Chapter 24 Reading CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx Arewa Novels

CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx

Author :  F&F Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   24 / 64

69K to 72K   out of 190.4K words

yawan gaske cikin labarin nan kar ki damu besty muje zuwa mu cigaban da bin hamda sannu a hankali zata warware mana komai, ni ba wannan gaɓar tafi bani mamaki ba waccen ɗan cigiyar sharrin Namir yake koma wa hmmm nur daga jin sunan shi tiger 🐅 kekin san akwai lauke cikin naɗi toh ammh mi yai mah gura yasashi fita hayyacin sa lokaci guda ke dai muje zuwa zaki san dalili daga haka muka buɗe next page muna tun karar hostel ɗinnmu Allah yayi mun dawo)

  Yana cikin wannan yanayin wayar shi tai ringing a karo na huɗu duk yana share ta jin zata fasa mashi dodon kunne ya jawota da niyar kashe wa baki ɗaya ammh ganin sunan Mimi ya bayyana (watau mahaifiya shi) yasa shi safke ajiyar zuciya mai zafi yana bin wayar da kallo kamar zai iya hango taswirar fuskar ta daga cikin sunan har ta tsinke wani ya kuma shigowa bai ɗaga bah sanin kanshi ne in ba wayar nan ya ɗaga bah zata iya kashe mashi battery waya yasashi dole ɗagawa yakai ta saitin kunnen shi tare da cewa "Hello"daga cen ɓangaren naji wata kamilalliyar murya tai mashi cikakkiyar sallama maimakon ya bata amsa sai cewa yayi "good day mimi" cikin damuwa matar ta kuma cewa JAHEED (HARDWORKING, DILIGENT AND STRIVING) baka da lafiya ne badai ciwon naka bane ya motsa  "ban sani bah mimi Ammh ji nake zan mutu zuciya ta ciwo take min" ya faɗa kamar zai fashe da kuka "Don Allah JAHEED ka dawo gida inga halin da kake ciki zuciya ta sam bata da natsuwa abinda kake min baka kyautawa yau kwanan ka nawa cikin ƙasar nan ammh baka iya zuwa inda nake  in ganka kuma ni ka hanani zuwa inda kake miyasa kake hukunta ni akan laifin iyalan gidan nan laifin da bani na aikatashi bah ko kana ɗauta matsayi ɗaya dasu ne  kake gudun na" cikin takaicin kansa da ganin bai kyauta bah don ya tsani mutanen gidan suba ai bai kama ta ya shafi iyayen shi bah dake tsaye akanshu suna nuna mashi kulawa da tattali. A raunane yace "mimi kiyi hakuri ba zaki gane kalar suyar  da ƙuncin da zuciya ta ke shiga bah duk lokacin da nake cikin gidan  "na sani JAHEED na fahimta so suke su raba ni dakai su shiga tsakanin mu ta Allah ba tasu bah Jaheed inshallah ba abinda zai faru dakai "Mimi kiyi hakuru yau zan bar ƙasar nan zanje ladon wurin likitana inna ji sauƙi zan shigo Inshallah "Allah ya yarda Jaheed ya baka lafiya" daga haka sukai sallama ya mai da akalar kiran nashi gun Eyon "kayan karmin ticket" abinda yace kenan bayan Eyon ya ɗaga wayar. Yayi shiru yana sauraron yadda jini da tsokar shi ke tafasa da fizga yayin da ƙashi da ɓargonshi ke dandaƙa zuciyar shi na bugun ganga.

Cikin ƙanƙanin lokaci Eyon yai settings komai abinka da masu ƙasa ƙarfe 10pm jirgin su ya tashi...

MIRAN 🌺🌺🌺

Tunda aka tabbatar mata da mawuyacin abu ne SABREENA ta cigaba da rayuwa da rayuwa saboda spinal cord ɗinta ne ya taɓu yanzu haka ana shirye shiryen aiki ake mata kuma shi wanda yai silar kwanciyar ta  zai ɗauki nauyin kula da ita ta ajiye maganar gefe bawai don ta manta bah sai dai matsalar da take neman kunni mata kai ita tasha gaban waccen saura 3 weeks bikin ya Aryan 1 january bayan munyi safkar mu kenan hidima sosai ake a gidan don gidan ya fara karɓar baƙuncin en biki samha tuni ta koma gidan su daman wurin momy take zaune saboda bata da ɗiya mace har zuwa yau hajja bata kuma cewa komai bah akan miran duk uban birthday da aka sha tana gidan tai kunnen uwar shegu  yooh  ina miran ta bari suka ƙara haɗuwa da ita balle ta faɗa mata ba daɗi ga hidimar jika na gaban goshi yasha mata kai miran aiki ba fasa zuwa tai bah sai mah Abinda yai gaba bare mah da Yanzu laba ta cigaba ta samu yadda take so ga Asibi ga gidan tv tana da full confidence na cigaba da aikin.

Yau ta kasancewar asabar ba bata fita aiki bah sai asibiti da take son zuwa anjima yasa tabin ya Aryan suka fita ..........................

[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜

             BAI SAN NA

                     GIDA BAH

                             SAI YA CIZAH

.STORY

     &

   WRITTEN BY

     F&F

    (  PERFECT PAIRS 🌺)

   29..........

Yau ya kama asabar bata fita bah sai asibiti da take son zuwa anjima yasa suka fita da ya aryan shopping tun safe har yanzu da ake maganar 12 a kuma dai dai lokacin ne hajja ke safkowa daga upstairs tashin ta kenan cike da kamewa da taka tsantsan a saman doguwar kujera tai ma kanta  mazauni waya na kare a kunnen ta tana magana da paah zaman ta ba daɗewa momy ta shigo da alama daga unguwa take kujerar dake kusa da hajja ta zauna tana sauraron hajja har ta gama wayar sannan ta kalle ta cikin sakin fuska hajja tace "harkun dawo Alifa babu dai wata matsala "babu wata matsala hajja kaya sun masu sosai saidai mu jira ranar ɗaurin aure  kawai "ina sauran en rakiyar "suna sashe na daman ke na shigo gaishewa  na faɗa maki yadda mukayi dasu su Aunty rahila nata gaishe ku murmushi hajja tai mai faɗi "Allah sarki kafin in koma duk zan kai masu ziyara  mu gaisa ammh sai bayan bikin nan "ai kafin ki je hajja duk zasu zo kawo maki amaryar taki ƙara faɗaɗa murmushin ta tai tana kallon maah dake tunkaro suda ture a hannun ta gaban hajja ta ajiye shi tana gaishe ta da kulawa ta amsa tana mata sannu sannan ta kalli momy tana mata sannu da zuwa "aike ke da sannu yaya wallahi naji daɗin ganin en uwa na "ai lailah kinyi dacen sirikai dangin Alifa basu da matsala mutanen kirki ne hajja ce mai wann maganar 'wallahi na gani hajja ni shaida ce Allah ya tabbatar da Alkhairi maah ta fada tana gyara zama. Cikin bada umarni hajja tace da momy ta kunna mata tv firar su suka cigaba dayi har lokacin da tv ta kama aiko a tashar jakada suka tsinci kan su ana haska zagayen da su miran sukai a ƙauyuka da irin matakin da adalin shigaban mu ya ɗauka wasu na fatin ciki da haka  wasu na soki burutsu kusan dai mutane baa iya masu.

Ɓoyayyan murmushi hajja tai da ita kaɗai tasan ma'anar kayan ta bata ce komai bah suka cigaba da firar su kamar ba abinda ta gani suna zaune a haka paah ya shigo da twins ɗin shi sai zuba mashi shagwaɓa suke suna son ya basu kuɗi bai kula su bah sai da ya zauna ya kalle su sai zumɓuro baki suke cike da dattakun shi yace muzaku dasu da wata sabuwar shagwabar humaida yace haba paah kasan next week zamu koma school kuma ba muyi siyayya bah hmm kawai paah yace yasan akwai abinda suke shiryawa duk kuɗin da suke samu ina suke kai su (don suma suna business humaid ball yake bugawa da team ɗin su guru junaida tare suke aiki da grandfah acen ƙasar Ammh duk da haka suna karatun su a Egypy) sai sun ci nashi duk da haka kuma fah a gidan hajja suke zaune ATM ɗinshi ya miƙa masu da kashedin iya abinda suka tambaya zasu ɗauka kallon hajja junaida yai lokacin da yake amsar atm daga hannun paah suna zuba godiya jin tana cewa ba tare da ku za'ai bikin Aryan bah knn kafin yai maganar humaid ya riga shi "a'a zamu dawo kafin lokacin hajja ptoject muke yi kafin ranar bikin mun kammala Inshallah "toh Allah ya yarda "Ameen" suka amsa suna ficewa

Sannan ne paah ya samu dabar gaishe da mahaifiyar tashi cikin girmamawa ta amsa mai da sakin fuska yayin da matan shi ke mashi sannu da zuwa nan mah da sakin fuska ya amsa maah ta yunkura zata tashi ta kawo mai ruwa hajja ta dakatar da ita ta hanyar cewa ta barshi tai zaman ta magana zasu yi ba musu maah ta zauna cikin bada umarni tace mah momy taje ta ɗauko mata system ɗin ta a ɗaki da toh tabi ta tatashi cika umarnin ta bata ɗauki lokaci bah  sai gata ta dawo gabah hajja ta ajiye system ɗin sannan ta koma inda ta tashi ta zauna sai da ta gama latse latsen ta sannan ta kalli paah fuska ba wasa "Aliyu ya maganar mu ta kwanakin baya" cikin tsare shi da ido tai tambayar "wace magana" idanu ta ƙanƙance akan fuskar shi kamar zata barbaɗe shi da masifa sai kuma tace "ta miran" ajiyar zuciya ya safke kafin ya gyara zama har yanzu shawara nake ban tsaida magana bah" kallon Karka raina mah kanka wayau ta watsa mai daya fi kama da kallo gargaɗi duk saida su momy suka sha jinin jikin su har sun fidda ran zatai magana don saida ta kwashi wasu mintoci kafin nan suka ji tace " Ammh Aliyu kama ji daɗin ka wallahi na baka na baka dama kayi watsi da ita nace ko miran tai aure ta cigaba da aikin ta na jarida ko kuma ta ajiye shi ta tsaya na Asibitin kawai shine kake cemin har yanzu bakai shawara bah ga sakarkaru sun maka magana toh mu da muka san mutuncin muka iya kare shi sannan muka san mahimmancin abun mun gama yanke hukunci ni da mahaifin ku  na riga na baka dama Aliyu a matsayin ka na uba  kayi watsi da ita, ta ida maganar tana juyo da fuskar system ɗin saitin shi a take fuskar balaraben mahaifin shi ta bayyana yana kishingiɗe a katafaren  falourn shi fuskar shi da murmushi kamar ko yaushe Ashe video call ta haɗa tunda suka fara magana dukan su saida gaban su ya faɗi musamman paah da yasan mahaifinsu kaifi ɗaya bai harka ta ƙananun mutane  duk da grandfah mutum ne mai sauƙin kai bai cika shiha safgar gidan ɗan shi bah.

Paah na ƙoƙarin magana hajja ta riga shi "toh kai kai mashi bayani da kan ka naga yafi ganin ka da gashi yafi bin umarnin ka" ɗan muzguɗawa tsohon yayi fuskar shi a sake kamar baya fahimtar jawabin hajja cikin sassauƙar muryar shi yace da yaran larabci "Abutturab kabi umarnin mahaifiyar ka kar kai mata musu in dai umarnin baici karo da dokar Allah bah kasani mahaifiya ta wuce wasa "Inshallah baba hajja mikike son nayi" yai maganr cikin bata girman ta. Wani lalataccen murmushi hajja ta saki da momy kaɗai ta ganta watau haƙarta ta cimma ruwa cikin bada umarni ta soma magana "buƙatata ba mai girma bace so nake ka haɗa auren miran da Aryan ayi su lokaci guda  so nake naga gidan nan  zuwa shekaru kaɗan naga ya cika da jikoki "uhmmmm" paah ya fidda sauti cikin son cikin son danne abunda ke niyar taso mashi "na amince hajja Allah ya tabbatar mana da Alkhairin hakan da amin hajja ta amsa ta ɗaura da cewa " kuku ma sai ku tuntuɓi miran da maganar aure" maah ta bita da toh momy mace taso nuna rashin amincewar ta ta ka mata birki  duk da haka saida tace "hajja Ammh fah miran kamar bata da saurayi caraf hajja ta cafke zancen "Ai mijin ba wani wahalar nema ne dashi bah samari nawa ne ke gararamba a gari a cikin sai ace baza'a samu bah "ammh hajja wannan irin aure kamar an gaji da ita aure ba ai mashi irin wannan hayen kisan yanzu duniyar abin tsoro ce yana da kyau a tsanan ta bincike a san halin su da dangin su mutanen yanzu basu da tabbas kar aje ayi abinda za'a dawo ana nadaam daga baya  "Sannu Alifa nace sannu ni kike ma wannan karatun kin san shekara nawa ne ina bitar shi har ni kike mah gyara ke mai tilawa toh ki shiga taitayin ki wallahi kar ki kai ni bango kar ki yarda in sa ƙafar wando ɗaya dake  auren miran in kinga ba ayi shi toh mutuwa ce nayi  "ayi hakuri hajja Allah ya tabbatar mana da Alkhairi  daga haka falour ya ɗauki shiru sai hajja dake lissa wai gobe ko zuwa jibi zata kira wasu daga cikin samarin dangin su zasu zo ganin miran wanda tai mawa shi zai aure ta

(A gaishe ki hajja watau ba ma wanda yai mata bah wanda tai mawa ammh hajja kina sha'a karon ki da fan's ɗin miran don ba sassautawa maki zasu bah suna nan shirin maki zanga-zanga) .

Ohoo miran batasan wainar da suke toya bah yau ya Aryan ya sama mata nishadi da bai da limit sun shaƙata sosai da yayan ta dake ji yafi kowa  ji da ita bayan sun bar shopping mole gidan su samha suka wuce sun ɗan jima a cen daman ba gidan baƙuntar su bane inda mutunci an zama ɗaya ya bata tsarabar da yai mata sannan suka wuce gidan ya Aiman zuwan ta gidan ya mantar da ita duk wata damuwar ta sun sha fira sosai cikin so da shaƙuwar su kamar su haɗiye juna wannan haɗin kan nasu na matuƙar birge iyayen su a cikin firar tasu ne ya Aryan ke cewa "soon za'a raba ziyarar nima na kusa girma a gidana wata rana za'a zo fira hararar wasa ya Aiman yai mai (mai hali irin na mahaifiyar su zurfin ciki) "Ammh aryan baka da kunya yaushe ya ka kwarkware haka kai big bro aure fah zanyi mi ake da kunya a cikin rayuwar aure kuma ai nan ba wanda zanji kunyar sa" pollow dake kusa da su ya Aiman ya jeho mashi da hannu biyu yasa ya cafke shi suna dariya.

Matar shi sai iri wannan abu take tan en yatsine yatsine da en harare harare wai don duk ta caka miran ammh baiwar wallahi bata san mah tanayi bah miran bata fahimtar kana fushi da ita musamman in bakada mahimmanci wajen waɗanda tavdamu dasu dadu take sha'anin ta don tunda ta shigo gidan bayan gaisuwa bata ƙara bita kan taba  (kuji aikin banza ana harkar arziƙi wasu na fama da mugun halin Allah ya kyauta)  ita kan ta bata da sahihiyar hujja na tsanar miran kawai rashin mass ne da rashin sanin ciwon kai ammh ba damar magana saboda ya Aiman wargi ne ya sha maganin zama da ita ba sakaran na miji bane tsayayyen na mijine da yake tsaye akan gidan shi shiyasa big aunty ke shakkar shi.

Sun daɗe sosai a gidan ya Aiman har twins suka isko su da uban niƙi niƙin shopping da suka yi suka biyo kawo ma ya Aiman nashi haka suka fito  su duka suka nufi gida a mota ɗaya ya Aryan ke driving ya Aiman na a mazaunin banza yayinda su uku ke baya sun sa miran tsakiya a cikin motar ma kamar zasu fasata musamman na bayan da dama basu cika jituwa bah sai er tsama suke na gaban share su sukai da alama magana mai mahimmanci suke motar ya Aiman da twins sai dai guard ne suka biyo su da ita.

A tare suka suka nufi cikin gidan bayan sun isa gida sai dai a yadda suke zaune a mota a mota a haka suke tafiya a yanzu ma lokacin da suka shiga daidai grandfah na cewa "Amina na amince da auren nan don nasan bai saɓa Shari'a musulinci ba ammh kar kice zaki tilasta mata auren wanda bata so itama ai tana da haƙƙi wannan auren fin ƙarfin da kike shirin haɗawa akan miran duk abinda ya biyo baya ki kuka da kanki duk da  ina  kyakkyawan zato Allah ya tabbatar mana da Alkhairi wata 3 ne koh "haba kai kuwa ka bar maida mu baya sati 3 ya rage da zara idanu ta ida maganar paah dai da ameen ya amsa.

"AURE" miran ta furta kalmar Muryar ta na masifar rawa babu wanda bai kalle ta ba harda grandfah ganin irin kallon da ake mata yasa ta watsa da gudu ta haye upstairs yayinda da sauran yayyan nata suka zauna a falourn jin ba'asi paah kuma tashi yai ya fita daman sauri yake.

HAMDA 🌺🌺🌺

Rabo na da fita tun lokacin da aka kai Apip asibiti gashi yanzu 2 weeks ya rage saukar mu saboda wutar da en rugar mu suka Kunno wai sai mun bar masu gari wallahi su ba zasu zauna da mayya bah in lashe su kai in taƙaice maku zance wani guntun yaƙi akai mulook shi ya sanyaya su suka haƙura ai da tuni sunyi farfesu na ko miye dalilin shi ohoo daman tunda yai fira da en jarida ya zama so silent kamar sabon tuba yai sanyi sosai shi ya riga basu hakuri yaso ɓatar da maganar ammh ammh ina sun murje ido sun sha toka sam basa fahimtar yaran shi daga ƙarshe aka zauna zaman sulhu sun haƙura su Arɗo su cigaba da zama ammh fani lallai sai nabar masu gari  jauro ya kafa mah Arɗo sharaɗin wata ɗaya ya bashi ya fitar dani daga rugar ko su kore ni ta ƙarfi Arɗo ya amshi sharaɗin su hannu 2 ya ƙara da cewa in har nasamu mijin aure kafin lokacin zan ma tafi ohoo su dai duk yadda zaiyi dani yayi ko saida ni zai yi ba damuwar su bace indai zan bar rugar bukata ta biya. Uhmmm ni abun nasu mamaki yake bani wani lokacin dariya damuwata ɗaya hanani zuwa islamiya da Arɗo yai a jiya Adda ta same shi da maganar zuwa na islamiya bai kula ta bah ganin haka yasa tace Arɗo ni a gani na hana hamda fita ba shi bane mafita bah kasan hukuncin da dattawan garin nan suka zartar

24 / 64