Author : F&F Category : New Hausa Novels 2026
banbami take tana kumfar baki ranta yakai ƙololuwa wajen ɓaci koda ta koma gidan saita hakince kan turmi tana jiran dawowar jauro ayi ta ta ƙare yau zugashi zatayi dole sai ta ida manufar ta akanshi ko ta samu sauki dama ga autanta ya liƙema yarinyar nan kamar jela tunda ta ɓata shima baida lpy ba ci ba sha, tsabagen takaicin HAMDA da take har shafeshi tayi taƙi maida hankali ta nemo masa magani jauro ya biye mata duk kanshi suke hirar haushin HAMDA kam inda za'a sa masu wuƙa a wuya baza su faɗi me hamdar tayi masu sukayi mata wannan mashahuriyar tsanar ( kuji fa munafurci da bakin hali mtswww nayi tsaki na gyara zamana yayin da bestyy bata ce komai ba ta kafe littafin da ido nasan takaici ne ya hanata magana )
Wani wawan tsaki ASP ya ƙara ja a karo na ba adadi tunda yazo garin nan ranshi bai taɓa ɓaci ba irin yau ba da ƙarfi ya faɗa bisa kujera yana latse kiran da ya addabi ƙunnuwansa ko sau ɗaya bai duba mai kiran ba lokaci guda yana dannama TV harara kamar idanunshi zasu zazzago yayi bala'in tsanar wannan shirin da wata bugaggar yarinya ke gabatarwa ( acewarshi) wai ita mummy's girl......
[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜
BAI SAN
NA GIDA BA
SAI YA CIZA
STORY
& WRITTEN
F&F
PERFECT PAIR
7....
Tana mashi take da MATERNAL RIGHT a ganinshi wannan shirin ya saɓa ma dokar kasa in banda ɓata tarbiya yara mata da take bai ga amfanin shi ba Ita ala dole ga mai kishin mata amma da yake ubanta wani ƙwaro ne a ƙasar ba wanda ya isa ya take mata burki tsaki yaja lokacin da ya yi wurgi da remote ya faɗi cikin kujeru murmushi ɗawisu yayi da shigowarshi knn ya nufi gaban table ya kwashe takardun da yazo nema cikin zuciyarshi yana gulmar ASP duk da ba wani dadewa sukayi tare ba amma ya fahimci wasu daga cikin hallayanshi ASP mutum ne mai masifaffen son girma indai kaga ranshi ya yi bala'in ɓaci toh wanine ya nemi kawo masa raini murmushi ya ƙara saki a karo na ukku kamar zai fita sai kuma ya ƙarasa inda yake zaune Sai cika yake yana batsewa bai tsaya wata-wata ba kai tsaye ya tafi ga maganar da ta tsayar dashi yace "sir madam fa ta kirani sai masifa take kaƙi daukar kiranta tana tunani raina mata wayau kake kayi hakuri ka ɗauki kiran nata " ASP bai wani ja aji ba ya buɗe idanunshi da ɓacin rai ke kwance aciki ya kunna hasken wayarshi yana dafe goshi tare da jan siririn tsaki a ɗan fusge yace " wllhy ɗawisu aikin nan ya isheni na rasa da wane zanji ɓangare guda ga ƙabilar can wnn ɓangaren ga siyasa wannan matar ban san mi ta ɗauki jami'an tsaro ba izzarta zata sa muyi mata aiki kasan dai ba wanda ya isa ya mun dole " nine shaida cewar ɗawisu , amma abi lamarin a sannu kai ka ɗauki zafi itama haka kasan abun akwai ciwo murmushin takaici ASP yayi yasan murmushin datayi a waccan ranar da abinda take shiryawa yace " ɗawisu bari inɗan maidamu waccen ranar su waye aka bari a station ɗin nan har wannan ɗan ta'adar ya samu damar tserewa nifa abin nn yana bani mamaki a inda na ajiye shi ba kowa yasan da wurin a station ɗinnan ba ɓoyo nayi masa na musamman saboda nasan hatsabibancinsa gsky raina na bani muna da 'yan leken asiri ". shiru ɗawisu yayi alamar nazarin maganganun ASP kafin yace " maganar ka kuma kamar akwai alamun gaskiya ni kaina yadda yabar station ɗin nan cikin sauki abun yayi masifar ɗaure man kai batare da hayaniya ba ko zubar da jini kuma abun tashin hankalin manyan ƙasar nan ya fara dawowa kanmu mun yi abinda ba wanda ya kokarta yinshi a wannan ƙasar nan, cikin gamsuwa ASP ke jinjina kai yace "ɗawisu muna buƙatar sanin wani abu su waye a station akwai jami'ai da yawa sergent nibran da rashid duk suna nn ina tunanin abubakar ma ba mu tafi operation dashi ba". Good ɗawisu call for emergency meeting now!! Ok sir har yakai kofa sai kuma ya dawo yana cewa "sir issue ɗin mutanen can 'yan ruga ka......." Dakatar dashi ASP yayi cikin takaici yace " na gama da mutanen nan baka ji me mutanen gari suka ce game da su banima na gani da idona yaron nan" hmm numfashi kadai ɗawisu yaja sannan yace " amma sir wani hanzari ba gudu bakasan target ɗinmu akan issue ɗin nan tsuntsu biyu zamu harba da dusti ɗaya muddin yarinyar nan ta dawo da rai dole zamu samu hint a tsarin ƙabilar nan tunda mu bamu da karfin ikon da zamu tunkaresu sai mu sa yarinyar HAMDA naji suna ce mata ta zamar mana tarko" maimakon ASP ya maye mashi da wani comment sai cewa yayi " ɗawisu kaje kayi abinda na ce kaɗai". Ɗawisu ya cije soft lips ɗinshi yana wani kanne ido ga magana bakinshi amma ba damar yi hakan yasa ya hakura ya fuce .......
Ajiyar zuciya ARƊO ya sauke a karo na ba adadi tunda inna ta gama ba shi labarin wulakancin APIP da yayi ma kusan duka matan garin shima ya basu wanda yayi ma su JAURO da jami'an tsaro tsabagen takaici ya hana ARƊO magana dole ma ya mike tsaye don neman masa magani amma ya lura harda iskanci wani lokacin , in yana abu kaikace wani autan ma ya fishi katsari. ARƊO bai tanka ma kowa ba ya tashi ya shige dakinshi yana maganar zuci bai da burin da ya wuce yaga dawowar HAMDA cikin koshin lafiya amma zuwa wannan Lokacin ya fara fidda rai da ita ga APIP na neman rikita masa lissafi......
APIP bayan fitarshi daga gida direct gidansu JUHUD ya wuce yana tafiya yana wani yatsine fuska sai kace wani yayi mashi dole cike da izza, kasaita da jin kai haka wannan ɗan neman rigimar ke taka ƙasa a haka ya isa gdnsu JUHUD yadda yake buga gidan zaka dauka sabon kamu ne a hauka suk ya diegita Mutanen da ke kewayen wurin an fito anyi cirko-cirko saidai gidan da yake ma mahaukacin bugun babu alamar akwai rai mai motsi Cikin sa, kusan haka ne mammah bata nan taje unguwa juhud na islamiyya har hannunshi ya fara jini saboda kyauren da ya tsufe yayi tsaysa duk ya lallauye amma ba alamar APIP zai tsaya sai ma ƙara kaimi yake wajen kaima kyauren duka sai dai Cikin mutanen ba wanda yayi kuskuren tarar numfashin shi sun san hali sai dai ƙananan maganganu suke,zuwan JUHUD shi ya katsesu kai tsaye wurin APIP ta isa tana rike hannunshi cikin damuwa tace "haba yaya minene haka baka ganin kana jima kanka ciwo" ko kaɗan bai motsa ba saidai ya tsaya da bugun gidan zuciyar shi na masa kaikawo apip ya tsani gidan nan ko kaɗan bai son tuna gidan balle har wani tsautsai ya kawoshi saboda a kofar gidan ne aka tsinci gawar ya AJMAL a wulaƙance kamar bashi da kowa abun takaicin ma babu ko kai jikin gawar gangar jikin har ta fara tsutsa alamar an daɗe da mutuwa in APIP ya tuna wnn ranshi kuna yace ya AJMAL mutumin kirki ne wllhy bai cancanci irin karshen da yayi ba shiyasa kaf mutanen garin nan ɗaura fansar ran ya AJMAL a wuyansu musamman gidan nan fa aka tsinci gawa acewarshi da gudunmawarsu ai sunga gawar miyasa basu zo suka faɗa mishi ba har saida jikinshi ya fara tsutsotsi ,kai APIP akwai riko masifaffen riko gareshi in ka masa abu na alkhairi ko akasin haka sai ya sakanta maka dashi shysa har yanzu ya kasa mantawa da wannan kusan shekara nawa da suka wuce......
A slowly ya janye kwayar idanunshi ta light ash ya maidasu a wani gefen a dake a kuma fizge yace " wurin ki nazo magana akan ɓatan HAMDA ance man daga islamiyya bata dawo ba kuma nasan tare kuke tafiya" sai da JUHUD ta share hawaye tana kallon gefen fuskar APIP da yake ta wani ciccika yana basarwa ita kuma Allah ya jarabceta da mugun son APIP tana son shi sosai tana masa kallon yayanta ( saboda ita kadai ce a wurin mahaifiyarta) tana kuma tausayin halin da yake ciki, da ba haka suke ba muguwar shakuwa ce tsakaninsu yanzu ya canza mata ta rasa gane kansa. " Yaya mushiga ciki na baka labarin abunda ya faru bazai yiwu muyi shi a tsaye ba" wani matsiyacin kallo APIP ke binta dashi kanar ya kwaɗa mata mari haka yakeji ya wani danna ma gidan harara fahimtar hakan yasa JUHUD ta nuna wani dutsi dake ɗan nesa da gidansu kaɗan wannan karon bai musa ba ya bi bayanta amma duk da haka yaƙi ya zauna sai dai itace ta zauna .......
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fara da cewa " ya APIP sun ƙara waiwayar mu a karo na 2 kuma nasan fansa suka zo ɗauka ka tuna abunda ya faru lokacin mutuwar ya AJMAL irin kurar da ta tashi har muka samu galaba akansu yadda suka sace HAMDA da gayyane kuma da sa hannun da yawa daga cikin mutanen garin nan ne ranar muna hanyar dawo daga islamiyya hamda tace yau baxan bi ta hanyar gidanmu ba bata jin daɗi kuma ARƊO yace ta koma gida da wuri ya nason magana da ita, munyi sallama lafiya da ita ta bi hanyar gida nima na mike har nayi nisa na tuna wayarta na hannu na a hanzarce na juya sai dai kafin na ida karasawa na jiyo murya nakiran sunan Allah cikin zafin nama na ida karasawa lokacin tana sulalewa ƙasa ta faɗi fuskokinsu duka a rufe bansamu damar ganin su ba suka saɓe ta suka danna a mota har ɗaya daga cikinsu yaso ganina hankalina yakai kololuwar tashi, kaine mutum na farko daya fara zuwa man a rai sai lokacin da nazo na tarar wai kaima kana wajen jami'an tsaro sun kamaka kuma........." Yadda APIP ke tafasa yana huci yasa tayi shiru tana kallonshi tnda take bata taɓa ganin bacin ranshikamar irin haka ba fuskarshi tayi jawur bakinshi na motsi kamar mai sonyin magana amma yakasa a fusace ya juya kai tsaye hanyar fita gari ya nufa JUHUD na masa magiya taku 1 zuwa 2 yayi ya tsaya cak sakamakon hannun shi da yaji an rike a fusace ya juyo da niyyar kaima ko wanene bugu sai dai wanda ya gani ne yasa shi tsayawa cak duk garin nan wannan mutumin kaɗai ke controlling nashi yana girmamashi yana ganin girmanshi. Murmushi mutumin yayi wanda suke kira da ARZU ya shafa sumar kan APIP da ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya still akwai murmushi a fuskar shi yace " abokina ina zuwa haka " a fuzge APIP ya ce hamda zanje in ɗauko hannun wadancan azzaluman cikin son shi da wasa, ARZU yace " yaushe abokin nawa ya fara aikin jami'an tsaro ban sani ba " baba jami'an tsaron yanzu sun zama 'yan daba ne basu son madafar aikinsu ba duk bakinsu a haɗe yake ji ni na samu information akan HAMDA cikin sauki su me sukai yunƙurin yi da aikin suke akan gaskiya da HAMDA baza tayi kwanaki da ta kai yanzu a hannunsu ba, baba ni ka sakani zan iya sadaukar da komai nawa akan HAMDA kamar yadda ya AJMAL yayi ya tafi ya bar ma amanar HAMDA nibkima sai in gagara rikewa cikin lallashi ARZU yace " kayi hakuri abokina yanzu ko kaima kaje watakil muna iya rasa ka, ka bari muma mu shirya wa mutanen da kake shirin yima dirar mikiya ba ƙauye guda bane,ba gari guda bane, ba yanki guda bane ƘASA guda ce kasan kuma ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi ka ƙara lokaci mu shirya zuwa gobe muyi shawara da kyar ya samu APIP ya fasa zuwa ya bi bayanshi bayan yace ma JUHUD ta koma gida. Amma har cikin zuciyar shi ba hakura yayi ba yadda yake jinshi yanzu zai iya tunkarar mutuwa kai tsaye balle wasu banzaye wai ƙabilar AFTABUDDEEN waɗanda yake da tabbacin mutane ne kamar shi hakuri na yaune kawai amma gobe saidai suji kurar tafiyarshi da wannan gurguwar shawarar APIP ya shige gida. ..........
[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜
BAI SAN NA
GIDA SAIYA
CIZA
Written
by
(F&F)
(Perfect pairs)
8 ....
A babban dakin taro na station nan ɗawisu ya tattara duk wani staff da ke ckin station din kamar ydd A.S.P y buƙata bayan shigowar A.S.P ya faɗa masu dalilin wannan meeting din kai tsaye akan waɗanda ke a station a rnr sergeant akab ne ya fara mgn da cewa "sir sihiri fah gsky ne duk wanda yake a matsayin Mu a wannan lokaci ba wani yunkuri da zai iya yi na ga halitta ranar mutanen dake tare dashi kadai sun isa su firgita tunanin ibni adam balle mutum yai kuskuren tunkarar su, mutane ne masu matukar hikima da basira da salon iya taku,
Kusan gaba ɗayan mu waje suka tattara mu inspector kalid da Abubakar sae wasu da ba'a rasa bah suka samu a ciki ban san ydd ta kaya a tsakanin su bah har sukai nasarar cimma burin su nan fah kallo ya koma kan mutane 2 da sunan su yai including sunyi tsiru-tsiru
Cikin zaƙuwa ASP yace miya faru a cikin ko ku kuka watsa mana shiri, inspector kalid ne mai karfin halin yin mgn don Abubakar wasu abubuwa yake yi da alamu suka nuna a tsorace yake don haka inspector yace "sir a wnn gaɓar iya rainin wayau an raina mana shi wllh sir mutanen nan shegu ne plan ɗinsu ya dame namu ya shanye, sir ni a fahimta ta tunda ga harin da aka kai ma rugar fari , dauko yaron nn da mukai, da sace yarinyar nan duk yana cikin shirin su kuma sir abinda zai baka mamaki shine ba DODONSU kuka kama bah yaron shine ammh ckn manyan yaranshi shiyasa wannan karon da kanshi ya taka station din nan yazo cetonshi"
A fusace ASP y dake table dake bayan shi ckn tsananin ɓacin rai ya ce impossible inspector how come's zaka ce min bah boss nasu muka ka ma bah ina yaronshi ya kasance haka yake da zafin rae da shegen giraman kai shifa ogana nasu ya zamu tarar dashi gsky I'm tired over.
Ckn tsananin takaici inspector ya ƙara safke ajiyar zuciya yace tabbas mgana ta haka take sir daga yanayin ydd suke zube har ƙasa suna kwasar gaisuwa zaka fahimci hkn sannan wani abu da nai observing dangane da su shine su ɗin jinin sarauta ne tun daga yanayin takunsu zaka fahimci hkn , tsabagen takaici ya hana ASP magana daman tun ranar da suka bi bayan motoci nan ya fahimci akwai lauje ckn naɗi .
Sergeant ya ɗaura daa cewa kenan sace ɗiyar madam da sukai sunyi ne don su bada kafa suna so su janye hankalin mu su aiwatar da son ransu lallai kam wann lergent ne capacity ɗinshi is good.
No wonder nima nayi mamakin yadda ya yarda muka kamashi cikin sauƙi, hmm sir munyi maganar nan tun farko da yaron nan da ya za hannun mu da kashe shi mukai da mun rage mugun iri da kaasansu zaka ka suna tona ma kansu Asiri da kuma mun samu wata ƙofa sir ina tunanin mafita ɗaya ce gare mu yanzu"
Da suri kowa ya kalli ɗawisu don jin. wace mafita ce wnn
Kanshi tsaye yace HAMDA' saida ASP ya nisa sannan tuna mai sunan, dole fah rugar fari zamu koma mu fara bincike da zafi-zafi yadda mutanen garin suka tsane su ba abin mamaki ba ne in mun tarar da sa hannun wasu a cikin wasu a cikin su ta hakan ne zamu samu informa na waccen ƙabila kuma in mukai nasarar ceto yarinyar ta dawo a raye kuma ckn hayyacin ta ko yaya ne zamu samu wata makafa."
Ammh sir da kamar wuya ka sani na sani muddin mutum yai kuskuren ko da taka ƙasar dajin da suka mamaye suka ka mayar nasu ta ƙarfi da yaji sunan shi gawa balle mutum har yaje ya ƙetara zuwa sansanin su yai kwanaki kuma ya fita da rai gaskiya abin da kamar wuya is impossible nashwan ne mai wannan maganar ɗawisu ya girgiza kai in full confidence yace by GOD everything is possible"
Da wannan shawara suka kafa hujja kan gobe zasu koma rugar fari
*******✓✓✓✓✓✓*******
Ikon Allah itace kalmar da ta fito daga bakin Adda tana riƙe da haɓa lamarin rugar ta bar kallon shi a zalunci tana kallon shi a taɓin hankali yooo in banda taɓin hankali da tsantsagwaron jahilci dake ɗawainiya da su taya za'a ce an sace mutum ba'a san halin da yake ciki bah ammh wai bikin mutuwar shi suke shirye shiryen yi su kanya daman mutanen rugar sunyi Alƙawarin muddun Ahlin "MAS'OOD WAGINI" suka zamo zamo tarihi zasuyi wannan waleemar da sai yanzu Allah ya cika masu burinsu ( a cewar su ) dama HAMDA ce kaɗai ta raye yau kuma su yada kwallon mangwaro sun rabu da ƙuda
Hidima mutanen gari suke sosai sun kwantar da dabba tafi a ƙirga wai a haukansu burin su a cika dole su fantama su faranta ran juna in kaga yarda sukeyi zaka ɗauka wani abun arziki ne bare mah ace mu gangara gidan Arɗo abin ba'a ce komai
( Watau tsohon nan na lura besth zararre ne dama mutanen rugar baki daya in banda taron aradu watau waleema ma ma zasuyi lallai mutanen