Author : F&F Category : New Hausa Novels 2026
matsala Paah yayi farin cikin hakan wannan makamin da shi momy tai amfani ta siye zuciyar mijinta saidai a ɓangaren hajja manyan gari ganin momy ita ma bata da alamar motsi a ɓengare ta don ko ɓatan wata bata taɓa jin ance tayi bah ya matuƙar fusatata aiko ta tsiri sabuwar masifa wai sai ya kuma aure aiko wannan karon ba ƙaramin rikici akai bah harda dangin momy ganin bah sarki sai Allah ga grandfah ya xuba masu ido yaƙi cewa komai yasa ya kuma haƙura ya sake auren FATIMA abokiyar aikin sace ko wata basu cika bah Allah ya basu rabo a lokacin ne kuma ciki ya bayyana jikin momy hajjah an samu abinda ake so shiyasa suka ɗan ji daɗin ta a tsakani tare sukai rainon cikin su abin mamaki kuma a rana ɗaya suka haihu saidai fatima a wurin haihuwa ta mutu ita da abinda ke cikin cikin ta sai momy ha haifi tagwaye junaid shine babba sai humaid hajjah duk da ba haka taso bah ta danne komai ta haɗiye ba komai ai sun ƙara yawa kuma maza ne zasu iya auren mace fiye da ɗaya su haifa mata jikoki dozen 😁 . Hajjah naji da jikokin ta 4 kamar ta haɗiye su.
Kwatsam wata rana ba zato ba tsammani sai ga ciki ya bayyana jikin maah ita kanta bata san dashi bah saida yai wata 3 lokacin su junaid nada shekara 3 ya Aiman 10 sai ya Aryan 8 kowa na family yayi farin ciki musamman da likitoci ke hasashen da yiyuwar macece kai bayyana farin cikin hajja da maah baya musultuwa haka dai aka cigaba da rainon cikin har yakai watan haihuwa ta haifo zukekeyar budurwa ya salam a wannan lokaci in kaga wanna family zaaka ɗauka bushara akai masu da gidan aljanna gagarumar waleema suka haɗa ranar suna saida duniya ta sheda MIRAN {PRINCESS👸} ta diro duniya harta kakan su grandfah saida yazo Paah na masifar ƙaunar ɗiyar shi ɗaya da Allah bashi tsakanin shi da hajja bansan wanda yafison ta ba itama hakane a ɓangaren momy maah ce mah ke ɓoyewa in ka gani zaka ɗauka ba ita bace ta haife ta bah tsakanin ta da ita shayarwa daga inda bata jin yunwa ko ganin ta bata yi koda aka yaye ta hajja ta tattara da ita suka koma Egypy duk da Paah baiso bah ammh ba yadda ya iya.
A cen tai primary da secondary shiyasa ta gama makaranta da ƙananan shekarun ta sannan ta shiga University ta karanci medicine burin miran kenan ta zama Dr. tsakanin ta da iyayen ta sai ziyara sun gama shekarar farko sun samu hutun ƙarshen zango ta matsa mah ta matsa ma hajja sai tazo kasran ba don hajja taso bah ta barta tazo da garguɗi sati 1 kawai zatai ta dawo gida.
A ranar data isa ta tarar da dangin mahaifiyar ta sun kawo mata ziyara waɗanda bata taɓa sanin tana da su bah tasha mamaki saidai a Yadda tatarar dasu hankalin ta ya tashi nan ta tsare su da tambayar mike damun su miyasa maman ta ke kuka miyasa kuma bata taɓa sanin labarin su bah maah bata taɓa faɗa mata bah tana da dangi ba kuma bata taɓa kai ta wurin su bah maah taso mazewa ammh Aunty sugra (kanwar maah ce ) uwar surutu saida ta bata labarin rayuwar mahaifiyar ta a gidan mahaifinsu acewar ta ai itama tana da haƙƙin sani
__-_ mahaifinsu maah irin mutanen nan ne da jahilci ya aure su ya tare a muhallin su irin jahilan da aka daina yayin su yooh dole a kira lamarin shi da jahilci tun kafin ma jahilan su kaiga wayewa aka bar ɗabi'ar da yake ta ƙin 'ya'ya mata bai ƙaunar yara mata ko misƙala zarratin a haukan shi wai suna janyo kunya da talauci saboda su ba yadda za'ai ka moresu saidai kai zaka fita ka nemo kai wahala ka kawo masu su girma ka aurar dasu shikenan tsakanin ka da su su kau 'ya'ya maza sunje gona su taya ka aiki in sun girma su tsayu da ƙafafun su har kai ma su ringa taimaka mah. Cikin ikon na rabbus samawati ya jarafce shi da da 'ya'ya mata kusan 13 maza 2 iya wahala sun shata a hannun mugun uban su babu irin karan tsanar da ƙasƙancin da basu gani bah a hannun mahaifinsa su da suka fi ma kallo mai ruƙon su ba uba bah don kamar 'ya'yan ruƙo haka suke rayuwa a cikin gidan nan. Dan mah Allah ba azzalumi bawa bane yana basu mazaje salihai masu rufin asiri maah ce kawai ƙaddara ta faɗa mawa ta faɗa hannun azzalumin mutume wai shi Habu wanda take gani gwara zaman gidan mahaifinsu da zaman gidan shi ya maida ta baiwa marar enci gata da shegen zurfin ciki gidansu ba wanda take sanarmawa ta sha wahala hannun mutumin nan ta ƙoɗe ta dafe ta lalace ta tsomale kai ta fita kamannin ta da mah hayyacin ta baki ɗaya duka, bugu, zagi, noma, kiyo, ba wanda natai bah gah horon yunwa ko wurin zaman sai a hankali saboda uban yawan dasuke dashi matan shi 4 banda wanda ya aura ya saki ga yara en kuci kuci saboda auri saken shi kuma muhallin zama ba wani ba sun takura sosai.
Lokacin da en uwan ta suka kai mata ziyara hankalin su ya tashi hayƙam da suka ganta daba barcin ƙarfin tasirin JINI bah da baza su gane ta bah zasu bigi ƙasane su rantsa ba ita bace itama mamar ta hankalin ta ya tashi da labarin yaje mata ammh koda maganar taje kunnen shanyayyen uban su sai cewa yaiyi "Ai hakan ya kamata a ringa hora mata marar sa enci da galihu wallahi ai yai mata adalci daya cigaba da zama da ita in ba'a yabe shi ba ai ba aan zage shi bah in kuma ta yarda ta kashe auren ta wallahi sai dai ta ta canza uba ba dai shi bah".
maah ta rungumi ƙaddarar ta hannu bibbiyu ta cigaba da zama da Habu Amma en uwan ta sun kasa jurewa sun kai limit ɗin da ko tsine masu zaiyi saidai ya tsine masu ammh a wannan gaɓar bazasu yi shiru bah sai sun ceci er uwar su lokacin da suka je ɗauko ta Habu na gida ai ko takan shi basu bah suka jaah er uwar su da bata san da zuwan su bah zasu fita maganar da yai yasa su dakatawa "in kika taka ƙofar gidan nan a bakin auren ki" juyowa tai ta kalle shi yana wankin takalmi da bakin shi mai ƙarfin halin maganar ta kalli sauran matan gidan sannan ta kalli en uwan ta dake jiran ganin wazata zaba a cikin su ta maka mashi wata shegiyar harara da tun zaman su bata taɓa bah tace " Allah ya isa tsakani na da kai habu haƙƙi na bazai barka bah" tana gama fadin hakan tabi en uwan ta suka tafi sanin kan sune mahaifinsu bazai karɓe ta bah yasa suka wuce da ita cikin birni bisa shawarar maman su gidan yayar ta (mahaifiyar su) ta samu kwanciyar han kali na ban mamaki haka har Allah ya haɗa ta da paah silar rage mata hanya daya taɓa yi (estate ɗin da yake zaune kafin aure da unguwar da maah take makwafta ne ) ".
Jin wannan labari na mahaifiyar ta ya canza mata duk wani burget na rayuwar ta taji a ranta sai ta ƙwato ma mahaifiyar ta enci (kamar dai yadda muka sani miran akwai ƙarfin hali a jinin ta yake) ta ko wane hali daga lokacin taji aikin jarida ya shiga ranta koda tai shawara da momy da Paah sun bata goyan baya 💯 har Paah na bata shawara maimakon kyakkyawar niyar taki ta tsaya iya kan mahaifiyar ki mai zai hana ki taimaki wasu dake cikin hali irin nata tunda ita yanzu nata ya zama labari mahaifin nata ya ma rasu sai dai mijin. Taji daɗin wannan shawara tace zata bar karatun likita ta koma jarida paah yace a'a hajja bazata yarda bah saboda duk abinda ta tsana a duniya ya biyo bayan aikin jarida musamman gake mace saboda haɗarin dake cikin sa ɗan uwan ta ɗan jarida ne taga yadda aka kwashe dashi Paah yai mata alƙawarin zai buɗe mata gidan tv ta ɗauki ma'aikata en jarida sai su ringa aikin tare kuma zata cigaba da karatun likitan ta kamar yadda hajja ke so
Haka ko aka yi Paah shi ya buɗe mata gidan tv na jakada (sunan ƙauye su maah) ammh a makaranta ta canza course daga medicine zuwa gynecology (likitan mata kenan) .
Ya rahman faɗin ɓacin ran hajja akan wannan.............................................
[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜
BAI SAN NA
GIDA BAH
SAI YA CIZAH
STORY
&
WRITTEN BY
(PERFECT PAIRS 🌺)
25............
Ya rahman faɗin bacin ran hajja akan wannan yunƙurin baya faɗuwa ran ta yakai ƙololuwar ɓaci musamman da akai komai ba'ai shawara da ita bah ba'a ɗauke ta da mahimmanci ba kenan tun tana lallashin miran ta daina wannan haukar da ta ɗauka abinyi har ta koma mata tijara saboda sam miran ta murje ido ita ta samu aikin yi kuma inshallah sai ta taimaka ma mata en uwan ta musamman wadanda suke cikin ƙauyuka wannan saɓanin ra'ayin da suka samu da Hajja shi ya surar da soyayya da take mata ta ringa kunno mata wuta ta ko wane ɓangare yasa har tai fushi ta zuciya ta tattaro yanata yanata ta dawo gidan baban ta daman bata kaiga fara karatun bah a cen, a nan ya Aiman ya sama mata admission ita kau hajja ta ɗauki alƙawarin bazata taɓa jin daɗin ta bah idan har bata aje karatu nan bah har sai ta bar aikin jarida zasu daidaita Yanzu dai takun saƙar da suke kenan kowa ya rike wuta yana ganin shike da gaskiya hajja ta ɗauki alƙawarin ta kowace hanya saita rabata da aikin nan en gidan su kaf na goya mata baya har Paah dake ƙoƙarin fahimtar da hajja Amma da yake ƙanƙara ta daskarar da ƙwalwar bata ganewa maah ce kawai bata goyan bayan sosai, sai dai tun daga lokacin da ta fara taɓo manyan ƙasa abin ya fara basu tsoro duk da suma suna ciki su shiyasa some time ya Aiman da ya Aryan ke take mata birki.
Miran koda take zaune gidan su tafi sakin jiki da momy ta fi sabawa da ita shiyasa ko kaɗan bata sakewa sosai da maah daman ba gaban ta ta tashi bah sometimes yayyan ta na kiran ta da mommy's girl saboda shaƙuwar su har sunan ya bita wannan kenan lavarin gidan su miran nan gaba za mu ƙara sanin wasu abubuwan_-__
Dalilin fitar Paah yasa basu samu damar magana da hajja bah ya bata uxurin en gidan en gidan nasu duk sun shigs damjwa Musamman ya Aryan maah na danne wa ta haɗiye (nan na fahimci a nan miran tayo gadon zurfin ciki)
Suna tsoron suyi wani kyakkyawan motsi wannan zautacciyar tsohuwar tai masu wankin babban bargo cikin takaici junaida yace "wallahi shiyasa banson hajja tazo ƙasar nan fiti na ke kawota wallahi duk in tazo sai lil sis tai ciwo "kul ɗin ka junaid kakar ku face hakuri zamuyi da ita momy tace tana jera food flack saman daining bayan ta gama ne ta tukaro falour tana cigaba da cewa kuje kuyi break fast ɗin ku in ta gama fushin nata da kan ta zata safko cikin damuwa ya Aryan ya miƙe yana cewa lokacin da yake nufar daining "wallahi maah MIRAN na cikin damuwa baki lura da hakan bah tun bah yau bah nake observing har momy nai mah magana ya ida maganar yana hawa stairs dake daining area sai kuma ya juyo yana kallo momy dake cewa bari naje wurin ta nasan zuwa yanzu ta tashi.
Tana ƙoƙarin knocking ƙofar bedroom ɗinta ta buɗe kofar lokacin tayi shirinta na fita aiki kamar kullum kaya ne masu faɗi da basu kama mata jiki bah doguwar ta material sai babban mayafi da tai rolling tayi masifar kyau fuskarta tai fresh kamar ba waccen ta kwana kuka bah sai ka rantse barcin salama tai ta tashi cikin aminci tana ganin momy ta faɗa jikin ta ta rungume abin gwanin birgewa kamar ba kishiyar mamar ta bah cikin shagwabar da zame mata jiki tace " wallahi momy nayi missing ɗin ki aiki nake kwanan nan kamar bazan kai labari bah cikin son yarinyar tace aikin Alkhairi ya gaji haka sai hakuri daman taimakon al'umma ba sauƙi yanzu kuma ga wata matsala cikin gida Allah dai yai maki albarka ya shige maki gaba "ameen momy na da addu'ar ku da goyan bayn ku Inshallah zan cigaba bazan share bah yawwa mommy's girl muje kici abinci don bazan barki ki tafi da yunwa bah suna firar su cike da shaƙuwar su suka safko lokacin duk suna daining tun kan su ƙaraso ya Aryan ya taso ya kama hannun ta tare da tambayar ta lafiyar ta cikin matsanancin son yayan nata ta saki murmushi "yaya nifa lafiya na qlau kasan jiya na kwaso gajiya barci da wuri yazo mani "morning maah" ta gaishe ta suna sakarma juna murmushi "an tashi lafiya ya jikin naki "uhmmmm da sauki sosai maah ina Paah "wurin aiki "ba dai ya koma bah tai maganar cikin zaro ido duk saida ta basu dariya," sai bayan sai bayan bikin Aryan zai koma ki kwantar da hankalin ki ajiyar zuciya ta safke mai nauyi ta cigaba da break fast ɗin ta,
Saida ya Aryan ya tabbatar ya cika mata ciki sannan ta miƙe cikin shagwaɓa "ya Aryan na fah ƙoshi wallahi ciki na fashe wa zaiyi na kuma makara ba ta jira cewar shi bah ta kama hanyar barin wuri tana gab da shiga falour maah ta tsaida ta juyowa tai tana kallo maman ta "karki daɗe irin na jiya kin san banson neman fitina ina son har hajja ta koma baku sake samun matsala da ita bah kuma kafin ki wuce ki tabbatar kin shiga sashenta kun gaisa toh kawai miran tace tana cinno baki bawai don zata je ɗin bah waje ta juya zata fita ya Aryan yace sis jira ni mu tafi tare nima na gama bata jira shi bah ta fita tana wurga hannuwa kamar mai shirin tashi sama muddin ta shiga gaishe da hajja yau bazata je aiki bah don haka direct wurin motar ya Aryan ta wuce tai zaman ta Allah yaso saida ya jima bai fito bah koda ya tambaye ta taje sai ce mashi tayi ehhh ammh tana barci ne bata tashi bah bai kawo komai a ranshi bah ya tada mota suka ɗauki hanya .
Wani kalar mummunan bugu zuciyar ta tai ganin motar hammad kar dai ace nan ya kwana kamar yadda yace motar tabi da kallo duk da tana son basarwa kar ya Aryan ya fahimci wani abu koda sukai 4eyes dashi kai ta kawar gefe shima baice mata komai bah ita kuma cikin ƙunar rai ta cigaba da zama tana tausayin hammad saida sukayi nisa cikin tafiyar kamar daga sama taji tambaya daga bakin ya Aryan " wa kike kallo a waje ya saki firgita irin haka" da sauri ta kalle shi Bama ita yake kallo bah kai ta shiga gilgiza mashi cikin alamun rashin gaskiya, murmushin gefen baki yayi kamar bazaiyi magana bah sai kuma sai kuma yace "HAMMAD koh" cikin suɓucer baki tace yaya a ina kasan shi shiru yai mata kamar bai ji ta bah (hmm ya Aryan akwai muskilancin) saida taji tsayuwar motar ta ɗago kai ashe sun iso jakada tv bata lura bah ya juyo yai mata kallon seconds "Allah ya bada Sa'a in kin koma gida mayi magana yanzu na makara " sukuku tai mashi godiya sannan ta fita saida ta ƙure ma ganin shi sannan shima ya tafi .
Yauma ta tadda en uwan ta sun shirya HAMMAD ne kaɗai babu a cikin su duk ta damu har saida ta tambayi hairan ko ya shigo yace a'a bai kaiga shigowa ba shima suna shirye shiryen tafiya sai ga motar shi mugun nauyin shi ya hana miran wannan karon shiga motar shi don haka yau a motar station ɗin su ta tafi wadda take mallakin ta suka ɗauki hanya gayyar yau yafi ta jiya yau take son ta gama komai tsaf.
Sun shiga ƙauyuka da ruga da dama wasu sun samu haɗin kai wasu akasin hakan wani wurin suna kai masu tallafi masu ɗaukar rahoto na nasu aikin don su haska mah government halin da en uwan su suke ciki, a ƙauye na ƙarshe da suka shiga wanda daga shi sai rugar fari rugar mu kenan daman yau tashirya haɗuwa dani shiyasa wannan karon harda rugar mu a cikin jadawalin ƙauyukan da zata ziyarta Bayan sun gama da ƙauyen mutanen cikin sa sun bata haɗin kai sosai sun kuma fahimce su basu samu ƙalubale sosai tattare dasu bah saboda akwai masu ilimi sosai naɗe cikin su har suka taimaka masu suka zazzagaye garin bayan sun gama ne suna shirye shiryen tafiya from no where suka ji muryar wata yarinya na kiran Aunty duk suka juya a tare suna kallon kyakkyawan yara guda 2 ta hanga en mata kansu guda da gudun su suna tunkaro su saboda akwai er tazara tsakanin su farkon data fara isowa jikin miran ta faɗa cikin murnar ta sai kuma ta ɗago tana kallon ta bayan ta magana ƙyalƙyata dariya "Aunty ina son in zama kamar