lokacin da zata samu lafiya su samu mwanciyar hankali jinyar ta Arɗo yaso ya bijire bawai don baya son Hakan bah kawai baya son ya kara mashi nauyi ne bayan wanda ke kan shi nauyin neman mu da ya ɗauka kawai ya ya wadatar dashi Chief imam ya nuna ɓacin ranshi sosai ganin hakan yasa Arɗo zubar da makaman ya amsa da mutuntawa tare da yi masa godiya fatan Alkhairi da addu'ar neman da cewa shi kan shi zaifi samun natsuwa da kwanciyar hankali idan yai nisa da kasar Nan rikicin da yake fuskan ta a cikin ta ya isa haka nan ɓatan yara 2 a lokaci guda ai ba abun wasa bane sun rabu da chief imam a cikin satin tafiyar tasu zata kama saboda ciwo baya jiran lokaci ciwon cin ta yake sosai.
Bayan tafiyar Arɗo waya ya ɗauko cike da kwarewa yake sarrafa ta yana gyara zaman shi na magada mulki da yai a kilisar shi number da yake shirin kira missed called ɗinta ya fara cin kari dashi bai tsaya ɓata lokaci bah ya bi kiran saidai kusan sau 3 yana kira ba'a ɗaga bah sai ana 4 yai Sa'a itama tana gab da taikewa "Duk abinda kake UMAR ka baro shi ka shigo masarauta yanzu ina son ganin ka" abinda mai martaba yace kenan ya tsinke wayar ba tare da jiran jin ta bakinshi bah.
🌺
ARƊO yai Tunanin komawa asibiti daman yana cen ya samu kiran gaggawa daga Chief imam tuna ko yaje ba abinda zai yi yasa shi yanke shawarar wucewa gida kawai saboda har yanzu likitoci basu bari aga Adda kwana 2 da suka wuce ta garfaɗo saidai ko 2hrs bata cika bah ta koma saboda jinin data zubar bana wasa bane a yanzu inna ke ɗawainiya da ita da wasu daga cikin dangin ta da suka zauna jinya sai ɗawisu da suke gani giccin sa jefi jefi haka Arɗo ya isa gida da matsananciyar fargaba abinda ya tara akan hanya ya kara mashi kwarin gwiwar barin rugar nan daman kwana 2 nan yana fuskantar barazana daga sassa mabanbanta musamman akan Apip da aka gindaya mashi shariɗɗa nemo shi nan da wasu kwanakin da basu gaza kwanakin wata bah tunda ya baro hannun su Leena suka koma bibbiyar rayuwar shi a tunanin su ko guduwa zaiyi ko zai sama mah kan shi garkuwa saidai babu alamar hakan tare dashi babu mah wani sauyi a cikin salon daya saba gudanar da rayuwar shi sun rasa mi ya taka tuni Arɗo ya gama fahimtar zaman cikin rugar fari a gare shi yanxu kasada ne dole mah ya ɗan bada kafa shima ya gama kimtsa kan shi lokacin da zai dawo yana sa ran kura ta ɗan lafa sai ya ɗaura daga inda ya tsaya yai nashi ya barma Allah sauran da wannan tunanin ya shige ɗakin shi ko salla bai bah ya manta ne ko duk damuwar ce ohoo ganin a halin da ya shigo inna dake shara ta saki tsintsiyar tabi bayan shi......
MIRAN 🌺🌺🌺
Zaman ɗakin ne ya ishe ta ya sata fitowa waje shan iska hijabin da tai sallah na a jikin ta ko cire ta ba tai bah bata iske kowa a falour bah kamar yadda ta zata sai motsi data ji daga kitchen da ɗaɗɗare ƙamshin daya game kofofin hancin ta murmushi tai tana kallon direction ɗin kitchen ɗin kamar zata iya hango wanda ke cikin sa just 2 days suka yi da matar ammh ji take kamar life time sukai tare tunda Aunty sugra ta kawo ta..............
[16/12, 10:01 pm] Teemah MS 🥰💖: CINNAKA 🐜🐜🐜
BAI SAN BAH
GIDAH BAH
SAI YA CIZAH
STORY
&
WRITTEN BY
F&F
(PERFECT PAIRS 🌺)
66,..........
Tunda Aunty sugra ta kawo ta ita take gani ita kadai ta sani mace mai matuƙar mutunci da saurin shiga rai da iya zama da mutanen cikin ƙanƙannin lokaci tai sabo da ita tsawan kwanakin datai a gidan ita ke kula da ita kular da ko a gidan su take zaune bata wuce samun kamar ta shiyasa bata damun da sanin wanda ake ikirarin an ɗaura mata aure da shi don tunda tazo gidan bata ji ɗuriyar wani bah bayan mama da take gani akai-akai sai dai in ta tuna abin na damunta cikin rai maganar mata ta katse mata tunani bata san da fitowar tawa ta bah " A'a ɗiyar nan wani abun kike bukata ne ko har yanzu jikin naki ne" da murmushi all over her face tace "a'a mamah na fito taya ki aiki ne naga duk aikin gidan nan ke ke yinsa baki ko gajiya" murmushi mama tai ta ajiye bowl din hannu ta saman C/table sannan takai zaune kujerar dake bayan ta "Er nan inda sabo ai na saba in banyi bah wazai yi daga ni sai mai gidan ki ke zaune cikin gidan kuma shi ba zauni bane sai ya samu saukin aiki nake ganin sa" murmushin yake miran tai itama takai zaune kusa da ita bata ce komai bah don bata da abin cewar tun zuwan ta gidan yauce rana ta farko data taɓa jin mamah tai maganar mijin nata data kasa fahimtar alaƙarsu da shi ammh tafi hasashen ita din mahaifiyar sa ce matar nada kirki sosai tana kula da da ita fiye da hasashen mai karatu tunda Aunty sugra tai mata bayanin rashin lafiyar miran bata boye mata komai bah harda dalilin aure duk akan rashin lafiyar tata mamah ke bata kulawar data dace da yanayin ta kamar yadda ta alƙalwanta mah mata, Aunty sugra taso gamuwa da mijin shima tai mashi bayani kamar yadda tai ma mahifiyar sa don bazata kara lamuntar cin fuska da wulaƙancin a wurin kowa ba akan miran kuma shi kar yai Tunanin auren sadaka akai mata kamar yadda hammad yai masu wannan karon baza tai wasa bah a ida kashe mata diya zatai tsayin daka wajen nema mata lafiya da kare mata mata martaba ai ciwo ba hauka bane sai akai rashin Sa'a bayanan ta yanke shawarar bayan sati guda zata dowa (ranar da zasu sake zama da likitan da zata kula da rashin lafiyar ta) idan ya dawo sa yi maganar ai lokacin daman bai kure bah.
Kafin tafiyar Aunty sugra saida ta tabbatar ta wanke mata duk wata damuwa da sabunta kwarin gwiwar ta da farfaɗo da asalin miran (mommy's girl) dake tsaye wajen kwato mah mata hakkin su kuma akai Sa'a kalaman sune makamin data riƙe matsayin garkuwar take zaune cikin gidan da murmushin nannauyan lumfashi taja ta ture tunanin da karfin tsiya ganin zai sa mata damuwa musamman in tana tuna en gidan su "Ai na ma cimma rabin aikin bana son ya shammace ni kamar yadda ya saba nasan ba zai wuce yau ko gobe bah bai dawo bah" a wannan karon mah murmushin yake tai ta kawar da maganar ta hanyar cewa "mamah da mi zan taya ki "A'a yarinya kiji da jikin ki kisan baki da lafiya kina buƙatar hutun" fuska miran ta marairaice sosai kamar mai shirin fashewa da kuka tai kalar tausayi Sannan tace "Don Allah mamah ki faɗa min abinda zanyi ai ciwon nawa bazai hanani aiki bah" ƙayataccen murmushi mamah tai tana najin soyayyar yarinyar na kara linkuwa cikin zuciyag ta "shikenan tunda kin matsa karasa gyaran wannan kayan marmarin bara naje da duba in shinkafar da ida" miran bata kara cewa komai bah ta amsa ta cigaba da aikin ta.
Kusan tare sukai aikin daman mamah ta cimma rabin sa karasawa sukai saida marece likis gab da mangarib suka samu kansu mamah ta bata umarnin shiga ɗakin ta tai wanka zata kawo mata abinci in taci tasha magani sai ta kwanta miran ta bita da toh bawai don hakan ta shirya bah.
⭐⭐⭐
Agogon ya kalla a kato na ba adadi yana cigaba da Safa da marwar sa yafi karfin minti 30 a haka tsananin damuwa da tashin hankali shimfuɗe a fuskar sa kamar ya zaro zuciyar sa a kirjin sa haka yake ji saboda tururin da take masa ko ya samu salama da aminci "Aiman ka kwantra da hankalin ka mana kar ka haifar mah kanka da wani ciwon kaima ai uwa kwance ɗa kwance insha'Allah zasu samu lafiya" kamar ko yaushe ya Aiman baice mata komai bah a halinda yake ciki yanzu baya jin yana da karfin yin Magana, itama momy mai mganar bakin ta ta tsuke ta koma mazaunin ta tana binsa da kallo cike da tausaya wa ta lura kwata kwata hankali shi baya tare da shi tunda suka zo asibitin.
Damuwa ta gama rinjayer zuciyar sa yana cikin matsanancin yanayi mai wahalar gaske suna a wannan halin sai ga likita daya share fiye da 40 minutes a cikin dakin da aka kwantar da big Aunty ya fito zufa duk ta gama jiƙa masa goshi tun daga facial expression ɗin shi gwiwoyin ya Aiman suka sake yin sanyi bai iya karasa wa wajen shi bah sai momy ce matsa da sassarfa tana tambayar yaya jikin nata Fuska Dr ya ɗan tsuke idan shi