Author : F&F Category : New Hausa Novels 2026
ta tashi a banza "kayi hakuri kanina da inada da hanyar taimakon ka da nayi ammh wannan shine tsarin "Don Allah 'yallaɓai ba abinda za'a iya mana karatun nan shine gatan mu shikenan itama wannan shekarar mun rasa ta kenan" Apip ke wannan maganar cikin rauni bakin shi har rawa yake tabbacin at any moment yana iya bashe masu da kuka. Murmushi na zaunan yayi bayan APIP ya gama koro jawabi na tsayen na badu hakuri na zaunen ya katse mashi hanzari "A'a talal wannan magana ce ta taimakon kai da kai tunda sune kuma har suka nemi alfarma baza muyi rejecting nasu bah mu gwada shigar da bayanan su "cikin rashin fahimtar inkiyar da na zaunen kema wanda aka kira da talal ya zuba mai idanu yana mamakin shi sosai "muga takardun ku na zaunan ya kuma magana yana miƙa mah Apip hannu ba musu ya miƙamai murmushin shi na ƙara faɗaɗa da yasa suka kara zuba mai idanu.
Iatse latsen 10 minutes yai ya ɗago ya yana kallon Apip "ya sunan abokin nawa" duk da yaga sunan na shi a takardun Ammh hakan bai hana shi ƙara tambaya bah "USMAN ADAM" duk saida suka kalle shi harda Aqqab kamar yaune ya fara jin sunan, basu ƙara zaman 30 minute bah aka kammala masu komai harda aqqab kuma ko sisin su basu amsa bah sun dai ce masu nan da 1 week su dawo
Sai bayan fitar su talal ya kalli najeeb cikin neman ƙarin bayani "mi kai haka kenan miye ma'anar abinda kai "wallahi matsala ta dakai abokina wani lokacin kanka bai kawo light tsuntsu biyu na jefa da dutse ɗaya nayi niyar taimakon su har cikin zuciya ta kuma inshallah zan shiga in fita naga sun samu gurbin karatu a makarantar nan "akwai wata hujja bayan wannan" cikin tsatstsare shi da idanu yai tambayar saida najeeb yai murmushi yana shafa siririn sajen shi dayake a kwance kamar bazai bashi amsa bah don system dake gaban shi yake cigaba da dannawa talal mah ya fidda ran samu amsa cen ya tsinkayo muryar shi yana cewa " ko ba komai mun samu details ɗin shi ko yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli yaci ribah" still dai talal bai fahimci manufar zancen nashi bah don haka ya watsar da zancen suka cigaba d aikin su.
Ashe ɗazu ba komai suka gani bah akan kallon sai yanzu da suka fito en wani department sun fito break ya rahman Apip kamar ya nutse tun yana basarwa har abin yaso fin ƙarfin zuciyar shi ammh yana ƙoƙarin tausar ta wasu mah harda nuna su suna gulma haka dai suka cigaba da hakuri har suka kusa zuwa babban gate shewa da dariyar samari da en matan da sukai gungu harda nuna su ya zafafa zuciyar Apip wannan karon kasa hakuri yai ya dangwarar mah Aqqab takardun hannun shi ya tunkare su gadan gadan yana tattare hannun riga kamar mai shirin dambe tsit sukai su duka yadda kasan anyi ruwa an ɗauke har saida Apip ya tsaya gaban su yana baza sumar kanshi dake masifar mashi zafi a karon farko naga sumar kanshi a bushe fuskar shi totally ta canza a fuzge yace "wai guys miye haka kuna abu like zautattatu ko nace taɓaɓɓu what is special to me ya babbanta ni da mutane ne har na zama abin kallo da tsokana "sorry mr.man share kawai is not important" ɗaya daga cikin su yace "anƙi a share rashin mahimmancin nasa ne yasa nake son sani tell me" masifa ya cigaba da zazzaga masu kamar uban su ta inda yake shiga bata nan yake fita bah haka aka ringa bashi hakuri yana tirjewa serious abun na damun shi da iya gaskiyar shi yake faɗan nan batun yau yake fuskantar irin haka bah shikenan bai da damar shiga mutane sai an sa ya raina kan shi mi hakan ke nufi ko yana da wani aibune da ya zama abin wasan su maganar da wata yarinya tai wai ita surayya duk suka kalle ta har dashi
Uban gayyar "kaje ka tambayi uwar ka ai tafi kowa sanin ka zaka wani rufa kanmu da tijara" mtswww taja tsaki surayya ba tayi maganar bane da wata manufa tayi ta a sigar baƙar magana ammh kalaman ta ba ƙaramin dukan zuciyar Apip sukai bah sunyi tasiri matuƙa ya ƙara kallon kanshi daga sama har ƙasa yana matuƙar mamakin abinda ke ajikin shi da yasa mutane ke mashi haka har ya zama abin kallon su da kyal Aqqab ya jashi suka bar wurin bayan an bashi hakuri sosai. Wani yanki daga cikin en mata da samari sukai ma surayya caah suna nuna rashin dacewar maganar data gwalɓa mah Apip daman an bata lambar yabo a wuri sakin maganar ba taunawa sam yarinyar bata iya magana bah suma dai baƙaƙen maganganu ta daddanƙaro masu ta barsu da jan tsaki.
Tunda suka fara tafiya aqqab ya rasa gane kan Apip fuskar shi har wani jajajah take yi yooh Apip mutum ne da bai saba aikin wahala bah gashi bah jimirin tafiya shiyasa bai yawo daga bakin ruwa sai gida sai in ta taƙure yake shiga cikin gari fiii shaa ya dawo gida da wuya yai tafiya mai nisa irin haka shiyasa duk ya ya mutse ga waɗancen agalawan daya bama matsayin sabun kamu a hauka suna rikita ƙaramin tunanin shi sun ɗatata zuciyar shi first day in school ta zama bad day a rayuwar shi (hhhh nace bah haka za'ayi karatun a lallai mr. Apip sai sun sake zama ) har jiri jiri yake gani Aqqab ya tsorata matuƙa da yanayin shi duk tunanin shi mutanen shi ne kusa duk da dama harda su suka ƙara rikita mashi lissafi yanzu in ya zube mashi bai san ta ina zai fara bah dole Aqqab ya tallabo shi don ya lura bawai hanya yake gani bah yana jera mashi sannu sai kanshi yake kirta dake mashi masifar zafi sama kujera Aqqab ya zaunar dashi ganin lumfashin na fita cen ƙasa "Apip kana lafiya kuwa minkake buƙata "ruwa" ya fada cikin wata murya da bai taɓa jin Apip ɗin da ita bah Allah dai ya taƙaita masu wahala kujerar da yake zaune akwai pampo kusa tunda ya kafa kanshi bai ɗago bah tsawan Lokaci har Aqqab ya fara tunanin wai ruwan makarantar zai ƙarar ne ganin abin nashi bamai ƙare wa bane yasa ya ɗago shi yana tambayar shi anya kanshi ɗaya shidai Apip baice mashi komai bah sai artabun yake da lumshin shi dake mashi barazanar ɗauke wa sai ya shaƙi iska mai ƙarfi sassan jikin shi ke wadatuwa zuwa shuɗewar wani lokaci komai ya lafa kanshi ya gilgiza da karfin ruwan da suka ƙi dai bin jikin shi suka ragu lokaci guda yana sakar mah Aqqab murmushi da mamaki ya nemi mashi illa "na warware muje "ka tabbata" Aqqab yai tambayar cike da taraddadi "am telling you my friend kai nane ya ɗauki zafi shiyasa yanzu ai na sanyaya shi" Aqqab bai ƙara kuskuren barin Apip haka bah saida yai mashi guzurin ruwa .
Haka suka cigaba da tafiya suna firar su kamar bashi ne ya shiga wannan halin bah kasancewar sabuwar anguwa ce ta manyan mutane yasa basu samu napep da wuri bah sai da suka sha uwar tafiya har saida suka kusan barin anguwar tafiya suke suna zuba kamar birkakken pampo Aqqab har mamakin sakewar Apip yake haka ko shi da yake abokin shi da wuya kaga suna fira mai tsayi dai dai zasu sha kwana wata mota da basu san da tahowar ta bah ta kusan sam da Apip Aqqab yai azamar janye shi motoci 3 ne suke tafiya da shahararren gudu kai kace sama suke niyar tashi silar tsayawar ta gaban da ta kusa kaɗe shi yasa 2 suka rage gudu driver ya zuge glass ya cigaba da wanke su da masifa kamar zai ari baki yadda Apip ke kallon shi cike da rainin hankali yana yamutsa fuska ba ƙaramin baƙanta ranshi yai bah watau hawan mashi kai yake ko ga kashi ya gani baki apip ya taɓe ya juya ƙwayar idon shi a motar tsakiya da glass ɗin ke zugewa a hankali har har fuskar wata hamtsaƙiyar matah ya bayyana sukai mah juna kallon ido cikin ido mamaki ƙarara a fuskar ta kallon maitar da take mashi yasa shi danna mata uwar harara like ƙawar ido shi zasu zube ƙasa ya taɓe baki yana kallon aqqab dake basu haƙuri shima hararar shi yayi ya juya ya cigaba da tafiya cikin wani irin salo kamar da gayya yake sai da aqqab ya haɗa da gudu sannan ya iya cimma shi ya ɗan masa nisa. Ganin wurin ya fara tunkusi yasa driver sassautawa motoci suka doshi inda suka nufa ko mi yafaru ohoo maimakon motoci 3 dake tafiya a tare 2 suka kutsa cikin anguwar yayin da da ɗaya ta canza hanya.
A katafaren gidan dake cen ƙarshen anguwar motocin suka nufa tun kafin isar su driver ke danna horn ko ida daidaita parking driver baiyi ba bayan shigar su cikin gidan matar ta ɓalle marfin motar ta fice sai cika take tana tunbatsa duk ta ruɗe bata bi takan ma'aikatan gidan dake miƙo mata gaisuwa ba ta hankaɗa sashen ta ba kowa bace face MADAM
waini kam kun taɓa tunanin wacece matar nan🤔🤔 manufar ta da rawar da zata taka a cikin tafiyar nan bara na sauƙaƙa maku
^_________^ Madam mata ta 2 ce a wurin hamshaqin ɗan kasuwar nan SAIFULLAHI GANUWA da duniya ta yankar mai fili suke ci daga albarkatun ta babban mutum ne mai wasu irin ƙazaman kuɗi da ƙasar kasran ke ji dashi matan shi 3 waɗanda suka zauna waɗanda ya aura ya saki bassu da iyaka saboda son zuciya. Saratu maji daɗi (nasan baku mantata bah) itace babba danta ɗaya JASIM sai dai Allah yai mashi rasuwa sai da ya kawo ƙarfi Allah ya amshi abun shi (nasan zaku iya tuna yayan Afra) sai madam ta biyu suwaiba yaran ta 2 (Afra da shuraim) sai amaryar sa hadiza nada 3 (surayya, sultan, saleem).
Gida ne da kishi ya zaman masu abokin rayuwa basa jituwa ko kaɗan shiyasa yaran su mah haɗin kansu sai a hankali kullum cikin rikici kamar gidan gandu musamman madam da tafi kowa rikici da rawar kai matar nan iyaka ce shu'umar macece da ita kaɗai tasan kanta ko wane faɗa kaji ya tashi a gidan toh inshallah in baka samu da ita akeyi ba toh ita ta haɗa makirci saboda wani dalili nata da tabar ma kanta sani ta hana gidan zaman lafiya.
(Ku ƙara hakuri sannan ku cigaba da bibiya ta sannu a hankali nasan ina kuma saka ku ruɗani haka shi salon wasn yake koni wani lokacin sai nayi da gaske nake warware wata kitimurmurar in zamuyi la'akari da kalaman farkon litattafin nan ammh in zaku cigaba da bibiya ta sannu a hankali da kanku zaku kamo bakin zaren babu abinda ke faru a duniya sai da dalili baza'a samu dalili bah sai da sila Allah shine maƙaddari akan bayin ammh a cikin abokin halitta ake samun sila kar in cika ku da surutu muje zuwa)
A falour ta iske Afra da shuraim kowa da abinda yake yi suma bata kula su bah ta ta shige bedroom kamar zata tashi sama daga Afra har shuraim da kallo suka bita sai kuma suka taɓe baki cikin nuna rashi damuwa akan halin da suka ga mahaifiyar tasu. Ita kau saida ta tsinci kanta a bedroom sannan ta fidda tsammanin zata iya tashi saman tun a cikin mota take kiran wata number ammh har yanzu ba'a da niyar ɗagawa wannan shi ya ƙara ingiza fargabar ta dailing ta karayi a karo nafin takun maɗin ki har ta fidda ran wannan karon mah za'a ɗauka tana gab da tsinkewa aka ɗaga, ajiyar zuciya ta safke a bayyane da har wanda ya ɗaga wayar saida ya iya jiyo ta kafin ta saisaita yanayin ta ta soma magana "Ranki ya daɗe in ki ka ji ban iya gudu sa gudun ce bata zo bah shiyasa a yau wata karin magana ta addabi zuciya ta hanani sukuni wai reshe na niyar juyewa da mujiya ana zaton wuta a maƙere ammh an same ta a masaƙa anya bamu rufe kofa da ɓarawo a ciki bah LEENA-". 'mi ya faru" wata sassauƙar murya ta ambaci kalaman nan a kame "leena ki yarda baƙar inuwa ce ke tunkaro mu da alama gini muke daga sama ba tare da mun fidda Foundation bah ba zamu fidda ran rushewar sa ako wace daƙiƙa bah ..........................., Ban samu damar jin ƙareshen maganar tasu bah dalilin shigowar shuraim ta yanke wayar.
HAMDA 🌺🌺🌺
Apip bai isa gida bah saida ana kiraye kirayen sallah la'asar ga yunwa ga gajiya ga rana sun kwaso duk da ba irin mai zafin nan bace sosai amma mutumin naku yaji jiki sosai yana shiga gida ko ƙarfin sallama babu ajikin shi ɗakin shi ya wuce bai ɗauki lokaci bah barcin wahala yai awon gaba da shi inna sallah take yi lokacin shiyasa bata san da shigowar sa bah ni kuma ina islamiyya har na dawo bai tashi bah inna sai jaje take Ardo ma ya shigo yana tambayar ko ya dawo inna tace maganar da muke kenan ɗan siririn tsaki ya ja ya shiga ɗaki jim kaɗan ya fito yana nufar inda inna ta tanadar mashi ruwan alwala yana cigaba da cewa "gashi shi ba riƙe waya yake ba balle a kira shi yaji lafiya hamda in kinyi sallah kiji bakin ruwa ki duba ko ya dawo ya zauna cen nasan baida wurin zuwa in ba cen ɗin bah " toh nace ina shigewa ɗaki inna ta manta shaf da ɗazu sunyi waya dashi shiyasa bata tada maganar bah . Hankali na duk ba'a kwance yake bah ka nai wannan sallah ina gamawa na fito cika umarnin Arɗo shima lokacin yake shigowa yau ko zaman karatu baiyi bah da suke tsakanin mangarib da isha sallamar shi tasa Inna fitowa itama "hamda ki hanzarta in baya cen musan abinyi kafin dare yayi nisa rufar bakin Arɗo dai-dai lokacin Apip...................................
'
[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜
BAI SAN NA
GIDAH BAH
SAI YA CIZAH
STORY
&
WRITTEN BY
F&F
(PERFECT PAIRS 🌺)
37.................
Dai dai lokacin Apip ya fito yana miƙa yasha barcin sa mai isar shi idanu ya ɗan zaro yana kallon mu bayan ya wartsake lokacin guda yana takowa inda muke "lafiya mu tsaya ko mu gudu irin wannan cirko cirko haka kamar dogarai" Arɗo bai nuna alamar yaji bah balle aje matakin magana sai ma fucewa da yayi inna ce ta kula shi daman ta iya biye mah shirmen shi "tun yaushe ka dawo "la'asar" ya bata amsa a taƙaice "Allah ya yauta toh....... "Wallahi Apip ka tsoratar damu dakai zanje nema" nice mai maganar cikin damuwa miskilar dariya ya kwashe da ita lokacin da yake ɗaukar buta zai shiga bayi "Ashe ana ji dani irin haka woo ni Apip taurari na na haskawa .......... Bai samu damar ida jin maganar tashi bah saboda ya she bayi ko ya ida bayan shigar sa ohoo nasan Apip ba control ne dashi bah yau bamu samu damar yin fira bah balle har Apip ya bamu labari abinda ya faru a makaranta kwata kwata baida walwala ganin yau en surutu basu bisa kan na wuce ɗaki na daman inna tana wurin Arɗo.
Number da tun kwanakin baya nake gani missed call ɗin ta na isko tana kira na still , wannan ne karo na haɗu ban san dalilin addabata da kira bah har na haddace number saboda naci yanzu mah ban ɗaga bah na haye katifa na kwanta ina tunanin shekara 2 da suka wuce
^_________^ kamar yanzu fah muna tare da ya AJMAL ina karanto mashi sakon da zai faɗa mah Abban mu in yaje rubuta mashi nayi saboda yawan su kuma bana son ya manta ko ɗaya faffaɗan murmushi yai kamar yadda ya saba ya amshi takardar maimakon ya karanta sai ya shiga jujjuya ta "hamda wannan wasiƙa ce ko saƙon gaisuwa "kai yaya babu ruwan ka in kaje kawai ka bashi kuma kar ka manta da alqawarin mu "karki damu ko baiga wannan bah yasan kin damu dashi "taya yaya ni kasan mah tunanin da nake kai ya gilgiza man yana kishingiɗa "anya Abban mu ya sanni in ya ganni zai iya gane ni " murmushi yai mai sauti "gaskiya Adda ki daina hada mah ɗiyar nan taki fura mai daɗi irin ta yau kinga har yanzu bata sake ta bah har ta fara zarewa ya faɗa yana kallon Adda dake zaune nesa damu lokaci guda yana dungurar mani kai" yasan ina son fura shiyasa ya faɗi haka fuska na tamke ina turo baki ashe ma zarewa a'a kwance wa don na tambaya ai abune mai yiyuwa "kai AJMAL in baka son abu duk hanyar da zaka kushe shi kasani yanzu fura zata zarar da mutum" sai kuma ta kalle ni tasan ba amsa zata samu ba bayan murmushin da yayi "taso nan hamda kora yai maki da hali kin hana shi aiki kema ki zuciya dashi" ban musa bah na koma inda Adda ke nuna min na zauna ina kallon yadda ya AJMAL ke murmushi dake ƙara mashi kyau yana karantar takardar dana bashi shiyasa bai maido amsa bah shigowar Apip yana ƙyalƙyata dariya ba ƙaƙƙautawa da ka gani kasan ta mugunta ce fuskar shi tai masifar jaah "ga zararran nan ammh ake laƙa ma mai hankali sharri" shiru nai ganin ya AJMAL ya yunkura ya tashi zaune sassaukan abune inji ƙwanya saidai hankalin shi bama kaina yake bah Apip yake