Chapter 13 Reading CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx Arewa Novels

CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx

Author :  F&F Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   13 / 64

36K to 39K   out of 190.4K words

tsuntsaye dake saman bishiyu saida suka kama gaban su  da maɗaukakin sauti ya kira sunana HAMDA!!! Wanda ina da tabbacin da yawan mutanen rugar mu sun jiyo amon muryar shi a tsorace na juyo na kalle shi tare da zubewa bisa gwiwoyi na jin abinda yake cewa "hamda kisan kai kin fah kashe shi yafa mutu ",  a sukwace juhud dake durkushe har lokacin gaban ruwa ta iso inda nake ina kallon adnan yadda yake fitar da annuri cikin fitar hayyaci juhud ta fara tattaɓashi a ƙoƙarin ta nason tabbatar da da gaske wai ya mutu itama jagwab ta zubu kusa dani "hamda ba alamun rai fah tattare dashi dai dai kunnen arzu dake tun karo mu da alama daga gona yake *subhanallah mike faruwa ne kafin ɗayan mu yai magana wasu mutane daga cikin en rugan mu sun rufa kan mu haka mutanen suka cigaba da tsatstsafowa ta kowace kusurwa harda wadanda ke makwabtaka da rugar mu da man abinda wasu ke jira kenan abu ya faru su samu na gulma

*Innalillahi wa inna illaaihir raju'un*

Ita kadai ce kalmar da abkina zai iya furtawa a wannan lokacin don mulook ya gama kashe ni wata zabura  mutanen dake zagaye damu sukai jin mulook na cewa.........

🌺🌺🌺

A hankali motocin suka hararo cikin harabar EVERTEX UNIVERSITY university mafi girma da ƙayatuwa a ƙasar kasran ta ƙawatu da ababan more rayuwa da furanni masu sanyin kamshi itacen mango, zaitun, guava d.s suka ƙara bada gudunmawa wajen fitar da ajin ta ya rahman tsayawa laburta maku haɗuwa EVERTEX ɓata lokaci ne a binda zan iya cewa haɗuwar ta iyaka ce .

Motocin basu zarce ko ina bah sai wani babban building da kallo guda zakai mai ka fahimci hostel ne yanayin tsarukan ginin ya iske ka shaida , saidai maimakon su shiga main building da zai sada su da ainahin farfajiyar hostel ɗin sai suka yanke wani titi bayan sun shiga babban gate motoci 2 dake take ma ta gaban baya a wannan gate ɗin suka tsaya yayin da ɗayar ta zarce shantalelen titin da matsakaici gudu saida suka zo gaban madaidaicin gate sannan motar ta rage gudu lokaci guda tana danna horn jim kadan wani dattijo ya zuge gate ɗin ya rabu gida 2 ba tare da ɓata lokaci ba motar ta cinna hanci cikin gidan mashallh gida ne madaidaici na iya zaman mace ɗaya daya ƙawatu da kayan more rayuwa abin ba'a magana a inda aka tanada don parking nan motar ta tsaya tana mutuwa driver ya fito cikin rawar ƙafa ya ɓuɗe back sit duk gwarazan mazajen dake sintiri cikin gidan wasu na aikin da ya zaman masu dole sai da suka sha jinin jikin su ganin yadda gaza ke rawar ƙafa sunsan duk lokacin da duka ganshi cikin wannan halin toh  ogan nasu baya cikin yanayin happy wasu samari da fitowar su kenan daga kofar da nake da tabbacin in ka bita zata sadaka da main folour suka matso kusa da gaza da ya gama bushewa a tsaye yana jiran guru ya fito ammh kamar Allah baiyi ajiyar mutum bah "gaza how far what is wrong ɗaya daga cikin su yace     "their is any problem? Wanda ke kama da bature ne yai ƙara jefo wannan tambayar Eyon kenan na hannun daman guru a fagen wasan ƙwallon kafa, hararar sa na hannun daman shi ya watso mai "the answer is straight forward u know Duk wanda yasan guru yana cikin bad mood see abinda ajalawan nan sukai mai damma mun tara masu jakukuna iya jakuna mun rage raɗaɗi  ya ida maganar yana matsowa kusa da motar sosai tare dasa yatsan sa manuniya ya fara knocking guru ka sarara mana ka fita mu shiga ciki sai mu ida tattaunawa.

In motar ta motsa toh wanda yake cikin ta mah ya motsa zai sake magana Eyon ya rike shi yana gilgiza mashi kai "pls leave him u know yayi loosing temper mtwsss!! Gaza yaja tsaki "Please guys kubar ni naji dashi l know what to do kada ku ida hautsina mana lissafi.

Shiru sukai su duka sakamakon wawan.................

[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜

          BAI SAN NA

                  GIDA BAH SAI   

                              YA CIZAH

    

STORY

     &

    WRITTEN BY

          F&F

      (PERFECT PAIRS 🌺🌺🌺)

18..............

       Shiru sukai su duka sakamakon wawan tsakin daya ziyarci kunnuwan su da suka tabbatar daga cikin motar ya fito guru yayi shi daga cikin guru dake kwance malala a back site kwalbar giya da ya sha Fiye da rabi na hannun shi na dama na haggun ya dafe kanshi da shi, shi kaɗai ya yasan halin da yake ciki a wannan point ɗin ga waɗannan karnukan (acewar shi 😳) dake mai haushi akae muryoyin su ba ƙara ingiza ɓacin ranshi suke bah wani kallar tuƙuƙi zuciyar shi ke mashi tana tafarfasa in bah giyar nan ya sha bah bazai taɓa samin sassauci bah cikin son huce takaicin shi akan yaran nashi da yanzu yake bah matsayin kifaye da basu fahimtar mayan kalamai yasa ƙafa ya hallaba kofar da ƙarfin shi na ƙarshe har sai da ta bada sauti abnormal alamar duk yadda za'ai ta samu case ya zuro ƙafafun shi waje tare da yunkirin mikewa still yana dafe da kan shi  daya fara ɗaukar chagi  suko ba ƙaramin firgita zukatan su yai bah musamman yadda fuskar shi da idanun shi sukai masifar jaah ya cije lower lips ɗin tare da kanne ido yai masu kallo ɗai ɗai yaa kauda kai yana ƙara tare kanshi dake barazanar tsagewa gida 2 ya kafa bakin kwalbar saman reddish lips ɗin shi saida ya tsotse ta tsaf sannan yai wani kalar tilli da kwalbar duk wanda ke gaban shi saida suka dare kwalbar ta faɗa cikin folours

Sannan ya yunkura ya mike yana kwafa lokacin da ya ɗauka idanun shi kan daimond watch ɗin sa dake ɗaure a tsintsiyar hannun shi ɓacin ranshi na ƙara linkuwa yana tsanan ta, ba komai yaja hakan bah sai tuna wa da yai yana da march dai dai wannan lokacin yanzu haka mah ita akeyi wannan figaggiyar yarinyar da ya bata matsayin robot ta tarwatsewa mashi lissafi yoooh ina ba robot bah baya tunanin a duniyar nan an haifi wani mutun mai karfin halin da zai challenging ɗinshi da kalamai masu zafi irin haka ba (hhhhh 🤣 🤣🤣 ashe 🤖) kuma ya kasa mayar da martani one Day one time zai aika mata da virus da xai chakalkala system ɗin gaba daya ta yadda zata ji gwara mutuwa da rayuwa.

(Ashe akwai kallo gaba lallai wannan ba ƙaramin takun saƙa bane masu karatu kudai muje zuwa har yanzu ba'ai komai bah )

Ta tarwatsewa mashi lissafi duk wani shiri nashi ta hautsina mashi shi watau ita gamai kishin.mata zatai masu bayani dalla dalla ne yai kwafa yana haurawa sama ba wanda ya kula cikin yaran shi tunda ya fara tafiya .

Kai tsaye tsaftataccen bedroom ɗin shi ya nufa da aka wadata da jigunan furnitures masu masifar kyau da tsada wani kallar yatsine fuska yai yana kallon ɗakin a kaikaice idanun shi na lullumshewa mayataccen barci na ɗibar shi gefen bed ya zauna ya mika hannun yana ɗaukar wayar data addabi kunnuwan shi dake saman side drower sai ringing take ba ƙaƙƙautawa wayar ya tsura ma kyawawan idanin shi kamar za ta iya hasko mashi fuskar mai kiran har sai da ta gaji ta yanke dan kan ta sannan yai tilli da ita tsakiyar gado shimfiɗaɗɗan gdon ya tsura mah ido kamar ana bashi umar ni daya wadatu da tausasan blanket da bedsheet irin wanda idan ka hau koda baka ji barci sai yazo  a hankali ya zame ya kwanta ruf da ciki ya fara lissafa duminiyar shi..

MIRAN 🌺🌺🌺

cak ta tsaya daga tafiyar da ta soma da baya baya ta cigaba da tafiya tana komawa upstairs idanun ta na tara kwalla da suka nuna bakin rai take da sauri ta shige bayan labule saboda kusan cin karo fa sukai da samha dake fitowa daga ɗakin maah ta sa hannayen ta duka biyun ta rufe bakin ta alamar dai bata so kowa ya fahimci hali da take ciki kuma bata son sautin kukan ya fita ,

Ba komai yasata shiga wannan halin bah sai maganar da taji paah nayi bayan ya Aiman ya gama kora mashi bayani haɗa auren ta dana ya Aryan da yanzu saura 1month.

Tun ɗazu ta gama shirin ta bata fita bah ta hau kan system tana rage aiki koda Paah ya dawo salla take shiyasa bata samu damar tarar shi bah, Paah da tun ɗazu ya dawo da farin ciki ta safko zata tare shi wannan tattaunarwa ta katse mata nishadi.

Bata san da wace kalmar zatai masu bayani ba su fahimci cewa bata shirya mah aure ba a wannan stage ɗin da take ciki aure bazai yiyu bah ita kadai tasan halin da take ciki yanzu, ta rasa da wa zatai sharing wanna secret da ƙarfi ta rufe idanun jin cikin ta na mata sukuwa ya hautsina mata lokaci guda yanayin fuskar ta ya canza tana cije lower lips ɗin ta tun ɗazu take tsumayin hakan duk farkon wata tana Fuskantar matsanancin ciwon ciki (bakon wata) hasken wayar ta takunna yau 3 ga wata suke da sauri ta toshe bakin ta saboda kukan dake neman fin ƙarfin ta kukan tausayin kan ta babu wanda zata iya ma bayani ya fahimce ta kai tsaye a slow ta fara yunƙurin miƙewa ganin kiran da momy ke jero mata ba ƙaƙƙautawa ya aryan da junaid (shima yayan ta ne ) sai da tai na mijin ƙoƙari wajen saisaita yanayin ta duk da yadda marar ta ke ƙugi haka ta daure ta shanye komai ta daidaita zaman doguwar rigar ta pitch color mai faɗi da suka zaman mata sutura ta buɗe mata sosai ta yadda duk maimaitar mai kollo bazai iya ganin surar jikin ta bah.

Cikin natsuwa ta safko down stairs tana sakin murmushin kamar ba ita bace ta gama gabzar kuka ba kaf familyn ta ta iske bisa daining table kowa da kalar abincin da ke gabanshi

Ya Aiman ne babban sai ya Aryan dake bi mashi sannan twins ɗin su kyawawa humaid da junaid (yaran momy ne ) sai ita auta yadda suke gudanar da rayuwar gidan su abin zabbirgewa ba'a cewa komai sai san barka Basu da wata matsalar relationship family ne masu masu matuƙar shaƙuwa da tsananin nuna ma juna tattali da kulawa .

Ba wanda ta kula direct wurin kyakkyawan mutum dake hakimce a mazaunin sa ta nufa wanda daka gani baka buƙatar ƙarin bayani zaka fahimci mahaifin ta ne ko ba'a faɗa ba a bayyane zaaka ka ga kama ta jini murmushi ne kwance a fuskar shi ammh daga yanayin Yadda yake fita zaaka gane ba mutum bane mai yawan fara'a wannan mah ganin ɗiyarshi ɗaya tilo da Allah ya ba shi kuma mafi soyuwa a wurin shi ya sa yasa ya fita ba tare da shiri bah ya buɗe Mata hannaye ta faɗa jikinsa ya rungume ta ( a tsarin gidan su wannan is nirmal en boko bah) .

Maah ce kwai bata tolerating wannan ɗabi'ar ita ke tsawatar masu wani lokacin, ammh da yake anfi ƙarfin ta yasa take kauda kai wani lokacin, yanzu mah abinda ya faru kenan baki ta tsuke tana kauda kai yayinda sauran ke kallon su cikin shauƙi.

"Paah i miss You sooooo much "same too you daughter yai maganar yana raba jikin su tare da ja mata kujerar dake kusa dashi ta zauna wadda ya hana mommy zama yace yana son yaji gumin diyar sa good afternoon Paah tace tana yunƙurin zama afternoon dear ya gida da Wurin aiki "Alhamdulillah Paah .

Humaid ne y maka mata harara irin ta wasa yai kwafa  yana tattara hankalin shi wurin paah bata dae  kula shi bah bawai don bata ganshi bane ba tada dai lokacin sa yace " paah ai dole take cewa Alhmdllh tunda ta mayar da martani hankalin ta ya kwanta wallahi Paah wannan yarinyar ita zata sa wata rana a birne mu da ranmu "mi kuma tai Paah yayi tambayar lokacin da yake ƙoƙarin wanke hannu zai fara cin abinci "Paah kana nufin duk abinda ke faruwa a social media baka gani bah cewar junaid yana zare eyepiece dake sagale a kunnen shi baki miran ta murguɗa masu cikin halin ko in kula tace "magana kuke akan guru " wallahi ita Sam ta manta da rayuwar shi sai yanzu da suka tado da zancen sa maganar paah ta katse mata tunani "wai kuna magana akan ɗan wurin ƊANDIJAS ohoo ni Paah ban sanshi bah kawai doka ce tabi ta kan shi"Gaskiya ne ƙanwar tawa akwai tsauri ido watau haja ta cigaba harda manyan mutane kike taɓowa irin su CHAMPION so kike ai withdraw ɗin mu daga team "wai da shine champion da sunan shi ya gama gundura ta abakin ka kace shine uban gidan ka i pity your life junaid "yi Mai isar ki da da ɗaurin gindin momy da Paah kike baza capacity son ranki murmushi momy tai dake dannar waya tun zaman miran tana sauraron chapter su sama sama tace karku saka ni ciki, ajin ta ne da yakai shiyasa take bazashi yadda ta so kuma a zauna lafiya "yawwa momy na takai na fada masu dai kawai don suna supporting ɗinshi shine zasu ringa kare shi dokar ƙasa ya taka shiyasa na shiga gonar sa "Ammh miran ki bi a sannu karki cika zakewa rayuwar ta yanzu baki san mi ƙaddara zatai ba a matsayin ki na mace mai ƙananun shekaru wannan aikin haɗari ne a rayuwar ki sai dai ya na da kyau ina son aikin ammh ina tsoron haɗarin shi maah ce mai wannan maganar cikin rauni da sauri ya Aryan ya ɗauki zancen da cewa wannan shine bayani maah wannan aiki ne mai kyau musamman aka gina shi akn ingantacciyar hanya yana da kyau ga mata like you lil sis ammh zai zama haɗari in kina taɓo manya  ƙasa irin haka ni shawarar da zan baki kiyi Aure ki samu garkuwa mukan mu hankalin mu sai yafi kwanciya kema kanki ki zaki ƙara kwarjini .

Ai nan take yanayin fuskar ta chanza cikin ta yai Wani kalar katsawa tana kallon ya Aryan dake maganar da iya gaskiyar shi ta juya ta kalli humaid,junaid da maah da maganar ya Aryan ta gamsar dasu sannan ta kalli Paah da en muskilancin ke kusa yayi shiru yana sauraron su murmushin yayi irin nasu na manya ya kalli MIRAN da ke jira jin mizai ce ganin bazaiyi magana bah yasa ta kalli momy da ita kadai take sa ran zata kare ta saidai hankalin baya kan su waya take mayi da bahijja (matar ya Aiman) sannan finally ta dire idanun ta kan ya Aiman da tun zaman su baice komai ba kanshi na ƙasa yana wasa da abincin da ke gabanshi ko one spoon bai mashi ba yayi  nisa cikin tunanin da ya tafi sannan ta ƙara kallon paah da still murmushi ne kwance a fuskar shi zatai magana yai gyaran muryar da duk ta jawo hankali su suka kalle shi banda ya Aiman da zuciyar shi ta daɗe da barin gangar jikin shi, sai da ya kira suna sa kusa sau uku da babbar murya sannan ya ɗago rinannun idanun shi da damuwa ta bayyana ƙarara a cikin su yace "yess Paah"Are u oh right "yess fah lafiya ta kalau ba abinda ke damu na" kallon nazari Paah yai mashi irin na karya kake min ammh a zahiri baice komai bah sai momy ce da yanzu ta gama waya  tace "haba Aiman duk wanda ya sanka ai yasan ba lafiya bah kana cikin damuwa murmushin dake ƙara mashi kyau yayi 34 teeth ɗin suka bayyana a jere farare kal yace "ba komai momy matsalar wurin aiki ce"toh Allah ya kyauta ya tsare ammh bai kamata abin ya dame ka ba koh matsalar babba ce kai ya gilgiza mata alamar a'a cikin damuwa en uwan suka ci-gaba da jero mashi addu'a samun sauƙi a wurin Allah yana amsawa da kulawa, da girmamawa momy ta kalli Paah dake kallon yaran shi one by one cike da alfahari da tsantsar kauna tace "baban yara idanunsa ya juyo kanta ba tare da yayi magana bah "munyi waya da hajja ɗazu da safe tace tana hanya cikin satin nan tana so ai komai na bikin angon nata tana nan (Aryan) kowa sai da ya kalli momy cikin yanayin damuwa har paah rashin jin dadin maganar ya bayyana akan fuskar shi bare mah MIRAN daa tuni fuskar ta ta ƙara chanza wa lokaci guda cikin taɓe baki da ɓacin rai humaid da junaid suka mike junaid na cewa uhmmmm jakadiyyar tsiwa zata bayyana kenan kowa yai takan sa " kul junaid kar in kuma ji mahaifiyar tawa cewar Paah cikin haɗe fuska "sorry Paah suka haɗe baki wurin bashi hakuri sannan suka fice a hankali miran taja kujerar da take kai baya ta yunkura zata tashi ya Aryan ya dakatar da ita ta hanyar cewa "miran kunyi magana da samha gobe zaku shopping ehh yaya ammh nace mata mu ɗaga fitar zuwa jibi don gobe zamu je workshop "ok hakan ma normal sai kuma ya kalli iyayen shi ni fita zanyi kumin addu'a a tare suka haɗe bakin wajen nema mashi tsari daa dukkan sharri sannan yabar wurin ya rage daga Paah maah mommy sai ya Aiman don miran bayan ya Aryan ta bi.

HAMDA 🌺🌺 🌺

Kuma dai wannan yarinyar da alama super star take son zama ta criminals kullum cikin laifi take wallahi na gaji da case ɗin ta ASp ke wannan maganar yayin da ɗawisu ke gefen shi sai gaba inspector kalid ne da nashwan murmushi ɗawisu kawai yayi da

13 / 64