Chapter 29 Reading CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx Arewa Novels

CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx

Author :  F&F Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   29 / 64

84K to 87K   out of 190.4K words

ya kalle ni bah ya bani amsa " scull nake son shiga gobe an fara saida form so ina haɗa cridecials ɗina ne "school kuma wace? "EVERTEX UNIVERSITY gobe ne date line mun riga da mun gama magana Arɗo tare da aqqab zamu je". Duk wannan amsar yana bani ita yayin da kan shi ke ƙasa yana yana harkokin gaban shi kafin na samu damar bashi amsa inna ta shigo da sallama ita jin shiru yayi yawa yasa ta biyo sawu.

    Murmushi tai tana kallon Apip "daɗi na dakai zalƙi Apip duk zumuɗin zuwa makarantar ne ya mantar dakai cikin ka ince dai sai gobe  "ai inna da zafi zafi ake dukan ƙarfe goben sammako zanyi shiyasa  "toh Allah yasa albarka, sai kuma ta kalle ni " hamda ga jajjage cen na fara ki ida ki haɗa min miyar in ba zama nai bah Apip ba abincin nan zai ci bah  "A ɗan gatan inna abincin mah sai an lallaɓa ka ai ni wallahi inna da kin ƙyale shi yunwa bake bace da zata tausaya mashi  idan taci sa da kanshi zai nema" cike da tsokana nai wannan maganar sai dai shi ko kallo ban ishe shi bah da alama bama jin mu yake bah hankalin shi ya ɗauku sosai, gaskiya sha'anin makarantar nan ba ƙara min mahimmanci ya bashi bah da gaske yana son kowa karatu. Inna ce ta mayar min da mar tani tana kare ɗan ta ni dai fita nai na cigaba da aikin da ta saka ni fira suka sha sosai irin ta uwa da ɗa ina jin dariyar su nima kewar tawa uwar ta dawo min sabuwa ina sonta duk da ban taɓa ganin ta bah ammh ba yadda na iya wanda yafi mu san ta ya amshi abun shi ganin tunanin zai haifar min da damuwa yasa na tunƙuɗe shi da ƙarfin tsiya  cikin ƙanƙanin lokaci na gama miyar daman komai a haɗe yake kuma tayi ɗan karen daɗi 🥰  wuraren ɗaya na kammala komai.

   Jiya kwana akai ana mana ruwa har yau da safe shiyasa garin muka tashi da sanyi sosai don ko kaɗan bamu ga giccin rana bah kuma ta kama juma'a shiyasa nai tunanin ɗaura ma APIP ruwan zafin wanka lokacin masallaci ya kusa kuma nasan dole ya buƙaci ruwa.

    Ban daɗe da ɗaurawa bah sai gashi ya fito da shirin wanka yana neman bokiti lokacin ina ɗaki motsin shi yasa na leƙo ta window "Apip ka ƙara ma ruwan nan lokaci su zafi sai kai amfani dasu" kallo na kawai yai ya cigaba da abinda yasa kan shi sai da ya mula yasha iska sannan yace "  sai kace wani mai jego wanka da ruwan zafi wannan sai ku kinga dai dai mu na "kana nufin dasu zakai wankan  cikin zaro idanu nai maganar "sosai mah" kallon shi na ƙara yi da ruwan da yake ina jinjina kai da wauta irin ta Apip "bawai ruwan da aka killace suka ɗumama bah a'a ruwan sama da aka tara jiya su yake hari marabar su da ƙanƙara dutse ai ban ma ƙara bi takan shi bah na cigaba da harkokin gaba na ina zama waya ta na ƙara alamar shigowar message ban wani ja aji bah na duba message ne daga unknown sender kamar haka

" WHAT EVER THE MIND OF MAN CAN CONVINCE AND BELIEVE CAN ACHIEVE, ASK AND IT WILL BE GIVEN TO U SEARCH AND WILL FOUND, KNOCK THE WILL BE OPEN TO U. DO OR DON'T THEIRS NO TRY IN LYF"

Abinda message ɗin ka ƙusa kenan shiru nai ina jin tasirin kalaman har cikin zuciya ta ina sabunta ƙwarin gwiwa ta ko waye wannan dayai min ɗaurin goro ba ƙaramar gudunmawa yake bayarwa a cikin rayuwa ta bah duk da wani lokacin abin na bani tsoro.  Apip ya katse min tunanin da ya leƙo shai dami. Zai tafi mashallh Tsarki ya tabbata ga wanda yai wannan halittar na faɗa kasan raina  haƙiƙa yayi kyau over ya tafi da imani na

duk da bawasu kaya yasa bah nazo agani shadda ce mai ruwan madara Ammh ta amshi fatar shi "kallon fah" ya faɗa cikin ɗage min gira murmushi nai ina mai alamar nice da hannu 👌👌 ban barshi ya tafi bah saida muka sha photon da ban san adadin su bah fitowar Arɗo ya katse mana nishaɗi ya tisa ƙeyar shi gaba suka tafi.

  Bayan tafiyar tasu ne inna ke tambaya ta ruwan nan fah mi zaki yi dasu "APIP na ɗaura mawa ya gwalishe ni wai da waɗannan ruwan yai wanka masu ɗan karen sanyi na faɗa da ƙara kanbama lamarin  "hmm hamda indai Apip ne kin san shi bansan tsakanin shi da ruwa bah sai kace jikan masinci mu muyi amfani dasu ki fara kafin na gama raba abinci  "toh inna Adda wai kwana zatai (taje garin su biki). "Ehh mana kusan sati zatayi kin san in an haɗu da dangi mutum baya son barin su "toh Allah ya maido ta lafiya daba barcin saukar mu ai da na bita  "wallahi kau sai a tari gaba.

    Sosai yau tamin daɗi abinda muka daɗe bamu yi bah yau ya faru zama baki ɗayan mu muci abinci cikin raha da nishaɗi kamar bamu da wata damuwa dake addabar mu  Apip ya gamsar damu da barkwancin sa rabon da inga Arɗo ya sake haka gaskiya an jima ada duk friday haka muke yanzu ba mutum 2 Adda da ya AJMAL.

Ya salam haƙiƙa munyi rashi ya AJMAL duniya ne kar kuyi tunanin don yana yaya na na cika zuzuta shi haka mutum ne mai cikar kamala da nagarta son Kowa kin wanda ya rasa duk wanda ya zauna da ya AJMAL sai ya shiga ran shi koda na yini ɗaya ne duk da mutanen rugar mu ba su sanmu ammh mutuwar sa ta gigita su baƙin hali ya hana su bayyana wa balle Ni dana ɗauke bango abin jinginawa idanu mai sanyaya ruhi da gangar jiki na ya bani kulawar uwa ya bani ta uba ya bani ta yaya ya bani ta ƙani Allah ya jiƙan ka ya AJMAL ya kyautata masaukin ka Inshallah nima ina nan tafe mu haɗe a aljanna murmushi nasa ya baye gurbin raunina muka cigaba da fira kamar ba gobe.

Wannan yinin ranar haka nayi shi kamar kar da ranar ta wuce kuɗin da Excellency ya bani ina son bama Apip su contribution na makarantar shi ammh ban san ta ina zan fara mashi bayani bah wani lokacin yana da matsala kamar alƙali yake wajen bincike da bin diddiƙi ammh nasan yadda zan bi dashi na gama shawara da zuciya ta na hau kuma na zauna.

Washe gari haka muka tashi cikin kwanciyar hankali Apip uban zalƙi tunda suka dawo asuba bai koma bah shiri ya hau yi zuwa 7 ya kammala komai cikin shigar shi data fi ta jiya haɗuwa ya wanku iya wuya irin sune ke sa kyau yayi kyau ko bashi da kyau shigace ta kamala manyan kayan hausawa yadi blue ammh sun amshi fatar jikin shi kan shi kamar kullum da damshi a kuma buɗe ban taɓa ganin shi da hula bah duk sanyi baya rufe ta yama ɗan fi amfani da p cap itama bata jimawa yake cire ta. Break fast sai da inna ta tusa shi gaba yayi shima kaɗan yayi shi iyayen shi na suɓurɓuɗa mai addu'ar samun nasara da dacewa ya tafi ni kuma nai mashi rakiya saida muka biya gidan su Aqqab shima ya shirya a hanya Aqqab ke bamu labarin rikicin tsakanin jauro da fawwaz yana son amshe mashi sarauta saboda yanzu baida magaji rikici ne sosai ke aukuwa tsakanin su ita kau inna ramma taje garin su sake sabon shiri ko nace neman ganin haukan daya tiso ta gaba ga bikin ɗiyar ta ta ɓalangantar da kuɗin wajen waleemar mutuwa ta (hhhhhh 😏😏 gwanin ban tausayi) yanzu kiciniyar neman kuɗin suke gashi tun farko sun sa mah rayuwar su ƙarya su ala dole sai sun kankaro girma wajen sirikan su wannan gwagwarmayar da suke ita ta ɗauke hankalin su akai ne suka shafa min lafiya Allah ya kyauta kawai nace bani da abin cewa bayan hakan Apip kam yi yai kamar baya wurin bai ƙaunar mutanen nan har cikin zuciyar shi kuma yaba abu baya ya barshi kenan ko waiwaya baya yi saida na raka su har mashigar garin mu nai masu fatan Alkhairi sannan na jiyo na kama hanyar gida a hanya naci karo da fawwaz da mulook da alama gona zasu fawwaz ya watso min kallo mai cike da tsana da ƙasƙanci mulook kam ɗauke kai yayi yana hura hanci ni dariya mah suke bani saida nakuma murmusa ran fawwaz ba ƙaramin soyuwa yai bah watau na maida shi mahaukaci kenan ban damu da tsanar da yake min bah ni dai gida na wuce ban san yadda suka ƙare bah .

Nai gida nai en aikace aikace da inna bata ida bah har barci nai kafin girkin rana lokacin islamiyya yai muka tafi da juhud kamar yadda muka saba.

Kasancewar lokacin waleema ya matso yasa duka an gama mana karatu sai shirye shiryen da ake tayi bah kama hannun yaro sosai malamai da ɗalibai ake ta hidima zuwa wannan lokacin sauara shafi 3 na datse Abu muslim na taimaka min sosai yana min gyaran hadda daga yau kuma mun gama karatu sai waɗanda aka zaɓa zasuyi program suna riga zuwa bita ajin mu ni kaɗaice ban ciki Abu muslim ba yadda bai bah a sani ammh malan zayyan (for master mu) yace ba yadda za'ai a fidda wani a sani ya bani haƙuri sosai na nuna mashi rashin damuwa ta akan hakan duk da abun da ciwo ammh na basar.

Malamai bata mu suke bah hidima tasha gaban su ana gab da tashi saiga abu muslin ya shigo wai shi zai rufe mana taro da addu'a kuma zai man karatun da baza mu taɓa mancewa da shi bah ya koyi shi nasiha akan rayuwa ya bamu shawarwari daga karshe ya rufe da addu'a samun nasarar mu a rayuwa saida yaga ma komai sannan ya buɗe kofar tamabaya kowa nayi akan abinda ke mashi ƙaiƙayi ya shige mashi duhu tamabayar da Aseey bazariye tai itace ta ƙarshen amsawa tayi tamabayar kamar haka "malam don Allah ƙarin bayani zakai min akan SHIRKA lokacin da kai karatun nayi fashi. Jim kaɗan malam yayi kafin yace

_-_ wannan maudu'ine mai girma da faɗi Aseey ba zai yiyu in fasa maki shi yanzu bah amm zan maki a taƙaice saboda ƙarancin lokaci " ita dai shirka kishiyar Tauhidi ce, TAUHIDI shine tsantsar kaɗaita Allah da bautar sa duk abinda yaci karo da wannan sunan sa shirka SHIRKA itace haɗa Allah da wani ko bautar wanin Allah. Ina son ku riƙe wannan idan kasan Allah ya halicce kane don ka bauta masa toh ku sani bauta bata amsa sunan ta bauta sai tare da tauhidi kamar yadda salla baza'a kira ta da Sallah sai tare da alwala, idan shirka ta shigo cikin bauta ta ɓaci kamar yadda in najasa ta shigo cikin tsarki take ɓata shi.

Shirka nada nau'o'i da dama, duniyar mu a yau wannan zamanin da muke ciki in mukai duba akan ayyukan junan mu zamu ga cewa kamar kowa mah ɗan wuta ne musamman ga masu ilimin shirka saboda haɗarin ta yawa ne dashi zaka tabbata cikin tsinuwa da fushin Allah ka taɓe a duniya a lahira ka dawwa ɗan wuta. Yana da kyau musan wanda muke bauta abinda yake so da wanda ya hana neman wannan ilimin farilla ce ta ainahi yana daga cikin ire-iren na shika SHIRKUL AKBAR (shirka babba) dalilin ta faɗa Allah maɗaukakin sarki.

(Lallai Allah baya gafartawa idan akai shirka dashi da wani abu ammh yana gafarta wanin hakan ga wanda yaso duk wanda ke shirka ga Allah haƙiƙa ya ƙirƙiri wani zunubi mai girma ). {Suratul nisa'i : 48

A ƙalƙashin wannan nau'i na shirka akwai shirka a cikin addu'a shirka a cikin niyar mu akwai shirka a cikin biyayya akwai shirka a cikin so. Sannan nau'i na 2 SHIRKUL ASGAR (Shirka ƙarama) ta ƙunshi riya ( yi aiki don mutane su gani su yaba ba don Allah bah) sai rantsuwa da wanin Allah sanan Alfahari (ganin fifiko akan wanin mu)

Allah maɗaukakin sarki nace (Duk wanda yake fatan haɗuwa da Ubangijin sa toh ya aikata aiki na ƙwarai kuma kar ya haɗa Ubangijin sa da kowa a cikin bautar sa ) { suratul kafh : 110}

Kuma dukan su malan yayi ƙaƙarin kawo dalilin su a cikin Alqur'ani mai girma ba zan samu damar maku bayanin su duka bah zan zan ɗauki biyu in fasa maku su shirka a cikin biyayya da shirka a cikin kira saboda ƙarancin lokaci.

A yanzu muna cikin wata al'umma da shiraka ta ɓoyu a cikin mu take cigaba da yaɗuwa kamar yadda wani malami mai fikira yace "shirka ta fi ɓoyuwa akan sawun baƙar turwa akan wani bakin dushe mai faɗi a cikin duhun dare"

Ku auna min taya zaku iya ganin sawun baƙar turwa a kan bakin dutse a kuma cikin duhun dare bari na tabbatar maku da hakan misali shirka ta biyayya sau da yawa mutane suna wuce gona da iri a wannan ɓangaren a ɗabi'ance addinin mu ya wajabta ma yima na gaba da mu biyyaya ammh yadda za'ayi biyayyar shine matsala muna wuce iyakokin Allah misali mu ɗauki gaisuwa wasu mutanen suna ganin duƙawa har ƙasa wurin gaishe su shine asalin biyayya ammh wannan kuskure ne "ku tambaye ni dalili" Abu muslim ya faɗa yana kallon mu "toh miyasa malan " saboda gaɓan sujjada madamar zasu taɓa ƙasa da zummar yi ma wani biyayya shirka ta shigo idan babu makawa sai an duƙan ki zauna in a zaune yake ko ki runsuna duk an samu saɓanin makamai runsunar ma shirka ce saboda kai ya motsa duk abinda aka ce na Allah ne ba'a haɗa shi da komai shi kadai ake mashi dalilin da zai ƙarfafa Magana ta faɗar Allah madaukakin sarki

(Dukan nin gurabun sujjada ko dukkan nin masallatai na Allah kada ku kira wani tare dashi )

{Suratul jinn : 18}

Gurabin sujjada guda 8 ne wasu malaman suce 7 goshi da hanci suna ɗaukar su ɗaya wasu daban daban sai tafukan hannaye 2 gwiwoyin ƙafa 2 sai saman babban ɗan ɗan yatsa na ƙafa 2 bai halitatta bah ɗaya daga cikin yakai ƙasa bah a wurin yima abokin halitta biyayya ko waye.

Sannan akwai wani kuskure da mutane keyi basu san kuskure bane shine shirka a wurin lafuzzan su da yau da kullum kunga halshe halshe halshe ku kiyaye shi shine abu maifu sauƙin halakar da dan adam kusan faɗa waɗanda kalaman shirja ce

"DA TAIMAKON ALLAH DA TAIMAKON WANE" ko

"DA YARDAR ALLAH DA YARDAR WANE" ko

"HAKA ALLAH YASO KUMA WANE YASO" D.S

Duk Mutumin da ya faɗi hakan yayi shirka ga Allah ya nuna cewa da Allah da wanen nan sukai gamayya suka biya mashi buƙata wannan kuskure ne a kiyaye. Annabi (SAW) ya faɗa mana kaffarar wannan shirka ita ce kamar haka

(Allahumma inni auzubika an ushrika bika shai an wa ana a'alamu a Astagafiruka minaz zambil lazi la a'alamu)

Da ƙarshe abinda nake son jan hankalin mu akai. Shi shine duk wanda ya mutu yana shirka Allah ya haramta mai aljanna zai dawwa ma wuta kalidina fiha ba ranar fita. Allah yasa mu dace _-_

Shigowar malan zayyan ya katse mana shi nasan ba don ya gama ba wai suna da meeting daman lokacin tashi yayi dole yai mana addu'a muka kama haryar gida . Gaskiya mun ilman tu sosai da ƙaramar lecture malan kamar karb ya bari ammh lokaci yayi halin sa an dade da tashi makarantar tsit . Mun baro makaran ta muna ta yabon Abu muslim da zunduma masa albarka sundi sundi da mashi fatan Alkhairi samun mata ta gari kamar shi. En groud ɗin mu namin tsiya wai ko dani zaiyi wuf mun dace kuma sun ga yana ji da ni su k bai harda rantsuwar ta sona yake ba wadda na ƙara kulawa cikin su saboda ni tausayi suka bani wallahi har muka rabu dasu magana ɗaya ake sai da na biya gidan su judud na amso mah Apip p cap ɗin shi da har yau bai ƙara tanka min bah akan ta yayi zuciya kenan yayi fushi da abu ya gama dashi ko minene har abada bazai ƙara bi takan shi bah daman da 2 nayi so nake ya bar min ita ammh ta ƙiya shiyasa nai mashi haka na tadda fawwaz gidan sai surfa masifa yake koshi dawa ohoo "ƙurun banza sai masifar tsiya" juhud tace tana taɓe baki ni dai bance komai bah ban mah bi takan ta bah na shiga yin abinda ya

kawoni nai gaba gida na wuce direct.

MIRAN 🌺🌺🌺.

Washe gari iyayen hammad...........................

[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: ,CINNAKA 🐜🐜🐜

                BAI SAN NA

                            GIDAH BAH

                                         SAI YA CIZAH

STORY

   

   &

WRITTEN BY

     

F&F

(PERFECT PAIRS 🌺)

   

  35.............

  

       Washe gari iyayen hammad sun zo sun tattauna da Paah an tsaida rana kamar yadda suka saka sati biyu murna a wurin hajja ba'a magana sai ta ƙara ƙaimi wajen haɗa gagarumin biki tana son tayi bikin dazai kafa tarihi a family

29 / 64